QANIN MIJI 4
Ba ta samu
bakin amsa masa ba, ita dai abinda ta tsaya akai shine kuka da shessheqa
Tsawon
mintuna ya tsaya shiru yana kallonta yayin da kukan
yake tafasa masa heart, ba
tare da ya tantance abinda ya dace yayi ba a wannan lokacin ya ja wata doguwar
tsaki ya mai da idanunsa kan hafeez yace
"mu je
dan Allah, bana son matsala wallahi, ban san waye zai iya fahimtata ba idan
fareedah ba ta fahimceni ba"
Hafeez da
yake tsaye qiqam kamar namijin soja, tsayuwarsu ya gyara ya ɗan kalli fareedah
sannan ya dawo da kallonsa kan yayansa ya motsa bakinsa tare da yin gyaran
murya kaɗan yace
"ni
kuma a ganina yaya bai dace ku rabu a haka ba, kamata yayi ka lallaɓata, ka rarrasheta,
four to five months abin....., is not easy fa, gaskiya da nine da ba haka zan
yi ba, in ma na iya tafiyar kenan, pls yay......"
A harzuqe
fa'eez yace
"rarrashi
na nawa zan mata, ko kuma kawai dan ban da aikin yi sai in tsaya ina ta
maimaita magana ɗaya?, ka kiyayeni fa, kai ka jira kayi auren mu ga irin
tunaninka, shashanci kawai"
Murmushi mai
kama da dariya yayi tare da zare glass ɗin idanunsa ya sanya idanunsa cikin na
fa'eez yace cikin tsokana da wasa irin na tsakanin yaya da qani
"ai ni
da ka barni na yi aure, da a gurina zaka koyi salo da iya zamantakewar rayuwar
aure, ni fa ka ga mr boss ɗin nan, haka zan mai da mata wallahi, balle matar ma
irin fareedah, ah... ina!, ai four legs as two,
ko za a ɗan gwadane yaya"?
Ya qarashe
maganar da sake yin dariyar shaqiyanci
"um, da
yake kai mahaukacine ba, an faɗa maka ko ina ake iya zuwa da mace, dallah ni
kauce min a hanya in wuce, tunda kai ka iya rarrashi sai ka rarrasheta ai,
kauce dallah, da ma hakurin ka bata da shegen surutun da ka tsaya yi min"
Ja da baya
hafeez yayi yana dariyar halin yayan nasa, ganin ya zaburo kamar zai make shi
Har ya ɗaga
labule zai fice sai kuma ya juyo kaɗan yace
"sai
mun yi waya fareedah, sai na dawo, dan Allah ki daina kukan nan, na tafi"
Yana gama faɗin
haka ya sa kai abinsa
Ita kuwa
hamshaqiyar ta fa'eez tana ganin ficewarsa ta sake fashewa da wani kukan ta
juya za ta koma cikin gidan, Allah ne kaɗai ya san damuwarta kan tafiyar mijin
nata, ita kanta ba za ta iya misalta haukacewar da zuciyarta tayi kan tunanin
rashin ganin kyakkyawar fuskar fa'eez ɗinta da murmushinsa ba har na tsawon
watanni,
Ji tayi an
riqo hanunta ba tare da tayi aune ba, hakan yasa tayi gaggawar juyowa ta kalli wanda ya riqe mata hanun, kasancewar
yanzu ta saba da yawan taɓa jikinta da yake yi ya sanya ba ta wani damu ba, sai
ma cigaba da kukanta da tayi a gabansa danta san a irin wannan lokacin shi ne
kaɗai mutumin da yake iya fuskantar matsalarta ya kuma rarrasheta da daɗaɗan
kalamansa masu tafiyar mata da damuwa
Seconds biyar
ya ɗauka yana bin fuskarta da kallo sannan ya fara magana cikin tausassar
muryarsa wanda ya saba rarrashinta da ita
"fareedah,
ban san me yasa kika ɗauki kuka a matsayin magani ga kowacce matsalarki ba, na
sha faɗa miki kuka bashi da muhimmancin da kika bashi, fareedah pls, kiyi
hakuri, ina qara baki hakuri akan wanda yayana ya baki, ki daure, ki cije, nan
da wata uku ne fa ko huɗu ko biyar?, za su zo kuma za su wuce, ke ina mai
tabbatar miki ma, matuqar zai dinga tuna wannan kyakkyawar fuskarkin ba zai iya
yin wata ukun ba balle huɗu ko biyar, musamman idan zai dinga tuno wannan
kyakkyawan murmushin naki mai abubuwan mamaki, ga beauty point ga jerarrun
fararen haqora, Allah ina mai tabbatar miki matuqar zai cika ukun ma to a
daddafe ne, da ni 'yasu da shiga uku ina faɗa miki" ya qarashe yana mai ɗan
zare idanunsa irin na barkwancin nan tare da murmushi
Tsagaitawa
tayi da kukan ta ɗan murmusa, hakan yasa shi ɗaura yatsarsa kan fuskarta yana
share mata hawayen yana faɗin
"yawwa ko kefa, toh yanzu kin san abinda nake so da ke?, ki je ki cire
wannan damuwar daga ranki ki kwanta kiyi baccinki, amma fa sai in kina son in
dinga zama a gida ina tayaki hira, dan ni ba zan zauna ki isheni da kuka da
kiran fa'eezu ba"
Ya qarashe
da dariya, ita ma ɗan dariyar tayi ta ture hanunshi tare da masa hararan wasa
ta juya ta fara tafiya cikin gidan abinta tana sauke ajiyar zuciya, ba laifi ta
ɗan ji qarfin gwiwa kan lamarin tafiyar nurul-ma'eesh ɗin nata
Cikin
tsokana hafeez ya ɗaga murya yace
"mai
kukan tafiyar miji, sai ta yayah fa'eez mai daɗin girki"
Ba ta juyo
ba sai dai ya juyo sautin dariyarta, hakan ya sanyashi mai da glass ɗinsa ya
juya ya fice daga gidan yana murmushi mai sauti
**
Yana buɗe
qofar motar faeez ya hau faɗa
"kun je
kun tsaya shegen surutu ko?, ku da ba kwa gajiya da magana, kuma ba wai zan
tafi ka ɗauka na barka sasakai bane, ko da wasa na samu labarin yawon banza
ranka zai yi mummunan ɓaci, musamman yawon dare, balle ka je ka yaudaro 'yar
mutane, domin aure ba yanzu ba sai ka kammala wannan degree ɗin, lokacin ka haɗa
degree biyu ka san meye duniya ka san ina za ka nufa, ba wai kayi aure cikin
hayaniya ba, ko da wasa na ji labari zan sassaɓa maka, dan nima kafin alhaji ya
min aure sai da na haɗa masters ma, kuma ban taɓa kula kowacce yarinya ba sai
fareedah, dan haka kai ma hanyar da na bi ita za ka bi, kai kan ma na sauqaqa
maka, tunda yanzu alhajin baya raye, ba sai ka kama aiki ba, kana kammalawa zan
maka aure da wurwuri tunda na lura kai namamajone"
Sun fice
daga gate ɗin gidan kenan faeez ya dire maganarsa, hafeez kuwa yace mai zai yi
in ba dariya ba, dariya yayi sosai sannan yace
"toh
boss, hafeez ya gode, Allah ya ja kwana, kai hafeez ka zama tamkar budurwa 'yar
shekara shashida, sai tsaronka ake yi, wayyo Allahna..."
Ya qarashe
da yin magana wa kansa cikin marainiyar murya
Fa'eez da ke
zaune a baya hannunsa ya kai ya ranqwasheshi, da sauri ya riqe gurin yace
"washhh....
yaya, am so sorry"
**
Zaune ƴyake
a harabar hotel ɗin da yake a cikin babban birnin qasar da yaje domin shiga
taron haɗaka na qara wa juna sani da yayi wanda idan har komai ya tafi yadda
yake so, ɗaukakar companynsa za ta wuce na da sosai da sosai,
shaqatawarsa
yake yi abinsa cikin shigar
baqaqen kayan sanyi da hularsu
kasancewar qasar qasace mai ɗan banzan sanyi mai ratsa jiki, yau satinsa
biyu da zuwa qasar, tun satinsa ɗaya a qasar kewar fareedarsa ta fara kawo masa
farmaki saboda sababbin yanayin da ya
shiga a zuwansa qasar
Na farko
yanzu bai da yawan ayyukan da suke ɗauke masa hankali a kanta lokacin da yake
tare da ita, duk ya handling ɗinsu wa maxwell da ja'afar abokinsa, suna tashi
daga conference ɗin zai dawo hotel ɗinne ya zauna, sai 'yan ayyukan da suke
zuwar masa kan hanya ta cikin laptop ɗinsa, nan ma ba wasu masu jan lokaci
bane, daga haka sai bacci sai sallah, wanka da cin abinci, daga nan kuma sai
zaman harabar hotel ɗin da ɗan yawace yawacen zaga gari
Abin da yafi
takurashi a qasar shine qarfin sanyin gurin da yake ɗago masa da sha'awarsa a
kai akai, duk da qwayoyin da yake amfani da su, musamman idan ya zo bacci, da
juye juye yake iya samun damar yin baccin, musamman idan ya ji muryar
fareedarsa da take narka masa lakarsa kafin ya kwanta, haka zai yi ta narke mata
a waya yana kunna mata wata wutar a can ita ma
Babban
tashin hankalinsa farmakin da ya fara samu daga wata sheɗaniyar baturiya, domin
tunda ta qyalla ido ta ganshi a hotel ɗin hankalinta ya tashi, ta ji duk duniya
ba ta taɓa ganin namijin da take muradinsa matuqa kamar wannan ba, hakan ya
sanyata tunkararsa tunda dai su ba su san wata aba wai kunya ba, saidai tun
daga yadda ya amsa mata gaisuwar farko ta san wannan ba irin nasu bane, amma
saboda baqar naci haka ta fara gabatar masa da kanta a matsayinta ta 'yar iska,
saidai tun bata qarasa ba ya korata ta bar gurin da wata mahaukaciyar tsawa da
kallon da suka kusa sanyata fitsari a jikinta, shima ko minti ɗaya bai qara a
gurin ba ya tashi ya shige ciki ya kulle ɗakinsa, dan ya san halin irinsu su bi
namiji ba abin kunya bane a gurinsu
Toh tun daga
nan bai sake ganin ta a hotel ɗin ba, saidai yana yawan ganin mata suna gilmawa
cikin kayan da babu maraba da tsirara dan masifa, duk da sanyin qasar amma su
ba sa ji, ko sabo da yanayinne oho
Hakan kuma
na matuqar takurasa, saidai idan ya ga hankalinsa zai tashi sai ya koma cikin ɗakinsa
yayi ta bincike a yanar gizo gizo da laptop ɗinsa, da haka yake qwatar kansa da
mutuncinsa, sannan ya ɗora da tablet dan rage wa kansa zafi
Bai yi
tsammani da zuwan mace ba saboda yayi nisa cikin rubuta saqon da yake yi wa
maxwell a waya kawai sai ji yayi an
rungumeshi ta baya da waɗansu tausasan hannaye masu matuqar sheqi da laushi
tare da saqalo kai ta gefen kunnansa aka raɗa masa "hi....."!
Wani irin
yarrrr ya ji a jikinsa
ISLAM IS MY
IDENTITY
No comments