QANIN MIJI 6
QANIN MIJI🤵🏻
6
Bai kai ga
samo nutsuwa da sassauci ba yaji ta a jikinsa, duk yadda zuciyarsa taqi abun da
qyamatasa ya gagara control ɗin gangan jikinsa, saboda mahaukatan abubuwan da
ta fara masa wanda suka saka shi rawar jiki, ba tare da ya iya tuna tsananin
baqin duhun zina ba ya sallama wa Tina kansa suka shiga duniyar zina, a ransa
yana raya cewa gwara ya sauke wa kansa nauyin da yake ji na yau kawai, daga nan
sai ya ɗauki matakan kare kai daga sake afkawa mawuyacin hali irin na yau da ya
tsinci kansa a ciki, sannan kuma ya raya cewa daga yau zai tuba ya daina
kasancewar daman bai taɓa aikata zina ba sai a yau ɗin
Tina shaiɗaniyace
kuma gogaggiyar 'yar barikice, tana cikin qungiyar matan da suke da lasisin
zina a qasarsu, qungiyarsu tayi qaurin suna cikin faɗin qasar, su zina ko
kyauta suna iya yi da mutum ba sai ya biya ba, musamman idan suka ga mutum ya
musu, toh fa duk yadda za su yi sai sun yi gurin samun damar kwanciya da shi, ko kana qi dole sai sun san
yadda suka yi suka rinjayeka ta qarfin tsiya da iya shege, a taqaice dai,
qungiyar su tina qungiyace da ta shahara gurin fyaɗe wa mazaje😂🤭, Allah ya kiyaye matasan musulmi
Ba a nan
qungiyar su tina ta tsaya ba, suna da kaifafan sunadaran da suke amfani da a
jikinsu ta yadda zai yi wuya a kusancesu sau ɗaya ba a yi marmarin kumawa ba,
saboda qarfin qwayoyin da sukesha, sun ɗau wannan matakinne tunda suka fahimci
a karan kansu basu da wata cikakkiyar ni'imar da za ta iya ribace musu zuciyoyin
mazaje kamar yadda suke buqata, toh ta hakane qungiyar ta yi qarfi domin kuwa
karuwaine na manyan qasar, ba a isa a taɓasu cikin qasar ba, duk kuma wanda
suke son gani cikin manya ba ɓata lokaci suke samun damar ganinshi, domin kowa
rawar jiki yake akan qungiyar thousands butterflies, saboda yadda suka qware
gurin iya sarrafa mazaje a shimfiɗarsu ta Allah tsine
Tunda fa'eez
yake a rayuwarshi bai taɓa jin daɗin kwanciya da mace irin Tina ba, ba wai
fareedah ba ta kai bane, fareedah mace ce iya mace a shimfiɗa kuma ta san me
take yi, saidai bata ko kama qafar Tina ba a wannan fannin, duk da a zahiri
fareedar ta fi Tina sahihiyar ni'ima ba ta coge ba wacce ake saya, amma fa'eez
bai fahimci hakan ba saboda qarfin sinadarin da su Tina suke amfani da shi
Tina ta
wahalar da shi matuqa kasancewar bai taɓa daɗewa da mace irin haka ba a shimfiɗa,
duk haɗuwar fareedah baya bata lokacin da ya fi awa ɗaya, ita ma fareedar kunya
irin ta ɗiya mace ɗiyar hausawa ta kan nuna masa awa ɗayan ma da qyar ta
kaishi, dan haka ko da ita ba ta samu nutsuwar ba, ba ta nuna masa ganinta zai
ga zaqewarta ko kuma da kunya tunda shi bai da dogon zango game da al'amarin
mace
Ita kuwa
Tina sheɗaniyar, daga wannan style sai wancan duk a dare ɗaya, kuma rura wuta
irinta shaiɗan la'anatullahi alaihi sai ya mance ma da cewar yanzu fa zinace
yake yi, ba halaliyarsa bace, haka yayi ta biye mata tare da nuna jin daɗinsa
har zuwa lokacin da aka iso magaryar intaha, ta fahimci ta gajiyar da shi sosai
sannan ta qyaleshi, nan kuwa suka saɓi barci suka runtuma suna rungume da juna,
ba kyace fa'eez ɗin fareedah bane mai qin kula mace da ba ta muhimmanci, sai ga
wannan kamar zai mayar da ita ciki
Hmmmm, wato
matasa, qin jawuwa qin kamuwa, bahaushe yace tsalle ɗaya ake yi a faɗa a rijiya
amma sai ayi dubu ba a kuɓuta ba, kada ka kuskura ka jefa rayuwarka cikin datti
da gubar zina, ka sani ɗan uwa, zina masiface, zina bashi ce, malamai sukace ba
kowane zai biya maka bashin zina ba sai 'ya'yanka mata, yanzu tsakani da Allah
mazaje kuna yi wa matanku adalci?, tsakani da Allah kuna yi wa 'ya'yanku
adalci, manzon Allah ne fa ya faɗi magana, kana ganin maganar ba za ta tabbata
ba, manzon Allah s.a.w yace duk wanda yayi zina da matar wani sai anyi da
tashi, duk wanda yayi zina da uwar wani sai anyi da tashi, duk wanda yayi zina
da 'yar wani sai anyi da tashi, duk wanda yayi zina da qanwar wani sai anyi
zina da tashi, shi ka qaryata manzon Allahn ne?, me ka ɗauka zai sameka bayan
ka ɓuya wa halittu ka yarda mahaliccinka ya ganka kana zina, wai ma wacce
ribace cikin zina bayin Allah?, me zaki samu?, me zaka samu ga abokiyar zinarka
wacce matarka ta aure ba ta da shi?, ashe ka gwammaci ka tozarta 'ya'yanka mata
ta hanyar ciyo musu bashin da zai taɓa mutuncinsu a duniya, qarshe ya gangarasu
cikin fushin Allah da azabarsa a lahira?, mene ne ribarka bawan Allah, shin
kana tunanin ranar da za a tona maka asiri a gaban waɗanda ka ɓuya daga garesu
ka aikata laifin, ka manta akwai yauma tubulassara'ir, me ya aikeka ɗan uwa?,
wallahi tallahi, billahi matuqar zaka riqe zina toh sai ta rabaka da
mahaliccinka, domin ita zunubice da ba ayinta sai an cire wa mutum rigar imani,
kai da zaka ga yadda kake a lokacin da kake zina toh da ba ta sake baka sha'awa
ba, ka sani malamai sunce matuqar ka sanya kuɗi kayi zina da wata mace, toh kai
wallahi kyauta za ayi da taka, ya zaka ji lokacin da aka ce maka ga 'yarka can
ba ma mazan ne suke bibiyanta ba, ita take bibiyarsu, ɗan uwa kar ka yarda da
ganin hakan a rayuwarka, idan mace ɗaya ba ta maka ba akwai m asna, wasulasa,
wa ruba'a, sam zina Allah ba a daina yace ba, kar ma a kusanceta yace, ita
kanta kusantar zinar haramunce balle zinar da kanta, ɗan uwa idan an maka wa'azi, kar ka ce ba
yanzu zan tuba ba, kar ka ce na kusan tuba, domin ka sani wasu a kan gadon
zinan suke mutuwa, me kake tunani zai sameka idan ka mutu a lokacin da aka zare
maka imani?, ɗan uwa kar kayi, ɗan uwa kar ka cigaba da aikatawa, wallahi zina
mummunan laifine, ko a wuta mazinata suna da baqin jini balle a duniya, ki duba
zafin wuta da azabarta da aka faɗa amma dattin zina da yake fitowa daga farjin
mazinata yafi ɗaga wa 'yan wuta hankali akan zafin wutar, ɗan uwa aljanna kake
so ko wuta?, kai a gaisheku matan mazinata, wallahi kuna da hakuri, Allah ya
tsareku ya qara muku hakuri ya kuma kawo muku mafita amma kar ki garda ki biya
bashin da ya ci 'yar uwa, ki nemi tsarin Allah akan hakan, Allah ka shiryi
matasa da dattawan musulmi, dan wani azzalumin tsoho da na gani da aids wai
shima a neman mata ya samu ana ta gaisheshi, ya ban tausayi amma ban iya
tsayawa a gurin ba, mu ji tsoron Allah 'yan uwa😭
**
Duk yadda
fareedah ta so ta samu relief akan sha'awarta ta kasa, sai ma qarin sha'awar da
ta qara wa kanta, haka tayi ta juye juye ta lumshe lumshen idanu har sheɗan ya so jefa mata wani abu cikin
zuciyarta sai Allah ya taimaketa a wannan lokacin tayi istirja'i, da qyar bacci
ya ɗauketa a wahalce, da safe da qyar ta tashi ta haɗa wa hafeez break fast
saboda tafiya school, saidai duk yadda ya so janta da wasa yau ba ta da
walwala, kallonta kawai yayi tayi har ya gama break sannan yayi murmushi yace
"matar
zan wuce"?
Idanunta da
suke lumshe ta watsasu a kansa ta buɗe baki da qyar tace "toh hafeeez,
Allah ya ba da sa'a"
Ameen yace
ya ɗora da cewa cikin tausasa murya tare da matsowa jikinta daf da ita kamar
zai haɗa fuskarsu yace
"akwai
baqon yanayi yau a tattare dake, bana sonshi domin na tsani damuwarki, ki je ki
kwanta kiyi bacci, kar kiyi komai, idan na dawo zan mana ayyukan, ba zan daɗe
ba amma zanyi kewarki matar" ya qarashe da murmushin da ya sanyata jin
tsikar jikinta sun zuba, ba ta samu bakin amsawa ba sai lumshe idanu da tayi
tana sauke numfashi a hankali
Hannunsa ya ɗora
akan kafaɗarta yace
"matar
ko in fasa school ɗin ne mu je asibiti, sai na ga kamar ba lafiya ko"?
Hannunsa ta
janye daga kafaɗarta tace cikin juriya da qarfin hali
"No
hafeez, baccine kawai bai isheni ba, yanzu zan je in rama, a dawo lafiya mijin,
ina so ka cinye test ɗin nan duka" ta qarashe da 'yar dariya
Yana
murmushi yace "na miki alqawari kuwa, inshaa Allah, bye matar zan missing ɗinki" yana gama faɗin hakan ya tashi yana mata
murmushi kamar yadda ita ma take masa sannan ya juya ya tafi ta bi bayansa da
kallo har sai da ta daina kallonsa,
ɗakinta ta
wuce ta kwanta, maimakon ta yi abinda ya dace sai ta sake ɗaukar wayarta ta
tafi wattpad duniyar novels ta fara bin wani ɗan banzan littafi na turanci
wanda arnakun duniya suka rubutashi na batsa, wanda ake iskancin da gaske
saboda ba addini, toh kema in kika yi koyi da su kin rushe addininki da
mutuncinki da ta iyayenki,
Ba tayi nisa
cikin novel ɗin ba muguwar sha'wa ta ninku mata fiye da farko, haka dan jaraba
ta cigaba da karantawa har ta fitar da abinda kai tsaye ba za a kirashi
releasing ba domin sauqi kaɗan ta samu amma tana nan tare da guguwar muguwar
sha'awarta, amma ita a gurinta shaiɗan ya qawata mata abin dan haka ta ji yin
hakan ya mata daɗi, ta ji kuma tana da ra'ayin cigaba da hakan
Hmmmmmm
***
Ba qaramar
makara faeez yayi ba, dan haka yau ya rasa sallar jam'i da yake yinta kan
lokaci a ɗakinsa, wannan ita ce illar zina, domin basa haɗuwa da sallah, wasu
malam sunce matuqar ka ga kana yin zina kuma kana sallah, toh sallarce ba ka
yinta daidai, domin ita Allah yace tana hanine ga aikata alfasha, Allah ya
kyauta
Duk jikinsa
a mace yake dan haka koda ya farka motsi kawai yayi amma ya kasa ture Tina daga
jikinsa, ita ce ta ji motsinsa ta buɗe idanunta ta kalleshi, idanu kawai ya
qura mata ba tare da yayi magana ba, murmushi ta masa tace cikin harshen
turanci
"kana
buqatar taimakone"?
Kai ya gyaɗa
mata ya buɗe baki a hankali yace
"ina
son yin wanka"
Bakin da
yayi maganar ta sumbata tare da masa murmushi ta sauka a haka tsinanniyar ta
shige toilet ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi daidai yadda ta tsara ta fito ta
yaye masa lulluɓin jikinsa ta kamo hanunsa zuwa toilet ɗin, da kanta ta masa
wanka ta mammatsa masa jiki saboda fahimtar da tayi bashi da qarfi, kafin ta
gama masa wanka cikin hikimominsu na butterflies faeez ya nemi gajiyarsa da
mutuwar jikinsa sun sakeshi, tsabar yaudara irin na Tina sai da ta so ta rinjayeshi
a toilet ɗin, da qyar ya yaqi zuciyarshi yace ta bashi minti biyu, da qyar ta
fice ta barshi ya yi wankan tsarki cikin gaggawa ya fito ɗaure da towel, yayi
saurin sanya jallabiya tare da dakatar da Tina ganin tana shirin raɓarsa, ya
fara gudanar da sallah misalin qarfe takwas da rabi na safe, a gaggauce yayi
adduoi ya tashi saboda ya makara da halartar conference hall ɗin
Cikin
gaggawa Tina ta shiryashi tunda ta fahimci sauri yake yi, shiko ya wani sake
mata jiki tamkar wanda aka canza wa qwaqwalwa, sai ma kallonta yake yi shaiɗan
na raya masa wasu abubuwa game da ita dan har yanzu ba kaya a jikin Tina
Yoh toh ta
zo da su ne?😔
Da zai fita
kuwa cikin karuwanci da barikanci ta maqalqalesa ta bashi kisses sannan ta ce
"I love you, you are the best among the men"
Cikin jin daɗi
da qawatawar shaiɗan ya manneta a jikinsa yace "ki zauna da ni, kar ki
fita daga nan, ki bari in dawo, duk abinda kike so za a kawo miki, pls"
Murmushi
jakar ta masa ta sake haɗa bakinsu sannan ta janye hannayenta na rataye a kafaɗunsa
tace
"kana
sona?, ban ji matsayina a darenka ba"
Abin tsoro
abin mamaki sai ga faeez yayi murmushi ya sumbaceta yace "baki da misali,
kin fi qarfin furuci, darena dake rayayyene a cikin sauran dararena"
Murmushi
tayi tace "then say..., you love me"
Ba msu ya raɗa
mata hakan a kunne sannan yayi saurin kama hanya tare da janyeta yana waving
mata hannu, ita kuwa ta hura masa kiss
Toh mata, da
haka ake qwace muku mazaje, ke kin zauna, kune na bara kune na bana, kwanciyar
aure ɗaya kika iya, bance kiyi koyi da turawa ba domin su sun zaɓi jin daɗin
duniyane ko da zasu cutu amma ki canza, ki nemo waɗanda babu cutarwa a cikinsu,
amma ke tun irin kwanciyar iyaye da kakanni ba canji toh a gurin mazajen yanzu
da kwai matsala, ki shiga hankalinki
ISLAM IS MY
IDENTITY
No comments