QANIN MIJI 13
13
Qarar
buguwar wayar ta razana fareedah, da sauri ta bar jikinsa tana waro idanu tare
da bin gurin da ta jiyo qarar da kallo
Wayarta da
ta gani ta damage yasa ta juyo da sauri ta kalli Hafeez, shi ko huci ma yake yi
kamar wanda yayi tsere da zaki
"Hafeez
lafiya"?
Tace tana
riqo hanunsa, qin magana yayi sai da duk ya ga ta shiga damuwa tace
"wani
mummunan abu ya samu Faeez ne"?
Sai a
lokacin yayi magana a zafafe cikin faɗa da buɗe idanu
"idan
wani abu ya sameshi ina da asarane, ni murna ma zan yi idan hakan ta
faru"!!
Zaro idanu
tayi waje tare da dafe baki da tafin hanunta tace
"ɗan
uwankan"?
Zabura yayi
ya riqota da qarfi yana zaro mata jajayen idanunsa yace
"a
kanki ban san kowa a matsayin ɗan uwana ba, ina da kishi nace miki!!!, na
tsaneshi"!!
A tsorace
murya na rawa tace
"innalillahi
wa inna ilaihirrajiun, haba Hafeez, dan Allah ka daina irin waɗannan
maganganun, ba ka isa ka yanke alaqar da ta ke tsakaninka da Faeez ba, dole ka
kirashi ɗan uwanka"
"saboda
shi kike so ba, na ce saboda kina sonshi ko"?!!!
Ya qarasa a
faɗace yana mata ihu
Rintse
idanunta tayi saboda ihun yana shiga mata har qwaqwalwa, hanunta ta ɗora a
goshinta ta dafe tace "wasshhh... "
Kallonta ya
fara yi yana mai nazarin yanayin da ta shiga, yadda ya ga tana yatsina fuskane
tana ɗan jujjuya kan, sai ya ji tsoro kar wani abin ne ya sameta
Cikin nuna
damuwa yace bayan ya sassauta murya
"me ya
sameki Reedah, mene ne??"
Ba ta amsa
ba sai ma cigaba da tayi da jujjuya kai, janyota yayi jikinsa cikin rawar jiki
yace
"yi
hakuri dan Allah, na bar maganar, wallahi rainane yake tafasa, Faeez yana nan
dawowa cikin satin nan, ko satin sama"
A tsorace ta
bar jikinsa, kamar ba ita ce mai ciwon kai yanzu ba, tsabar tsorata ko magana
ta kasa yi sai kallonsa da take yi kamar ta ga abin tsoro
Janyota yayi
ya sake mai da ita jikinsa cikin lallashi ya fara magana domin da gaske har
cikin zuciyarsa ba ya son tashin hankalinta
"mene
ne abin tashin hankali Swampy?, ba mun gama magana a kan wannan ba, babu abin
da zai faru, ki kwantar da hankalinki dan Allah, just for me my Reedah"
Cikin muryar
kuka tace "Hafeez ina jin tsoro"
"No,
kar ki damu, ina tare da ke, akwai shirin da zan yi akan hakan, dan Allah kar
ki bari hawayen nan su zubo"
Ai duk daɗin
bakin da yake ta mata Fareedah ta qi kwantar da hankalinta, haka suka kusan
kwana a zaune tana masa rigima, duk yadda ya so ya ɗauke mata hankali da
wasannin da zai sa su gangara duniyar masha'arsu Fareedah ta qi yarda, duk
nacinsa haka ya haqura, shi da ya samu tayi bacci daf asuba ma daɗi ya ji
**
Wani iskanci
a gurin Faeez shi ne, tun kiran da hafeez ya ɗaga bai sake kiransu ba, ya maida
hankalinsane gurin tunanin kewar Tina da zai yi, tsabar fushin Allah da ya
gayyato har aka cire masa tunanin zinar haramunce ta hanyar ɗiga masa RAN a
zuciyarsa, kwata kwata baya tunanin abinda yake aikatawa bai dace ba, shi hakan
ma daɗinsa yake ji saboda an qawata masa hakan a cikin zuciyarsa
Wanka suke
yi da Tina a swimming pool suna ta wasannin banzansu tamkar ba Hafeez ba, ya
saje sak da turawa gurin sheɗana, toh idan ba haka ba, yaushe cikin tsakiyar
guri zai zauna daga shi sai boxer kamar yana gidanshi ko ɗakinsa
Fitowa suka
yi bakin gaɓar swimming pool ɗin Faeez daga shi sai boxer yayin da Tina ke
sanye da pant da wata shegiyar bra da ni dai ban ga amfanin sanyata ba, zama
yayi akan wata kujerar qarfe yayin da Tina ta zo ta ɗale masa cinya ta manna
masa kiss tare da ɗan ciza lips ɗinsa cikin salon 'yan bariki, wasshh yace
sannan suka yi dariya a tare, ya fara mata cakulkul, zillo ta fara yi har ta
sauka qasa ya bi ta ya kwanta a jikinta ya mata rumfa ya haɗa bakinsu ya fara
kissing ɗinta kamar wani kare, ni ko nace jaki kawai, Allah ya shirya
Da yake ita
ma ba baya ba dan haka nan ma sai da suka yi ta wasanninsu kamar yadda sauran
turawan da suke bakin ruwan suke tayi da 'yammatansu, wasu ma zina qiri qiri
suke yi ko tunani babu balle kunya da kiyaye mutuntaka, ta gama dulmiyar da
Faeez kawai, sai fatan Allah ya kyauta
"Tina
ki bini qasata mana" cewar Faeez cikin harshen turanci bayan sun kammala
dabbancinsu
"mene
ne ba ka samu ba daga gareni a cikin watannin da muka yi da kai, wanda har sai
na bika nigeria"?
"ji
nake yi kamar jiya muka haɗu, ba zan iya rabuwa da ke ba, ko na tafi, nutsuwata
da hankalina suna baya, pls ki bini mu cigaba da rayuwarmu a can, na miki
alqawari zan zaunar da ke a gurin da zaki ji daɗin rayuwarki tamkar kina nan,
ba za ki samu wata matsala ba"
Shiru tayi
tana kallonsa, ta qi yin magana, cikin roqo da neman alfarma yace
"pls
Tina, ki ce kin yarda"
Idanunta ta
lumshe ta gyaɗa masa kai
Tsabar murna
bai iya ba ta amsa ba sai ɗagata da yayi cak yayi cikin hotel ɗin da suka kama ɗaki
Cikin hauka
da ɗabiun karnuka da ya saba da su yanzu suka lula duniyar zina da ita, ba tare
da ya sanya komai na kariya ba, domin tun sau ɗaya a zinarsu ta biyu da yayi
yunqurin sakawa Tina ta yaudareshi tace ba ta so tare da janye hankalinsa,
shikenan ya daina sakawa, kuma bai taɓa tunanin hakan bai dace ba a ranshi,
burinshi kawai ya ji daɗi ne kawai, domin a tunaninshi ba wani abu da zai iya
biyo baya
**
Rana bata
qarya..
Cikin shirin
tafiya airport ɗauko Faeez suke, fuskar Hafeez a ɗaure kamar wanda aka masa
mutuwa, duk ya bi ya tashi hankalinsa akan kishi, sai hararar Fareedar ma yake
yi domin shi a ganinsa rawar jiki take yi mijinta zai dawo, ita kuwa sai lallaɓashi
take yi dan ba ta so ya ɓallo musu wani liqin a gaban Faeez
Kamar yadda
Tina da Faeez suka kwana tsiyarsu, haka Hafeez da Fareedah suka kwana
holewarsu, kasancewar cikin kwanakin zazzaɓinta ya tafi, babu kuma wani laulayi
sai cin tsiya da ta buɗe babinsa, Hafeez kuwa murna yake yi da hakan dan har
abu yake tanadar mata a kan bedside drawer idan ta farka cikin dare ta ci,
yayin da shi ma zai tashi sai ya tabbatar babu abin da take buqata sannan su
koma su kwanta
Hannayensa
ta riqo tace "haba my love, dan Allah ka ɗauke wannan damuwar daga
fuskarka, ka san ina sonka ko"?
Waro
idanunsa yayi a kanta domin ba ta taɓa faɗa masa hakan ba
Murmushi ta
masa ta kama hannunsa ta zaunar da shi ta ɗale jikinsa ta saqalo hannayenta a
kafaɗarsa ta bashi kiss ta ɗago tana masa kallon love tace
"da
gaske ina sonka Hafeez, kuma a shirye nake tsab da in rabu da Faeez in aureka,
kaine irin mijin da nake ta burin aura
ba Faeez ba"
Farincikine
ya lulluɓeshi, nan ya fara mata sambatun kalaman soyayya da qauna tare da fara
mata wasanni, har ya manta da ɗauko Faeez, ita ma kuwa ta biye masa
Wayar Hafeez
ce ta dakatar da su, ya ɗauko wayar yana tsaki ya picking ba tare da ya lura da
mai kiran ba
Muryar
maxwell ya ji, hakan ya sakashi ɗaure fuska kamar yana ganinsa yace "mene
ne maxwell"?
Cikin ladabi
yace "Oga yace in faɗa maka, ya kira nambarka ya qi tafiya, wai bai biyo
jirgin ba, sai gobe"
"ok"
yace tare da katse wayar ya ja doguwar tsaki ya ajiye wayar ya juyo ya cigaba
da abin da yake yi yana cewa "shashashan ba zai dawo ba sai gobe" ba
ta amsa ba dan ta san da wa yake yi, ga shi wasanninsu yayi nisa ba ta son su
katseshi, dan tana matuqar nishaɗantuwa da wasannin, ita koda yaushe suka shiga
duniyar nan da Hafeez ba ta so a daina, ta rasa me yake faruwa da ita, musamman
a kwanakin nan
Ni ko na ce
bashin da mijinki ya ci, kike biya abinki😂
*
A ɓangaren
Faeez, ya daɗe da shigowa qasar tare da Tinarsa, hotel kawai yayi wucewarsa da
ita ya kama mata ɗaki mai tsadar gaske tare da niyyar gyara mata ɗaya cikin
gidajensa ya mayar da ita can dan su fi jin daɗin holewarsu, ko tunanin mutuwa
Faeez baya yi, ya gama hallakar da kanshi saboda son zuciya
*
Suna zaune a
dining suna cin abinci suka jiyo horn ɗin mota tare da qarar shigowarta cikin
gidan, Fareedah da take zaune jikin Hafeez yana ba ta abinci a baki ce ta fara
magana
"Hafeez
kamar qarar shigowar mota"?
"eh
nima haka na ji, tashi ki je ki saka hijab dan ban san ko waye bane, kar ya
kalle min ke a haka" ya qarashe da kashe mata idanu, ita ma idanun ta
kashe masa ta tashi daga jikinsa ta haura ɗakinta yayin da Hafeez ya bi bayanta
da kallo
Hijab ɗin ta
sako ta fito, tana tako matakalar da za ta sauqo da ita gurin dinning ɗin
sallamar Faeez ta doki kunnuwansu, duk tsanar Faeez da Hafeez yake ji, da
rashin tsoronsa cikin zuciyarsa sai da gabansa ya faɗi, balle Fareedah uwar
tsoro, a toh marar gaskiyane ko a ruwa sai yayi gumi
A dabarbarce
suka amsa sallamar suna bin fuskarsa da take haɗe da kallo, dan tun a hanya ya
shirya shi ma makircin da zai wa Fareedah, gudun kar ta buqaceshi a yau ɗin,
dan ya matuqar gajiya a gurin Tina, ba ya ma da wata buqatar mace a yanzu, dan
haka ma ya sayo magunguna da yawa a wani chemis wanda zai mata qarya da su
Kamar ba
Hafeez ɗin Fareedah ba, wanda idan ya dawo za ta je da gudu ta rungumeshi, yau
kam duk da tana tsorace sai ta ɗaure fuska ita ma, ta qarasa gurin dining ɗin
ta ja kujera ta zauna tayi banza da shi
Hafeez ne ya
kalli fuskokinsu duka yayi murmushi ya kalli Faeez da ya ja kujera kusa da
Fareedah ya zauna yace
"amma
ka shammacemu ya Faeez, kai da ka rage mana murna ka ce sai gobe"
Yamutsa
Fuska yayi sannan ya murmusa yana kallon Fareedah yace "na so in baku
mamakine kawai, amma yadda kboy ya ɗaga min hankali a waya dolena in dawo ai,
ko shi yasa mutumiyarka yin fushi haka"?
Yaqe Hafeez
yayi ya ce "ba ita kaɗai ba, nima a cike nake da kai yah Faeez"
Fara ɓalle
botir ɗin jikin coat ɗin da yake jikinsa yayi yana kallon Fareedah yace
"toh ai
sai a min uziri ko madam, kar ku haifoni, yanzu haka wallahi da zazzaɓi na
sauko qasar, ga gajiya da bacci da suke jikina, mu je ki haɗa min ruwan wanka
in watsa in sha magani in ɗan kwanta ko zasu sake ni, wallahi duk jikina ciwo
yake min, wasshh" ya qarashe da rintse idanu, haɗa idanu Fareeda da Hafeez
suka yi suka taɓe baki
Da sauri ya
buɗe idanun ya miqe riqe da coat ɗin yace "ina jiranki, kai kuma Hafeez je
ka shigo min da briefcase ɗina" babu wanda ya amsa masa, har ya fara
tafiya ya juyo yace "amma fa ban ga alamar kun yi kewata ba, na ga kowanne
qara girma yayi da haske, ko da yake ita wancan na san me ya kawo hakan"
Cikin alamun
rashin gaskiya suka kalleshi cikin yanayi na tambaya, murmushi yayi kaɗan yace
"eh, na sani mana, tun shigowata fa take ɗura abinci, ba ji ba gani"
Allah ne ya
kare, tsakin da Hafeez ya ja ta qi fitowa, yana kallon fuskar Fareedah yace
"lafiyace ta kawo haka, da kuma kwanciyar hankali"
Cigaba yayi
da tafiya yana cewa "shiyasa ai nace ba ku yi kewata ba"
Yana shigewa
ɗakinsa Hafeez ya ja wata shegiyar tsaki yace "banza, ko uwar me yake mana
idan yana nan da za mu yi kewarsa oho, ko garin yaya ma ya miki kallon qurillah
haka oho, wallahi ni dai kar ki sake da shi sosai, kina haɗa masa ruwan wankan
ki fito daga toilet ɗin, kar ki yarda kuyi tare, ko plan ɗinmu ma cikin baqin
duhu zaku gudanar, wallahi ban yarda ba, dan ni ba sakaraine irinshi ba, ina
kishin abinda nake so, nan ma ki bashi
minti goma zuwa shabiyar, duk qarqari kar ya wuce ishirin, kuma dole ya
kusanceki a yau, ba zazzaɓi ba ko mutuwa zai yi, na ji daɗin hakan ma da zata
kasance a halin bashi da lafiya, zan baki abu ki sanya masa cikin jarababbiyar
coffee ɗinsa, dole sai ya kusanceki a yau ɗin" qarfin hali irin na Hafeez har
idanunsa sun rine saboda kishi
ISLAM IS MY
IDENTITY
No comments