QANIN MIJI 14
14
Kallon
Hafeez kawai ta tsaya yi, ta ma kasa ba shi amsa, shi ko cikin jin haushi yace
"shashasha
yana magana ko"?
Yanzu kam
dariya ya ba ta, rufe bakinta tayi tana 'yar dariya yayin da shi kuma yake ta
banka mata harara, sannan ya tashi zai bar gurin, da sauri ta riqo hanunsa ta
miqe tsaye ta dakatar da shi ta fara magana cikin raɗa
"kai kaɗaine
fa, tilo, kana ɓata ranka akan faeez abin da kai kanka ka sani, duk daɗewar nan
da yayi a wata qasar, zai yi wuya yayi sati ɗaya a gidan nan bai sake wata
tafiyar ba, toh ka ga muna tare ai, ni idan kace kar ya kusanceni ma shikenan
an wuce gurin, kawai sai in fara neman takardar sakina daga gurinsa mu zo muyi
auren mu"
Ajiyar
zuciya ya sauke ya ɗanyi murmushi yace "dole sai an yi hakan swampy, ki je
ki haɗa masa ruwan wankan"
Ba ta ce
komai ba sai murmushi kawai da tayi masa, ta juya ta fara tafiya, shi ma ya
juya ya fice zuwa ɗauko brief case"
Tunda ta
shiga ɗakin yake wani yatsina fuska yana wani ɗaɗɗauke kai, ba ta kulashi ba ta
cire hijab ɗin jikinta ta ajiye a kan resting chair tayi wucewarta toilet ɗinsa
Tana haɗa
masa ruwan wankan ta fito, kamar za ta fice ba tare da ta masa magana ba, sai
kuma ta fasa ta taka kusa da gadon da yake kwance idanunsa a lumshe ta ɗan
bubbuga gefen filon da ya ɗora kansa a kai, ya buɗe idanu a hankali ya watsasu
a kanta
Harara ta
banka masa tana me haɗe fuska tace
"na haɗa
maka ruwan wankan"
Murmushi
yayi ya riqo hanunta ya janyota ta afko jikinsa, nan ta fara qoqarin qwace, dan
ita har cikin ranta haushinsa take ji, ba wai saboda huɗubobin Hafeez ba kawai,
yadda ya cutar da ita har ya kai ta ga kusantar qaninsane yake matuqar qona
mata zuciya, ita yanzu ma da ta ganshi sai ta nemi son da take masa ta rasa
Mutsutsun ta
gama har ta hakura dan ba riqon wasa ya mata ba, murmushi yayi yace
"sarkin
rigima har kin gama?"
Ko alamar za
ta yi magana ba ta yi ba, hakan yasa shi cigaba da cewa
"shi ne
har da hararata ko?, dan kawai ban dawo da wuri ba, ban kuma ce ki je ba,
shikenan kawai?, toh ai yanzu gashi na dawo, ki yi fatan zazzaɓin da yake
damuna ya yi sauqi, ko zuwa jibi sai in baki abin da kike buqata, na san shi ne
ko?, toh ai shikenan, an wuce gurin, yanzu dai kafin in fito coffe dan
Allah"
Haushine ya
taso mata ta taqarqare ta fisge jikinta, domin rainin hankalin yayi yawa, ta ma
fara ganin abin a matsayin wulaqanci
Harara ta
banka masa tare da jan tsaki ta juya ta fice abinta da ɗan banzan sauri,
idanunsa ya waro cike da mamaki, a ranshi yana raya cewa lallai yanzu fareedah
ta sauya, yau ita ce da masa tsaki?, gaskiyar magana tsakin nan ya taɓa masa
zuciya, cikin qanqanin lokaci ranshi ya ɓaci, qwafa yayi ya tashi ya shige
toilet ɗin
Kitchen ta
shiga da nufin haɗa masa coffee, amma abin mamaki sai ta ga Hafeez a ciki yana
haɗawa
Cikin
farinciki ta rungumoshi ta baya tace "I love you mijin?"
Dawo da ita
yayi ta kan qirjinsa ya rungumeta ta gefe yace "me too my swampy, komai
zan iya dominki saboda bana so ki wahala, soyayyarki a cikin jinina take"
Qanqameshi
tayi sosai a jikinta ita ma tana qara jin sonshi na huda mata zuciya
"washh
my swampy, kar ki tsokanoni, bar ni haka" yace yana mai dakatar da ita
daga wasannin da ta fara masa
Siriruwar
dariya tayi ta sake shi ta bar jikinsa tana masa kallon love, hancinta ya ja
yace
"ai kin
ma tsokanoni, sai na rage zafi" bai jira amsarta ba ya janyota jikinsa ya
fara sumbatarta, ni ko nace ikon Allah, abu kamar maita
sosai yayi
abin da ya so sannan ya sake ta yana kallon cikin idanunta ya ce "shimfiɗata
za ta yi kewarki yau, ba zan iya bacci
ba"
Lumshe idanu
kawai tayi ta kwanta a jikinsa, dan ita kanta ta san za ta yi kewar Hafeez, duk
da Faeez zai kusanceta amma ta san ba zai nishaɗantar da ita tamkar Hafeez ɗinta
ba
A hankali ya
janyeta daga jikunsa ya juye coffee ɗin a wani cup da yake ajiye a gefe ɗauke
da wata qwaya, cikin qanqanin lokaci qwayar ta narke ya ɗauko cup ɗin ya miqa
mata yana cewa "pls my Reedah, kar ku ba wa babyna wahala, kin ji"
"wannan
alqawarinane, ka kwantar da hankalinka"
"ok, je
ki, zan yi kewarki"
Lips ɗinsa
ta sumbata tayi saurin ficewa dan har ta ga qwalla sun taru masa a cikin idanu
Ko da ta
koma ɗakin Faeez ta samu ya fito daga wanka yana goge jikinsa, yana ganinta ya
haɗe fuska, ita ma fuskar ta haɗe ta je ta ajiye cup ɗin akan bedside drawer ta
juya za ta fita, ya ɗaga murya cikin ɓacin rai yace "keh"!!
Juyowa tayi
cikin haɗe fuska, yayin da shi ma ya fara takawa zuwa inda take
Sai da ya je
daf da ita ya janye towel ɗin da ya ɗaura a jikinsa ya sanya hannu ya fisgota
jikinsa cikin huci da zuga irinta sheɗan yace "ni kika yi wa tsaki, toh
wlh sai na yi maganinki, ba dai na san abinda kike buqata ba?, toh nan da sati
biyu ma ba za ki sameshi ba, ai jiki dai nawane ko, kuma qwalelenki, idan kin
isa marar kunya ki kamani da qarfi ki kwanta da ni dole, gani a gabanki, wlh
sai kin zo kin ban hakuri akan gwiwowinki, idan kin qi kuma, ke ce a wahale,
shashasha"!!!
Maimakon ya
ga ɓacin rai a tare da ita ko fushi, sai ma dariya da ta dinga tuntsire masa da
shi, sai da ta yi mai isarta sannan ta tsagaita ta masa kallon banza ta ce
"toh malam me jiki, idan ma mafarki kake
yi toh ka farka, wannan ba Fareedar da ka sani da ba ce, da kai da jikin naka
bana buqatarsu har abada, maganar in zo in durqusa a gabanka kuma, hmmmm,
tsakanin ni da kai, zan ga mai durqusawa a gaban wani, nice dream malam
Faeez" ta qarashe da kashe masa ido ɗaya ta juya ta fita tana dariya
Sandarewa
yayi a gurin cike da tsananin mamaki, lallai lamarin fareedah ya girmama, da
qyar ya ja qafarsa daga gurin ya je yayi zaman 'yan bori a kan gado, ya daɗe
kafin ya tashi ya shirya cikin kayan bacci yayin da Tina ta faɗo masa a rai,
bai san lokacin da murmushi ya kubce masa ba, a hankali ya furta my darling
Hhh ko ba
darling ba?, za ka ci babanka
Tas ya
shanye coffee ya ajiye cup ɗin ya kwanta abinshi tare da kiran nambar Tina da
ya haɗa mata duk a yau ɗin, layukansa
cikin na nigeria ya bata ɗaya kafin ya haɗa mata wani layin
Sun yi nisa
cikin hirar batsarsu ta waya ya fara jin wani azababben yanayi, tun yana ɗaukan
abun wasa har dai ya ji ya kai maqurar qarshe, duk yadda Tina tayi ta masa sheɗana
a waya ya kasa samun nutsuwa, sai ma sake rura wutar sha'awarsa ake yi, ba
shiri ya katse wayarsu da Tina, dan ya ɗauka maganganun da suka yine ya yi
tasiri a jikinsa haka, saidai fa duk yadda ya so lamarin ya sauqaqa masa abu ya
ci tura, ba shiri ya fice zuwa ɗakin Fareedah a gigice yana ji kamar yayi kuka,
dole ko da rigima da bala'i ya durqusa ya roqi fareedah ta bashi kulawa, idan
ba haka ba, bai san halin da zai shiga ba, dan
ji yake yi kamar zai mutu
Cikin kayan
barcin da ba su fi tsirara da komai ba Fareedah ta kwanta saboda ta san plan ɗin
su, suna hira da Hafeez ɗinta a waya ta ji shigowarsa tare da buɗe qofar a
gigice, kashe wayar tayi gaba ɗaya ta haɗe fuska tana masa kallon banza
Da sauri ya
je jikin gadon ya durqusa akan gwiwowinsa cikin rawar murya yake magana
"Fareedah
dan Allah ki yi hakuri ki taimakeni, gani bisa gwiwowina, ina roqonki da ki yi
hakuri da maganganun da na faɗa miki, sharri shaiɗan ne, ba zan sake ba
Fareedah, dan Allah"
Sake haɗe
fuska tayi tace "na yi hakuri, je ka, ai sati biyun basu yi ba balle su
wuce"
Kasa magana
yayi saboda mawuyacin halin da ya shiga, har hawaye sun fara bin kumatunsa,
tashi yayi kawai daga durqushen ya haura gadon tamkar mayunwacin zaki, ita kuwa
Fareedah dama plan ɗinsune dan haka ta biye masa suka lula
Saidai
dukkansu sun fahimci baqon al'amura ga junansu mabanbanta, abubuwan da Faeez
yayi ta mata su a yau ɗin baqine a gurinta da ba ta sanshi da su ba, shi ma
kuma hakan take a gurinsa, abubuwan da ta dinga masa bai sansu ba a gurinta,
hakan kuma ya taimaka gurin daɗewarsu a tare, saidai abinka da marasa gaskiya,
dukkansu sai zargin juna suke yi, musamman Fareedah da kunnenta ya so ya ji
kamar ya kirata da wani suna na daban
Dan haka
suna dawowa hankalinsu suka kafe juna da idanu cikin alamar tambaya
"wace
ce Tina"? Cewar Fareedah
Waro idanu
Faeez yayi cikin rashin gaskiya yace "wace ce kuma me wannan sunan"?
Ajiyar
zuciya ta sauke tace "ok, sai na ji kamar ka faɗi hakan"
Ajiyar zuciyar shima yayi ya janyota jikinsa
yace "kunnenkine kawai"
Ba ta yi
magana ba ya ɗora da cewa "amma yau kamar ba Fareedar Faeez ba" duk
da ta ji faɗuwar gaba sai da ta dake tace
"ni
kaina gani nake kamar ba Faeez ɗin Fareedah ba"
Dammm ya ji
qirjinsa ya buga, cikin in ina yace "kai wallahi bacci nake ji, zan wuce ɗakina,
mu kwana lafiya" yana gama faɗin hakan ya bar jikinta ya sauko daga gadon
ya sanya rigar baccinsa ya fara tafiya ba tare da ya yadda sun haɗa idanu ba
har ya fice daga ɗakin
Bayansa ta
bi da kallo tana ɗora alamar zargi a kansa, ji tayi ba ta yarda da shi ba, ni
ko nace toh ke kin yarda da kanki fareedah?, hhhhh
Toh fa,
cakwakiyar aure, Hafeez saidai hakuri fa, dan yau unborn ɗinka ya ci qaniyarsa,
Allah sarki duniya, ku ji matasa masu zina, cikin.mutanen da Allah zai
inuwantar da su a qarqashin inuwar al'arshi akwai matashin da mace mai kyau da
nasaba ta bashi kanta ya qi yace yana tsoron Allah, toh ku mazinata masu bin
boobs da hips kuna ina kenan?, wallahi zaku sani,idan baka shiga wannan inuwar
ba za ka ci ubanka a lahira, yanzu dai shi hafeez da faeez ma, sun rushe wannan
damar wa kansu, toh yaya kenan?, ku kenan bin matan masu kuɗi da kyawawa kuna
zina da su, wani a fbook yace "duk wani wanda yake zuwa gurin budurwa dan
ya lalatata Allah ya talautar da shi" abun kunya, wlh har da masu tsine
masa, toh kuma Allah ya tsine muku, ko kuma ku shiryu
ISLAM IS MY
IDENTITY
No comments