QANIN MIJI 12
12
Cikin zaro
idanu tare da dafe qirji Fareedah tace
"what"?
Shi ko gogan
naku yalwataccen murmushi yayi wa likitan tare da furta alhamdulillah sannan ya
miqa wa likitan hanu suka yi musabiha haqoransa waje yace
"lallai
wannan babban albishirne, zan kuwa baka tukuicin da kaima za kayi farinciki
kamar yadda nayi, ka turo min account number ɗinka, ko yanzu a nan gurin zan
tura maka da kyautar farinciki"
Dariya
likitan yayi cikin jin daɗi da kwaɗayin abun da za a bashi yace
"Allah
ya qara arziqi yallaɓai, na gode, na gode"
"kar ka
damu, ka cancanci hakan daga gareni"
Fareedah da
ta ga babu wanda ya damu da damuwarta cikinsu, hafeez sai murna yake yi abinsa
kamar wanda aka masa kyakkyawan albishir, sai kawai ta fashe da kuka mai
matuqar taɓa zuciya
Daga likitan
har hafeez kallonsu suka mayar kanta yayin da likitan yace cikin sakin fuska da
barkwanci
"hajiya
kukan mene ne kuma, ko na tsoron haihuwarne"??
Janyota
Hafeez yayi jikinsa ya rungumeta yana ɗan bubbuga bayanta sannan ya mayar da
kallonsa ga likitan yace yana murmushi
"ka san
su mata da raki, musamman wannan tawan shagwaɓaɓɓiya, abin kuka tayi kuka,
abinda bai kai kuka ba tayi kuka"
Dariya
likitan yayi yace "oh!, ashe hakane?, toh sai ka rarrashi kayanka, ka faɗa
mata haihuwa ba zafi ko kaɗan, tana bacci ma za ta iya haihuwar"
Tare suka
qyalqyale da dari da Hafeez suka sake yin musabiha, Hafeez yace
"toh
mun gode likita, sai na jika"
"toh
angon madam, godiya nake"
Miqewa yayi
tare da ɗago Fareedah da take rusar kuka ya sake rungumeta a jikinsa ya ajiye
wa likitan card ɗinsa a kan table ya ja fareedah suka fice
A rungume a
gefensa tana kukan ya kaita mota, mutane sai kallonsu suke yi suna faɗin
"ayyah
sannu, jikin ne ke damunta"?
Godiya kawai
Hafeez yake musu, daga nan ba ya sake cewa komai
Tana rungume
a jikinsa a cikin motar yana shafa mata baya tare da hura mata kunne cikin salo
na rarrashi har sai da ya ji ta fara rage kukan sannan yayi magana cikin
tausasa murya
"my
swampy wai mene ne na kukan?, kina son ɗaga min hankali ko?, haba my reedah,
yaya kike so ki rabani da nutsuwata"?
ɗagowa tayi
daga qirjinsa tana tsiyayar hawaye tana kallonsa tace
"Hafeez
ciki fa?, cikin wata ɗaya da kwanaki yayin da Faeez yake da wata kusan biyar ba
ya gida, wayyo Allahna na shiga uku ni Fareedah"
Take
fuskarsa ta rikiɗe da ɓacin rai, cikin haɗe fuska yace
"akan
cikin ne kike kira wa kanki shiga uku?, ko dan ba cikin wancan jakin bane
azzalumi"
Cikin
matuqar mamaki bakinta na rawa tace "Hafeez...ka...ka fahim...."
Dakatar da
ita yayi da cewa
"No
Fareedah, na fi kowa fahimtarki da gano matsalarki ko ba ki faɗa ba, ni a
gurina kukanki da shiga damuwarki sune masifa da tashin hankali, ba wai wannan
cikin ba, wai shin ba ki san ubanshi bane"?
Hawayene ya
sake zubo mata ta sake cewa
"Hafeez
na san cikinkane, amma yaya zan yi in fuskanci Faeez da shi balle idan al'umma
suka sani"
Hawayen ya
sanya hanu yana share mata ya ce
"tamkar
ruwan dalma ake ɗiga min a zuciyata a dalilin zubar waɗannan hawayen, Fareedah
ko na minti ɗaya kar ki sake ɗaga hankalinki, dole abu biyune za su faru akan
wannan cikin, na farko, idan daqiqancinsa da rashin kularsa ba su barshi ya
gano cikin ba a dawowarshi shikenan, hankali kwance zaki cigaba da rainar min
kayana, idan kuma ya san da cikin toh shi ma zan yi farinciki domin zai sakeki
in aureki kuma shi zai qunshi baqin cikinsa shi kaɗai dan ba zai iya faɗa ma
wani ba, kin ga nan ma hankali kwance zamu cigaba da more rayuwarmu qarqashin
inuwar aure, sai me kuma daga nan"?
Ya qarashe
yana mata murmushin nuna zallar qauna
Turo baki
tayi tana hararansa still wasu hawayen suna sake zubowa tace "kai jin daɗin
rayuwane damuwarka ko?, ni dai wallahi ina cikin tashin hankali, bana son cikin nan mu zubar kawai"
Cikin haɗe
fuska yace
"mu
zubar?, cikin nawa?, wallahi ba za a zubar da shi ba, yadda shi ma ɗansa ya
tako qasa ni ma sai nawa ya taka"
Ita ma cikin
fusata da faɗa tace
"wallahi
sai na zubar da cikin nan, dan ba zan iya ganin tashin hankalin da zan shiga ba
idan mijina ya san da cikin nan, ba zan iya ba"!!!
Da qarfi ya
rungumo kafaɗarta cikin kishi da masifa yace "kar ki sake cewa wani banza
mijinki, kar ki sake nace"!!
Tureshi tayi
ta ce "na faɗa mijina, mijinane, cikine dai sai na zubar da shi, ba zan
haifeshi ba"!!
Yadda ya ga
take masa masifa da kalaman da suke dukan zuciyarshi sosai, sai kawai ya rintse
idanu ya jingina bayanshi da seat, ya ɗau tsawon minti biyu a haka zuciyarsa
tana tafasa saboda kishin ɗan uwansa, hawayene suka fara bin kumatunsa yayin da
ya fara cewa
"ka
cuceni Faeez, ka cuci rayuwata, me yasa ka fara aurenta?, me yasa ka auri
matata?, me yasa?
Yana kaiwa
nan ya kifa kanshi a kan steery ya fashe da kuka tamkar qaramin yaro, dan
maganar gaskiya Hafeez ya kamu da zazzafar qaunar Fareedah da kishinta da suke
tafasa masa zuciya
Jikin
fareedah ne yayi sanyi, dan ita ma har cikin zuciyarta yanzu take jin son
Hafeez na mamayeta ba wai kawai ta ɗaukeshi a matsayin mai kore mata sha'awarta
bane, bayan hakan akwai qauna da take masa
Rasa abin
ƴyi tayi, kawai sai ta fashe da kuka ta kifa kanta ita ma
Kukan ta da
ya ji ne ya sakashi dakatar da nashi ya ɗago da kansa ya rungumota jikinsa ya
haɗe musu baki da nufin hana ta kukan
Tsawon
lokaci suna a haka sannan ya sake mata bakin ya qanqameta a jikinsa ya fara raɗa
mata magana a kunne
"kiyi
hakuri my swampy, ina sonki, ina qaunarki, bana buqatar kukanki, zuciyata za
tayi bindiga, zafi nake ji a qirjina swampy"
Ba ta ce
komai ba sai ajiyar zuciyar da take yi a hankali
"mu je
gida kiyi bacci ki huta, bana son zazzaɓin nan ya cigaba, kin ji"
Yana gama faɗin
haka ya ɗagota daga qirjinsa ya fara share mata hawaye, sai da ya gyara mata fuska tas sannan ya gyara mata
zama zuwa kwanciya tare da kanta a
cinyarsa sannan ya tayar da motar suka bar asibitin
A hanya ya
shiga wani guri na sayar da kayan qwalama ya faka motar sannan ya juyo ya
kalleta yana murmushi, ganin ta fara lumshe idanu sai ya shafi fuskarta yace
"my reedah me kike so in shiga in sayo miki"?
Cikin muryar
jin bacci tare da shagwaɓe murya tace "ina muke"?
Yana
murmushi ya sunkuyo ya ja hancinta yace
"qwalam
da maqulashe store, na san zaki buqaci wani abu ko"?
Murmushi
tayi wanda bai kai zuci ba tace "cake kawai"
"toh
madam, an gama, ko za a min uzirin tafiya"?
Sake
murmusawa tayi ta yunqura za ta tashi ya taimaka mata ta zauna sannan ya fice
bayan ya raɗa mata I love you
Bin bayansa
tayi da kallo tana jin tausayinsa a cikin ranta sosai, dan ɗawainiyar da ta
fahimci yana yi da qaunarta
Mintunan da
ya ɗauka ba yawa ya fito riqe da leda a hannunsa, murmushi tayi da ta hangoshi
domin haka kawai ta ji daɗin ganin fitowarshi, shi ko sai sauri yake yi yana
dumfaro gurin motar
Wata
budurwace ta tareshi a daf da motarshi tace "Hafeez"!
Kallonta
yayi sannan ya ɗaure fuskarshi ya buɗe mota zai shiga
"Haba
Hafeez, wai me na maka a rayuwane?, masoyi ba zai taɓa zama maqiyi ba, ba fa ni
na ɗora wa zuciyata qaunarka ba, ya kamata ka tausaya min" cewar budurwar
tare da riqe qofar motar, ita tsabar makancewa a So ba ta ga Fareedah ba
Fisge murfin
motar yayi yana cewa
"keh
wai wacce irin mahaukaciyace Nazeefah, na faɗa miki bana sonki, bana sonki, wai
dolene?, kar ki kuskura ki ga fushina, dan in kika cigaba da bibiyata zan miki
rashin mutunci, zuciyata da wacce ta mallake, ki bi wani sarkin"
Yana gama faɗin
haka ya shige motar ya rufeta da qarfi sannan ya fisgeta da gudu ya buɗe
Nazeefah da qura
Fareedah da
take cikin motar tana jiyosu, wani irin kishine ya taso mata mai zafi a qirji,
tuni fuskarta ta haɗe, kamar ba ta taɓa dariya ba
"mene
ne swampy"? Yace yana kallonta ganin yadda take fushi
Harara ta
banka masa ta ɗaukè kai tana cika tana batsewa
Hanu ya kai
zai taɓata ta buge masa hanu ta sake banka masa harara
Murmushi
yayi ya shafa sajensa yana binta da wani irin kallo sannan ya cigaba da tuqinsa
yana murmushi jifa jifa
**
Kwance suke
da misalin qarfe 8:00 na dare, har yanzu fareedah fushi take yi da Hafeez, tun
dawowarsu yake ta bin ta amma ta qi kulashi, kishine kawai yake nuqurqusar
zuciyarta, shi kuwa sai nace mata yake yi yana lallaɓata, dan ko maganin da ya
sake komawa asibiti tambayar likitan kasancewar sun manta, da qyar ya lallaɓata
ta sha
"haba
my TILO, dan Allah ki rufa min asiri ki bar fushin nan, wallahi tallahi bani da
budurwa a waje, ke kaɗai nake so Fareedah, ni naki ne ke ɗaya tal"
A shagwaɓe
tace "toh ya aka yi ka san sunanta"?
"makarantarmu
ɗaya fa Swampy, irin 'yan matan nan ne marasa kamun kai, ai ni ba zan taɓa kula
macen da ta ce tana sona ba, me zan yi da ita, Allah ya sauwaqe, ita ce
wahalalliya da take qin sauraran samarukanta a kaina"
"Allah"?
Ta sake cewa a shagwaɓe
Qanqameta
yayi a jikinsa yace "Allah my Swampy, ke kaɗaice tilo"
Ajiyar
zuciya ta sauke sannan ta lafe sosai a jikinsa tana lumshe idanu ta sake cewa
"Hafeez
ni fa har yanzu hankalina a tashe yake akan cikin nan"
Tsawon
lokaci ya ɗauka shiru sannan ya fara magana a hankali
"ki
kwantar da hankalinki, zan jefa rayuwata cikin matsala domin in samo miki
kwanciyar hankali"
"kamar
yaya Hafeez"?
Cike da
damuwa yace "ki yi duk yadda za ki yi Faeez ya kusanceki idan ya dawo, a
kuma ranar da ya dawo, zan san duk yadda
zan yi ya dawo qasar nan a cikin sati me zuwa, sauran tsarin kuma ni zan shirya
da kaina, amma kar ya wuce sau ɗaya, dan idan ya kusanceki fiye da ɗaya zan iya
rasa hankalina, ko yana nan, babu ke babu shi, zan tsara yadda zamu dinga
kasancewa tare, pls my swampy"
Kafin ta ba
shi amsa wayarta ta fara ringing, shi ya ɗauko wayar, saidai ganin faeez ne sai
kawai ya ajiye ya haɗe fuska, musamman da ya ga sunan da tayi saving nambarshi
da ita, ita ma da ta ga haka sai ta yi lif a jikinsa tayi shiru, haka faeez
yayi ta kira, sai da ya ga dama sannan ya ja tsaki ya ɗaga kiran a zuciye
Bai amsa
sallamar faeez ba yace "ta bar wayar a falone, tana ɗakinta"
Bai damu da
yadda ya ji muryar hafeez ba yace "ok, Hafeez ne?, yah school"?
"lau"
"mashaa
Allah, toh ka sanar mata cikin satin nan zan dawo inshaa Allah, idan na wuce ma
toh next week zan dawo, bari in barka, na ga kamar kana jin bacci, sai
anjima"
Ba tare da
hafeez ya jira faeez ya kashe wayar ba, ya rigashi kashewa ya ja doguwar tsaki
ya jefar da wayar a jikin bango cikin zafin rai ta tarwatse
ISLAM IS MY
IDENTITY
No comments