QANIN MIJI 11
11
Rungume take
a jikinsa bayan sun idar da sallar, zaune suke akan darduma sai kalamai yake raɗa
mata ido cikin ido cikin wani irin salo mai ɗaukar hankali, ita kuwa sai wani
narke masa take sake yi tare da shagwaɓe masa, domin duk da hafeez qanin
mijinta ne amma ya
girmeta sosai
Hancinsu ya
haɗa guri guda yana gogawa yana wani lumshe idanu, ya fara cewa
"my
swampy, ko a mafarki cikin mafarkai kar ki gujeni, ina roqon alfarmarki da
kasancewar tare da ni cikin wannan sabuwar duniyar da kika kai ni a yau da ban
taɓa shigarta ba, ki min alqawarin hakan my reedah, idan ba haka ba zan zauce,
zan zauce reedah...."
Ya qarashe
maganarsa cikin sake tausasa muryarsa mai kama da yana yin raɗa sannan ya fara
kissing ɗin lips ɗinta yana binta da sheɗanin kallo
Irin waɗannan
abubuwan fareedah take buqata daga fa'eez tun farko, tana matuqar son a nuna
mata tana da muhimmanci amma ta rasa hakan daga gurinsa, sai ga shi cikin sauqi
ta samesu a gurin hafeez, dan haka cikin jin daɗi ta sake narkewa a jikinsa ta
qanqameshi ta sanya hanunta a kanshi tana shafawa a hankali idanunta a lumshe
ta ce
"Hafeez
ni ma zan so ɗorewar alaqarmu, ba zan so nisantarka ba"
"da
gaske Swampy"? Yace yana mai ɗago fuskarta kamar zai haɗa da tashi,
idanunta ta zuba masa tana murmushi sannan ta lumshesu ta gyaɗa kai
Kamar zai
mayar da ita ciki haka ya ruqunqumeta yana mai tsantsan farinciki tamkar zai
lasheta sai maimaita mata kalmar I love you my reedah yake yi, ita kuwa tun
tana murmushi ganin haukar murna da sambatun sun yi yawa sai ta fara masa
dariya qasa qasa
Shi ko bai
yi qasa a gwiwa ba ya ɗagata daga jikinsa ya miqe tsaye ya kinkimeta suka koma
bakin gadon da suka baro ya zaunar da ita sannan ya je ya ɗauko ɗaya cikin
ledojin da ya shigo da su ya dawo bakin gadon ya zauna, tana kallonshi ya ciro
wani akwai mai ɗan girma daga ciki ya buɗe, saidai abin mamaki duk girman
akwatin nan, qaramin zobene a cikinsa mai ɗan banzan kyau da qyalli
Zoben ya
ciro daga cikin akwatin ya kama hanunta ya sanya mata zoben, ita kuwa sai
binshi take yi da kallo
Kan zoben ya
sumbata sannan ya kalleta yana mata murmushi yace "wannan zoben na
alqawarine tsakaninmu, ki min alqawarin zaki aureni, bayan kin karɓi takardar
sakinki daga hanun wancan mutumin, sannan ba za ki sake kusantarshi ba, sai ni
kawai"
Dammm ta ji
zuciyarta ta buga, wani irin alqawarine wannan?, cikin zare idanu tace
"Hafeeez...."
Saurin
dakatar da ita yayi da cewa
"ki
cire wancan banzan tunanin a ranki, ki ɗauka kawai nine mijinki a yanzu, duk
wasu hakkokinki sun dawo kaina, na rantse miki da Allah da qani zai iya sakin
matar yayansa da a yanzu ba sai anjima ba zan sake masa ke, daga nan sai ki
zama mallakina, reedah ki sani wallahi tallahi, da zan iya gane namijin quda to
wlh idan ya sauka a jikinki kwanansa ya qare, balle wani qaton banza,
numfashina barin gangan jikina zai yi, haɗiyar zuciya zan yi in mutu, pls
Reedah, kar yarda da shi, ni kaɗai zan iya gamsar da buqatarki"
Cikin
qanqanin lokaci har idanunsa sun yi jajir tare da rawar murya
Cike da
damuwa ta fara magana "Hafeez ni a karan kaina ba zan taɓa neman hakkina a
gurin faeez ba, amma yaya zan yi idan shi ya nemi hakan"?
Cikin zafin
rai da ɗaga murya tare da tsabar baqin kishi yace
"ko shi
ne ya nemeki kar ki kuskura ki yarda, wallahi idan na san ya kusanceki sai na
illatashi"
A tsorace
fareedah take binsa da kallo ganin yadda ya haukace mata, ganin yadda ya
tsoratata ya sanyashi rungumota qamqam a jikinsa ya fashe mata da kuka, yayin
da zuciyarshi take wani irin bugawa tamkar wacce take neman hanyar fasowa daga
qirjinsa ta fito
Qanqameshi
tayi ita ma cikin tausayawa tare da jin wani baqon yanayi ya daki zuciyarta, saboda fahimtar da
tayi cewa ba qaramin so hafeez yake mata ba, ba ta taɓa tsammanin hakan daga
gareshi ba, cikin tausasa murya da rarrashi tace
"Hafeez
dan Allah kar ka cutar da kanka, na maka alqawari zan kiyaye duk wani abu da
zai sanyashi kusantata, hakan ba za ta faru ba ma inshaa Allah, ka ji, dan
Allah"
Bai iya
magana ba, sai shiru da sauke ajiyar zuciya yayin da ita kuma take ta
rarrashinsa ta hanyar masa waɗansu abubuwan na musamman, a haka ta samu ya
sauko ya ɗago daga jikinta ya zuba mata idanu yace cikin marairaice murya
"ina sonki my swampy"
Murmushi ta
masa ta kashe masa idanu tace "me too my Hafeez"
"ina
godiya" yace tare da lumshe idanu, bin sa take da kallo sai can ta ja
yatsun hanunsa tace "my hafeez in tambayeka"?
Buɗe idanun
yayi ya zubasu a kanta yace "girmankine, mene ne tambayarki my
swampy"?
Sai da ta
luguiguita maganar sannan cikin jin kunya tana aika masa da wani irin kallo
tace
"ka taɓa
kusantar wata mace"?
Yalwataccen
murmushine ya faɗaɗa a kan fuskarsa sannan yace
"kafin
swampy ban taɓa kusantar wata qazama ba, kuma a bayanta na haramta kaina wa
mata"
Yadda take
kallonsa sai ya ga kamar ba ta yarda ba, dan haka ya dafa kafaɗarta yace
"na
rantse da Allah, ban taɓa kusantar wata mace ba kafin yau, wallahi, tallahi, ke
kin san halina, ba zan iya faɗin qarya ba"
Nannauyar
ajiyar zuciya ta sauke, ba ta san me yasa ba, amma maganar ta mata daɗi matuqa
***
Tun daga ranar
Hafeez da Fareedah suka buɗe sabon babin rayuwa tamkar mata da miji, har sun fi
wasu ma'auratan ma, tare suke kwana suna aikata mashaarsu, ko su kwana a ɗakinta
ko kuma a ɗakinsa, duk yadda dai suka so, haka suke aikatawa, cikin qanqanin
lokaci kowannensu ya canza, Hafeez sai
wani haske yake yi da qiba yayin da Fareedah take qara cikowa tare da
sheqi da walwali, kowa ya ganta sai ya furta, sannan walwalarta ta wuce na baya
tare da kazar kazar ɗinta
Haka Faeez a
can qasar ya cigaba da holewarsa da Tina, duk da ya kammala abin da ya kaishi
can tun a wata ukun amma ya qi dawowa, sai online meeting da yake kiran
ma'aikatansa daga can ya isar musu da duk abinda yake da buqatar sanar musu,
daga qarshe ma ɗaukar Tina yayi suka fara bin qasashe hutawa da jin daɗi, yayin
da ya daina waya da su fareedah sai an yi sati ya kira sama sama yace aikine ya
masa yawa, su ko dama babu mai nemanshi cikinsu, rayuwarsu suma suke yi ba tare
da suna tunashi ba, ko hirarsa ba sa yi, idan ma ya kirasu kowanne cikin nuna
rashin kulawa yake amsa masa wayar, wani lokacin kafin ya ajiye wayar sun
ajiye, musamman Hafeez, dan ko fareedah ya kira matuqar suna tare idan ya
fahinci maganar za ta yi nisa sai kawai ya karɓe wayar ya kashe ya haɗe
fuskarsa, ita kuwa farinciki hakan yake sakata sai tayi ta rarrashinsa da daɗaɗan
kalamai masu tafiyar masa da zafin kishin daga qirjinsa
**
Kwance suke
da safe a kan gado, yau watansu guda da kwana ashirin da shiga duniyar jin daɗinsu,
duk da yau Hafeez yana da makaranta amma ya kasa tafiya saboda damuwa na Zazzaɓin
da fareedah ta tashi da shi mai zafi, duk da an fi sati zazzaɓin na damunta
amma bai yi zafi irin na yau ba, hankalin Hafeez a matuqar tashe yake gaskiya,
ji yake kamar ya zubar da hawayen tausayin Swampyn tashi
Cike da
damuwa da rarrashi ya fara magana
"my
love dan Allah ki yarda in kaiki asibiti, ba zan iya samun nutsuwa ba sai na
tabbatar da cewa zazzaɓin nan ya bar jikinki, ke kanki kin sani"
Jikinta na
rawa ta yi magana a shagwaɓe
"ni dai
ka barni kawai a gida ka je ka sayo min magani"
"a a
Reedah, dole in kaiki hospital, ba zan yarda da self medication ba, mu je in
miki wanka ki ji qarfin jikinki sai ina samar miki abin da za ki ci kafin mu
tafi"
Bai jira
amsarta ba ya tashi ya ɗagota tana masa kukan shagwaɓa haka ya qyaleta ya je ya
mata wanka shima yayi sannan ya je ya haɗa
mata abinci mai sauqi ya zo ya ba ta ta ci sannan ya shiryasu suka fito yana
riqe da ita, sai da ta ga sun zo falo ta qwace kanta daga gareshi tana turo
baki, dariya kawai ya mata ya wuce ɓangaren mai aikin da ba ta cika shigo musu ɓangarensu
ba saidai in su suka nemeta, abinci ma ita take yin nata a can
Umurnin
gyara gidan ya bata yana hararanta dan a ganinshi tana barin fareedarsa da aiki
da yawa, cikin tsoronsa ta amsa tare da miqewa tsaye, shi ko yayi tafiyarsa
abinsa ya dawo gurin fareeda ya sakar mata murmushi sannan suka fice
*
Zaune suke a
gaban likitan da ya sa aka wa fareedah gwaji daban daban dan gano ainahin
matsalarta, sun nutsu sosai suna sauraronsa yayin da yake karanta result ɗin, ɗago
kansa yayi yana murmushi ya fara magana cikin baiwa irin tasu ta likitoci
"sakamakon
farko ya nuna akwai typoid amma ba mai yawa ba, sakamako na biyu kuma sai ka
ban goron albishir" ya qarashe yana sake yalwata murmushinsa
Dam dam
qirjin fareedah ya buga amma hafeez yalwataccen murmushi yayi yace "Dr
name your price, ko nawane zan baka a matsayin goron albishir, faɗa min kawai,
mene ne"?
Murmushi
likitan ya sake yi ya ce "yanzu haka, matarka tana ɗauke da cikin wata ɗaya
da sati biyu, gaskiya congratulation, zaku haifo zallar kyau matuqar zai gaje
siffofinku"
😳khutmelesee fans idan kune a matsayin
Hafeez da Fareedah yaya za ku yi?
ISLAM IS MY
IDENTITY
No comments