NIDA AMARYATA 5 & 6
5⃣-6⃣
Kallonsu gaba Daya suka maida ga
Nihila,wadda ita ko a jikinta,illah ma suburbudar abincinta data ci gaba
dayi,banda harara babu abinda Alhaji sani ke aikawa yaran,hakan yasa kowannensu
ya gaggauta yin breakfast din,sannan suka mike tare da yiwa mamansu sai sun
dawo,addu'a tayi musu suka fice suna amsawa da ameen.
Kamar kowa
jira yakeyi su fita,aka hau rige-rigen magana tsakanin su uku,Amma kafin tasu
ta fito ta Nihila ta Riga ta kowa,hakan yasa sukayi shuru,aikuwa sai ji sukayi
tace,
"Allah
ko baba,dazun Nan abinda kaimin Saida naita Jin kunya,danma dai Aunty hama tace
Wai inka tabani Kar inyi maka musu wallahi da cewa zanyi Kai Dan iska ne,Amma
fa bakaji bakinka ba sai kamshi yakeyi,Kuma daka...."shut up! Ya fada
cikin daga murya,you are very stupid,ya karasa maganar kamar zai maketa,Nihila
dako alamar tsoro Bata Nuna ba illa ma kurbar shayinta da takeyi,sabanin Hajiya
Hafsa,da duk jikinta ya hau kyarma sanin halin Mai gidan,tana son yin magana
Amma tana tsoro ganin yadda mud dinshi ya canza,zuwa ainihin yadda ta sanshi.ji
tayi Nihila tace,"Allah baba ka fiya masifa,nifa ko'a gida Naga Aunty hama
na fada dariya take bani,Dan sai Inga tayi wani Muni,kamar namijin alade,Kai
Kuma fa yanzu baka ganka ba kamar namijin bauna......Tau..tasss...ya dauketa da
wasu tagwayen mari,Wanda Saida suka Sata wuntsilowa daga saman kujerar,Bata
Gama tantance kanta ba,taji Yana fadin,
"Ke Ni
sa'an ubanki ne,Naga alamar bakida tarbiya ko? Dan Kinga na kyaleki? To na daga
Miki kafa ne kawai Dan kina matsayin bakuwa,Kuma nayi tunanin ke din irin wadda
nake so ce,Ashe sabanin hakan ne,daga yau sai yau,duk ranar Dana Kara ji ko
Naga kin Fadi magana Akan wani Abu tsakanina dake,wallahi saina fasa Miki
baki...Bai Gama rufe baki ba sai ji yayi katsam a bakinsa,Bai Gama tantancewa
ba,yaji ta Kara buga Masa flak's din shayin dake kan dinning din,wani jiri
yaji,yayin daya Fara ganin bibbiyu,a
yanayin dayaga tayi tsalle Tayo kansa,in beyi karya ba zai iya cewa ganin ta
yayi kamar jackie Chen,ji yayi ta Dane wuyansa tare da sakar Masa gula a dukkan
kumatunsa,Wanda yasashi zubewa luuuuu kamar Dan maye, ita ko tamkar 'yar
takwando ta dire kasa.Hankali a tashe Hajiya Hafsa tayi kansa tana Kiran
sunanshi,ai kawai sai Jin kukan Nihila tayi a bayanta,Koda ta waiga sai ganinta
tayi kwance kasa tanata birgima tare da bare baki tana ihu iyakar iyawarta.Gaba
Daya Hajiya ta rasa inda zata Sa ranta,ai itama saita sa kukan tare da shigewa
daki kawai ta barsu anan.Tana shiga ta Danna wayar family doctor dinsu ta
kira,Yana dauka ta fashe mishi da kuka tana fadin yazo gidan ba lfy!,cikin
tashin hankali yace mata gashi Nan zuwa.
Alhaji Daya
Zama kamar Dan kwaya,Wanda kukan Nihila ke kokarin dawo dashi hayyacinshi yasa
shi dagowa da kyar,duk da jirin dayake ji,Saida yayi kokarin mikewa ya zauna,tare
da jingina da jikin kujera.
Lokacin da
likita ya karaso da hanzari ya shiga gidan, sakamakon jiyo ihu da yayi,ko masu
gadin gidan da sauran ma'aikata abinda ya hanasu zuwa Dan sunada Dan nisa da
anihin cikin gidan,Kuma suna kokonton kamar ba daga ciki ihun ke fitowa ba,Dan
haka sukayi yi zamansu.
Yana shiga
falon da Nihila ya Fara cin karo tana birgima.
Subahanallah!
Ya furta,tare da karasawa inda take Dan Jin mi aka mata,Yana shirin tabata yaji
an tunkudeshi,cike da mamaki ya waiga
Dan ganin me wannan karfin halin,ganin Alhaji tsaye akanshi Yana huci,ga
bakinsa Daya d'an tasa,yasashi Kara shiga mamakin.
Ji yayi
Alhajin na fadin,Kai bakada hankali ne da zaka tabata? Ko an fada maka Nan
gidan 'yan iska ne? Ya fada cikin tsawa,tare da rike kanshi dake barazanar
tarwatsewa.tsawar da yayi ne yasa Hajiya fitowa,yayin da ita kanta sarauniyar
kukan ta mike tana kallonsa.
Doctor da
mamaki ya Kara cika sa, Saiya maida kallonsa ga Hajiya Don neman Karin bayani.
Cike da
takaici hajiyar tace, ai dama kayi tafiyarka doctor,tunda naga harya Sami
sauki,tunda har yasami zarafin yin fada Dan an taba 'yar cikinsa wadda yake
fadin amaryarsa babu ko kunya.
Shi kanshi
doctor ya girgiza da Jin Wai Nihila ce matar Alhajin,duk da jikinta Bai Nuna
shekarunta ba,Dan tsab za'a iya Mata aure ta zauna ba Kuma anyi la'akari da
cewar yarinya bace,kawai abinda ya daure Masa Kai shine,a shekarun
Alhajin,Wanda ya zuwa yanzu ai Bai kamata ace Yana auren kamar wannan ba.Ganin
duk sun tsaya suna Masa wasu surutan banza,yasashi cewa doctor ya fice Masa a
gida,baya bukatar taimakon.dole doctor ya fice din kamar yadda Mai gidan ya
bukata.Hajiya na Shirin yin magana ya dakatar da ita ta hanyar daga Mata
hannu,dole taja bakinta tayi shuru.
Itako Nihila
ganin Alhaji sani ya tsareta da ido,yasata Kara kwabe fuska,Dan inta tuna Marin
daya yi mata,saitaji kamar taita cizonshi,Dan ita tunda suke da Aunty hama Bata
taba Koda yimata fada ba,bare Kuma duka,Dan haka tana kallonshi,ta furta
wallahi Allah ka isarmin.kallonta duka sukayi, shikuwa Alhaji ya Nuna kanshi da
yatsa tare da fadin "Ni kikewa Allah ya Isa?"
"NI
bada Kai nake ba,da bangon can nake",ta fada tana Nuna bayanshi.
Sallamar da
akayi ce tasasu fasa maganar da sukayi niyya daga shi har hajiyar.
Da gudu
Nihila ta karasa ta rungumeta,tare da fadin, oyoyoo,Aunty hama,shine kikacemin
da asuba zakizo kimin wankan Dan in fito Ina kamshi,shine baki zo ba,sai Kuma
tafara hawaye,tare da fadin,gashi Nan kin kawoni gidan mugaye sai dukana
yakeyi,da yi min fada.
Aunty ham ko
Gama ji batayiba ta Kara maimaita kalmar duka?
"Duka
fa kikace?
Gyada Kai
Nihila tayi,tare da Nuna Mata gefen fuskarta da yayi ja.
Aikuwa take
Aunty hama tacire hijabi tare da cin damara,ta Fara fadin Ashe ko yau da
bala'i,na rantse da Allah saina Rama Mata,daga auren jiya-jiya ka kamamin ita
da duka,duka nawa take,yarinyar da badan ta yaye kanta ba da Ina kyautata zaton
da yanzu tana Shan nono,ko an yayeta da ba'a Dade ba,Nan lokacin daka gani kana
so ba irin 'yar murya da bakayi,shine daga ganin an aura maka ita,zaka Fara
jibgarta Ani ban San namijin duka bane Kai da mezai Kai ni baka auren hantar
'ya'ya.wallahi yau saika San ka tabata Dan koka biya Marin da kayi Mata ko Kuma
wallahi inta jibagarka kamar an aikoni......
Tabdijam,shin
Wai ku tayani kallon Alhaji da Amaryarsa,shin wace iri ya dauko?
Alkalamin
khady ✍
No comments