BARIKI NA FITO (BOOK 2) 11
BOOK 2
PAGE 11
Dariya
bariki tayi tare da fad'in, amma ina tsoran irin fushin da Yarima zaiyi, Wlh
ban son inga ya shiga wani hali, bazan iya jura ba, ina sonshi da yawa.....
Habib yace
Toh fah, yau Ina ganin bariki.... Toh
yanzu dai Mai kika yanke....??
Bariki tace
abunda kuka fad'amin dashi zanyi aiki, ranan da aka d'aura aurenmu aka kaini
ranan zan fad'ama Yarima gaskiya.....
Habib shewa
ya saki tare da fad'in Aiko ki tabbatar kin fad'a mishi tun Kafin ya shiga yaji
ya shige zirif kaman bakin gate.....
Bariki duka
takai ma habib iya karfinta tare da fad'in rafi ne ba gate ba
Habib ya
ri'ke wajan da takai Mai duka yana fad'in na shiga uku zata kassarani..... Amma dai kekam bariki baki da mutunci yanzu
ki takarkare iya karfinki ki sakan min wannan uban dukan yanzu inda kin sameni
a wajan nono Nafa? Bayan kin San sarai ance a nan rayuwar mace take, salan kije
ki kasheni Banyi aure ba naji yanda ayabar nan take ba......
Bariki tace
andai yi Asara
Habib yace
ke kikaga Asara bani ba
Umman bariki
tace kudai dingayi a hankali Kun San Gidan mutane, yanzu sai su kaimu gaba....
Habib yace
gaskiyanki domin naga matar can d'akin ta kusa daku Tana min wani kallo wanda
ban gane ba, inta karamin sai na mata rashin mutunci in cire kaya mu daku Dan
ban son iskanci....
Suna cikin haka Yarima ya kirata tare da
fad'in baby come out Ina waje.....
Tashi tayi
tana fad'in bari inje inga Yarima na.
Habib yace
oh kunga salo a gayas....
Fita tayi
tana fad'in kaji dashi.....
Motarshi ta
nufa tunda ta fito idonshi ke kanta harta karaso ta bud'e motar ta shigo ciki
tare dayin sallama....
Amsawa yayi
tare da fad'in my princess na gaji, tunanin driving nakeyi in zan koma
Gida.....
Kallonshi
tayi tare da fad'in ko in tu'ka ka, in kaika gida??
Yace dakin
taimaka min kuwa
Dariya tayi
tare da fad'in kaman dagaske....
Yace dagaske
nake mana Kinga Idan kikaje can saiki zauna kin zama matata babu dawowa....
Hannu tasa
tare da rufe fuskanta tana dariya
Yarima kiran
sunanta yayi da Zainab.....
Da sauri ta
d'ago ta kalleshi domin jin ya kira sunanta daka gani magana zai Mata Mai
muhimmanci.... Wanda yake bukatar natsuwanta
Yace d'azu
kina son Yimin magana Ina jinki yanzu....
Murmushi
tayi tare da fad'in Yarima a kullum Ina tsoran fad'a maka cewa ni dakai bamu
dace ba, saboda kai ka fito gidan girma ni kuma ba y'ar kowa bace ina tsoran
auranka domin gudun wulakanci irin na mas......
Da sauri
yasa hannunshi a bakinta ya rufe Mata, tare da fad'in enough, dama duk wannan
nonsense din kike son fad'amin shine kike d'agamin hankali?..... D'an tsaki
yayi alaman jin haushi tare da kawar da kanshi gefe.....
Ganin ranshi
ya baci yayi banza da ita, yasa ta d'ago tana mishi magana Yarima kayi hakuri,
ban San zakai fushi ba.....
Katseta yayi
da fad'in Zainab ban taba tunanin zaki
dinga irin wannan tunanin ba.... And kina ma sona kuwa????.....
Da sauri ta
kalleshi tare da fad'in Yarima baki bazai iya fad'in irin sonda nake maka ba,
how I wish in bud'e maka zuciyata Kaga irin sonda take maka..... Yarima Ina Sonka yanda baka zato duk wani
jini dake gudana a jikina yana gudana ne da Sonka I..... Da sauri tayi shuru ganin yana kallonta.....
Jin tayi
shuru yasa ya ru'ko mata hannu tare da fad'in Zainab are you sure akan abunda
kika fad'a??
Kai ta d'aga
Mai alaman eh
Wani irin
murmushi ya saki cikin jin dad'i, tare da fad'in nace zan baki albishir d'azu
right?
Tace eh
Hannunta ya
saki tare da fad'in ina goran albishir din???
Dariya tayi
tare da fad'in zan baka in naji albishir din
Dariya yayi
tare da fad'in promise?
Tace yes I
promise....
Yayi
murmushi tare da fad'in mai martaba ya amince da maganan aurena dake.... But at first yace in Bari nan gaba tunda ban
dad'e dayin aure ba.... Daka baya kuma ban San mai yasa ya canza ra'ayi ba yace
za'a turo gidanku ayi magana d'azu waziri yake fad'amin May be cikin week
dinnan a turo......
Bariki gaba
d'aya komai nata ya tsaya ta rasa mai takeji murna take ko akasin haka??? Gaba
d'aya ta kasa ganewa gadai ta nan ne dai....
Ganin tayi
shuru yasa Yarima ya kura mata ido tare da fad'in lafiya kuwa my princess?
Kodai you are not happy ne dan za'a turo??
Da sauri
tace a'a am so much happy tare da sakin murmushi....
Ganin ta
saki jiki yasa Yarima jin dad'i sun dad'e suna fira sannan Yarima yace Zai tafi
tare da bata wani Leda Wanda bata san ko miye a ciki ba....
Amsa tayi
tare da fad'in ngd
Hancinta
yaja tare da fad'in sai munyi magana.....
Tace OK tare
da fita tayi cikin gida,.... Tana shiga
habib ya amsa ledan tare da fad'in Allah yasa Abun ciye ciye ne dan Wlh yunwa
nakeji tun safe babu abunda naci....
Su turare ne
Arabian perfumes masu shegen kamshi da kud'i a ciki.... Habib d'aukan kud'in yayi dubu d'aya d'aya
bandir biyu, dubu d'ari biyu kenan.....
Yace Kai Yarima akwai kyautar girma....
Uwar bariki
ta Karya tace ai gidan sarauta ya fito dole ya dinga kyautar girma.... Domin da
suji kunya gwara dukiyarsu ta k'are....
Bariki
kallon uwarta ta bariki tayi tare da fad'in mai kuke cine Wai??
Ummanta tace
abinci nake dafawa wani zubin kuma kowa ya siya...
Bariki tace
toh yanzu tunda nazo inyi sati d'aya nan sai a fara girki kullum, kallon habib
tayi tare da fad'in muje muyi cefane mu dawo......
****
Tsakanin
haulat da farhan soyayya ta shiga Sosai tun Haulat na nuna bata so harta yarda
domin tana sonshi kuma uwa uba farhan ya iya nuna ma mace kulawa tare da
kalamai masu dad'i da kwantar da zuciya......
Sai dai abu d'aya haulat da yake damunta shine tasan dakyar Hjy habiba
ta yarda d'anta ya aureta ..... Sai dai haulat din tana ganin in bata yarda ba
kaman ta nuna mata rashin adalci, and inma ta yarda ta auri d'an nata ya zasu
dinga yima juna kallo........
Farhan ne
zaune a falo shida mahaifinshi domin yana kasar.....
Farhan ya
kalli dad dinshi yace dad I find someone dat I wanted to marry......
Kallonshi
mahaifin nashi yayi tare da fad'in farhan aure Bayan baka kammala karatu ba
Yace dad Ina
final year ne, Ina son a fara magana b4 in Gama....
Dad din
nashi ya kalleshi cikin son gudan d'an nashi yace why are u so rush to marry??
Yace dad
just
Dad din yace
ok but wacece yarinyar and Waye mahaifinta??
Farhan yace
sunanta haulat mum tasan ta domin at tym Tana kwana gidan na......
Muryan hjy
habiba sukaji tana fad'in karyanka Wlh koda zaka mutu bazan bari ka aureta ba,
gwara ma kabar wannan maganan.....
Mijin hjy
habiba ya kura mata ido tare da fad'in akan wani dalili?? Har kike kiran koda zai mutu bazaki Bari ya
aureta ba?? Kin kuwa San abunda kike fad'a kuwa? D'an nawa kike ma fatan
mutuwa??..... Toh let me tell you Wlh
Indai Inada rai kuma yana Sonta dole In tsaya mai.....
Tace ni kuma
ban amince ba domin bai dace da ita ba....
Mijin nata
yace habiba akan wani dalili? Miye rashin dacewan? Kallon farhan yayi tare da
fad'in naji kaman kace yarinyar tana kwana a nan wani zubin....
Farhan yace
eh dad
Kallon hjy
habiba yayi tare da fad'in na tabbata inda yarinyar tana da aibu bazaki kawota
gidan nan ta kwana ba, harki kasa fad'amin, domin naga Idan kikai ba'ki kina
fad'amin but baki fad'amin wannan ba, ina son ki sani kaman farhan ya aureta ya
Gama Indai Allah yasa matarshi ce babu yanda za kiyi.....
Hjy habiba
tace ni kuma Indai har Ina numfashi kuma ni na haifeshi ban yarda ya aureta ba,
kuma bazan taba yarda ya aureta ba....
Dad din
farhan yace habiba Ina son ki fad'amin dalilin da yasa bakya son ya aureta??
Tace hakanan
kawai ban son ya auri yarinyar
Dad din yace
you are not serious.... Tare da kallon
farhan yace inka kammala karatunka I promise zan tsaya maka har sai ka
aureta.... Yana fad'in haka ya haura
sama Fuuuuu tare da fad'in rabo dai yana kisa.....
Kallon
farhan hjy habiba tayi cikin bacin rai tace wato ni ban isa bako?? Ka kyauta
amma ba laifinka bane.... Itama fuuuu tayi sama
Farhan d'aga
kafad'a yayi tare da fad'in whatever nidai Ina Sonta kuma tunda dad ya tsayamin
banda damuwa..... Fita yayi yabar gidan
***
Yarima Aliyu
ya fara aiki a asibitin shi, sannan an fara gina Mai filin da Mai martaba ya
bashi, da yake filin k'ato ne ko wacce za'a Mata gefenta ginin gidan sama, da
yake akwai kud'i an d'iba ma'aikata da yawa suna aikin domin Yarima yace nan da
wata biyu ko uku yake son a Gama duka ginin.....
Yarima ya
dawo gida yau ko wajan Zainab bai samu ya biya ba, kaman yanda Ya sabayi
kullum, domin ya gaji, yana shiga cikin falo gimbiya zinatu ta taso Tana kuka
tare da fad'in Yarima jita jitan da naji gaskiya ne???
Kallonta
yayi sannan ya kauda kai gefe tare da fad'in fad'amin abunda kika ji coz am
tired, I need to rest....
Cikin kuka
mai sauti tace Yarima naji ance ginin mata biyu kakeyi zaka K'ara aure......
Yarima Aliyu
murmushi yayi tare da fad'in gaskiya aka fad'a miki.....
Wani irin
ihu ta saki mai kara tare da fad'in Wlh bazan yarda ba, ai wannan cin fuska ne
yaushe ka auroni saboda rashin adalci ka Fara maganan k'arin aure, ko wata
d'aya Banyi ba amma kake fad'amin zaka K'ara aure Wlh baka isa ba.....
Yarima Aliyu
kallonta yake cikin bacin rai, domin ya tabbata ihun da takeyi kuyanginta suna
ji.... Dan haka ya wuce ba tare daya kulata ba.....
Ganin haka
tabi bayanshi Tana fad'in ai dole ka wuce wlh Yarima bazan yarda da rashin
adalci ba har d'akinshi ta bishi tana surutai....
Yarima kam
ko kallo bata isheshi ba, toilet ya fad'a Ya barta nan tana ta surutai kaman
zararra
Bayan yayi
wanka ya fito daka shi sai towel yana goge kanshi, tashi tayi ta nufeshi tare
da rungume shi tana kuka tana fad'in Yarima dan Allah ka tausaya min bana son
kishiya Yarima Ina kishin ka, maina rasa da kake kokarin K'ara aure, ko wata
d'aya Banyi a gidan nan ba amma har kana maganan aure...... K'asa tayi tana kuka mai ban tausayi.....
Jikin Yarima
Aliyu yayi sanyi tare da tausayinta....
Gimbiya dake k'asa tana kuka ganin kaman jikinshi yayi sanyi taji dad'i
dan dama tasan za'ayi hakan.....
D'agota yayi
tare da fad'in zinatu kiyi hakuri, ki d'auka komai kaddara ne, komai ya faru da
bawa ki d'auka wannan auren da zan kara a matsayin kaddara......
Tureshi tayi
tare dayin baya tace babu wani kaddara....
Karka kara cewa kaddara akwai abunda ba kaddara bane mutum shike sama
kanshi..... Duk namiji inya tashi aure
saiya dinga amfani da wannan Kalman kaddara kaddara ban yarda da wannan
kaddaran ba....
Yarima Aliyu
yace baki da ilimi baki san addini ba, so banda time din in tsaya ina bata
bakina wajan yi miki bayani...... Kaya
ya fara kokarin sawa.....
Ta Fara zunduma ihu tare da fad'in Wlh baka
isa ba ,ni nafi karfin wulakanci, sai dai ka zaba cikin biyu koni ko wacce zaka
aura..... Ni Wlh bama laifinka bane na
iyayenka ne da suka d'aure maka gindi kake son yin wannan rashin adalcin sune
munafukai marasa tsoran Allah d.....
Tas ya sauke mata Mari da sai da yasa ta dawo cikin hayyacinta......
Ri'ke wajan
tayi domin Marin ya shigeta Sosai...
Yarima Aliyu
yace you cross your limit kije na sakeki saki d'aya bazan zauna da macen da
zata zagi iyayena ba koda da wasa......
Gimbiya
zinatu tace saki?? Yarima kasan Mai ka fad'a kuwa? Ka manta cewa babu saki
tsakanin mu koda kuwa maina maka saika kamani da laifin Zi......
Yarima yace
keep quiet, wannan ne dalilin daya baki daman kiyi min komai saboda bazan
sakeki ba?ciki harda raina iyayena? U r wrong, al'ada ba addini bace, you better leave this place tun Kafin in miki
abunda za kiyi mamaki na Iletered ....... Tashin hankali🙆 Yarima Aliyu ya karya dokan masarauta koya zata kaya
muje zuwa........
plz masu min
magana ta messenger kuyi hakuri ku daina saboda bani da messenger na goge
facebook kawai gareni shima saboda posting ne, duk mai son magana dani yaje
page dina yamin magana zan gani Inba mutum amsa, amma in a messenger ne zan
gani babu daman bada amsa, dan na goge
MARYAM OBAM
No comments