DOCTOR NA'IM 6
Page 6⃣
Family koki
family ne Wanda suka shahara ta bangaren ilimin addini. Kusan daukacin iyalan
wannan gida mahaddata alkur ani ne.
A tsarinsu
Sam b batun boko, ammn ynx d yk abin yazo d zamanie dole alhaji ibraheem yabar
yayan shi maza suyi karatun. Alhaji Ibrahim shine babba a gidansu, sai kuwa
kaninshi Abubakar Wanda su kadai iyayansu suka haifa. Ba shahararrun masu kudi
bane ammn suna d rufin asiri dai dai gwargwado. Alhaji Ibrahim yayi auran shi n
fari kafun dg baya kuma ya karo wani auran. Hadizatou itace uwar gida sai rafi
ah kuma itace amaryah. Rayuwar gidan rayuwace wadda aka shinfidata bisa tsari
irin n addinin islama, kasancewar me gidan ma abocin ilimin addini ne.
Hadizatou ita ta haifa mishi yaya takwas ammn biyu sai rasu sai shida a cikin
yayan nata akwai. Ibrahim shine babba Wanda yaci sunan mahaifinshi ( abbansu
saleem kenan) sai Ahmad ( mahaifinsu
na'im kenan). Mukhtar shine n uku Wanda y xamo shine mahaifinsu abbas
Auwal kuma shine n hudunsu. Yayanta
mata biyu, maryam d surayya.
Wannan kenan, bangaren rafi ah kuwa yayanta
hudu, uku maxa mace daya. Akwai usman, aliyu d kuma nazifi sai macenta daya
rahama
Duk yayan gidan Kansu a hade yk. Bazaka
taba banbance yan can dakin ko yan nan ba, komansu tare suke gwanin burgewa.
Kasancewar zamany y ci gaba su b iya ilimin
addini kadai suka tsaya b sun hada dana boko. Ibrahim yayi karatun shine a
bangaran kasuwanci yayinda Ahmad kuma yy nashi a bangaran likitanci. Sauran
kuma duk professors ne d yan kasuwa. Ibrahim yy auran shine anan garin katsina
kuma dai dai gwargwado yana d rufin asirinshi bawai kudi ainun dinnan ba.
Ibrahim yaso hada Ahmad auran xumumchi d
yar kaninshi sai dai kash ko lokacin yaxo d maganar ni'imatullah.
Ni ima yar asalin garin kano ce. Sun hadu
ne sanadiyyar wata rana data rasa mota gashi anyi ruwa, ta dawo dg makaranta
aikin jinya sanye d farin uniform irin na likitoci
Dg taimako soyayyah mai karfi t shiga
tsakaninsu. Ahmad Sam bai dogara d aikin likitancin dy ke ba yafi maida
hankalinshi akan bangaranshi n kasuwanci. Dg karshe ma y hakura d aikin gaba
daya y jirkita ban garan dayafi kwarewa. Kusan b mazauni bane yau yana wancan
kasa gobe yana waccan yayi kudi sosai t yadda har ta n kewaye dashi suna
hutawa.
Toh d farko
mahaifinshi y nuna sam bai yadda d auran shi d ni ima b, ammn dg karshe d
mahaifiyarshi ta zauna tayi mishi gamsashshen bayani sai y amince
Bayan auransu a garin kano y ajiye ta,
yakan xo duba mahaifanshi d yan uwanshi lokaci bayan lokaci
Ni ima taci gaba d karatun ta n likitanci d
taimakon Allah d taimakon Ahmad. Cikin ikon Allah t karasa karatun ta ta xama
cikakkiyar likita
Ni ima mace
ce mai hakuri g taimako hk xalika tana d matukar tausayi. Marainiya babanta y
rasu tun suna yan yaara don hk suka taso karkashin kulawar amminsu, su uku ne a
gurin iyayensu itace babba sai kanwarta sumayya da kuma kaninsu sadik.
Ahmad mutum
ne dayake dason yara gashi ynx kusan shekararsu nawa d aure tare d ni imarshi
ammn har ynx haihuwar ta shiru. Hkn b karamin dg mata hnkl yayi b, ganin hkn
yasa shi y boye tashi damuwar don kwantar mata d hnkl. Ni ima tasha shawartar
Ahmad d ya karo aure tunda ita har ynx bata haihuba, ammn sai ya nuna mata shi
Sam baya so. Ana hk matar Ibrahim t haihu, murna a gurin ni ima ba a cewa komai
koda taje ganin baby sai d tayita kuka tace don Allah ta batashi. Fa'iza kuwa
tayi mata alkawarin indai t yy shi xata bar matashi kyauta. Ranar suna yaro
yaci sunan saleem
Watanni
kadan d haihuwar saleem kakansu ibraheem y kwanta ciwon ajali. Hakika rasuwar
alhj Ibrahim t gigita hnklin daukacin iyalin dk cikin family koki. Tun dg nan
kuma Ibrahim y xamo shine kamar uba g iyalin duk wani taro d komai a gidan shi
akeyi duk da ba wani kudi ne dashiba.
Muktar ma ya samu matarshi Fatima sunyi
aure. Ana hk kuma ni imatullah ta fara rashin lfy, wanda ita kanta batasan
abinda yk damuntaba. Ahmad y futa d ita dubai don a duba lfyr ta, anan ne
likitoci suka samu damar gano cikin dk jikinta wanda yy wata shida b tare da
ita kanta tasan dashi b, murna a gurin Ahmad ba a cewa komai
Watanni
kadan kuwa t haifi santalelen danta me kama da ita sak hatta farar fatar kuwa.
Ahmad yy alkawarin muddin ta haifi mace to sunan ta zaisa sai gashi kuma ta
haifi mace duk d hk sai daya sanyawa yaron sunan na'im. Kamar yadda fa iza tayi
alkawari kuwa hk tana yaye saleem ta barwa ni ima shi
Ni ima b yan uwantaba hatta patients dinta
suna jin dadin xama d ita Ahmad yaso iyayen nashi su dawo gurin shi d zama sai
dai Sam sunce baxasu dawo gidan surukai ba abin kunya m kenan
Shekarar ni ima bakwai d haihuwar na'im ta
samu wani cikin murna ba a cewa komai. Xuwa lokacin na'im d saleem sun soma
nisa a karatun d sukeyi n Arabic a tsarin iyayen biyu basa son karatun boko mai
xurfi
Cikinta n
shiga wata n bakwai suka rankaya dukansu suka tafi england a cewarsu sai ta
haihu xasu dawo. Sai dai wani abu y kawo musu tsaiko Wanda ko bayan data haihu
baxata samu damar dawowa gida Nigeria b sai nan d kusan shekara daya. Ahmad y
dawo dasu naim Nigeria gudun kada karatun su y tsaya, a gurin ammi aka barsu
yayinda ita kuma ta zauna a england d kyakywar diyarta wadda taci sunanta wato
ni imatullah ammn suna kiranta d sunan neehal
Cikin
shekaru uku rayuwa tayi musu dadi d rashin dd. An samu mummunan sabani tsakanin
hadizatou d abokiyar xamanta Wanda hkn y kawo rarrabuwar kawuna
Kowa y kama nashi guri a tsakanin yayan
gidan. Ahmad y siyawa Ummn su gida anan kusa d Ibrahim tana zaune y kara kaita makka a karo n kusan
Biyar kenan
A cikin
shekararda naim suke gab d kammala Junior a makarantarsu t qur anic
memorization a wannan lokaci ni ima ta kwanta ciwo.
Wanda tasha fadawa Ahmad a duk lokacin
dayazo asibitin cewa mutuwa zatayi y gafarta mata.
Ahmad yakan shiga tashin hnkl a duk
lokacin dayaji furucin matarshi gareshi sai dai shima yana nuna mata muddin ta
mutu to shima y mutu b abinda ya rage masa a fadin duniya don hk bb abinda xai
zauna yy
A ranar wata
juma ah ranar d daukacin family koki vaxasu taba mantawa d ita b ranar data
xamo silar rugujewar duk wani farin ciki nasu domin kuwa a ranar ne ni ima ta
amsa kiran mahalicci. Akan idon Ahmad ni ima ta daina numfashi. A take anan
shima y yanke jiki y fadi sai gawarshi aka daga
Allahu akhbar rayuwa naim hauka ne kawai
baiyiba. Kusan yadda t shagwabashi komai ita takeyi mishi hatta abinci wani
lokacin ita take xama d kanta tayi ta basu a baki har sai sun koshi, naim d
saleem dukansu sun shiga rudanin rayuwa. Tun dg rasuwar iyayenshi naim y
tabbatar y rasa farin cikin shi kenan har abada
Allahu
akhbar rayuwa
D hk n kawo
karshen wannan page din mu hadu a next page inda xamuji ci gaba d yardar Allah
Taku har
kullum Mariyat lawal Muhammad ( mommy)
👍👍jin jina ta musammn g aminiyar kwarai
haleema yazeed labo
No comments