BARIKI NA FITO (BOOK 2) 5
BOOK 2
PAGE 5
Y'AR UWA
KOMAI MUJINKI YAYI MIKI AMSA KIYI GODIYA TARE DA NUNA FARIN CIKIN KI DUK
KANKANTAR ABUN KARKI RAINA, DOMIN YAU IDAN MIJINKI YA KAWO MIKI PURE WATER YAGA
KINA TA MURNA TOH GOBE SWAN WATER ZAI KAWO MIKI YAGA WANI IRIN MURNA ZA KIYI,
BABU ABUNDA NAMIJI YA TSANA KAMAN YAGA YA KU'KE YAYI MIKI ABU AMMA KI NUNA
MISHI HALIN KO IN
KULA, Y'AR UWA IN KINA MA MIJI HAKA WLH KO YANA DASHI BAZAI
DINGA YI MIKI BA ZAICE BAKYA GODEWA IN YAYI MIKI GWARA KAR YAYI KI ZAGESHI DA
HUJJA, NAMIJI YANA DA SAUKI IN KIN IYA TAFIYAR DASHI DUK DA NASAN WASU MAZAN
KOYA KA MUSU🙆🙆 BASU CANZAWA, AMMA ANA CEWA IN KASAN
HALIN MUTUN SAI KASAN YANDA ZAKA ZAUNA DASHI, RAYUWAR AURE DUKA HAKURI NE IN
KINCE MIJINKI YAYI MIKI KAZA, TOH WATA ITA NATA MIJIN YAYI MATA ABUNDA YAFI
NAKI MUNI KUMA HAKA TAKE ZAMA DASHI BABU YANDA ZA TAYI, AURE BAUTA NE KUMA DUK
ABUNDA AKACE BAUTA TOH SAI ANJURE DAN HAKA MATA KUYI TA HAKURI DUK MAI HAKURI
YANA TARE DA ALLAH, SANNAN WUYA BAYA TABA DAUREWA HAKA JIN DAD'I DAN HAKA
HAKURI DAI SHINE ZAMAN DUNIYA
Yarima cire
hannunshi daka fuskanta yayi idonshi ya sauka akan yaron, ganin irin kallon da
yake Mai yasa yaron Ya daburce.....
Tare da
fad'in sir aikoni akayi na fad'a mata shine tace zata taga Waye, shine yace
ince taz.....
Bariki ta
Katse shi da fad'in ya isa haka, kallon Yarima tayi wanda fuskanshi ke d'aure
alaman bacin rai tace Yarima na yazo yace in bashi number dina shine.....
Labarin abunda ya faru ta bashi....
Yarima Aliyu
baiyi magana ba sai d'aukan wayarshi da yayi ya danyi danne danne sannan yasa a
kunne yana fad'in ina restaurant dinka kazo yanzu coz ina sauri, yana fad'in
haka ya ajiye wayar.... Ganin haka
mutumin daya kawo abincin ya zube a k'asa ya fara ro'kan yarima danya tabbata
Mai wajan ya kira, yace plz sir forgive me Wlh Aiko ni akayi saida nace bazan
zoba matar aurece, amma yace dole sai Naje ko yasa Mai wajan ya koreni, sir In
baka yarda ba kazo muje ka ganshi....
Tashi Yarima
Aliyu yayi yace muje.....
Da sauri ya
tashi ya shiga gaba amma suna zuwa wajan da yace mutumin na ciki suka ga wayam,
babu kowa.
Yarima Aliyu
ya kalli mutumin yace yana Ina?
Mutumin yace
sir Wlh a nan yake sai dai in fita yayi, hakuri yaita bama Yarima.... Bariki tace Yarima kayi hakuri kazo muje.....
Jan hannun
bariki yayi sukai waje Bayan ya biya kud'in tare da cema habib dake zaune ta
waje muje.....
Bayan sun
shiga mota Yarima tuki yake cikin bacin rai domin shi gaba d'aya laifin Zainab
din ya gani damme zata tsaya Tana magana dashi har tace tana son ganin mutumin
yanzu inda ban dawo ba zuwa za tayi.....
Wani irin gudu ya saki....
Habib dake
baya yace cikin ranshi Kar yaje ya kasheni ina cin gajiyar kuruciyata da sauri
yace Yarima zan sauka a kawo zan amsa sa'ko...
Yarima yace
ok suna zuwa kawo Yarima ya faka habib ya fita tare da fad'in a gayas haka
kawai aje a kashe ni ban shirya ba...... 🤣🤣
Yarima bai
tsaya ba sai maraban jos, da yake yau sati mutane nata kaiwa da komawa cikin
shigar banza, Yarima shidai ya rasa mai yasa baya son wannan anguwar shi inda
so samu ne baya son tana zuwa kwata kwata domin anguwar bata Mai ba, ga motoci
dake ta shigowa waima damma ba tanan bane Layin da bariki take ba......
Bariki
kallon Yarima tayi da fuskanshi babu alaman wasa..... Tace haba Yarima kofa
abincin baka ciba, aiya kam......
Yace ya isa
Zainab plz, ban son dogon magana, sauka kije zan tafi.....
Kallon
mamaki take mishi ganin yanda yake mata magana duk da hakan ya bata tsoro amma
saita dake tace haba Yarima, wannan fushin fah, karka manta kazo tayani murna
ne bai kamata ka sani cikin damuwa ba
Shuru yayi
ba tare da yace Mata komai ba, a tunaninta ya sauko ne, dan haka tace yanzu Mai
zaka ci in n.....
Ya dakatar
da ita da fad'in Zainab plz leave my car....
Tace Yarima
Mai.....
Yace I said
leave my car plz
Hawaye ne ya
fara zubo mata, garin yayi duhu, baya ganin hawayen da takeyi jin Tana
sheshekar kuka yasa ya gane kuka takeyi..... Bud'e motar yayi ya fita domin
bazai iya sauraranta Tana kuka ba uwa uba kuma abunda tayi ya bata mishi rai, a
duniya babu abunda ya tsana kaman yaga ana taba abunda yake so, wanda yake
ganin kaman Zainab din ta raina shine tunda har tayi magana da wani ya tabbata
inda bai dawo ba zata iya sauraranshi tunda harta yarda Tana son ganinshi din,
wata zuciyar tace amma tayi maka bayani.... D'an tsaki taja tare da nufa
masallacin dake kusa da wajan dan yin sallah isha'i da ake kira......
Bariki kam
tana cikin motar tana kuka, wanda ba kukan komai take ba saina tausayin kanta,
musamman abunda taga ya faru yau, jiba yanda Yarima yayi fushi har yake nuna
kishinshi a fili, tabbas Idan Yarima yasan wacece ni ban tunanin zai ragamin ko
kad'an, lokaci d'aya taji kanta ya fara mata ciwo, lallai Ina son Yarima bana
tunanin zan iya rayuwa ba tare dashi ba, sonshi yasa na daina aikata zina sonshi
yasa na daina aikata abunda Nayi niya dan inga na kuntata ma iyayena, wani
sabon kuka ta kuma saki.....
Yarima ne ya
shigo cikin motar jin Tana kuka Sosai yasa yaji jikinshi yayi sanyi, duk da
ranshi har yanzu a bace yake, domin Yarima namiji ne mai mugun kishi ya wuce
duk yanda Mai karatu yake zato..... Janyota yayi jikinshi tare da fad'in plz
stop it, bana son jin kukanki, Zainab Ina fushi dake inda kin San yanda nake
sonki da kuma kishin ki da Idan wani namiji yazo inda kike zaki nuna mishi ke
kurma ce, yanda ma bazaiji sautin muryanki ba, inda banzo a time ba only god
knows what will happen......
Bariki cikin
kuka tace Yarima Wlh abunda na fad'a maka gaskiya ne, nace mishi ya fad'a ma
mutumin inason ganinshi tunda nace ni matar aurece yace duk da haka a bashi
number dina, nayi hakan ne in kazo muje tare dakai amma badan wani ab........
Yarima Aliyu
yace ya isa haka mubar maganan yanzu kije gida ki huta, Nasan yau Kin gaji
Sosai....
Cikin sanyin
murya tace toh amma Yarima baka ci abinci ba??
Yace don't
worry, zanci in naje gida....
Kai ta d'aga
alaman Toh, tare da fad'in Yarima hope u trust what I said? Nd ina fatan ka
hakura?
Yace Zainab
plz nace mubar maganan go and rest, muje in raka ki bud'e kofar motar yayi....
Ganin ya
fita itama ta bud'e kofar motar ta fito har kofar gidan da tace mishi na y'an
uwanta ne ya rakata saida ya Bari ta shiga ciki sannan ya dawo ya shiga
motarshi yayi gaba cikin gudu
Bariki kam
tana ganin ya wuce ya fito danta nufi inda take, tafiya take tana tunani domin
ita bata yarda Yarima ya hakura ba, dan inda ya hakura da baiyi reaction haka
ba, lallai Yarima yana da kishi, duk ranan da yasan wacece ni ban tunanin zai
zauna dani a matsayin matarshi koda ya aureni..... Wata zuciyar tace mata kin
manta gidan sarauta basa saki, sai an Kama Ka da laifi biyu? Bata san lokacin
da tayi murmushi ba wannan tunanin da tayi shi yasa taji karfin giwa tare da
kara d'aura dammaran rufe sirrinta har sai ta auri Yarima dan tana sonshi kuma
tasan indai ya sani Bayan aure bazai saketa ba tunda ba'a saki...... Yarima Aliyu na tabbata kai mutumin kirki ne,
soyayarka a gareni gaskiya ce kaman yanda nima nake maka, Idan na tuna abunda
ya faru dani Ina takaici, tabbas Yarima ni Nasan baka dace dani ba, kafi
karfina domin irin rayuwar mu ba d'aya bace, duk shirin da nakeyi na auranka
Inayi ne kawai amma bawai dason raina ba, ina ganin kaman zan cuceka ne Sonka
yasa na zama mai son kaina, ban taba tunanin duk duniya akwai wanda zan boyema
halin da nake ciki ba tunda har iyayena sun sani kuma sun kasa yin komai akai,
duk da ransu yana baci amma babu yanda za suyi domin burina in rama abunda
sukai min na rashin d'aukan kaddaran daya fad'amin...... Jin ana mata magana
yasa ta waiga
Driver din
alh madu ne yake mata magana, yace sannu hjy tun dazu nazo ai inata jiranki,
mai gida yace ya kira baki d'aga waya ba, gashi hjy babba wayanshi shima baya
d'aga wa.
Bariki tace
Indai wajan hjy babba kazo yana filin rawa Nasan zaka iya dubashi a can , Tana
fad'in haka tayi gaba ......
Binta driver
din yayi yana fad'in a'ah Wajanki nazo oga yace inzo in d'auko ki sai yasa
nazo.......
Bariki tace
kaje kace Mai nace bazan zo ba, and kuma daka rana irin tayau karya kara kirana
domin ni yanzu Allah ya shiryar dani na daina wannan banzan rayuwar aure zanyi
Driver din
alh madu yace Kai Alhmdlh Wlh naji dad'i Sosai, dama Wlh tunda na ganki naji
Ina takaicin wannan rayuwar da kikeyi gaki yarinya karama amma babu daman inyi
magana karki fad'ama oga ya koreni, wlh Ina takaicin wannan abunda yakeyi Wlh
sai muje garin abuja muyi wata biyu uku amma baije yaga iyalanshi ba, sai dai
wancan macen tazo wancan tazo ta sameshi a guest house dinshi, ni Kece ma naga
yana bi kina Mai wulakanci, gashi mutum ya girma Mai yakon yabi Allah yaita
istigfari amma shi ina kullum hanyar bata ita yake bi
Bariki tace
Allah dai ya shirya, nidai ka fad'a mishi sa'ko na, Tana fad'in haka tayi gaba
Driver din
alh madu yace Kai Alhmdlh Wlh naji dad'i Sosai,
yanzu kam zani in fad'ama wannan tsohon banzan sa'kon yarinyar nan
***
Yarima Aliyu
saboda gudun da yayi kaman zai tashi sama 20mnt ne ya kaishi Zaria, Allah ya
taimakeshi ya sauka lafiya, domin gudun fitan rai yayi yana tuki yana tuna
abunda wanna yaron yazo yana cewa he said that you can come he is waiting for
you Yarima Aliyu Wanda yaga Abun a matsayin kaman Zainab ta raina shine dan
taga yana Sonta da yawa tsaki yaja tareda shiga gefenshi inda yaga gimbiya
zinatu a falo tana zaune tana danna waya tasha wata doguwar riga y'ar kanti
yayi mata kyau Sosai, kauda idonshi yayi daka kanta kaman bai ganta ba...
Tashi tayi
da sauri ta nufeshi tare da rungume shi tana fad'in Yarima inata kiranka baka
d'auka ba, tun dazu nake cikin damuwa tare da fargaban Allah yasa lfya
D'an janyeta
yayi daka jikinshi tare da fad'in plz allow me to go and rest ,gaba yayi
abunshi
Gimbiya
zinatu binshi tayi da ido alaman Mai yake nufi, kodai ya gano gaskiyan
al'amarin ne? Kai a'a bazai taba ganewa ba domin jinin daya gani zai sa ya
tabbatar da ita budurwace, kafada ta d'aga alaman shiya sani Nasan wani wajan
ne aka bata mishi rai, chatting dinta taci gaba dayi ita da gimbiya Amina.
Yarima kam
yana shiga bedroom dinshi wanka yayi tare dasa jallabiya, ya fito yaga gimbiya
nata danne danne dan tsaki yaja mara sauti yakan yi mamaki Idan yaga mutum yana
bama waya muhimmanci fiye da komai, danya Lura da gimbiya zinatu Tana son bama
waya lokacinta Sosai, dinning ya nufa dan yayi dinner....
Gimbiya
ganin ya zauna akan dinning yasa ta tashi ta danna wani abu saiga kuyangi nan
sun shigo, sun San abunda za suyi dan haka shi suka farayi zuba ma Yarima
abinci, Bayan sun gama suka bar wajan, Yarima Fara ci yayi amma baya jin dad'in
abincin dan ranshi a bace yake, yau princess dinshi ta bata mishi rai
Sosai, gimbiya zinatu zama tayi itama
akan dinning din tare da kura mishi ido tana kallon yanda yake cin abinci kaman
baya son ci...... D'ago kai yayi yaga
tana kallonshi a hankali yace stop starring at me like that,
Gimbiya
zinatu tace in ban kalleka ba wa zan kalla?
Yarima shuru
yayi ba tare daya kuma cewa komai ba, ya rasa mai yasa yake tantama akanta
Sosai, abunda yasa har yanzu yake ganin kaman akwai wani abu tare da gimbiya
zinatu shine lokacin da yayi sex da ita bai San sanda ya fara ba,hakan yana
nuna mishi baya cikin hayyacinshi, yaga Abun kaman mafarki har yake ce mata ita
ba virgin bace, abun daya d'aure mishi kai kuma shine yanda ya farka yaga jini
a jikinta alaman she is virgin, wannan Abun yana d'aure ma Yarima kai, ido ya
d'an lumshe lallai gimbiya she is a virgin Inba virgin bace taya zanga blood?
Bai kamata Ina tantama akanta ba, I have
to believe in what I see, tunda if she is not a virgin bazanga blood ba, duk da
Nasan bako wace mace bace take zubar da jinin budurci kuma budurwa ce, but da
yake Allah yana son nuna min sai gashi ita gimbiya Tana d'aya daka cikin masu
zubar da jini a daren farkon su, sabanin wasu matan dasu baya zuban musu kuma
suma virgin ne, ba lallai bane Idan jini bai zuba ba ace mace ba budurwa bace,
wata baya zuba wata yana zuba, shi budurci ba daka jini yake ba, yanda kaji
cikin mace Idan ka shiga zaka jishi a matse tun daka farko har ciki, wannan
shine budurwa, wacce kuma ba budurwa ba koda tayi matsi ana ganewa, domin wajan
ne zai matse cikin kuma yana shiga yaji kaman ya fad'a rami, dan haka y'an mata
ku daina rud'an kanku kuce AI akwai magani dana miji bazai gane cewa ni budurwa
bace wannan maganan karya ne wlh, domin budurci budurcine in kika rasa shi har
abada kin rasa shi bazai taba dawowa ba komai zaki ma wajan, domin abun daka
Allah ne, kuma budurci shine kimarki wajan mijinki daka yaji ya sameki kofa a
bud'e kin bani domin wlh har abada bazai dinga ganin kimarki ba sai dai in a
bisa tsautsayi kika rasa budurcinki tayu yaji tausayinki ya d'aga miki kafa,
shima ba lallai ba domin in bakiyi wasa ba wata rana saiya goranta miki Indai
namiji ne, sai yasa yana da kyau duk wani waje da zaki Indai kin San wajan ba
tsaro ki guji wajan Kar ki jaza ma kanki bala'i.......
Yarima tashi
yayi dan baya jin dad'in abincin d'akinshi ya nufa ya kwanta, jin karan
wayanshi yasa ya d'auka yaga zainab ce kashe wayan yayi gaba d'aya dan baya
bukatar magana da ita a halin yanzu.........
haba masoya
novel's din bariki na fito, yanzu dan Allah har sai kun Bari anzo ana tambaya
na akan in tura ma mutum novel daka page kaza zuwa kaza😫 taya akayi kuka bar haka ya faru plz in an tambaya ku
dinga badawa tura ma mutum novel yana mun wuya Wlh, sai inji gwara ma inyi
typing da in tsaya turama mutum novel
NGD SOSAI DA ADDU'A
ina matukar
yinku Sosai Alhmdlh my hrt taji sauki, a rayuwa babu abunda yake min dad'i irin
addu'ar da kuke min koda Banyi niyan yin typing ba sai inji Ina son yi muku
badan komai ba sai dan addu'ar da kukeyi min daka bakunan ku masu albarka, Ina
matukar yinku masoya na one luv
MARYAM OBAM
No comments