BARIKI NA FITO (BOOK 2) 4
PAGE 4
MAZA KUJI
TSORAN ALLAH LOKACIN DA KAKE NEMAN MACE KOMAI TACE TANA SO SAIKA MATA, WANI
ABUN MA BATA TAMBAYA KAKE MATA, IN ANYI AURE DUK HIDIMAR DA KAKE MATA SAIKA
DAINA, KUMA BAWAI DAN BAKA DA HALIN YI DIN BANE, IN BAKA KYAUTATA MA IYALINKA
BA WA ZAKA KYAUTATAMA, SAI KAJE KANA FAD'A AI BATA KWALLIYA BATA MAKA ABU KAMAN
DA KAFIN KA
AURETA, HMMM TAYA ZATA MAKA KWALLIYA TAYU KUD'IN POWDER DINMA BAKA
BATA, KO KUD'IN KITSO A INA KAKE SON TA SAMI KUD'I TAYI??? DA LOKACIN DA TAKE
GIDANSU TANA DA KYAU KOMAI NATA ABUN SHA'AWA AMMA KA AURETA KA MAIDATA TSOHUWAR
KARFI DA YAJI, BABU KUD'IN LALLE, BALLE NA TURARE😫 HABA MAZA MAI YASA KUKE HAKA?? IN KAJE GIDAN ABOKIN KA YA BAKA ABINCI
MAI DAD'I SAI KAZO KANA ZAGIN MATARKA BATA IYA GIRKI BA, BAYAN KAINE BAKA BATA
KUD'IN CEFANE WANDA ZAI IYA HAR AYI MAI DAD'IN BA, WLH KUJI TSORAN ALLAH MAZA
MASU IRIN WANNAN HALIN DAKA RANAN DA AKA BAKA ITA A MATSAYIN MATARKA KOMAI NATA
YA RATAYA AKAN KA, ABUNDA MUTUM YAKE GANIN BA KOMAI BANE ZAI IYA KAISHI GA
HALAKA, IN KANA DA HALI KA FARANTA MA MATARKA YANDA INTA FITO ZA'A CE MATAR
WANCAN NE SABODA AN GANTA FES, AMMA IN AKA GANTA SABANIN HAKA ZAGINKA ZA'AYI
TUNDA ANSAN KANA DASHI PLZ MAZA KU GYARA DOMIN ALLAH ZAI TAMBAYEKU TUNDA KANA
DA HALI DAMA BABU NE SAI AYI HAKURI
Kallonshi
tayi cikin tsoro tare da fad'in Yarima plz ka barshi Kawu nane yake kira, so
yake Inba ma Abba, wayan Abba ne ya sami matsala in an kira yana ji amma ba'a
jinshi, inna d'auka nace bana gida zai iya zuwa har gidan ya sami Abba da Umma
yayi musu fad'a akan Mai yasa zasu dinga bari Ina fita da yamma, kuma yanzu
inna shiga Gida Umma bazata Bari in fita ba, dan yanzu tana tunanin ina d'akin
makwabciyan mune.....
Yarima Aliyu
ajiyan zuciya ya sauke, lallai Zainab gidansu gidan tarbiya ne, sabanin yanzu
da iyaye suke sakin y'ay'ansu suna abunda suka ga dama, har ma wasu zaku ga
kaman su suke juya nasu iyayen sai abunda sukace iyayen nasu keyi..... Amma a fili sai yace Mata my princess na
fad'a miki tun Farko ai ki bani dama inga Abba kinki, yanzu Idan yazo ya gammu
ya kike so inyi???
Cikin sanyin
murya tace bazanji dad'i ba, domin na tabbata Abba zaiyi fushi Sosai, amma
Yarima tunda harna yarda yau kazo gidanmu hakan ya kamata ya nuna cewa Ina son
Kaga Abba din.....
Wani irin
murmushi Yarima ya saki cikin jin dad'i tare da furta Kalman Alhamdullilah
cikin ranshi, domin wannan maganan da Zainab tayi mishi yasa shi cikin farin
ciki Sosai..... Kallonta yayi cikin ido
tare da fad'in my princess kin tabbata kina son inga Abba.???
Ganin bazata
iya juran kallon cikin idonshi ba yasa ta kawar dakai gefe tare da fad'in eh
Ina so ka ganshi, domin hakan ya kamata Ayi tun Farko
Murmushi
yayi tare da fad'in zan iya ganinshi yau?
Tace eh amma
sai dai ka tura wani yaje ya maka sallama dashi duk da ban tunanin ya dawo amma
kuma hala ya dawo din dan lokacin dawowarsa yayi .....
Dariya
Yarima yayi tare da fad'in am joking bazan iya zuwa ni d'aya ba, but zuwa jibi
Zanzo da Usman da wasu friends dina sai mu ganshi mu nemi izinin zuwa zance
Kafin manya su shiga
Murmushi
tayi tare da fad'in Allah ya taimaka
Ya amsa da
Ameen, tare da fad'in where is my promise?
Kallonshi
tayi taga shima ita yake kallo da sauri ta kawar da kanta gefe tare da sakin
murmushi sannan tace wani promise??
Yace abunda
ya faru wajan Walima.
Dariya tayi
wanda ya kara mata kyau sannan tace Yarima ban samu daman d'aukan komai ba
saboda jama'a Wlh kunya duk ta hanani gashi mune masu saukan..... Amma munyi hoto a gida da kawaye na Wanda
mukai saukan tare
Yace OK
Nasan duk kinfi yin kyau
Tace a'a
tare da danna wayarta tace na tura maka ta whatsapp
Murmushi
yayi ya d'auko wayanshi ya fara dannawa, yace my princess duka sun sa nikaf
Kema Aida kinsa ko so kike ayi ta kallemin ke
Dariya tayi
tace a cikin gida nefa babu Mai kallo na sai Kai ta karasa maganan tare da rufe
fuska
Murmushi
yayi tare da fad'in my princess yunwa nake ji banci komai ba tunda safe.....
Da sauri ta
kalleshi tare da fad'in mai zakaci in kawo ma? Yarima taya zaka zauna har yanzu
bakaci komai ba ulcer zai kamaka plz mai zaka ci??
Murmushi
yayi cikin jin dad'i domin ganin yanda ta nuna kulawanta akanshi, ya tabbatar
mishi da cewa tana sonshi Sosai......
Katse mishi
tunani tayi da fad'in Yarima ko in kawo maka tea kasha Kafin in dafa maka wani
abu??
Yace a'ah ki
barshi zanje Inci abinci yanzu
Shuru tayi
tana d'an nazari can tace ko in kira habib yaje
ya kawo ma wani abu kaci?
Hannunta ya
koma tare da ri'ke mata su duka biyun yace my princess karki damu zanje wani
waje Inci, ko zaki raka ni?
Da sauri
tace eh muje Kafin Abba yasa Umma ta kirani a d'akin da take tunanin ina ciki
inya dawo Kar yasa a kirani yaga bana nan koda yake Nasan ma ya dawo ganin
habib Nasan bazai damu daya ganni ba.
Murmushi
yayi yace Nop Bari inje alone banso Ayi miki fad'a my princess
Tace Yarima
plz muje kaci abinci habib na nan bari in kirashi sai muje tare zance ma Abba
zani maraban jos In kwana bazai hana ba sai muje kaci
Yarima yace
ok my princess
Fita tayi ta
shiga cikin gidan Jim kad'an sai gata ita da habib da abbanta na Bariki Sun
fito daka gani ya fito raka habib dinne a yanda Yarima ya fahimta kenan🤣
har bakin titi ya rakasu sannan ya dawo ya shiga gidan yarima yana
kallonshi cikin ranshi yace wannan daka gani Dattijo ne yana yin kamalan shi ya
nuna ma Yarima hakan🤣🤣🤣 kai ana abu a duniya sai yasa akace sometimes abunda ka gani
bashi bane gaskiya......
Yarima tada
motar yayi shima ya nufa titi bai gansu ba kiran Zainab dinne yasa ya dauki
waya tare da fad'in my princess where are you?
Tace muna
gaba wajan NDA Abba saida muka shiga mota ya koma shine muka sauka a nda
Yarima yace
ok ga ninan zuwa, Yarima juyawa yayi ya nufi nda din ya d'aukesu ta shiga gaba
habib kuma baya, Yarima ya kalleta yace Ina zaki kaini Inci abinci??
Ido ta d'an
zaro tare da fad'in ni Ina na sani tunda ba zuwa nake ba
Habib dake
Bayan motar yana jinsu cikin ranshi yace bariki ko y'ar iska ke inane baki Sani
ba cikin garin kaduna yanda kuka san map din garin ne a kanta amma yanzu tana
wani nuna ita ta Allah ce..... 🤣
Yarima wani
babban restaurant ya faka motarshi wajan yayi mugun had'uwa gashi babu irin
tarkacen mutane a wajan, daka ganin alama wajan ba kowa ke zuwa ba sai y'an
gayu na gaske, private waje suka zauna, shidai habib cewa yayi cikin mutane zai
zauna danya dinga ganin masu shiga da fita
Bariki tace
muje tare mana
Yace ke
barni in zauna nan ko zanyi kasuwa
Bariki dai
dariya tayi sannan ta nufi ciki inda Yarima yake domin yace baya son su zauna inda
akwai mutum ko d'aya dan baya son ana kallon mishi ita.......
Yarima ya
fad'a abunda za'a bashi bariki kam tace ta koshi Yarima yace dole taci wani
abu, babu yanda ta iya tasa a kawo mata snack dan a koshe take shima takeaway
tace tana so, yarima yace abar snack din in Sun tashi fita zata zaba abunda
take so.
Wajan 15 mnt
aka kawo ma Yarima abinci lokacin ana ta kiran sallah magrib tashi yayi ya
Kalli bariki tare da fad'in bari inyi sallah.
Tace OK tare
da kallon Wanda ya kawo abincin tace maida kayan inya dawo sai kayi warming din
abincin ka kawo.
Mutumin yace
ok ma, Yarima bai tafi ba saida yaga mutumin ya fita dan ya Lura dashi yanda
yake kallon zainab kaman yana son yi mata magana.....
Yarima Aliyu na fita kam saiga mutumin ya dawo
da sauri yana fad'in ma plz I need to talk to you.
Bariki tace
lafiya maiya faru?
Yace ma ance
in amso phone number d'inki ne
Tace
what? Are you mad da aurena inzo da
mijina kazo kace min in baka phone number dina get lost frm hare Kafin mijina
ya dawo ya ganka
Mutumin yace
sorry ma Nima na fad'a mishi kina da aure saboda irin shigarki amma yace babu
damuwa koda kina da aure in amso mishi number d'inki
Bariki tace
Waye zan iya ganinshi??
Yace let me
go and ask him in yace in kawo ki sai kizo
Bariki tace
ok yana tafiya saiga Yarima ya dawo Allah yasa bai ganshi ba
Bariki tashi
tayi tare da fad'in har an idar kiran mutumin tayi da baiyi nisa ba yazo tace
Kawo Mai abincin
Yace OK ma
Bai dad'e ba
saiga abincin ya kawo, Yarima coffee ya fara sha sannan ya kalli bariki yace my
princess feed me plz
Dariya tayi
tare da fad'in feed ur self u r not a baby
Yarima
kallonta yayi tare da fad'in oh really?
Ni baby dinki ne
Ido ta rufe
alaman jin kunya
Hannunshi
yasa yana kokarin cire mata hannunta da tasa ta rufe fuskanta ..... Muryan
Wanda ya kawo abincin ne yazo yana fad'in ma he said that you can come he is
waiting for you......
Plz kuyi ma
my hrt addu'a Allah ya bata lfya my princess my queen phareejay, Allah yasa
kaffara ne🙏🙏😫😫
kuyi manage
plz Nima ba wani lfya gareni ba Nayi muku ne dan kusa my hrt a addu'a plz 🙏🙏
plz ku dinga
hakuri da typing error banda tym din editing
MARYAM OBAM
No comments