BARIKI NA FITO (BOOK 2) 6
BOOK 2
PAGE 6
Y'AR UWA KI
GUJI FAD'AMA KAWAYE SIRRIN MIJINKI, BAMA KAWAYE BA HARTA IYAYENKI DA SUKA
HAIFEKI KODA KUN SAMI SABANI DA MIJI, KARKI KALAMAN BATANCI AKAN MIJINKI, KICE YA MIKI KAZA YA MIKI KAZA, SAI
KIN GAMA BATASHI DAKA KARSHE ACE KIYI HAKURI KI KOMA, BAYAN KIN KOMA KE KINA
CAN KUN SHIRYA KUNA ZUBA LOVE DA MIJI, AMMA
IYAYENKI NA NAN NA KALLONSHI DA
ABUNDA KIKA FAD'A MUSU, Y'AR UWA KI GUJI BATA
MIJINKI WAJAN IYAYENKI DOMIN IYAYE BA KOMAI SUKE D'AUKA BA, YA KAMATA KI
ZAMA MAI HAKURI DA RUFE SIRRIN MIJINKI INDAI BA ABUNDA YA SABAMA SHARI'A YAYI
BA, SANNAN FAD'AMA KAWAYE SIRRIN MIJINKI ZAISA SU RAINA KI SU DINGA MIKI KALLON
SAUNA MARA WAYAU, GABA D'AYA ZAMAN AURE HAKURI NE ZOMU ZAUNA ZO MU SABA, SANNAN
CIKI BADAN TUWO KAWAI AKAYI SHIBA.......
RASHIN SANI
KAWATA HAUWA A USMAN JIDDERH
ina tayaki
murnan kammala novel dinki Mai cike da abubuwa da dama, a gaskiya kinyi namijin
kokari wajan rubuta novel din rashin sani, Littafin yayi dad'i Sosai tare da
Ma'ana, kin zuba basira a cikinsa Allah ya baki ladan fadakarwa yanda kika gama
lfya Allah ya baki ikon Fara wani lafiya
Bariki ganin
yayi rejecting kiran yasa tayi murmushi dan tasan dama inta kirashi baya d'auka
sai dai ya kirata koya bari ya tsinke ya kira koya kashe ya kira, minti d'aya
minti biyu har biyar Yarima shuru bai kirata ba, d'an murmushi tayi tare da
fad'in may be yana wani abune Nasan for sure zai kirani, jiran kiran Yarima tai
tayi taji shuru, d'aukan wayanta tayi ta duba time din data kirashi taga wajan
44mnt tace lafiya kuwa? Kar dai ace har yanzu yana fushi ne? Kai no Nasan
bazaiyi fushi irin haka ba.... Kara dialing number dinshi tayi taji ance mata
switch off, tace haba daman Nasan haka kawai Yarima bazaiki kirana ba, may be
yasa caji ne koh yana wani Abun......
wata zuciyar tace ko kuma yana wajan amarya ba, yana zuba mata tsantsar
soyayya..... Da sauri ta girgiza kai
tare da fad'in no..... Jin ana mata nocking yasa ta Fara fad'in Waye ne?
Muryan habib
taji yana fad'in bud'e mana, ba kwarto bane da kike zunduma ihun Waye ne......
Bud'e kofar
tayi habib ya shigo ,zama yayi yana fad'in Washhhhh Na gaji, d'anzo ki matsamin
baya na
Bariki tsaki
tayi tare da fad'in Koba baya ba?
Habib yace
eh shi nake nufi...... Ke bama wannan ba
wai maiya faru tsakaninki da Yarima ne? Naga yanda yake fushi yana ta gudu dama
kaman zai tashi sama, sai yasa Nayi mishi karya ya saukeni Kar yaje ya jefamu
kan trailer mu mutu, ban ajiye Mai min addu'a ba, ko d'an auren da mata keyi
koda shiga ki fito ne ace kadai taba koshi Nayi ai babu laifi......
Bariki tace
Hmmm Allah ya kyauta, tare da fad'ama habib abunda ya faru.......
Habib yace
amma da iskanci kike akan wani dalili zaki bama wani dama, ai gashi yanzu kinja
ma kanki sai ki nemi mafita, ni naga kaman ma nafi son ki auri Yarima domin in
Ina wajan da yake Mai kamun kai nake zama, amma ke in banda tsaban iskanci har
kice zaki ga wani kuma kin San da wanda kika je wajan.....
Bariki tace
ai ka tsaya ka.......
Habib
dakatar da ita yayi tare da fad'in Wlh bariki ban son bura uba, akan wani
dalili zaki dinga kaini jinsin da ba nawa?...
Gskya banso
Bariki tace
kwantar da jijiyoyin cillarka.....
Tashi yayi
tsaye tare da kama kugu yana fad'in bariki sanin kanki kin San wacece habiba,
wlh banki inyi tsirara ba ni dake mu daku......
Bariki tace
ah zauna kawata Ina ni Ina fad'a da babbar kawata Allah ya baki hakuri Hjy
habiba ikon god....
Zama habib
yayi yana fad'in ah toh in banda iskanci taya zaki dinga had'ani da maza har ki
dinga cewa in kwantar da jijiyon cilla ta, ni Ina naga jijiya ni da nake da
Fata, ai jijiya sai y'an maza ya karasa maganan yana dariya
Itama bariki
dariyan ta saki tare da fad'in nidai Wlh na k'osa Yarima ya turo ayi bikin mu
Ina gama istabra'i.....
Habib yace
yauwa Ina jinki kina ban labari.....
Bariki tace
Hmmm nifa Wlh nace ina son ganin mutumin ne saboda muje tare da Yarima amma
Yarima yayi min mummunan tunani, yana ganin inda bai dawo ba a tunaninshi zanje
wajan mutumin ne.....
Habib yace
Kema maiya kaiki?? Ni Wlh ba tun yau na
Lura da wannan Yarima dinba akwai shegen kishi Wlh bariki naga kaman kina wasa,
samun Yarima Aliyu ba karamin Sa'a bane, inko kika bari ya kubce miki Wlh kinyi
Asara, Kut Aina sha fad'a miki inda ni yace yana So Wlh da yaga yanda ake
soyayya amma keda yace yana So kina iskanci, namiji har namiji wlh Yarima ya
had'u so handsome.......
Bariki tace
uhm, waya ce ina wasa da Yarima?? Ni kam duniyar nan banga Wanda nake jin tsoro
ba tare dajin tsoran yasan koni wacece ba sai Yarima Aliyu, Kinga kawata inda
bana son Yarima yaushe zan damu yasan koni wacece?
Tabe baki
habib yayi tare da fad'in ai gashi yanzu kina kokarin ki nuna mishi halin naki
ke gindi babu control daka Kinji ance ana son ganinki kin yarda, Allah yasa ba
fushi yayi ba sai yasa ya kashe wayoyin nashi ba.
Bariki tace
uhm....
Habib yace
kyace uhm mana tunda kin shuka tsiya......
Ni tashi muje muyi rawa ko naji sanyi kwana biyu ban girgiza duwaiya
ba.....
Bariki tace
wa? Rufamin asiri Aini inka ganni a lahira kaini akayi haka kawai tsautsayi ya
kaini Yarima yazo a'a Wlh bada niba wai ance da tsohuwa tayi zina......
Shewa habib
ya saki tare da fad'in kunji salo nidai Kinga tunda banda tsayayye balle in takura
kaina nayi gaba dan yau sai na karkad'a kayan alatu
Bariki tace
nan akafi auki....... Lah mota ta na
barta a u/kanawa Wlh Yarima ne ya caza min Kai sai yanzu na tuna,
Habib yace
tsiyar y'an mazan nan kenan ai sai yasa ni naki yarda Nayi aure, suna auranka
suna kaika ciki ka zama nama, sai yasa nake tatsan su a waje... Ke gaki ko ciki baki shiga ba har an fara
miki duk da Kece da laifi
Bariki tace
uhm bari in kira ubana na Bariki ince a kulan min da motar ni saida ta zanyi ma
gobe inna fita
Habib dariya
Ya saki tare da fad'in ni sai naga kaman ma kina kama da mutumin Wlh.....
Bariki
dariya tayi tare da fad'in amma Allah ya isa......
Habib fita
yayi yana fad'in sai da safe zani wajan wasa
Yana fita
bariki tasa ma kofarta key ta kwanta tare da kiran babanta na Bariki ta fad'a
Mai ya kula da motar, sannan ta kara da fad'a Mai Yarima zai zo jibi dan neman
izinin zance..... Tace Bari koma dai miye gobe mayi magana in nazo Abba.
**
Driver din
alh madu koda ya koma abunda bariki ta fad'a haka Ya fad'ama Mai gidan nasa,.
Alh madu
dariya yayi tare da fad'in yaro man kaza, yaro yaro ne yaro bai San wuta ba
saiya taka, lallai Bariki har yau baki San Waye alh madu ba, amma naga kina son
in fito in nuna miki Waye ni dan naga kanki yana rawa very soon zanyi maganin
ki, sannan Indai bani zaki aura ba sai dai mu zauna muci gaba da mu'amala yanda
mukeyi, dan bazaki aura kowa ba inba niba.
D'aukan
wayanshi yayi ya doka ma Hjy babba kira, duk da yasan ba lallai bane ya d'auka
domin tun dazu yake ta kira bai d'auka ba, harya kusa tsinkewa aka d'auka......
Hjy babba ya
d'auka tare da fad'in Allah ya taimaki Sanata alh madu daka majalisan
dattawa sai Villa insha Allah
Alh madu
yace kana ina duk inda kake kazo yanzu sannan ina son kazo min da bariki kota
wani hali kafarka kafarta yau nake bukatar ganinta cikin daren nan a guest
house dina ......
Hjy babba
yace an gama ranka ya dad'e yanzu zaka gammu
Bayan alh
madu ya kashe wayan, hjy babba yace Toh fah hala bariki ta kara Karta Mai
rashin mutunci ne Bari inje d'akinta inji y'ar bura ubar itama har mota ya bata
ita da bata iya cin arziki ba inda Tana mishi yanda yake so Aida tafi karfin
abunda yafi wannan motar duk da tace baida kayan aiki abu kaman ayabar yara
kona jarirai ne tace ma oho ni na manta..... Gaba yayi tare da nufa d'akin
bariki data fara bacci nocking yaita mata da karfi.......
Tashi tayi
tare da sakin tsaki tana fad'in Waye ne??
Muryan hjy
babba taji yana fad'in nice bud'e kofar
Bariki tashi
tayi ta nufi kofar tana murza ido, bud'e kofar tayi taga hjy babba dinne tace
lafiya cikin wannan daren???
Hjy babba
yace lafiya mana, ko 12 bai karasa ba kike cewa cikin wannan daren sai kace
nazo miki da karfe biyun dare, Kinga ni bama wannan ya kawo niba, nazo ne muje
wajan alh madu dake yanzu ya kirani yace yana son ganinki dan Allah shirya
muje......
Bariki tace
hjyta babu inda zani domin wlh ni aure zanyi kuma istabra'i nakeyi dan so nake
inyi tsarkakken aure.....
Hjy babba
yace au me????!
Tace
aure.......
Yace gaskiya
banji dad'in wannan maganan ba Wlh Ina ke ina wani aure yanda kike da kyau da
lafiya ga kuruciya, gskya banji dad'in jikina ba wai mahaukaciya taji
duka...... Gaskiya bariki ki canza shawara
ai yanzu ne kike da dama kuma shi komai na duniyar nan lokaci ne gwara kici
naki lokacin daka baya kyayi auren in kin daina tashe amma haka kawai tsigai
fiyau kina tashe ki wani cuta kanki Muma ki cucemu dan abunda muke samu saboda
ke mu daina samu, ki makale waje d'aya da Sunan kinyi aure gskya raina ya baci
Bariki tace
hjyta nidai bacci nakeji yanzu wlh kuma shi nakeyi kika tasheni dan Allah hjyta
ki bari in koma bacci
Hjy babba
yace oh yau naga ikon Allah, amma dai wlh bariki kin canza kuma Nasan yanzu
bakya d'aukan maganan kowa saina Shegiyar habiba Dan naga yanda take shige
miki, karki manta Nina Fara saninki Kafin habiba kuma saboda ni kike nan
gidan.....
Bariki tace
hakane hjyta kena Fara sani Kafin habiba, and kuma kinmin hallaci Wanda bazan
manta dake ba, sai yasa har gobe nake mutuntaki hjyta
Hjy babba
yace bariki Indai kina ganin mutuncina kizo muje wajan alh madu ni koda bazaki
yarda dashi ba, dan Allah kizo muje Yadai ga na kawo mishi ke domin yana ganin
mutuncina ko so kike ya daina, sannan inma Kinje shida kika ce ayabar tashi
kaman ta yara Aiko yayi ba komai za kiji ba....
Bariki tace
nifa hjyta gskya babu inda zani domin na riga na yanke hukunci kuma na fad'a ma
driver dinshi sa'ko ya bashi, wato shine daya fad'a Mai shine ya Aiko ki, Toh
wannan karan zaisha mamaki domin babu inda zani kuma na fad'a
Hjy babba
yace oh na shiga uku an fasa aurena haka gasau kike fad'a babu inda
zaki??.... Amma kam in kikai haka baki
hallaci ba bariki ki duba fah har kyautar mota yayi miki......
Bariki tace
Aiba ro'kansa nayi ba shiya d'auka ya bani Dan haka kuma ta bayu,.
Hjy babba
yace dan Allah bariki Kar kisa nidai ya daina ganin mutuncina ki daure kizo
muje koda zaginshi za kiyi nidai yasan na kawo ki, sannan in Kinje kya fad'a
mishi abunda ke ranki Kinga tayu ya barki ya nemi wata......
Jin haka
yasa bariki tace muje, inji uban Mai yasa ga mata Nan a gari wanda suka fini
iya zuba bariki bai nema ba sai ni, muje inji dalili Danni Wlh na gaji da
wannan iskancin nashi.... D'akin ta koma
tasa hijab dogo har k'asa akan rigan baccinta tare da rufe d'akin tace ma Hjy
babba muje.......
Bakin titi
suka nufa da yake garin yau ake wasa akwai mutane birjit, samun Abun hawa bai
musu wuya ba, inda suka sami Mai keke napep suka shiga, direct gidan alh madu
ya kaisu hjy babba ya biya kud'in sukai nocking Mai gadi ya bud'e dan yasan hjy
babba da bariki, kofar falon alh madu a bud'e yake dan haka suka shiga baya
falo bariki bedroom dinshi tayi taganshi tsirara yana video call daka gani da
wata mace yake, alh madu waya yake bai Masan bariki ta shigo ba saida yaga hasken
wayarta alaman an d'aukeshi hoto......
Da sauri ya tashi yaga bariki ce murmushi ya saki tare da fad'in Kaga
manyan mata maganin kanana, nufanta yayi tare da janyota jikinshi Wanda babu
kaya yace Bari in d'auke mu kit kit ya fara d'aukansu a wayarshi bariki kokarin
Jan jikinta ta farayi tare da fad'in miye haka ne Dallah sakeni, andai ji kunya
wlh kaje can ka karata da sauran y'an iskan y'an matanka badai bariki ba
womanizer kawai fuuuuuu ta fita ta barshi yana kiranta ganin ta fita yasa ya
fara saka kaya da sauri dan ya cin mata dan yasan Indai ta zille Mai shida ya
kuma ganinta sai anji jiki tunda yanzu tazo yau yake son sanin Mai take nufi
domin ya shirya Mata kota yarda ta aureshi kota fasa maganan auren da take
fad'in za tayi suci gaba da cin juna babu aure, kuma yayi alwashin cikin biyu
dole ta zabi d'aya.......
Ina masoya
novel's dina ina muku albishir da novels din da nayi baya wanda babu su a
Wattpad zan fara sa muku su wanda na fara sa muku AMINIYA TA CE ,inna Gama
sashi zan d'aura muku wani shima insha Allah
MARYAM OBAM
No comments