BARIKI NA FITO (BOOK 2) 16
BOOK 2
Bariki gida
tayi, tana shiga ta doka ma habib kira akan yazo, kallon uwarta ta bariki tayi
tace Umma.....
Amsawa tayi
da fad'in ya akayi? Yau dai Kedai shar
Bariki tayi
dariya, tare da fad'in ina son miki magana Allah yasa zaki amince....
Umma din
tace name fah.?
Bariki tace
akan abbana, Mai zai hana kuyi aure, inaga zaifi muku.
Umma tace
aure? Dawa Rufamin asiri, barni inyi
abunda ya kawo ni.
Bariki tace
kin fiso ki zauna babu aure??
Tace a'a ina
so inyi mana inna samu dai dai ni
Bariki tace
gashi kin samu
Dariya tayi
tare da fad'in shiya ce miki zai aureni? Ko Kece kike son had'awa??
Bariki tace
shiya Aiko ni inyi miki magana, kuma naga Wlh auran shiya dace daku.
Tace hakane,
Allah ya tabbatar mana da alkhairi, saiki fad'a mishi na amince
Bariki tace
Alhmdlh, amma dan Allah Ayi bikin Kafin aurena..... Nan dai sukai ta tattaunawa suna cikin fira
habib ya fad'o kaman an jefoshi
Bariki tace
miye haka ko sallama babu
Tsaki yayi
tare da fita ya tsaya a kofar d'aki yana gafaranku dai masu d'aki, tare da kuso Kai.....
Bariki tace
wannan ne sallama??? Ai b....
Yace dakata
Mlm, nifa ban gane miki ba, tunda Yarima ya fara soyayya dake kika koma wata
iri iri, in ke kin zama ustaziya ni barni yanda nake.....
Bariki tace
Allah ya shirya, ni bama wannan ba zauna kaji.....
Kallon tara
saura kwata ya watsa ma bariki, sannan yace wlh Ina gab da in Tsiga miki rashin
mutunci, Idan kina kaini jinsin da ba nawa ba.....
Tace Allah
ya baki hakuri, zauna dan Allah
Zama yayi
yana bud'e hanci wai shi a dole ranshi a bace yake
Bariki tace
iyayen Yarima sun Aiko har Sun tafi
Yace haba
dan Allah?? Gud'a ya saki tare da fad'in inama inada duwawu babba dana tashi
nayi rawa da duwaiya guda d'aya....
Bariki
dariya tayi tare da fad'a ma habib yanda aka yanke bikin nan da wata biyu
Habib yace
Wlh bariki ban San mai yasa ba, ina sonki da Yarima,...
Bariki tayi
dariya tace ngd kawata, nan suka shiga tsara yanda za'a gudanar da bikin da
yanda za'a samo kawayen Haya duk habib yace abar komai a wajanshi......
Sannan
maganan gyaran jiki irinsu dilka, maganin Mata bariki tace y'ar Maiduguri take
So,da yar Sokoto
Suma habib
yace duk zai Kawo, cikin satin nan dan a Fara , sunyi magana Sosai inda tabi
habib suka je maraban jos domin ta Fara had'a kayanta wanda take bukata wanda
bata so kuma ta bayar.....
Koda suka je
sunga haulat ita da Hjy babba suna magana, ganin bariki yasa haulat ta nufi
bariki Tana fad'in Indai za'aga wannan kina wajan.....
Habib yace
Wlh Haulat zan miki bura uba, ban so
Tabe baki
Haulat tayi tana bashi hakuri,
bariki kam
wajan hjy babba ta nufa tana fad'in haka hjyta har yanzu fushin ake dani?.
Hjy babba
yace kyaji dashi, ni Kinga karki batamin rai yanzu da yamman nan
Bariki tace
haba hjyta kiyi hakuri mana
Hjy babba
yace Wlh bariki kina bani mamaki, da kyanki da kuruciyarki da lafiyanki, amma
kice zaki aure, keda ake rububinki haba bariki
Bariki tace
hjyta adai yi hakuri
Hjy babba
yace ya wuce yana tabe baki
Bariki tace
godiya nake tare dayin gaba ta nufi d'akinta.....
Tana cikin
had'a kaya haulat tazo, ganin bariki nata aikin had'a kaya yasa haulat tace
badai bikin yazo ba??
Bariki tace
eh Wlh, Kinga wata biyu aka sa, gwara in fara had'a kaya, in kyautar dana
kyautar wa inbar na Bari
Haulat tace
hakane, ni har yanzu ba'a fad'amin dan wani gari bane ko sunanshi
Bariki tace
saurin Mai kike ki jira koma Waye zaki gansa in lokaci yayi
Haulat tace
Allah ya kaimu, nan ta Fara taya bariki had'a kaya, haulat ta d'auko wata Leda
nan kayan suka zube dan ledan ya fashe, Aiko ayabar roba suka fito...... Haulat d'auka ta farayi taga har guda biyar
tace bariki dama kina dasu?? Ah ba banza
ba kika daina harka da maza ba, ashe kina da abunda yake d'ibe miki sha'awa
Bariki kai
ta girgiza tare da cema haulat ki d'auka duka na baki, ni ban taba amfani dashi
ba, yanda aka bansu haka na ajiyesu dan banda abunda za suyi min
Haulat ta
dinga godiya tare da fad'in amma wanda ya baki yasan kina son babban ayaba
tunda harya baki....
Bariki tace
Alh madu Yaban dan iskan tsoho, ci gaba da had'a kayanta tayi harta gama taba
haulat kyautan kayanta da yawa.
Haulat tana
ta mata godiya duk yanda haulat taso bariki ta fad'a mata wa zata aura amma
bariki ta'ki Tadai fad'a mata dan gidan sarauta ne, abunda kawai bariki ta
fad'a mata kenan..........
A kwana a
tashi babu wuya wajan uban giji, bariki ta gama istabra'i, sannan iyayenta sunyi aure, mai martaba ya
siya musu Gida Mai kyau 4bedroom a u/kanawa inda anan iyayen nata na Bariki
suka tare, sannan bariki tace ta bar musu gidan halak malak, domin suna Mata
aiki yanda ya dace, bariki ta K'ara kyau da haske domin ana mata gyaran jiki
Sosai.....
Yau bikin
bariki da Yarima baifi kwana Goma ba,
Yarima yanzu ba kullum yake zuwa wajanta ba, domin aiki sunyi mishi
yawa, ga hidiman biki, gana asibiti ga fitinar zinatu, abubuwa sunyi mishi yawa
Sosai..... Yana office ya Gama duba patient yaji yana bukatar ganin Zainab
dinshi dan haka ya tashi ya nufi gidansu, wanda yanzu in yazo ciki yake shiga
dan akwai falon ba'ki a gidan, kiran Zainab din yayi yace ta sameshi a waje
basai y'a shigo ba.
Fita tayi
inda ta sameshi a mota ta bud'e ta shiga tare da gaidashi
Mai makon ya
amsa sai yace Kai my princess Kinga yanda kike K'ara kyau kuwa?? Gskya ana
gyaramin ke dakyau,
Murmushi
tayi cikin jin kunya sannan tace Kai
Yarima wani kyau nake karawa?? Tayi maganan a shagwabance
Yace Zona
nuna miki tare da janyota jikinshi, wani irin kamshi ne ya daki hancinshi Wanda
tunda ta shigo yake ji, amma daya janyota jikinshi sai yaji kamshin ya fito
Sosai, gaba d'aya yaji jikinshi ya fara weak domin kamshin turaren yasa
jikinshi ya fara yin sanyi..... Itama ta
gefenta wani iri take ji domin maganin da ake bata ya tsumata Tana matukar
bukatar namiji amma babu yanda ta iya dole sai mijinta Bayan tayi aure, gashi
yanzu Yarima yana son tada mata bala'i.... Yarima Aliyu hura mata iska yayi a
fuska da sauri ta d'ago suka had'a ido
peck yakai mata a goshi tare da furta I love you my princess
Da sauri ta
lumshe ido
Ganin haka
yasa Yarima ya kura mata ido yana kallonta tare dajin wani irin mugun sonta na
K'ara shiganshi.... Jin shuru yasa ta bud'e ido a hankali idonta ya sauka cikin
kwayar idonshi da yake kallon nata idon.....
Dukansu wani irin yanayi mai wuyan misaltuwa suka shiga....... Karan
wayar Yarima yasa ya saketa ta tashi da sauri daka jikin nashi ta koma ta zauna
dakyau..... Daukan wayan yayi ya duba,
ganin mai kiran yasa bai d'auka ba, zinatu ce......
Bariki kam
gaba d'aya ta birkice, dan dan tabata dinnan da Yarima yayi har tana jin zuban
ruwa a cikin pant dinta, lallai ya kamata Yarima ya rage zuwa, ko kuma ya daina
tabata.... Domin Indai hakan zaici gaba
da faruwa zata sha wuya, ido ta lumshe tasan ba komai yake sata yawan sha'awa ba
sai maganin da take sha, wacce y'ar Sokoto take bata.....
Yarima ne ya
Katse Mata tunani da fad'in, my princess zan gudu, bata sim yayi guda d'aya
tare da cewa ta cire nata, baya son ta kara amfani dashi.....
Amsa tayi,
tace toh dama tun tuni take da burin canza layi, amma tana tsoran Kar Yarima
yace Mai yasa, yanzu tunda ya kawo mata, hankali kwance, sannan ya bata check
na 3mil yace a K'ara gyaran jiki domin naga suna gyaramin ke dakyau......
Tace Yarima
kafa ban kud'i cikin kwanakin nan, kaban a kalla wajan 7mil kace in siya kayan
akwati, kuma gashi kace May be gidanku su Kawo nasu gobe ko jibi, kai kamin
gashi gidanku zasu kawo, ga kud'i kuma kana karamin, gskya abun yayi yawa, ka
barshi.....
Bata fuska
yayi tare da fad'in in kin ciro kud'in ki zubar a bola tare da ajiye mata check
din a jiki.....
Ganin yanda
ya bata fuska, yasa tace Yarima kayi hakuri, wlh ba haka bane, naga hidimar
tayi yawa ne Sosai, Kaga y......
Yace enough,
komai na miki, kin can Canta inyi miki shi, and karki manta am your husband to
be, waya kamata inyi ma Abu Inba keba??
In my life ban taba kyauta ko wani abuba a nuna ba'a soba sai ke..
Da sauri
tace kayi hakuri plz na tuba, ngd Allah ya saka da alkhairi....
Jin ta fad'i
haka yasa yaji dad'i..... Ba komai yasa
Yarima ya bata wannan kud'in ba, sai sanin da yayi ba masu hali bane su, and
y'an uwanshi zasu Kawo akwati, ance ana bada kud'i, sai yasa ya bata wannan
kud'in dan iyayenta su bada tukwici...
Ajiyan zuciya yayi tare da fad'in zan tafi sai munyi waya,
Tace OK
Yace kin dai
ki zuwa kiga gidanki koh?
Tace Yarima
saurin Mai kakeyi?? Ka Bari har a kaini mana
Murmushi
yayi domin kin amincewanta yasa ya kara yarda damai tarbiya da kuma kamun kai
zai aura, sabanin matan yanzu da suka lalace suke ganin haka shine wayewa, tab
kunji Yarima shi'a dole zai aura ustaziya🤣
Sallama ya
Mata sannan ya wuce......
Bariki gida
ta shiga jiki a sanyaye lallai Yarima yana matukar sonta da yawa, hawaye ne ya
gangaro daka idonta, tare da tausayin kanta yanda zai dauketa in yasan ko ita
wacece......
Anata shirin
biki musamman ta gefen ango, domin dai ita amarya rufa rufa take ma auran ba
kowa bane ya sani, sai dai zargi da wasu sukeyi......
Ranan da
za'a kawo akwati saida bariki da habib sukai hayan mata guda biyar, An kawo akwati
guda ishirin da hud'u, dozen biyu kenan, kaya ne makil na Kece raini masu
tsadan gaske..... Ganin yawan kayan yasa
umman bariki taga 1mil yayi kad'an dan haka ta sami bariki dake boye cikin wani
d'aki, tace ya kamata a K'ara kud'in nan Kinga uban kayan kuwa? Bariki kara 1mil tayi ya zama 2mil, nan aka
basu kud'in tukwici, tare da abun ciye ciye da aka tanadar musu, bayan sun fito
sis din Yarima Fatima tace Kai ance yarinyar talakawa ne amma har da bata 2mil,
Aini ban d'auka zasu bada koda dubu d'ari ba, dariya sukayi sannan aka canza
firan,
Bayan sun
tafi bariki ta fito tana kallon kayan, itama Abun ya bata mamaki ganin kaya
masu uban yawa da tsadan gaske, yanzu ga akwati ishirin da hudu, gashi kudin da
Yarima ya bata itama ta siya guda sha biyu, duka talatin da shida.....
Ummanta ta bariki tace Kai gskya ki gode Allah
y'ar nan, Yaron nan yana sonki Sosai, ji uban kaya sannan kayan d'aki yace baya
bukatar komai, kai Kinji dad'i wlh
Bariki
murmushi kawai tayi jiki a sanyaye, domin sai yanzu ta Fara jin tsoran abunda
take kullawa na auren bariki, da tana ganin abun kaman wasa, amma tunda har
taga akwati yau an kawo ta tabbatar Abun dagaske ne, d'aki tayi ta Fara rusgan
kuka tare da fargaban abunda zai biyo baya..... Hmmm Allah ya kyauta dai zan iya
cewa
Biki ya kan
Kama amma amarya bata cikin nutsuwa kullum tana cikin fargaba, harta rame
saboda damuwa, kullum bata da wani aiki sai kuka tare da K'ara tsanar rayuwar
bariki........ Tana cikin wannan kukan Yarima ya kirata, da sauri ta seta kanta
dan Kar ya gane sannan ta d'auka...
Gaidashi
tayi
Amsawa yayi
tare da fad'in ya naji muryanki haka??
Da sauri
tace mura nakeyi Yarima
Yace toh
fah, Allah ya sawake zan Aiko miki da magani.
Tace nasha
tun dazu
Yace OK, toh
ya shirye shirye?
Tace
Alhamdullilah
Yace za'a
Aiko miki da kayan da zaki saka a dinner sannan masu makeup za suzo suyi miki
ranan, lil sis taban sa'ko in fad'a miki
Bariki tace
ok Allah ya kaimu
Ya amsa da
Ameen, sun d'an taba fira Kafin sukai sallama.....
Yana ajiye
wayar gimbiya zinatu ta shigo, Tana fad'in yanzu Yarima saboda cin fuska a
cikin gidan nawa kake waya da wacce zaka aura??? Kuka ta fashe dashi tare da
fad'in haba Yarima Wlh kana cimin fuska da yawa maina maka haka da kake Yimin
wannan abun??
Ganin yanda
take kuka sai yaji ta bashi tausayi, rarrashinta ya farayi.....
Gimbiya
zinatu ji take kaman ta tureshi Dan tsabagen kishi, Allah ya sani da badan
gimbiya Amina tana kokarin hanata wani Abun ba da Wlh babu abunda zai hana tayi
ma Yarima mugun tujara, amma Gimbiya Amina tace tayi hakuri ta Bari Ayi auran
zata nema Mata mafita, yarda da gimbiya Amina da tayi shine yasa har take dan
jurewa, amma ji take kaman zata mutu dan kishin Yarima take Sosai, bata son
ganin ko wace mace kusa dashi......
Toh biki ya
rage saura kwana biyu, inda a yau za'a gudanar da dinner, bariki da habib sunyi
hayan kawaye Wanda sune kawayen amarya, cikin kawayen harda haulat da khairat,
zuwan haulat gidan iyayen bariki yasa ta gane yanda bariki ta shirya auranta,
ta gano tayi amfani da iyayen bariki, haulat ta kalli bariki tace gskya kinyi
dabara, nima Ina tunanin haka zamma farhan, in samo iyayen bariki
Bariki ganin
Haulat ta gano komai, yasa tace inko za kiji shawarata karki Fara yin aure da
iyayen bariki, gwara ki koma Gida wajan danginki
Haulat tace
Hmmm kedai kawai Ayi sha'ani,
Anyi ma
amarya makeup na Kece raini, tayi mugun bala'in yin kyau, gaba d'aya makeup din
da aka mata yasa ta canza, ta kara mugun kyau dama yaya balle an kara da wanka,
an shiryata cikin wani tsaddan material Mai Kama da less anyi mishi dinkin
doguwar riga, k'asan kuma anyishi da fad'i kaman weeding gown, an saka mata
head maroon kayanta kuma golden, ba karamin kyau tayi ba, kawayenta kuma sunsa
kaya red head golden, ba karamin kyau bariki tayi ba, da kawayenta, 7 dai dai
aka turo motoci dan d'aukan amarya da kawayenta zuwa wajan dinner da za'ayi a
cikin garin kaduna, duk y'an uwan ango suna kaduna, an d'auki amarya an nufi
hall da ita, inda motarsu na zuwa na ango yazo, dan haka Yarima ya fito ya nufi
motar da Zainab ke ciki, Yarima daya ganta ido ya kara bud'ewa ganin irin kyau
data K'ara kaman ba ita ba, dama yasan tana da kyau gashi anyi mata makeup,
lokaci d'aya kuma sai yaji yana kishin ta shiga Ayi ta kallonta, ya dad'e a
motar yana nazari akan baiso ta shiga.....
Itama ta
gefen amarya fargaba take, karta shiga taga Wanda ta sani, asiri ya tonu.....
Jin Yarima
shuru yasa usman yazo yana buga glass din motar
Bud'ewa
Yarima yayi tare da fad'in Usman gskya aje abama mutane hakuri, an fasa wannan
dinner din, suci abinci kawai su wuce
Usman yace
Yarima. Kasan Mai kake fad'a kuwa?? Plz Yarima ku fito mu shiga
Yarima yace
kasan inna fad'a magana bana canzawa koh??
Usman shuru
yayi yana nazari can yace dan Allah Yarima kayi hakuri ka duba girman Allah
karka bamu kunya......
Yarima ya
dakatar dashi da fad'in am telling you kayi abunda nace, wannan umarni ne....
Karan wayanshi yasa ya d'auka ganin lil sis
Yana d'auka
tace Bros ku shigo mana kowa na jira, dan Allah kuyi sauri
Yace sis am
sorry bazan zo ba, kuba mutane hakuri .....
Tace what?
Tare da tashi ta fito waje dan taji dakyau, hango usman tayi da Yarima a tsaye
da sauri ta nufesu, tana fad'in bros miye haka plz kuzo ku shiga....
Zaiyi magana
tace plz koso kake ace akwai matsala ne??
Yace let
people say what ever, nidai bazan shiga wannan wajan ba.
Hafsat tace
bros akan wani dalili?
Yace ban son
ayita Kalle min Mata, inada kishin iyali na
Hafsat hannu
ta d'aura a Kai, alaman takaici, danta d'auka wani abune akayi mishi da yasa
yace bazai shiga ba, motar da bariki take Hafsat ta nufa, sai gata ta fito
Ganin amarya
a waje yasa Yarima ya fara yima Hafsat fad'an Mai yasa zata fito mishi da
mata....
Hafsat tace
bros nifa bani na fito da itaba
Kallon
bariki yayi yace Oya muje in kaiki gida
Tace Yarima
plz muje mu shiga, zaiyi magana tace dan Allah, karka sa mutane suyi zargin
wani abu tana maganan tare da kokarin San zubar da kwalla.....
Ganin haka
yasa yayi dan tsaki tare da fad'in karki Fara cewa zakiyi min kuka a nan, dan
naga kina da Arhan hawaye, babu yanda Yarima ya iya dole ya shiga shida
abokanan shi da amarya da kawayenta, cikin hall din yayi mugun tsaruwa, wajan
zaman amarya da ango daban su biyu, y'an jarida da masu hoto sai d'auka suke,
kowa yana fad'in amarya da ango sun dace dinner din ya had'a manyan mutane ciki
harda Mai martaba, Yarima bai San zaizo ba saida Ya ganshi shida abokanan shi,
harda Mai girma governor da wasu masu mukami a gwamnati sun halarta, anyi watsi
da naira kaman baza'a mutu ba, an yanka cake daka nan akace amarya da ango suzo
suyi rawa, nan suka fara rawa duk da bariki ba a sake take ba, dan tana jin
tsoran ko akwai wanda ya Santa a wajan, nan aka fito ana watsa musu naira mum
din Yarima tayi musu liki Sosai, a cikin masu likin idon bariki ya sauka akan
Alh madu, dam gabanta ya fad'i, musamman irin murmushin da taga yana sakar
mata, gaba d'aya jikinta taji ya saki babu kwari, Yarima kaman ya Lura da ita gashi
kuma mutane sunyi yawa ko ince maza dan haka Yarima yaja hannun Zainab suka
koma suka zauna, Anci ansha kowa ya watse, Yarima yakai bariki gida da jikinta
yake a muce ganin Alh madu a wajan dinner, yanda ta gode Allah ta canza layi ma
balle ya mata barazana, toh inya fad'a ma Yarima fah?? Nan taji gabanta ya fara fad'i
Bariki harta
Washe gari tana cikin zullumi Kar asirinta ya tonu, haulat Dai da khairat sunyi
Mata kara domin a gidan suka kwana, dasu kuma ake komai, bariki na kwance
haulat tace wai lafiya kuwa naga kinyi shuru??
Bariki tace
kalau nake
Haulat tace
dan bani wayarki in bud'e hotspots banda data gashi Ina son tura Abu.
Password din
wayar bariki ta cire sannan ta mi'ka ma haulat wayan.....
Toh rana dai
bata Karya inji masu iya magana yau juma'a aka d'aura auren Zainab musa da
angonta Yarima Aliyu, akan sadaki naira dubu hamsin inda dubban jama'a suka
shaida......
Bariki tunda
taji an d'aura take ta godema Allah, domin anyi auranta cikin nasara ba tare da
Yarima yasan gaskiya ba, a hankali tace yau zan fad'a maka koni wacece Yarima
Indai aka kawo ni gidanka,..... Karfe hud'u dai dai aka zo aka d'auki amarya
inda aka tafi da ita Zaria a can zata zauna Kafin a dawo da ita kaduna, gefen
Yarima Nada aka kaita inda aka gyarashi harta wanda suka kawo amarya bariki
hayansu tayi, an karrama amarya da danginta wajan su abinci da duk abunda suke
bukata, nan sukace zasu wuce tunda sun kawota, anyi musu shatara na arziki
Kafin nan suka wuce......
Wajan karfe
9 Yarima ya shigo d'akin amarya ba tare da Aboki ko d'aya ba, dan yace kallon
da suka mata wajan dinner ya isa haka, bariki na zaune akan gado Yarima ya
shigo tunda ya shigo gabanta ke faman fad'i, inda take ya nufa tare da cire
mata gyalen dake kanta yace Alhmdlh tsarki ya tabbata da Allah daya nuna min
wannan ranan, janyota yayi jikinshi yayi mata wani irin runguma, har tana jiyo
ajiyan zuciyarshi, lokaci d'aya ya saketa tare da d'agota ya sauketa k'asa yace
my princess muje muyi alwala muyi ma Allah godiya..... Gabanta taji yana fad'i yaka mata Yarima
yasan gaskiya Kafin wani abu ya shiga tsakaninsu, wayarshi dake ajiyu yayi kara
d'auka yayi yaga number kaman Karya d'aga, sai kuma ya d'auka, ban son mai aka
fad'a mishi ba naga ya kashe da sauri tare da fara danna wayar duk wannan
abunda ake suna tsaye shida bariki suna kallon juna amma shi idonshi nakan
wayar.... Lokaci d'aya hawaye ya fara
zuba a idonshi tare da fad'in today is our wedding night, the day dat I have
waiting for since d day dat I have meet u, but you destroy my life, you have cheated
me..... Cikin tashin hankali tace Yarima maiya far.... Yace keep quiet tare da
ri'ke kirjinshi alaman yana mishi ciwo yana kokarin yin magana ya fara tari
Sosai lokaci d'aya yayi k'asa......
TOH MASU MIN
KORAFI IN K'ARA YAWAN RUBUTU YAU DAI NA K'ARA, AMMA KUDA KUGA WANI POSTING DIN
SAI NAN DA KWANA UKU, BUT IN NAGA COMMENTS DINKU YAU YAYI YAWA MAY BE GOBE IN
MUKU
not edited
MARYAM OBAM
No comments