BARIKI NA FITO (BOOK 2) 17
BOOK 2
PAGE 17
Tari yake
Sosai, bariki kuka ta Fara Tana fad'in Yarima Mai yake damunka?? Tare da
tabashi tana son d'ago Shi ,hannunshi da yasa a baki yana tari ya cire ya fara
kokarin tureta alaman tabar tabashi, amma jikinshi babu kwari ya kasa tureta
din...... Wani irin tari yayi tare da
yunkurin yin amai saiga jini nan.....
Wani irin ihu ta saki mai ban tsoro tare da kiran nashiga uku Yarima
maiya
sameka??
Ganin jinin
a bakinshi yana fita yasa ta fita da gudu, tana fita taga fadawa tace dan Allah
kuzo Yarima zai mutu, tana maganan tana
kuka da ihu, kuzo mu kaishi asibiti.....
Da sauri suka shiga wasu kuma suka je fad'ama iyayenshi, koda fadawa
suka shiga ganin Yarima sukayi a kwance yana wani irin nishi ga jini na zubar
mai a baki, da sauri suka D'aukeshi suka fita dashi, suna cikin sashi a mota
mum dinshi tazo, ganin halin da d'an nata yake ciki yasa ta Fara fad'in
Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, Yarima maiya sameka, lokaci d'aya kuma tasa
kuka, shiga motar tayi da sauri suka nufi asibiti...... Bariki Kafin ta karaso
har Sun wuce dan haka ta Fara cewa sauran fadawan muje ku kaini dan Allah inda
suka je..... Ganin kanta ko dankwali
babu yasa wasu kuyangi dake tsaye wajan suka karaso suna fad'in Allah ya
taimaki gimbiya, ki koma ki saka mayafi sai a kaiki,.
Sai a sannan
bariki tasan a halinda take da gudu tayi ciki, inda ta d'auko mayafinta tana kokarin fita wayar Yarima dake d'akin ya
fara K'ara dole yasa ta koma ta d'auki wayar babu suna number ne ke kiranshi
harya tsinke bata d'auka ba..... Fita
tazo yi lokaci d'aya kuma ta tsaya cak domin tunawa da abunda ya faru da
Yarima, wanda tunda aka kirashi ta rasa gane kanshi,har wannan abun ya sameshi,
danna wayan tayi da nufin ta shiga taga Mai aka turo mishi, gani tayi akwai
password, shuru tayi tana nazari Mai Yarima ya gani?? Kodai wani ya fad'a mishi koni wacece?? Gabanta taji ya fara fad'i tunawa da kalaman
daya Fara Mata Kafin ya fad'i...... Wani
irin kuka ta saki mai ban tausayi, tare da fad'in shikenan2 sunyi nasara Sun
fad'ama Yarima koni wacece kuka take Sosai, lokaci d'aya kuma ta fita da gudu
inda taga mota na jiranta shiga tayi domin aka kaita asibiti da yake fadawa sun
San asibitin da suke zuwa nan aka nufa da ita dan suna da tabbacin can aka Kai
Yarima, tana mota tana kuka......
Kafin kace
Mai har labari ya bazu cikin masarauta, Yarima Aliyu bashi da lafiya rai a
hannun Allah, har wasu na cewa jini ke fita a bakinshi hala amaryanshi ba
budurwa bace, wasu kuma suce kodai wani abu tayi mishi?? Haka dai ake ta jita jita, koda kuyangin
gimbiya zinatu suka fad'a mata cikin tashin hankali itama tayi asibitin.....
Yarima Aliyu
ko Kafin akai asibiti, ya daina koda motsi, ana zuwa akai emergency dashi,
likitoci sukai kanshi aka fara dubashi, tare da bashi taimakon gaggawa....
mum ta kasa zama sai kuka takeyi ga fadawa a
wajan da yawa, kowa ya shiga cikin damuwa.
basu dad'e ba saiga bariki ta karaso Tana
kuka, tare da fad'in mum Ina Yarima?? Ina Yarima?? Mum din ri'keta tayi tare da rungumeta, ta
kasa ko magana sai shafa ma bariki baya takeyi alaman tayi shuru......
Suna cikin haka saiga Zinatu tazo cikin Tashin
hankali ganin Bariki wajan mum ko ba'a fad'a mata ba tasan itace amaryan da
Yarima ya auro, da sauri ta nufi bariki ta fincikota tare da watsa mata Mari
Tana fad'in mai kika ma Yarima?? Mai kika mishi?? Kuka ta saki Zinatu tare daci
gaba da fad'in Wlh Idan wani abu ya sameshi saina kasheki W.......
Mum sai
yanzu ta iya magana, tace Zinatu kina da hankali kuwa?? A gabana kike wannan
abun?? Shi Yarima dinne yace miki ita ta
mishi wani abu??
Cikin kuka
tace mum, daka ita sai shi, Nasan wani abu tayi mishi......
Mum tace ya
isa haka, plz ki barni inji da abunda yake damuna ban son rigima....
Bariki kam
tunda zinatu ta mareta take ri'ke da wajan Tana kuka, ko bata tambaya ba tasan
itace Uwar gidan Yarima Aliyu......
Bariki tasan lallai ko ba'a fad'a ba dole kowa yayi zarginta, abunda
Zinatu ta fad'a gaskiya ne..... Kuka tayi k'asa tanayi tare da fargaban Kar
wani abu ya sami Yarima dan bazata iya jura ba.....
Kowa na
cikin Tashin hankali, ga doctors har yanzu basu fito ba...... Suna nan zaune saiga Mai martaba shida Hafsat
Sun zo cikin Tashin hankali.
Mum ganin
Mai martaba yasa ta tashi ta nufeshi tana kuka, tare da fad'in ina jin tsoro
Kar Yarima ya mutu Aman jini yakeyi Ina tsor.....
Toshe mata
baki Mai martaba yayi, tare da fad'in ki daina fad'in haka, Hafsat itama kuka
ta Fara cikin Tashin hankali.....
Duka kowa
shuru yayi babu Mai rarrashin wani, suna nan tsaye d'aya daka cikin doctors din
ya fito, suna ganinshi suka nufeshi tare da fad'in Dr ya ake ciki, ganin Mai
martaba yasa yace ranka ya dad'e wacece Zainab a cikin nan??
Da sauri mum
tace ga tanan tare da nuna bariki, yace ok tare da kallon Bariki yace taso
muje......
Da sauri ta
tashi tabi Dr, kowa da abunda yake sakawa, Zinatu ta Fara fad'in mum kin gani
ko kin gani wlh itace tayi mishi wani abu.....
Kowa shuru
yayi ya kasa cewa koda uffam.... Suna jira suga ikon Allah......
Koda Bariki
suka shiga oxygen din da akasa ma Yarima yana k'asa alaman yana son d'aukewa,
kuma yana saka zero shikenan mutum ya mutu, da sauri Dr yace plz ki mishi
magana sunanki yake ta kira pls say something karku rasa shi.......
Da sauri ta
ri'ke Mai hannu tana kuka tare da fad'in Yarima karka bari wani abu ya
sameka..... You know that I can't live
without you, plz Yarima ka tashi kasan ina Sonka kaine rayuwa na, wlh bazan iya
juran inga wani abu ya faru dakai ba......
Lokaci d'aya
oxygen din ya fara k'aruwa alaman numfashin shi yana son dai daituwa.... Likitocin ganin haka yasa suka fara kallon
juna alaman jin dad'i an fara nasara..... Bariki kuka take Sosai tana fad'in
karya mutu ya barta....
Idonshi dake rufe ya fara zubar da
hawaye...... Lokaci d'aya numfashin shi
ya dai daita......
D'aya daka
cikin doctors din yace ma Bariki yauwa komai yayi dai dai mu jira muga kuma
yanda Abun zai kasance amma muna bukatar ki zauna har muga farkawanshi, muna
nufin Kar kibar asibitin nan har sai munga ya farka ....
Cikin kuka
tace babu inda zani Ina nan tare dashi
Dr din fita
sukayi, inda suna fita Mai martaba yace ya akayi?? Mai yake faruwa dashi??
D'aya daka
cikin Dr din yace ya samu bugawan zuciya ne, ina tunanin yaga abunda ya bashi
tsoro ko mamaki, kuma daka duka alamu abunda ya gani ko yaji yana d'aya daka
cikin abu masu muhimmanci a rayuwanshi, hakan yana faruwa wasu ma rasa ransu
suke, a gskya masu rasa ransu ma sunfi yawa amma shi yayi Sa'a ko ince mun samu
mun ceco rayuwanshi tare da taimakon Allah da kuma wannan baiwar Allah dake
ciki, magananta da yaji shine yasa zuciyarshi ta Fara harbawa, inda badan ita
ba toh gaskiya dasai dai kuji mummunan labari , dan haka dole ta zauna dashi
muga yanda Allah zaiyi.....
Mai martaba
godiya yayi ma Dr din tare da fad'in zamu iya ganinshi?? Sannan kana ganin zai
tashi babu wani matsala??
Dr yace zaku
iya ganinshi amma plz Kar kuyi magana, sannan zai tashi insha Allah Indai
yarinyar na kusa dashi kuma yana jin magananta a kusa dashi.....
Mai martaba
yayi ma Dr godiya, sannan suka shiga d'akin, ganin Bariki sukayi a zaune kusa
dashi hannunta na ri'ke da nashi tana kuka.....
Kowa tsayawa
yayi yana mamakin irin wannan Abun musamman mum damai martaba, ita dama zinatu
bata shigo ba domin maganan Dr yasa taji wani iri tare da takaici..... Mum ce
ta k'arasa kusa da inda Yarima din yake tare da kamo d'ayan hannunshi,
fuskanshi tayi fayau ga hawaye a idonshi na zuba..... Mum itama hawayen ne yake zuba daka idonta,
kowa dake wajan ya tausaya mishi......
Mai martaba ganin mum nason kuka mai sauti yasa ya kamota sukai waje,
Hafsat da Bariki suka zauna a d'akin
Zinatu ce ta
shigo d'akin ganin zinatu yasa bariki tashi tabar d'akin domin irin kallon da
taga zinatu din nayi mata, kuma ko babu komai ya kamata ta dan bata waje ta
gana da mijinta duk da bai farka ba.....
Fita Bariki
tayi tana fita, Mai martaba yace Zainab ya kika fito?? Ko wani abu kike bukata??
Tace a'a
Abba cikin jin kunya, na d'an basu waje ne.....
Mai martaba
ya gane ta fito ne saboda Zinatu.......
Mum tace
Zainab bai kamata ki fito ba ai, maza ki koma Kinji.....
Tace toh mum
jiki a sanyaye Bariki ta shiga, abubuwa sun mata yawa, na farko Tana zullumin
Mai aka fad'ama Yarima a waya, sannan maiya gani, duk wannan Abun suke ta faman
Mata yawo a Kai..... Koda Bariki ta shiga zintau fita tayi
Bariki zama
tayi kusa da Yarima tare da kurama fuskanshi ido, har yanzu yana hawaye, gaba
d'aya zuciyarta ta tsinke, shidai har yanzu bai farka ba, toh wannan hawayen
fah????..... Kiran Hafsat akayi a waya
ta tashi tabar d'akin Tana fita kaman ance Yarima ya bud'e ido , a hankali ya
bud'e idonshi ya sauka akan na Zainab wacce itama shi take kallo tana murna
tare dason yin magana murna ya hanata......
Murmushi ya
sakar mata, tare da kamo hannunta ya ri'ke tare da matse su.....
A hankali tace Yarima Ina Sonka I can't live
without you, tana maganan tana kuka, tace I was scare with your condition
I......
Hannunshi
yasa ya rufe Mata baki yana kokarin yin magana ya tsaya alaman ya tuna da wani
abu....... Lokaci d'aya ya sake mata
hannu tare da fad'in leave from hare I hate to see your face........
Cikin kuka
tace Yarima zainab din'ka ce Yarima nice maina......
Ya daka mata
tsawa tare da ri'ke kirjinshi yace I said leave from here ....... Su mum dake
waje Suka shigo harda su zinatu, ganin
Bariki na kuka Yarima shima hawaye ne ke zuba a idonshi gashi ya ri'ke
kirjinshi...... Kallon iyayenshi yayi
tare da fad'in mum tell her to leave from here....... Kowa kallonshi yake cikin mamaki da sauri
Hafsat ta fita kiran doctor...... Mai
martaba yace Aliyu matarka ce kake koranta?? Maita maka??...... Yace Abba plz tell her to leave I don't want
to see her face.... Why am I still
alive.... Dai dai lokacin doctor yazo yace kowa yabar d'akin........ Bariki da sauri ta fita Tana kuka lallai ta
tabbatar an fad'ama Yarima ko ita wacece
kuka take Sosai tare da barin asibitin ba tare da sanin kowa ba......
Hmmmm Ashe
masoya novel's din bariki suna da yawa?? Ban taba sani ba sai jiya🤣🤣🤣 lallai kuna son posting naga ruwan
comments harda Wanda ban San suna karantawa ba, jiya Sun zuba comments, tunda
hakane nima daka yanzu zan daina posting kullum Indai bakwa zuba comments kunga
50 50 kenan kuyi rowan comments inyi rowan posting😆😆😆 Ina sonku masoya novel's dina
MARYAM OBAM
No comments