BARIKI NA FITO (BOOK 2) 15
BOOK 2
PAGE 15
Tashi tayi
ta fita inda ta sameshi cikin mota....
Gaidashi
tayi cikin kulawa tare da fad'in ya aiki??
Mai yakon ya
bata amsa saiya kafeta da ido, ba komai yake tunawa ba sai kalaman mahaifin
nashi, inda yace karya K'ara mishi maganan auran da yake son k'arawa ..... Ido
ya lumshe yana tunanin abubuwa da dama, ya tabbata bazai iya juran rashin
Zainab ba, amma ya, ya iya tunda mahaifin nashi haka ya bashi umarni.... Tunda yake abbanshi bai taba cewa Kar yayi
abu ba ya ketare, yana ji a jikinshi bazai iya juran a hanashi auran Zainab
ba......
Jin yayi
banza da ita yasa ta d'ago taga ita yake kallo da sauri tayi k'asa dakai tare
da fad'in Yarima lafiya kuwa??
Murmushi
yayi tare da fad'in lafiya, kawai I miss you ne...
Murmushi
tayi tace kullum fa saika ganni jiya ne kawai baka ganni ba....
Yace hakane,
jiyan kawai da ban ganki ba, yasa naji kaman Nayi shekara ban ganki ba
Dariya tayi
mara sauti domin taji dad'in maganan da yayi.......
Sun d'an
taba fira, sannan ya mata sallama ya wuce.....
Bayan Yarima
ya koma Gida direct wajan mum dinshi ya nufa, bayan ya gaidata ya zauna kusa da
ita tare da fad'in mum plz ina son magana dake which maganan ya shafi
rayuwana.....
Gaba d'aya
hankalin mum din yayi kan Yarima wanda magananshi ya bata tsoro, musamman daya
ce maganan dazai Mata ya shafi rayuwanshi..... Tace Yarima Mai ya faru?? Maiya sameka? Wani abu ne?
Yace mum
akan maganan k'arin auren da nake son yine. Plz mum Ina son yarinyar Sosai, mum
Bari kiji tun a mafarki na Fara ganinta........
Mum tace
mafarki??
Yace eh,
tare da bata labarin abunda yake faruwa...
Ya d'aura da fad'in mum had'uwa na da yarinyar had'in Allah ne, ina
matukar sonta, mum Idan aka hanani auranta ban iya j......
Da sauri mum
tace ya isa haka, jikinta a sanyaye tace Yarima zanyi magana damai martaba,
Kaje ka huta dan naga alaman kaman yanzu ka dawo.....
Yace eh mum,
tare da tashi ya fita.....
Mum shuru
tayi tana nazari, lallai ya kamata abar Yarima yayi wannan auran, tunda har Ya
iya cire kunya ya Mata bayani irin haka.....
Tashi tayi ta nufi gefen mijin nata , toko ci Sa'a shi d'aya ne, zama
tayi tare da fad'in Barka da yamma.
Mai martaba
Ya amsa da yauwa, yana ga kaman kina cikin damuwa? Domin Fuskanki ya nuna
hakan.
Tace inada
magana ne akan Yarima.
Da sauri mai
martaba yace maiya sami Yarima din??
Tace babu
komai magana ne akan auranshi da yake son karawa....
Mai martaba
yace ba jiya nace abar wannan maganan ba, sai nan gaba
Tace hakane,
amma ina son fad'a maka Yarima yanzu yabar wajena, akan maganan auran nashi,
labarin yanda sukai da Yarima ta fad'a mishi harda mafarkin da Yarima yakeyi,
sannan tace ina son in baka shawara ,tunda muke da Yarima bamu taba cewa yabar
Abu ba, sannan daka baya ya dawo da maganan......
Mai martaba
ya dakatar da ita da fad'in, lallai wannan babban magana ne, Yarima yana mana
biyayya a matsayin mu na iyaye.....
Tunda har na hanashi maganan ya kara taso da ita bai kamata in hanashi
ba, domin hanashi zai iya sawa ya bijire mana, domin shi SO daban yake, sannan
muma ya kamata mu masa adalci mu amince da duk wata bukatarshi Indai bai sabama
Shari'a ba..... Yau na fahimta abunda ya dad'e yana damuwa, lallai iyaye k'alu
bale garemu Idan d'anka ko y'arka suna maka biyayya tare dajin duk wata magana
taku, Indai yaron ya Kawo muku abu kuka nuna bakwa so, Indai ya dage Toh ku
tayashi son Abun tare da mishi fatan alkhairi..... Sau da yawa wasu iyayen suke saka yaransu
suke bijire musu Bayan yaran suke da gskya amma iyayen Suki yarda da kudiran
yaran, in ba'a sami Mai hakuri ba saiya bijire musu, yaka mata iyaye su dinga
Lura da miye yaransu suke so tare da abunda suke bukata.... Kar matsayinku na iyaye yasa ku manta hakkin
yaranku akanku...... Haka zalika Kuma
yaran Kar soyayya yasa ku bijire ma iyayenku ,domin Kaf duniya babu mai muku
son gskya kaman iyayenku....... Akwai
wani labari da naji na wani yaro da yake son auran wata yarinya....... Yarinyar kowa yasan bata ji, Ma'ana dai y'ar
iska ce yarinyar, lokacin da yaron Ya fad'ama ma iyayenshi sai suka k'i yarda
suka ce ya nemi wata, shiko yaron yace Wlh ita yake so, aka buga aka raya,
Baban yaron yace sam bai yarda Yaronshi ya auro yarinyar ba domin y'ar iska
ce....... Ganin yanda babanshi ya dage,
sai yaron Ya daina musu komai dama iyayen ba masu karfi bane, yaron ke musu
komai tunda yana aiki,...... Toh Kunga irin matsalolin dake faruwa, a sanda
naji wannan labarin Nayi takaici Sosai, ai iyaye iyaye ne, yaka mata mu dinga
hakuri dasu, mu muna ganin mune akan dai dai, haka suma suke gani sune akan dai
dai, in kayi hakuri kabi umarnin su, kasan kwana nawa za suyi a duniyar?? Koko saika rasa su zaka Fara kuka dayin dana
sani?? Wlh baka taba sanin muhimmancin iyaye sai basa raye, sai munyi hakuri da
iyayenmu sau da yawa kana ganin abunda yake dai dai kuma kowa yasan dai dai ne
amma su sai suce sam, in mutum ya duba Aida basa haka, yanzu harda girma daya
kamasu sai yasa suke irin haka, Idan mutum yana girma tunaninshi yana kara
canzawa...... Idan har yaro yana tuna haka ya kamata ya dinga hakuri da
iyayenshi, sannan abunda kama iyayenka kaima haka naka za suyi maka shairi ko
khairan, sannan Indai kai burinka kuntata ma iyaye bazaka taba ganin haske ba a
rayuwa..
Mum tace
hakane, Allah yasa mu dace
Mai martaba
ya amsa da Ameen, tare da fad'in zan tura aje a nema masa auran yarinyar cikin
satin nan insha Allah, saiku Fara shiri
Mum tayi
y'ar murmushi tare da fad'in Allah ya bada Sa'a zamma Yarima albishir
Dariya Mai
martaba yayi tare da fad'in dan nema ba, Ashe tun a mafarki yake ganin yarinyar
ikon Allah.
Mum tace Wlh
nima nayi mamaki, Allah dai yasa abokiyar zama ce.
Mai martaba
yace lallai soyayyarsu had'in Allah ne, duk Wanda yace zai shiga tsakani akwai
matsala
Mum tace
hakane, tayu rabo ne na kusa tsakani sai yasa ya kasa hakuri, kuma rabo na kisa
Mai martaba
yace hakane, Allah ya shige mana gaba.....
Mai martaba
yasa an tura gidansu bariki, inda su waziri suka je, kuma babu laifi su waziri
Sun yaba da irin gidan tarbiyan da bariki ta fito, domin tunda Yarima ya fad'a
mata ranan da za suzo bariki ta hayo wasu mutum biyu Sunan sune y'an uwan
mahaifinta, sannan duk ta tsara musu yanda za suyi.
Koda waziri
yayi maganan sadaki akan nawa zasu yanke
D'aya daka
cikin kawun Bariki na karya yace dubu hamsin ya isa, domin karancin sadaki
shine albarkan aure,
Waziri yaji
dad'i Sosai domin ya gano gidan mutunci Yarima yake neman aure sannan ba masu
kwadayin abun duniya bane, duk da ya gansu talakawa kuma ko yanzu a sauron
gidan suke zaune, Ma'ana a zaure.
Nan take
Waliyan Yarima suka biya sadaki, dubu hamsin tare da K'ara million d'aya suka
ce wannan kaman matsayin kyautatawa ne, tunda iya abunda suka yanke shine na
sadakin,
Dakyar
iyayen bariki suka amshi kud'in, domin cikin mutanan Yarima sunce gidan sarauta
in sun bada Abu dole ake amsa, ba'a miyar musu. Sannan an tsaida rana nan da
wata biyu
Nan dai akayi
addu'a tare da tashi kowa Ya wuce.....
Cikin Wanda
sukazo daka gefen Yarima harda Mai Anguwa, ma'ana sarkin u/kanawa, wanda Kafin
su zo shine aka bama damar yin bincike akan gidansu yarinyar da irin
tarbiyanta, kuma yace babu wani matsala gidan tarbiya yarinyar take Yadai yi
magana Mai Kyau akan gidansu bariki 🤔 ko Mai yasa yayi haka?? Bayan yasan yanda sarauta take??
Sannan hausawa na cewa shidai ramin karya kurarre ne, koma dai miye dalili za
muji zamu gani....
Koda su
waziri suka koma, sunyi ma Mai martaba bayanin irin gidansu bariki, Sun fad'a
mishi gidan mutunci Yarima yake neman aure, sannan suka kara da fad'amai sai
dai talakawa ne Sosai ba masu karfi bane, domin yana yin gidansu ya nuna hakan,
kuma kaman gidan Haya suke, waziri ya kara da fad'in sai dai abunda ya kara
burgeni duk da irin talaucin su , suna da wadatar zuci, basu da kwadayin abun
duniya
Mai martaba
yaji dad'i Sosai, tare da fad'in ina son Kafin Ayi bikin a nema musu Gida su
koma, wannan kyauta ce daka gareni
Waziri yace
an gama godiya suke .
Bariki bayan
magabatan Yarima sun tafi, ta fito ta sami babanta na Bariki da sauran mutanan,
nan suka bata kud'in, sannan ta sallami mutum biyu din akan saita kara nemansu.
Tafiya sukayi suna godiya.
Kallon
abbanta na Bariki tayi tace gskya aiki yayi kyau
Yace Sosai
kuwa, sai naji dama auran nan da iyayenki na gskya kika had'asu, ina tsoran
ranan da asiri zai tonu
Bariki tace
karka damu, komai a tsari nake tafiyar dashi.
Yace dakyau
tare da fad'in ni kam inda mmnki zata yarda Aida munyi aure
Bariki tace
dagaske kakeyi?
Yace dagaske
nake Wlh
Bariki tace
Aikam zan mata magana sannan ni zan biya sadaki, da kayan lefe akwati guda biyu
ai zan had'a maka Indai dagaske ne wlh, nima na samu lada
Yace ina
godiya Kinga gwara Ayi auran, tunda nida ita Kar tasan Kar ne
Dariya
bariki tayi tare da fad'in wannan haka yake.
Yarima Aliyu
yana barin asibiti ,direct wajan bariki ya nufa, inda bata ma San da zuwanshi
ba, saida ya kirata yace ta fito yana waje, Dan haka ta tashi ta fita ta
sameshi a mota
Yarima
kallonta yayi cikin jin dad'i tare da fad'in amaryata
Murmushi
tayi cikin jin kunya tare da gaidashi
Amsawa yayi
tare daja mata hanci, yace am so happy today
Kallonshi
tayi tare da fad'in happy for wht?
Yace soon
zaki zama tawa ..... Oh na manta kin ma
riga kin zama, Ashe an bani ke har an biya sadaki...
Murmushi
kawai tayi
Yarima yace
yaushe za muje kiga gininki?
Tace a'a
basai Naje ba,
Yace toh ni
ina son kije ki gani , ya za'ayi kenan??
Tace zan
tambayi Umma inta amince sai muje
Murmushi
yayi kawai tare da kawar da maganan yace, Mai kike bukata Ayi da bikin mu??
Tace kaman
me??
Yace event
din da za'ayi
Shuru tayi
tana nazari inta yarda Ayi event Kar a wajan event taga Wanda ta sani, Kar su
fad'ama Yarima gskya Kafin ita ta fad'amai, kai gskya a'a.. Kallon Yarima tayi wanda shima ita yake kallo
tace Yarima inaga Kar Ayi wani bidi'a.....
Kamo
hannunta yayi tare da fad'in, a'a ya kamata muyi koda Abu d'aya ne, muyi
dinner, inaga zaifi
Tace toh
amma fah badan taso ba, ta dai amince ne dan Kar yaga kaman ta'ki yarda da
maganansa.....
Kallonta
yayi yace tunda an gama maganan event saura na akwati zan baki kud'i Kisai irin
kayan da kike so, duk da za'a kawo miki daka gidanmu, wannan wanda zan baki
akwai wanda nake bukata ki siya wanda only me zan dinga ganinki dashi, saiki
K'ara da irin naki choice din .
Bariki ido
ta rufe ciki jin kunyan maganan Yarima, ta rasa mai yasa Idan yayi mata wata
maganan take jin kunya Bayan tasan ita bata jin kunyan magana gaban kowa, kodan
Yarima badan iska bane sai yasa nake jin kunyan shi? Tabbas hakane domin duk
Wanda kuka ga yana maganan banza gaban wani in kuka duba za kuga shiya bada
dama Ayi mishi.
Sunyi fira
akan in zai dawo zai Kawo Mata kud'i cash ta siya abunda take so sannan ya Mata
sallama ya tafi ..... Toh andai ce duk
abunda akace an yishi had'e da karya komai daren dad'ewa gskya zata bayyana,
zamu gani asiri zai tonu Kafin biki ko sai Bayan biki muje zuwa........
MARYAM OBAM
No comments