BARIKI NA FITO (BOOK 2) 14
BOOK 2
PAGE 14
Gimbiya
Hafsat tace ok bari in d'auko hijab, komawa tayi ta shiga bedroom d'inta Jim
kad'an sai gata da hijab a jiki tace muje......
Direct gefen Mai martaba suka nufa suka fara nocking...... Mum ce ta bud'e kofar..... Ganin su zinatu yasa ta fad'in lafiya kuwa??
Bakuyi bacci ba har yanzu??
Hafsat tace
mum plz Abba muka zo gani Dan Allah.
Mum tace ku
shigo, bari in kirashi..... Ciki tayi Jim kad'an sai gasu ita damai martaba
Mai martaba
yace zinatu lafiya??
Cikin kuka
tace Abba dan Allah kayi hakuri a fito da Yarima.....
Mai martaba
shuru yayi yana nazari can yace Babu damuwa ki tashi kije, zai zo yanzu ya
sameki....
Cikin kuka
take ma Mai martaba godiya akan yarda da yayi zai sako Yarima, tare da tashi ta
fita ita da Hafsat.
Bayan sun
fita Hafsat ta kalli gimbiya tace, ngd da kikai magana za'a fito da Yarima ba
karamin dad'i naji ba.....
Gimbiya
zinatu tayi murmushi tare da fad'in karki damu, nima ba karamin dad'i naji ba,
domin bazan iya bacci ba Yarima yana kulle a kurkuku.
Hafsat taji
dad'in maganan gimbiya Sosai, dan haka tace mata taje gefenta Kar Yarima ya
fito yaje yaga bata nan.......
Bayan fitan
su gimbiya zinatu daka wajan Mai martaba, yasa aka bud'e Yarima tare da fad'in
yazo inda yake...... Bayan an bud'e Yarima direct wajan mahaifin nashi
yaje......
Bayan Yarima
yazo gaida iyayen nashi yayi da fad'in Barka da dare.... Zama yayi a k'asa tare
da fad'in Abba Nasan yau na bata maka rai Nayi abunda baka taba tunanin zanyi
ba, Abba Ina neman gafaran ka, domin fushin ka a kaina baraza ne a rayuwa na,
dan Allah Abba ka yafe min.......
Mai martaba
ya Katseshi da fad'in Aliyu tunda nake dakai baka taba sani cikin fushi irin
yau ba, amma babu komai ni musulmi ne Nayi imani da kaddara kuma haka Allah ya
tsara, babu wanda ya isa ya canza, umarni kawai mukebi...... Amma ina son in ro'ki alfarma akan Kar wannan
Kalman ta K'ara fita daka bakinka ba tare da babban laifi ba, Wanda yake cikin
dokan wannan masarautar, wanda bama fatan hakan ya faru......
Yarima
kanshi na k'asa yace Abba ka daina bani shawara ko neman alfarma, koda yaushe
nafi son kace kaban umarni, Idan kace min alfarma ko shawara Ina jin wani iri,
Abba Nasan na aikata kuskure Wanda Nayi nadama,
ina ro'kan gafara tare da bada hakuri.....
Mai martaba
yace Allah yayi maka albarka, kaima Allah ya baka yara masu maka biyayya, Mai
martaba yayi ma Yarima nasiha Sosai tare da K'ara fad'a Mai muhimmancin hakuri...... Daka karshe yace
ya Tashi yaje ya kwanta.....
Yarima tashi
yayi tare dayi ma iyayenshi saida safe ya nufi gefenshi......
Bayan fitan
Yarima Aliyu, mum din Yarima tace Kai Allah ya kyauta.
Mai martaba
ya amsa da Ameen, Aliyu yana da hakuri amma bai iya fushi ba.....
Mum tace ai
halinku d'aya.....
Mai martaba
murmushi yayi tare da fad'in Kai Anya kuwa? Amma yana da zuciya kuma ina
tunanin irin naki zuciyar ya d'auko.....
Dariya duka suka sa.......
Yarima koda
ya shiga bedroom dinshi ya shiga Kai tsaye ya fad'a toilet ya sakeyin wanka,
tare dasa jallabiya, lokaci d'aya kuma ya tuna da wayoyinshi fita yayi yaje ya
amso tare da dawowa a falo yaga gimbiya zinatu wannan karan, kallo d'aya ya
mata ya kauda kai tare daci gaba da tafiya.....
Binshi tayi
da sauri tasha gabanshi tana kuka, tare da fad'in dan Allah Yarima kayi hakuri,
nasan nayi maka laifi, wlh shairin shaidan ne da kuma na zuciya, Yarima nayi
nadaman zaginka dan Allah ka yafemin Wlh shairin zuciya ne kuka take Sosai tana
magana....
Yarima ganin
yanda take kuka yasa ta tashi tausayi, yace ya isa haka, kibar wannan kukan
komai ya wuce tunda har kin gane kuskuranki.....
Tace Wlh
Yarima Ina jin kunyan kallonka domin abunda Nayi maka sai inga kaman bazaka
yafemin ba
Yarima Aliyu
murmushi kawai yayi tare da jan hannunta suka haura sama, d'akinta ya kaita
tare da fad'in go and sleep sai da safe......
Hannunshi ta
ri'ke tare da fad'in Yarima plz let slp together plz
Yarima zaiyi
magana tace plz Indai harka hakura akan abunda nayi maka let slp together am
your wife....
Yarima yace
ok let go to my room, I can't sleep here.....
Gaba yayi
itama ta bishi, suka nufa d'akinshi Yarima bai samu ya kunna phone dinshi ba
saboda bacci ne Sosai a idonshi dama yau ya gaji ga kuma abunda ya faru.....
Gimbiya
zinatu duk yanda taso tayi Yarima danya kulata amma ya'ki domin bai dad'e ba
bacci ya D'aukeshi.... Duk da shima ya
Lura da abunda take bukata amma bawai ya kyaleta bane akan abunda ta mishi yana
da burin hukunta ta, domin inya barta haka nan gaba zata K'ara abunda yafi
zagan mishi iyaye.... Ganin yayi bacci yasa tayi tsaki tare da fita daka d'akin
tayi nata d'akin.......
Message tayi
ma gimbiya Amina akan yanda ta aiwatar da abunda ta sata, tare da fad'in an
sako Yarima gobe za suyi waya ta karasa Mata sauran bayani.....
Washe gari
Yarima Aliyu tun 7 yabar gida ya shigo garin kaduna, direct hspt dinshi ya
nufa, Sai a lokacin ya kunna wayoyinshi yaga sa'kon Zainab dinshi, murmushi
yayi tare da ajiye wayan ya fara aiwatar da abunda yake gabanshi......
Bariki koda
ta tashi ummanta ta bariki tayi musu abinci, ci tayi sannan taje tayi wanka,
tare da shiryawa don Tana son zuwa maraban jos wajan haulat domin tun shekaran
jiya take ta kiran bariki akan tana son ganinta..... Kallon ummanta ta bariki
tayi tace zan fita amma anjima kad'an zan dawo....
Bariki
direct maraban jos ta nufa inda ta sami Haulat a d'akinta.....
Haulat ganin
bariki da hijab yasa ta fad'in mai zan gani haka?? Yaushe kika Fara sa hijab
kodai maganan da naji gskya ne?
Bariki tace
wani magana??
Haulat tace
ji nayi Anata jita jita zaki aure wai Idan Wanda yazo a Bayan layi kuke
had'uwa, ance kaman wai dan gidan sarauta ne....
Bariki cikin
ranta tace oh mutane, komai kayi ana Lura dakai kai baka damu da mutum ba amma
shi yana nan ya damu dakai..... Amma a
fili sai tace su suka sani saji dashi, Munafukai....
Haulat tace
bariki Wai boye boyen mai kike min? Karki manta bariki bana boye miki komai
nawa, haka Kema bai kamata ki boyemin komai naki ba..... And Idan Auran za kiyi dagaske zanfi kowa
murna, nima Kinga auran nake son yi,.... Yauwa ban baki labari ba dama kiran da
nake ta miki kenan..... Yaron hjy habiba ya ganni yana sona, kuma son aure, da
Farko Ina shareshi akan banso, amma yanzu wlh bariki ina matukar sonshi
Sosai...... Harna amince mishi but
abunda yake damuna mum dinshi irin abunda muka aikata tare wlh shi nake tunani
nake tsoro, ta gefe d'aya kuma ina gani bazata yarda d'anta ya aureni ba......
Bariki tace
Hmmm haulat, gaskiya dole kiji tsoro, Kinga tsiraicin surukar ki, kin tsotse
inda yaronta ya fito sannan kuma yanzu kike son auranshi...... Tashin hankali
ashe ni nawa Mai sauki ne...... Haulat a
duniya babu abunda na tsana kaman lesbians yana d'aya daka cikin abunda ya fara
tarwatsa rayuwata duk da ban taba aikatawa ba, haulat Mai mace zata bani?? A kullum sai yasa nake fad'in nafi son in
sami namiji mai cikakkiyar ayaba Wanda zai gamsar dani..... Mai mace zata baki Wanda namiji bai baki ba,
Kinga misali yanzu mace tayi kissing dinki, shima namiji zai miki, duk wani abu
da mace zata ma mace namiji zai miki sannan ya kara miki da sandar girma, wanda
mace bata dashi..... Ni Ina mamakin
dad'in Mai kuke ji haulat Idan kukayi lesbians dinnan, ni Kinga babu wata
Shegiyar matar da zata bud'emin hq insha
Mata, sucking, wlh babu ita, ni kyama ma wannan abun yake bani Wlh, gashi wasu
matan warin gaba garesu haka kuke sa baki.....
Haulat tace
Kedai bari, wlh bariki haka muke sa baki, dan kawai a bamu abun duniya, Aini
zan baki labari, ita kanta hjy habiba wani zubin dauriya kawai nake, sai yasa
ai nakai mata Miski nace Kafin muyi ta dinga sawa, domin wani zubin wari
gabanta yake Kai AI Wlh inda badan kud'i ba nima da banyi ba, dan tana ban
kud'i Sosai sai yasa nake biye mata, amma fah akwai dad'i kizo mu gwada
kiji.....
Bariki tace
ni? Allah ya kyauta, Allah karya nuna min wannan ranan, AI gwara in mutu dana
aikata wannan abun, Tabdi.....
Haulat tayi
dariya tare dakai hannunta fuskan bariki ta shafa mata, tace nikam bariki ki
d'aure koda sau d'aya ne, dan Allah ki bani muyi nima inji irin zumar dasu
kwartayenki suka manne miki. Ni sau d'aya kawai za muyi....
Bariki tace
haulat you are mad. Kin San takan wannan abun zamu iya samun matsala dake??
Haulat tace
bariki Wlh wasa nake miki, AI nasan bazaki taba aikata wannan abun ba... Kinga
mubar maganan kiban shawara akan abunda ke damuna....
Bariki tace
uhm, gskya Abun naku ne babba, toh amma inaga Indai auran kike son yi dagaske
kuma tsakani da Allah, ya kamata ki daina aikata abunda kike yi, Indai kina son
Allah ya taimakeki ki daina aikata sabo, and ita hjy habiba Indai zatai adalci
ya kamata ta Bari d'an nata ya aureki, tunda harda ita cikin masu kara
lalataki, inko ta hana d'anta auranki bata da adalci, sannan ita in Tana da
hankali ya kamata ta gane Allah yana Sonta da shiriya ne, tunda har hakan ta
faru d'anta na cikinta yake son abokiyar cin mushen ta, Kai Allah ya
kyauta.... Uwa taci d'a zaici ta hanyar
sunna 🤦♀
Haulat tace
Kedai bari Wlh Ina cikin tsaka Mai wuya
Bariki tace
ai bamu ga komai ba, tunda tun Farko mun zabi sabama Allah, yanzu muka fara
gani ta karasa maganan tare da zubar da hawaye, taci gaba da fad'in haulat, sai
yanzu na hango abunda ake cewa rayuwar mace kalilan ce, yanzu ki duba ki gani
Ina manyan karuwai irin su magajiya jummai yanzu wake son zuwa wajansu tunda
Sun tsufa, yanzu kowa mu yake rubibi daka mun Fara girma sai Muma a watsar
damu, muna ganin ana rubibin mu duniya na rudar mu, sai muki yin aure, in mun
Fara girma sai muji muna son aure lokacin mun daina samun kasuwa , sai a
lokacin zamu fara dana sani, domin mun k'asa samun mijin aure, saboda mun bata
rayuwar mu, amma namiji saiya Gama she'ke ayarsa ya auru, sannan kiga tsohon
namiji yana neman yarinya y'ar shekara Goma sha, amma karya ne kiga matashi
yana neman tsohuwar mace, wlh haulat aure shine ya dace da mace ba bariki ba,
bariki babu komai sai dana sani fushi bacin rai, wanda bai isa ba ya fad'a maka
magana, in bakai wasa ba wata rana wani ya zaneka, babu kuma yanda za kayi, kai
rayuwar bariki rayuwar banza ce da shirme, duk da wasu suna fad'awa bariki
domin Sun rasa abunda za suyi, wasu kuma kaddaran rayuwarsu ce hakan, wasu kuma
ra'ayi ne yasa suka fad'a..... Kuka Bariki
ta saki Tana fad'in haulat a duk ranan dana aikata zina Sai nayi kuka tare da
takaicin fad'awa ta wannan harkan, sai yasa bana wasa da ibada domin neman
gafaran Allah, tare da ro'kan shi ya canza min rayuwata, wanda kuma Alhmdlh
Allah ya amsa ibada ta, na daina aikata abunda nakeyi..... Kuka yaci karfinta
Haulat itama
idonta yayi ja alaman any moment zata iya zubar da kwalla daka idonta.... Tace bariki Magananki gskya ce, da yawa matan
da suke fita Bariki bada son ransu bane, amma mutane basa gane kowa da irin
tasa jarabawan sai su dinga aibanta mutum, wasu mutane are selfish Indai
mummunan kaddara ba akan mutum ya fad'a ba sai su dinga ganin kaman da gangan
mutum yake aikatawa, har Su dinga ikirarin cewa duk wacce ta zama karuwa ita
taso, suna mantawa da Allah suma zai iya jarabtansu sai yaga yanda za suyi,
yana dakyau in kaga mutum yana sabon Allah, Kayi mishi fatan shiriya ko kayi
shuru...... Bariki duk karuwa Tana da
burin tayi aure kaman ko wace mace but our destiny take us to where we are now..... Itama hawayen ne ya zubo mata, taci gaba da
fad'in ni Nasan komai mutum yayi tashi kaddaran kenan Allah ya riga ya tsara
komai, babu yanda za muyi, sai dai muyi fatan shiriya na har abada......
Dukansu kuka
suke alaman tsoran Allah ya kamasu su duka biyun, suna cikin kukan wayar bariki
ta Fara K'ara ,ganin Yarima Aliyu yasa ta d'auka tare da sawa a kunnenta Tana
kokarin goge hawayen fuskanta.....
Yarima yace
you are crying??
Ganin ya
gane yasa cikin muryan kuka tace how did you know dat am crying??..
Mai makon ya
bata amsar tambayan da tayi mishi, sai yace kina ina??
Tace ina
maraban jos
Nanata Sunan
yayi maraban jos??
Tace eh
Yarima
Ok kawai
yace tare da fad'in I will come to your house in d next 30mnt so ki dawo yanzu,
yana fad'in haka ya kashe wayan.....
Bariki
sororo tayi tare da tashi,
haulat tace
ashe dagaske ne aure za kiyi,?
Bariki tace
hakane zan baki labarin komai in mun had'u ko kuma muyi waya, zan tafi ana
jirana.......
MARYAM OBAM
No comments