BARIKI NA FITO (BOOK 2) 13
BOOK 2
PAGE 13
wat a
funny.... Wlh readers kuna bani dariya, ana baku novels a free daka writer tace
novel d'inta ya koma na kud'i sai ku Fara zaginta.... Hmmm which bata ce dole saika biya ba, in
kana da ra'ayi ka biya ka karanta in baka da hali saika bari bawai ka dinga
zagin taba, tana da right ta mayar da Littafinta na kud'i tunda
basirarta take
zama ta rubuta muku, wasu ko comment basa iyawa, amma writer dan tace ta
maidashi na kud'i saiku Fara zaginta, miye Abun zagi a ciki??.... Haba ku dinga
yima writers adalci mana, in kina ra'ayi biya ki karanta in bakya ra'ayi babu
dole🤷♀
writer zata bata lokaci ta muku typing amma comment ya gagara akwai alot of
mutane da suke karanta novels din mutum amma basu taba comment ba sai anjika
shuru za'a fara biyoka PC ana tambaya which hakan bai dace ba, idan writer tayi
muku posting bata bukatar komai sai comments d'inku in taga bata samun comment
ba dole ta maida na kud'i ba, in kud'i kuka biya inta tura ko kuyi comment ko
Kar kuyi bai damu writer ba tunda kudinku kuke karanta wa, so ku gyara ko kuma
writers suyi ta maida muku novels dinsu na kudi
Hafsat ri'ke
fuskan tayi tare da fad'in ni kika mara??
Gimbiya
zinatu tace eh ko zaki rama ne??
Hafsat
murmushi tayi tare da fad'in bazan rama ba, saboda kinci darajan Yarima inda
badan shiba Wlh da Kafin ki sauke hannunki saina nuna miki kuskuranki.....
Dasai kinyi dana sanin Marin Hafsat a cikin masarautar su.....
Gimbiya
zinatu tabe baki tayi tare da komawa cikin d'akinta, domin tana ganin kaman
Hafsat din zata iya ramawa Dan yanda taga lokaci d'aya har tana iya ganin bacin
ranta K'ara ra.....
Hafsat fita
tayi ta koma d'akin mum dinta, bata ganta a falo ba dan haka tayi bedroom
dinta, inda ta sameta ta fito daka wanka......
Mum din tace
Hafsat Wai ba zaki ki kwanta ba? kike ta zarya??
Tace mum
wani bacci zanyi Yarima yana kulle cikin sauro babu fanka babu katifa, haba
mum..... Kuka ta kuma saki.....
Mum din tace
wlh kina da aiki Hafsat, kallon Hafsat din tayi tare da fad'in maiya sami
Fuskanki naga ya tashi??
Cikin kuka
tace mum Wlh gimbiya zinatu bata da kirki, bama mum labari tayi, tare da cewa
mum Wlh Yarima shine mai gaskiya amma Abba baima saurareshi ba, jiba Nima daka
zuwa kalla abunda tamin....
Mum ranta ya
baci amma saita boye Dan Kar y'ar tata ta gane, tace Hafsat komai zai faru ni
dake bamu da ikon bud'e Yarima sai abbanku, dan haka kije ki kwanta kina zaune
zai sa a bud'eshi Kinji.....
Hafsat jiki
a sanyaye ta fita ta nufi gefenta.....
Mum kaya
tasa ta nufi gefen Mai martaba, inda ta sameshi zaune a cikin bedroom dinshi
Yana kallon news, zama tayi dan nesa dashi har aka gama Labaran sannan tayi
gyaran murya tare da fad'in ina son magana dakai inka bani dama.....
Mai martaba
yace tunda nake dake, baki taba tambayana izinin magana dani ba, dan haka kiyi
maganan ki Kai tsaye.....
Tace magana
zanyi akan Yarima wacce nake bukatan amsa, Nasan Yarima yayi laifi babba, na
sakin matarshi wanda kayi amfani da maganan matarshi kayi mishi hukunci, sannan
maganan al'ada shima a......
Mai martaba
ya dakatar da ita, tare da fad'in Khadija koke da kika haifa Aliyu bazaki
fad'amin halinshi ba, abunda nake son ki sani bawai naki sauraran Yarima bane
ko Nayi amfani da maganan matarshi ba ko d'aya, na hukunta shine ta hikima akan
Kalman saki daya furta, wannan hukuncin dana mishi zaisa nan gaba komai zai
faru tsakaninshi da iyalinshi bazai yi saurin furta Kalman saki ba, duk kuwa
yanda ranshi ya baci, Idan har namiji ya fara furta Kalman saki in ba'ayi wasa
ba ya fara kenan tun kana d'aya biyu har sai Ayi uku azo ana nadama..... Wannan hukuncin da namai shine zai nuna mishi
cewa komai zai faru ya zama mai hakuri ya daina saka Kalman saki..... Namiji da hakuri aka sanshi mace shu'uma ce
in ranta ya baci babu abunda bazata fad'a maka ba, in kaga haka sai ka fita ka
barta karka biye mata har Kalman saki ya shiga, yana dakyau namiji ya daina
saka Kalman saki a duk sanda matarshi ta bata mishi rai domin a lokacin shaidan
yana kansu, zaiyi ta ingiza su, in yaji anyi saki sai yasa ma kanshi rawani
yayi nasara, sai yasa ba'a so mutum ya yanke hukunci cikin fushi and Idan mace
ta maka laifi akwai hanyar da zaka hukunta ta harta gane tayi kuskure .... Sai yasa nake muhimmanta wannan al'adan
masarautar na hana saki sai an Kama mutum da laifi biyu...... Na farko zina domin duk matar da take da miji
tayi zina hukuncin jifa ne a kanta, sannan a lokacin da mazinata ke zina ana
cire musu imani...... Wa'iyazubillah
yanzu in mutun ya mutu yana aikatawa Mai zaice ma Allah😭😭😭 Wanda yanzu zina ya zama ruwan dare
ga matan aure..... Duk saboda san duniya
shaidan yayi tasiri a zukatan wasu al'umma, suna aikata alfasha basu daukeshi
bakin komai ba, suna ganin kaman za suyi tsawon rai Kafin su mutu zasu daina,
wanda shaidan ne ke sa musu haka, kaita zuba iskanci kana ganin Aini ba yanzu
zan mutu ba Kafin in mutu zan shiryu haka Kai baka shiryu ba mutuwa zata zo
maka babu notice sai dai ka farka ka ganka cikin kabari😭😭😭😭😭 ka girbe abunda ka shuka.... Wlh
hawaye nake ina rubuta wannan wajan😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭 kawai Ina tuna irin azaban kabari
da ukuban da mutum zai Tarar in bai
aikata Abun al'kairi ba.... Bayan azaban kabari tashin alkiyama, hisabi
tsallake sirad'i, saka mako wuta ko Aljanna 😭😭 kai Wlh duniya ba komai bace.... Allah yasa mu
dace..... Mai martaba yace sannan wanda
ya aikata kisan Kai shima bashi da imani zai iya kashe kowa.... Kinga mutane biyun nan kaji tsoran zama
dasu........
Mum ta sauke
ajiyan zuciya sannan tace hakane Allah yasa mu dace..... Amma maganan auran da
yake son ya kara fah??
Mai martaba
yace wannan maganan ki bari inya fito naga irin yanda yake ma matar tashi sai
in yanke.....
Mum tace
babu damuwa duk da tasan itama matar tashi tana da nata matsalan, mum tace
sarki Mai adalci Ina neman ma Yarima sassauci domin wajan da zai kwana babu katifa
filo ga sauro....
Mai martaba
yayi murmushi tare da fad'in karki damu kin San bazan barshi haka ba nasa a
bashi maganin sauro..... Da abun lulluba amma bai San nina tura mai ba, zaiyi
tunanin fadawa ne suka bashi.....
Mum ta
d'anji sanyi da taji haka dan haka ta saki ranta Sosai.......
Bariki dake
zaune tana kallo gidan iyayenta na bariki, tashi tayi ta d'auki wayanta ta
danna, taga miss call din Yarima, ido ta zaro tare da fad'in ya akai banji
K'ara ba, da sauri ta Fara kira lokaci d'aya kuma ta kashe saboda ganin dare
yayi Sosai tare da fad'in bari ta mishi message In idanshi biyu zai kira,
Message ta
Fara rubutu mishi kaman haka......
Barka da dare Yarima na, sorry ka kira
wayan yana silent yanzu kuma naga dare yayi, Ayi min afuwa ur wife to be insha
Allah.......... Tura mai message din
tayi tana murmushi.....
Ganin bai
mata reply ba bai kuma kirata ba yasa tayi tunanin yayi bacci ne, dan haka
itama ta fita ta nufi toilet ta Kama ruwa, ta dawo ta shiga Uwar d'aka ta
kwanta inda ummanta na bariki take akan gado, tunda bariki tazo abbanta na
Bariki baya kwana a gidan, dama a falo yake kwana Wanda bariki ta Fara tunanin
dama suyi aure amma bazata musu magana ba dan tasan dukansu ba yara bane, and
shima mahaifin nata na Bariki ba'ko
yaushe yake kwana ba dan yana da iyali yana dan kwana ne wani zubin
saboda mutanan gidan Kar su Fara zargi wannan kenan.......
Gimbiya
zinatu Bayan ta koma d'aki, kiran gimbiya Amina tayi ta fad'a mata abunda ke
faruwa harda sakin da Yarima yayi mata da Marin da tayi ma gimbiya
Hafsat........
Gimbiya
Amina salati ta saki tare da fad'in Kai saki fah kika ce??
Gimbiya
zinatu tace eh saki Wlh akan zai K'ara aure, dan Nayi magana shine nayi laifi .
Gimbiya
Amina tace lallai Yarima hukuncin damai martaba ya yanke yayi dai dai dashi,
amma ina son kiban hankalinki kije ki roki,
Mai martaba kaman yanda Hafsat tace miki akan a sako Yarima, ina son ki
nuna mishi saboda ke yasa aka sako shi, Idan kikai hakan iyayen nashi zasu gane
kina sonshi, Kinga zasu K'ara d'aura Mai laifi...... Sannan kije yanzu cikin daren nan kiba Hafsat
hakuri ki nuna mata kinyi nadama Inba haka ba zaki jama kanki ba'kin jini keda
kike da y'an uwan miji Mata, bata haka ya kamata kiyi ba, yanzu kije kiyi
abunda na saki, ke kije har wajan Mai martaba dinma yanzu amma ki Fara zuwa
wajan Hafsat din, ita zata raka ki wajan abban nasu ,
Gimbiya
zinatu tace my love kefa da kanki kin San bama Hafsat hakuri a wajena ba abu
bane mai yihuwa
Tsaki
gimbiya Amina tayi tare da fad'in kiyi abunda na saki, zinatu ban son musu Tana
fad'in haka ta kashe wayan..... Ganin
haka yasa Gimbiya zinatu saka dogon hijab akan kayan baccin da tasa ta fita
domin aiwatar da abunda gimbiya Amina tace mata.......
Kai tsaye
gefen gimbiya Hafsat ta nufa..... Nocking tai tayi..... Gimbiya Hafsat dake
zaune ta kasa bacci taji ana mata nocking tashi tayi ta bud'e kofar ganin
gimbiya zinatu yasa ta tamke fuska....
Gimbiya zinatu
tace Hafsat nazo in baki hakuri akan abunda ya faru d'azu ... Rai nane a bace
akan abunda ya faru tsakanina da Yarima, d'aura hannunta tayi akan kafadar
Hafsat tace Hafsat Nasan Idan Kece a matsayina May be kiyi abunda yafi haka in
zaki min adalci ya kamata kisan duk wata mace ranta zai baci in taji mijinta
zai K'ara aure ko wata d'aya batayi ba da aka aurota..... Hafsat Ina son
Yarima, sonshi yasa nake kishin shi, Hafsat Kema mace ce, nasan zaki fahimceni,
d'azu sanda kika zo idona a rufe yake saboda bacin rai, Nayi nadaman zagin da
nayi ma Yarima tare da Marin da nayi miki, gashi saboda ni aka rufeshi dan
Allah zoki rakani Inba Mai martaba hakuri a sako Yarima ta karasa maganan tana
kuka.
Hafsat gaba
d'aya tausayin gimbiya zinatu ya kamata, har take ganin k'arin auren da Yarima
yake son k'arawa tabbas baima gimbiya adalci ba , inma zai K'ara aure ya Bari
nan gaba Kafin gimbiya ta Gama cin amarci, amma daka zuwanta yace zai K'ara
aure gskya baiyi adalci ba ko kad'an Hafsat gaba d'aya sai take ganin laifin
dan uwan nata ne, kallon gimbiya zinatu tayi tare da fad'in kiyi hakuri gimbiya
komai ya wuce, sannan ina son ki sama ranki komai ya faru da bawa kaddara ne.
Gimbiya
zinatu cikin ranta tace ke kika ga kaddara amma bani ba, sai mutum ya tsula
maka tsiya ace min Wai kaddara ce...... Amma a fili sai tace hakane, tare da
fad'in muje mu sami Abba dare Nayi a samu a fito da Yarima.....
MARYAM OBAM
No comments