BARIKI NA FITO (BOOK 2) 12
BOOK 2
PAGE 12
Idonta na
kanshi ganin dagaske yake zai iyayi mata komai yasa tayi gaba tare da tsayawa
wajan kofa tace Yarima nika saka? Auren
dako wata d'aya baiyi ba amma ace harka sakeni? Lallai kayi babban kuskure a
rayuwanka
daka furta min wannan Kalman, sannan inaso ka jira Kaga Mai zai biyo
baya tunda har ka karya wannan dokar ta masarauta..... Fuuuuuu ta fita
Yarima Aliyu
yace mad girl tare da saka, saka jallabiya ya kwanta danya huta domin yayi
matukar gajiya gashi wannan matar tashi ta kara jagula Mai lissafi, yana
kwanciya yaji Phne dinshi na ruri kallon wayar yayi tare dakai hannunshi kan
wayar, Sunan Mai martaba ya gani, d'auka yayi ban San mai mahaifin nashi yace
mishi ba naga yace gani nan zuwa.....
Tashi yayi
ya canza kaya sannan ya nufi gefen mahaifin nashi inda yaga mum dinshi damai
martaba a cikin bedroom dinshi..... Yana
kokarin gaida mahaifin nashi Kafin ya karasa sai saukan Mari yaji tas tas har
guda biyu abunda ba'a taba mishi ba tunda ya taso gashi yau mahaifin nashi yayi
mishi.....
Cikin fushi
da bacin rai Mai martaba yace ka zubar
min da k'ima, saki cikin wannan masarautar?? Bayan kasan sai an Kama mutum ya
aikata laifi biyu ake saki????
Yarima Aliyu
yace Abba Ina Mai neman gafaran ka, Abba zagin iyay.......
Mai martaba
ya daka Mai tsawa Wanda ba Yarima ba harta mum dinshi saida ta tsorata da irin
tsawar damai martaba yayi ma Yarima Aliyu....... Yace na baka umarnin Ka maida
matarka, sannan daka yau Indai harka K'ara Karya wannan dokar ban yafe maka ba
duniya da lahira..... A haka kake
kokarin K'ara aure??? ..... Mata d'aya ma ka kasa da ita ko wata d'aya bakayi
da itaba amma har Kalman saki ya shiga?? Am really dissapointed with you......
Ina son daka yau kaje ka zauna kaida matarka karka K'ara taso da maganan
auranka dan banga alaman zakai adalci ba ko kad'an...... Sannan wannan al'adan daka karya saina
hukunta ka, kaje kaida kanka kasa a rufeka sai kayi sati biyu Kafin ka fito
mutumin banza......
Tunda Mai
martaba ya fara magana kan Yarima Aliyu na k'asa, har Mai martaba ya kammala,
sannan Yarima Aliyu ya fara magana da fad'in Allah ya huci zuciyar
Mai...... Dakatar dashi Mai martaba yayi
tare da fad'in tashi kaban waje....... Ban son jin komai daka gareka....
Yarima Aliyu
jiki a sanyaye ya tashi ya fita direct cikin kurkukun masarauta yaje tare da
bada umarnin a rufeshi....... Fadawa
babu daman tambaya face aiwatar da abunda Yarima ya basu umarni.......
Bayan fitan
Yarima Aliyu mahaifiyar Yarima tace ma Mai martaba hukuncin da aka yanke ma
Yarima yayi tsauri da yawa ya...... Mai
martaba dakatar da ita yayi tare da fad'in banso ki kuma saka baki cikin wannan
maganan, kije ki fad'ama zinatu ta koma d'akinta......
Mum din
Yarima amsawa tayi da Toh tare da fita dan tasan mijin nata yayi fushi
Sosai.... Kuma tasan Kafin ya sauko sai
anji jiki mutun ne mai hakuri amma bai iya fushi ba, ta tabbata tunda har Ya
iya rufe ido ya hukunta Yarima tasan dakyar ya saurareta yanzu...... Koda ta koma gefenta taga zinatu nata kuka
rarrashinta tayi akan tayi hakuri tare da fad'in ta koma d'akinta komai ya
wuce, kiran Hafsat tayi tace ta raka gimbiya gefenta.....
Hafsat ta
amsa da toh tare da cema gimbiya zinatu muje..... Direct gefen gimbiya suka shiga suna shiga
gimbiya ta wuce sama tabar Hafsat nan.....
Hafsat tace kina da aiki......
Hafsat
komawa tayi wajan mum din tasu Tana tambayarta maiya faru,?
Labarin
abunda ya faru mum taba Hafsat.
Hafsat cikin
tashin hankali tace Abba da kanshi yasa Yarima yaje kurku?? Bari inje in ganshi
mum tana maganan tare da fita
Direct
kurkun ta nufa inda taga Yarima a ciki a rufe, kuka ta saki tare da bada
umarnin a bud'e ta shiga.
D'aya daka
cikin fadawan yace afuwa gimbiya Mai martaba ya bada umarnin Kar a bud'e kofar
nan sai yayi sati biyu......
Yarima Aliyu
murmushi yayi cikin takaici tare da ganin ba'a mishi adalci ba danya karya
dokar daba addini bace, sannan abunda yafi d'aga mishi hankali yanda mahaifin
nashi yayi amfani da mummunan kalma wajan cewa inya K'ara Karya al'ada bai yafe
mishi ba, hakan bai isa ba saida Ya fad'a Mai ya dakile maganan auranshi da
zainab...... Ido Yarima ya lumshe lallai mahaifinshi yana son rasa shi, domin a
yanda yake ji, bazai iya rayuwa ba tare
da Zainab ba, bazai ma iya ganin wani ya aureta ba inba shiba, inko hakan ta
faru baya ganin zai iya jura ko kad'an......
Muryan Hafsat ne ya Katse Mai tunani da take
fad'in bros Tana tsaye a waje tana kallonshi tace haka zaka kwana a nan? Tana
maganan ne cikin tausayawa tare da kuka
Yace lil kin
San ban son kuka koh?
Tace Bros
taya bazanyi kuka ba, mai yasa Abba zaisa a rufeka danka saki matarka aiya
kamata aji maita maka..... I dnt knw why
Abba yake d'aukan al'ada kaman addini yake daraja wannan al'adan ya kamata duk
a barshi is not fai........
Yarima Aliyu
sa hannunshi yayi a bakinta tare da toshe mata yace enough lil sis, karki kara
fad'in haka Kinji??.... Abba yana da
ilimin addini Sosai baki ga duk cikin al'adan da yafi bashi muhimmanci shine na
saki ba, karki manta Idan akayi saki sai al'arshan uban giji ya girgiza.....
Abunda Abba yayi shine dai dai bai kamata inyi saki ba duk da raina ya
baci..... But thank god saki d'aya ne
and kuma na maidata but I will teach her a big lesson for insulting my
parent..... Zan iya tolerating komai but
banda zagin iyaye koci musu mutunci..... Yanzu Ina son kije ki zauna da ita
Kafin in fito
Hafsat
kallon Yarima tayi tace bros gskiya ban tunanin zan iya zama da ita, matarka
she use to show her attitude to anyone ,and ni kuma I won't tolerate it, in
Naje haushinta zanji coz saboda ita kake nan
Yarima Aliyu
yace lil wani attitude??
Tace dazu
fah mum tace in rakata d'akinta muna shiga ta wuce ta barni, ko magana babu ai
wannan haline mara kyau....
Yarima duk
da ranshi a jagule yake saida yayi murmushi, kaf sisters dinshi yafi son Hafsat
tana sashi nishad'i, yace lil ki daina sawa a ranki haka ne, kina jin haushinta
kawai dan tasa an rufe miki bros d'inki.....
Hafsat tace
uhm uhm Dan tasan ya ganota... Tace Bros
sauro zai dameka bari insa a kawo maka magani
Yarima Aliyu
yace Nop leave it ko kin Kawo zasu shigo tunda kofar abude take....
Hafsat shuru
tayi tana kallon d'akin da babu haske saina fitila domin ba'a Kai hasken huta
ba dan dai kawai a horar damai laifi da duhu..... Gashi babu katifa balle filo,
Hafsat ajiyan zuciya ta sauke tare da fad'in ina zuwa.......
Yarima Aliyu
yana nan zaune shi d'aya...... Hafsat bata dad'e da tafiya ba saiga wani daka
cikin fadawa yazo yana fad'in Allah ya taimaki Yarima Mai martaba ya bada
umarnin a amshi wayoyin hannunka domin cikin nan ba'a shiga da waya......
Yarima shuru
yayi tare da d'auka wayan yayi dialing number din Zainab ( bariki ) harya
tsinke bata d'auka ba, kara kira yayi shuru, dan tsaki yaja kad'an Kafin ya
kashe wayan ya mi'ka musu......
Hafsat
direct gefen Mai martaba ta nufa, inda tayi sallama.... Amsawa yayi cikin sakin
fuska tare da fad'in Hafsat baki bacci ba??
Tace eh Abba
Yace
lafiya??
Tace Abba
nazo neman alfarma ne
Yace Hafsat
alfarman me?
Tace Abba
dan Allah Nasan baka taba ce mana a'a ba akan duk abunda muke so, Abba kayi
hakuri kasa Yarima ya fito dan Allah Abba, ta karasa maganan cikin kuka....
Mai martaba
yace Hafsat tashi kije ki kwanta sannan daka yau karki kara zuwa inda Yarima
yake daka yanzu na hana kowa yaje inda yake.
Tace Abba
d......
Yace tashi
ki tafi
Tashi tayi
jiki a sanyaye domin dama tasan dakyar ya yarda dan tasan mahaifin nasu bai iya
fushi ba.... Tasan mutum d'aya ce zata ma magana Indai tayi ma Mai martaba
magana zai yarda a fito da Yarima itace gimbiya zinatu..... Toh amma bata son zuwa wajanta dan bata son
raini, dan haka ta nufi gefen mum dinsu a falo taga mum din na zaune tana
karanta al'qur'ani......
Mum din
ajiye al'qur'ani din tayi ta kalli Hafsat tare da fad'in baki je kin kwanta
ba??
Tace mum
taya zan iya bacci Yarima na kulle, mum wajan fah ko katifa babu babu abun rufa
ga sauro.... Dan Allah mum kije Kema
kiyi ma Abba magana....
Mum tace
Hafsat tunda Mai martaba yace a rufeshi ko Nayi magana bazai sa a bud'eshi ba,
so Kinga gwara kije ki kwanta zaifi miki....
Hafsat cikin
kuka tace haba mum, wajan fah akwai sauro Wlh ciwo zai Kama shi Dan Allah
m.....
Mum ta
dakatar da ita da fad'in go and slp plz.
Hafsat fita
tayi direct ta nufi gefen gimbiya zinatu koda ta shiga haurawa tayi har bedroom
dinta taje tana mata nocking...... Ta
dad'e tana nocking saiga Gimbiya zinatu ta fito tana fad'in lafiya cikin wannan
daren? Maiya faru?
Hafsat tace
kin San mai martaba yasa a rufe Yarima kuwa??
Gimbiya
zinatu tace ban sani ba, amma Nasan zai iya zama gaskiya tunda ya karya
al'ada.....
Hafsat tace
kiba Mai martaba hakuri yasa a bud'e shi
Gimbiya
zinatu tace hakuri akan a saki Yarima? Dariya tayi tare da fad'in Aiko bazai
fito ba, gwara yaji a jikinshi koda na kwana biyu ne Kafin a fito dashi......
Karki manta yau ko wata d'aya Banyi ba amma yayanki yamin saki d'aya.... Ke kina ganin yamin adalci? And akan wani dalili zanje ince ma sarki a
sakeshi tunda gani mara kunya ni Uwar son miji ko??
Hafsat
kallonta take cikin mamaki, tace amma Banyi zaton haka ba, kina maganan kunya
AI baki dashi tunda har kika iya zagin iyayen mijinki.....
Gimbiya tace
kin fad'i gskya, gashi na zagi iyayen nashi kuma har yanzu ina matsayin
matarshi, sudai iyayen nashi su suka dawo dani....
Hafsat tace
banyi mamakin jin haka daka gareki ba, and bazan biye miki ba domin irin tawa
tarbiyan daban take, da taki...... Tas
takai ma Hafsat Mari tare da fad'in karki manta koni wacece yayanki nake aure
nafi karfin raini a Wajanki har abada.........
zadai kuga
typing error yau sosai domin typing din gaggawa Nayi yau
No comments