BARIKI NA FITO (BOOK 1) 5
PAGE 5
Jin an kashe
wayan yasa abun ya bata mamaki tare dayin takaicin kiranshi, amma wata zuciyar
tace kiyi mishi uzuri dan baisan number dinki bane, kara kira tayi harya tsinke
bai d'auka ba, message ta mishi tare da fadin slm
Gimbiya zinatu ce Nasan baka kusa ko kana wani uzuri nakira
inji kun koma lafiya tunda ka dawo ba muyi waya ba, ni nace bari in kira bayan
ta tura sa'kon sai kuma ta tsinci kanta dajin haushin kanta kamanta ace tana
kiran namiji bai d'auka ba harta wani tura mishi message, takaici duk ya cika
ta, nikam nace aikin gama ya gama.
Yau sati duk
ranan sati gidan karuwan magajiya jumai dake maraban jos suke wasa, wanda
karuwai ne harda na wani anguwanni suke zuwa aita kid'a ana shaye shaye masu
cin ayaba nayi masu rawa Nayi, kaman yau wajan ya cika makil da mata da maza,
bariki kam tana d'akinta tana shiryawa dan ita a duniya Tana kaunar rawa, wata
tsinanniyar riga tasa wanda ya tsaya mata dai dai cinyanta nononta tsun
bullu'ko sun cika rigan dan dama Allah ya bata su, gashinta ta saki Dan batai
kitso ba, inka ganta zaka d'auka aiswariya rai ce, tayi mugun kyau, kud'i ta
d'auka y'an d'ari biyu biyu bandir uku, tasa a karaman jakarta ta fita, Karo
sukaci da habib tace ah sai ina? Yace Wlh Wajanki zanje Kedai bariki baki da
kirki, dama Hjy babba tasha fad'amin yanzu Hon salis ya kirani yace tunda kika
tafi kika daina d'aukar wayanshi, gaskiya kin iya rashin mutunci kinje kin
d'ana mishi zuma sai ki gujeshi, murmushi tayi tana rawa dan kid'an ya fara
tsumata tace habib ka..... Yace dakata ban son rashin mutunci miye kuma wani
habib y'ar A din kike kyashin karasawa Mai yakai mace jin sin maza gaskiya ban
so, tace Habiba Ayi hakuri yanzu dai kin San babu inda zani dan yau ranan rawan
gwatso ne, tabe baki yayi tare da fad'in arziki yana kiranki kina wani rawa
kina bangare duwaiya, dariya tayi tace Aini bariki kud'in namiji baya rud'ata
abunda har yau basu gane ba kenan, suna ganin in sun ban kud'i da yawa zai sa
in koma, murmushi tayi tace ba kud'i na fito nema ba, bariki nazo Nayi danshi
ya fito dani, tana gama fad'in haka tayi gaba tabar habib baki sake, tabe baki
yayi yace Kedai kika sani, ni in banda iskanci ai duk wacce ta fito bariki
kud'i take nema, Muma nan shiya fito damu neman kud'in, shima gaba yayi. Bariki
tana zuwa ta shige filin rawan tana kad'a duwawu tare da girgiza nonuwa, wasu maza
dake zaune suka fara mata liki, sauran matan suka fara jin haushi dan da
yawansu haushin bariki suke ji, domin ta had'u ga fatar jikinta fresh gwanin
sha'awa, rawa takeyi nawakin ya fara mata kirari bariki in kin doso sauran mata
matsawa suke, binki ake kina wulakanci bariki tafi karfin ko wani shege, bariki
mai daukanki sai yayi Sa'a bariki in Mata sun ganki kishi suke saboda kyanki...
Jin dad'in kirarin da yake mata yasa ta Fara mishi liki tare da rawa tana wani
karkad'a mai duwawu har tana dan tabo shi,jin ayabarsa kaman tana taba Mata
duwawu yasa tayi gaba dashi kad'an, laurat itama shiga tayi tana ma mawakin
liki tare da bariki, gaba d'aya kudin da bariki ta d'auko ta like ma mawakin
nan, fita tayi daka filin rawan duk tayi zufa, zama tayi akan wani benci tana
kallon masu rawa, wani ne yazo kusa da ita ya zauna tare da fad'in bariki
kallonshi tayi sama da 'kasa sannan tace Shina fito, murmushi yayi yace hakane
sai yasa nazo dan nima Shina fito, murmushi tayi tare da fad'in sai dai kuma
kayi rashin Sa'a domin bariki bako wani namiji take biba, tana fad'in haka ta
tashi ta koma filin rawan tana karkad'a jiki tare da girgizawa sai wajan d'ayan dare bariki ta nufi
d'akinta, koda ta koma wanka tayi tare dayin alwala dan yin sallah nafila bayan
ta idar taji ana mata nocking, cikin siririyan muryanta tace Waye? Jin shuru
yasa tayi tsaki tare da bud'e kofar, jamil ne abokin su Hjy babba shida Mai
kid'an da yayi musu kid'a, bariki tace lafiya? Tabe baki jamil yayi tare da
fad'in inda ba lafiya ba ai bazaki gammu ba, ba'ko na kawo miki yazo ya dibe
miki kewa, yana maganan yana nuna mata Mai kid'an, kallon mai kid'an tayi sama
da kasa shiko murmushi yayi tare da fad'in haba bariki kinzo kina goga mun
duwawa kinsa ayabata ta tashi sai kuma ki gudu ai tunda kika tasar da ita yanzu
saiki kwantar min da ita, jamil yace oh ni wannan zance yafi karfina zaku
lalata ni y'ar karamar yarinya dani kunga tafiya ta, gaba jamil yayi yana wani
rangwada shi'a dole mace, bariki kallon mai kid'an tayi tace kalleni dakyau,
yace Aina ganki sai yasa nazo, murmushi tayi tare da girgiza nononta tana
kallon yanda bananarsa ke tashi ta cikin wando wani irin murmushi ta kuma saki
tare dakai hannunta kan ayabar tasa, janta ta farayi har wani irin nishi yake
tare da lumshe ido, tureshi da karfi bariki tayi tare da rufe kofarta tana
dariya, shiko buga mata kofar ya farayi tare da ro'kanta akan dan Allah ta
bud'e suyi Koba yawa, tana jinshi tayi banza dashi tana ta dariya ganin bazata
budeba ga maranshi ya fara kullewa ruwan daya taru a wajan yana bukatar fita,
yasa yaja kafa ya fad'a d'akin wata karuwan dan biyan bukatarsa, jin ya daina
buga mata kofa ta kwashe da dariya tare da fad'in karamin d'an iska an gaya
maka barikin y'an tasha nake, tashi tayi ta Fara had'a kayanta cikin akwati
domin gobe zata gidan Alh madu jibi Monday zasu wuce.
Koda Yarima
Aliyu ya d'auki wayarsa yaga message din da aka masa, karantawa yayi tare da
dan sakin tsaki a hankali ya furta Kalman I hate u, saboda ke yasa banga fuskan
da nake burin gani ba, karan wayan ne ya kara shigowa dubawa yayi yaga lil sis,
d'auka yayi fuskanshi dauke da murmushi yace Hafsat how far? Tace not too far
gani na dawo gida, yace haba zo in ganki lil sis, dariya tayi tace bros ban
dawo ba har yanzu Ina kaduna sis Fatima ta hanani dawowa, plz kazo gobe ka tawo
dani bros, yace OK zan gani in zan iya zuwa, tace plz bros kaine kawai zaka zo
ta yarda in dawo, murmushi yayi tare da fad'in ina nan tafe toh insha Allah,
cikin jin dad'i tace that may bros I love you so much. Kashe wayan tayi tare da fad'in lil rigima,
Aliyu yafi sabawa da Hafsat kaf cikin y'an uwanshi kodan ita kanwarshi ce oho,
wanka yayi yasa kananan kaya yayi kyau Sosai fita yayi fadawa suka bishi sashin
mum dinshi ya nufa inda ya sameta ita da jakadiya suna magana kuma duk akan maganan
bikin nashi ne, zama yayi akan kujeran falo din, yace Barka da wannan lokacin
mum, tace yauwa my son, muna nan muna ta tsara yanda bikinka zai kasance,
murmushin Ya'ke yayi, jakadiya tace gaisuwa Magajin sarki, kai ya d'aga mata
alaman ya amsa, kallon mum yayi tare da fad'in mum ya kamata in fara aiki a
hospital dina, mum tace toh kaine ai Aliyu babu abunda ba'a saba amma kaki
bud'e asibitin, yace cikin week dinnan nake gani ya kamata in bud'e, mum tace
ko kaifa, yace gobe zani kaduna zanje d'auko lil sis, daka nan zan biya in
'kara ganin hspt din, mum tace hakan yayi zadai kaima Fatima tsiya, zaka d'auke
mata Hafsat, yace mum haba yau wajan satinta biyu a can fah aita Mata kokari,
mum tace Kunfi kusa Allah yasa ta yarda ku tawo taren dariya yayi wanda ya kara
fito mishi da kyanshi yace zan tawo da ita, mum tace toh yanzu Mai kake gani ya
dace Ayi a bikin ka? Jin mum ta kawo maganan aurenshi yasa ya tashi tare da
fad'in mum Inna dawo daka kaduna sai muyi maganan, mum tace toh shikenan fita
yayi dan baya son wani maganan bikin shi.
Washe gari
wajan karfe 1 bariki ta fito da d'an karamin akwatin ta, yau dressing din da
bariki tayi yaba ma kowa mamaki domin wando tasa saita saka hijab, abunda basu
taba ganinta dashi ba kenan hijab, habib ne yazo ya tare ta, yace Mai zan gani
haka? Oh ikon Allah bariki wani ustazun kika samu haka? Hararanshi tayi tare da
fad'in maika gani? Yace naga kinsa hijab kin rufe komai, tace naga tunda na
fito ake ta kallo na ashe dan nasa hijab ne, kaida gulma take cinka a
tsuliyarka shine saida ka fad'a abunda ke cikinka, yace Wlh bariki zan miki
bura uba, damme zaki dinga kaini jinsin da ba nawa ba, Kina wani cemin kai y'ar
ke dince ba zaki iya fad'a ba, tace ni ba wannan bane a gabana muje karaka ni
bakin titi inhau mota, yace muje mi'ka Mai akwatin tayi tace dan taimaka min
mana, tsayawa tayi tare da fad'in taya ina mace zaki ban Abu Mai nauyi sallan
in d'auka ya bud'ani in rasa d'an budurci na a'a bada niba, bariki dariya take
Sosai tare da fad'in wani budurcin bayan an gama bulaki, habib yace wa Rufamin
asiri in mutu maza su kaini, yace ni baki fad'amin inda zaki ba, tace Wlh zanje
wajan wani saurayi nane gobe zamu bar kasar, habib yace shine babu sallama?
Tace tafiyan na sirri ne shiya sa, tabe baki yayi sukaci gaba da tafiya har bakin
titi kiranta akayi a waya Wanda yasa ta d'auki wayan tana magana, dai dai
lokacin motar su Yarima Aliyu tazo wucewa, baka jin karan komai saina jiniya ga
fadawa sun ri'ke bulala, jin karan jiniya din yasa hankalin bariki yayi kan
titi din, Yarima Aliyu yana mota yana karanta news paper kaman ance ya d'ago
idonshi ya sauka akan bariki wacce take waya tana murmushi......
No comments