BARIKI NA FITO (BOOK 1) 4
PAGE 4
Bariki sai
wajan 2 ta tashi, da sauri tayi toilet tayi wanka, tare da dauro alwala tayi
sallah azahar, Bayan ta idar ta tashi ta nufi falo a nan taga alh madu, dariya
yayi tare da fad'in yau
gaskiya kinsha bacci harna fita na dawo kina bacci,
baki ta tabe tare da zama tace yunwa nake ji, abinci ya nuna mata akan dinning
Wanda ya siyo Mata takeaway yace gashi can na siyo miki, tashi tayi ta nufi
dinning din ta bude ledojin fried rice ne da kaza, sai su snack, Fara ci tayi
shida kanshi ya tashi ya nufi fridge ya d'auko mata Su drinks, taci abincin
Sosai sannan ta tashi Tana mi'ka alaman ta koshi, kallonta yayi yace bariki Wai
Mai zai hana ki aureni ne? Bata fuska tayi tare da fad'in dan Allah mubar
wannan maganan zan wuce gida, murmushi yayi tare da fad'in toh ya maganan
tafiyan mu? Tace zamu je tunda nace zanje inna fad'a magana bana canzawa, yace
dakyau driver dina zai kaiki gida, amsan account number dinta yayi nan take ya
Mata transfer din 1mil, murmushi tare da fadin thanks, fita tayi driver din alh
madu ya kaita har gida, koda suka karasa sanda ta fito saiga Hjy babba yazo
yana wani tale kafa a dan dole shiga mace, wajan bariki yazo yana fad'in oh
duniya Kaga Abu, kodai dadiron da Habiba ta had'a miki jiya da alh madu ne?
Tace a'a da wani ne, Bayan na dawo daka can na hadu da driver din alh madu
shine na bishi, Hjy babba tace toh mai kike kullawa ne kodai ya gyara kayan
aikin nasa ne? Tace hjyta hjyta wani gyara yayi abu kaman gindin yara, manage
kawai nakeyi, Hjy babba tace ai gwara kiyi ta maneji kina gwagurawa kiyi ta
tasan kud'in dan banzan, dariya bariki tayi tace Kai hjyta ai baki San wani
abuba nifa kud'i bai daman ba nafi son
banana babba yafi min komai, bari kiga inje in huta jiya na ciwu na had'u da
Maye, dariya Hjy babba yayi tare da fad'in ai irinshi ya dace dake, bata ce
komai ba tayi ciki, tana shiga d'akinta ta rufe tare da d'auko sigarinta ta
Fara zu'ka.
Yarima Aliyu
sai wajan isha'i suka dawo daka katsina, kai tsaye gefenshi ya nufa dan yayi
mugun gajiya, yana bukatar hutu, bayan ya shiga toilet ya fad'a yayi wanka
sannan yasa wata jallabiya Fara, kwanciya yayi akan lallausan gadon d'akinshi,
lumshe ido yayi lokaci d'aya yayi tsaki tare da fad'in akan wannan mummunar aka
sa na bata lokaci na, har zuwa garin katsina, jin karan wayanshi yasa ya tashi
d'auka yayi yaga mum, dannawa yayi tare da fad'in mum, tace ka dawo shine baka
shigo ba? Yace Wlh mum nagaji ne, tace maza kazo Mai martaba yana jiranka,
tashi yayi tare da fad'in ganinan zuwa, manyan kaya yasa yana fita fadawa suka
mara mishi baya suna mishi kirari har gefen mahaifin nashi, bayan ya shiga Ya
gaida iyayen nashi, mai martaba fuska a d'aure yace haba Aliyu Mai yasa daka
zuwa zaka dawo yau, mai yakon ka zauna kayi kwana biyu, amma babu damuwa tunda
Kun dawo lafiya sannan sarkin katsina yace yarinyar ta amince toh kasan wannan
karan ba yardanka nake nema ba dan haka saika Fara shiri domin zani katsina
dakai na cikin wannan satin dan a tsaida maganan aurenku, kanshi na k'asa yace
Toh Abba Allah ya taimaka, mai martaba ya amsa da Ameen tare da sama d'an nashi
albarka, Yarima Aliyu tashi yayi yabar d'akin tare dayi musu saida safe,
d'akinshi ya nufa yana ta faman sintiri domin shi harga Allah baya son wannan
auren danshi yarinyar batai mishi ba kwata kwata, amma babu yanda ya iya dole
ya yarda ya amsheta a matsayin mata, domin wacce yake so ta cikin mafarkinsa bai
ma sani ba ko Tana cikin wannan duniyar tunda har yau bai taba ganin fuskanta
ba.
Mai martaba
yaje katsina ya nema ma d'ansa auran Gimbiya zinatu, sarkin katsina yaji dad'i
sosai, inda akace an basu nan aka tsayar da watan biki nan da wata d'aya, domin
dukansu a shirye suke, koda Gimbiya zinatu taji wannan Labarin ranan saida ta
y'anta bayi hamsin dan tsabagen murna zata samu Yarima Aliyu a matsayin miji,
shiko ango takaici ne ya cika shi domin ya d'auki auren da za'a mishi a
matsayin auren dole, tunda bawai so yake ba, amma tunda an Mai dole babu yanda
ya iya dole hakuri zaiyi har sanda Allah zai nuna mishi yarinyar da yake
mafarki, kwanciya yayi bacci ya
d'aukeshi ganinshi yayi cikin wani d'aki Wanda akwai duhu jin motsin tafiya
yayi wanda kobai tambaya ba yasan mace ce ke tawo wa, jin kamshin jikinta yasa
ya fara magana Mai yasa kike boyemin kanki? Mai yasa bakya son in ganki? Magana
ta Fara cikin muryanta Mai dad'in ji tace Yarima na Ina tsoran Kaga yanda nake
ka gujeni, nasan Idan ka ganni zaka tsaneni matsawa ya farayi kusa da ita yana
fadin bazan gujeki ba ina sonki bazan barki ba saura kad'an ya karasa inda take
da sauri ya farka yana salati duk ya had'a zufa Sosai jin karan wayanshi ne
yasa ya tashi tsaki yayi tare da daukan wayan yaga number ne kashewa yayi tare
dayin jifa da wayan.......
Naji korafi
akan ina typing kad'an insha Allah zan kara yawan rubutu, domin farin cikin
masoya na shine nawa, nima saiku faranta min ta wajan comments da sharhi
No comments