BARIKI NA FITO (BOOK 1) 16
*PAGE 16*
Habib
kallonta yayi yace bariki Wlh son Yarima kike.
Bariki
hararan shi tayi tare da fad'in tunda ni na fad'a haka koh? Kawai daka had'uwa
na dashi sai in fara sonshi.
Habib tabe
baki yayi tare da fad'in, toh mai yasa kike cewa zaki gujeshi saboda kin kasa
fad'a Mai gaskiya?
Bariki shuru
tayi tana nazari....
Habib ya
Katseta tare da fad'in in bakya sonshi Mai yasa kike tsoran fad'a mishi
gaskiya? Saboda kina tsoran ki rasa shi koh?
Da sauri ta
kalli habib
Murmushi
habib yayi tare da fad'in Kinji na fad'a miki abunda ke ranki koh? Toh Bari
kiji gwara da baki fad'a mishi koke wacece ba, domin na tabbata dan gidan
sarauta bazai auri karuwa ba, balle ke da kikai suna cikin wannan anguwan
Bariki tace
nace miki auranshi zanyi ko cewa nayi ina sonshi? Dan Allah tashi ni mubar
wannan gidan in koma d'aki na Ina bukatan in huta.
Habib dariya
yayi tare da d'aukan Mata ledan da Yarima ya bata, yace duk dai boye boyen mai
ciki dole wata rana ya fito, fita yayi tabi bayanshi har d'akinta habib yakai
mata kayan sannan ya fita tare da fad'in ina da ba'ko zanje in Kai mishi
yarinya sai na dawo nazo mu tattauna.
Bariki tace
toh tare da rufe kofarta..
Habib yace
bariki ki gama Munafuncin ki, Danni tuni na baro jirgin soyayya ta kama ki,
yana tafiya yana magana tare da bokare duwawu Wai shi a dole yana rangwada.
Bariki
kwanciya tayi tare da lumshe ido duk abunda ya faru ita da Yarima Aliyu yake
dawo mata, da sauri ta bud'e ido tare da tashi d'auko card din daya bata tayi
ta bud'e wanda yake ta faman kamshi Fara karantawa tayi kaman haka........
I have liked many but loved very few. Yet
no-one has been as sweet as U. I would
stand and wait in the worlds longest queue. Just for the pleasure of a moment
with U.
Ido ta lumshe
Bayan ta gama karantawa a hankali ta furta so romantic, ledan daya bama habib
ya bata, ta Fara bud'ewa, kwalin waya ta farayin karo dashi iPhone Xmas, sai su
turare masu tsadan gaske kuma duk Arabian perfumes ne, a kalla sun Kai Kala
goma sha biyar, banda su body spray, murmushi tayi domin a duniya tana son
kamshi, d'aukan kwalin wayan tayi ta bud'e tare da sawa a caji, ba karamin jin
dad'in kyautar tayi ba, wannan ne karo na farko da namiji ya bata kyauta harta
yaba kuma taji dad'i Sosai, d'aukan wayanta tayi tare da shiga wajan message ta
Fara rubutu kaman haka....
Naga sa'ko nagode Sosai ban San wani irin
godiya zanyi ba, Allah ya biyaka da gidan Aljanna, amma wannan kayan kaman sun
min yawa Yarima na.
Tunani tayi
ta tura mai ko Karta tura, tayi wajan minti biyar tana tunani sannan ta tura
mai.
Harga Allah
ansha yi mata kyauta Kala Kala, toh mai yasa bata jin dad'i irin haka sai wanda
Yarima ya Mata? Ido ta lumshe tare da fad'in kodan shi ba irin sauran samari na
bane? Kai ta d'aga alaman hakane shine wanda ya fara min kyauta tunda na fito
bariki ba tare daya nuna yana son wani abu daka gareni ba. Murmushi take tayi
tuna firanta dashi ga kamshin turarenshi da har yanzu yana hancinta yaki
tafiya, lokaci d'aya kuma ta dan gimtse fuska data tuna yace Mata auranshi rana
ita yau, tabbas ya kamata inyi gaggawan rabuwa dashi tun Kafin ya zaman min
matsala a cikin rayuwa na, tashi tayi ta d'auki wayanta tare da dannawa taga
har yayi mata reply da cewa....
My princess I really miss you, komai na baki
u deserve it, so ban son daka yau ki karamin godiya, love you so much, I will
call you when I arrived home, take care.
Ido ta
lumshe lokaci d'aya kuma ta bud'e idon tare da kashe wayanta.... Tace Yarima
bazan cuceka ba,nasan da kyakyawan zuciya kazo min, rayuwa ta abun kyamace ga
duk wani namiji mai kishin kanshi, na tabbata rabuwa dakai shine Alheri a tare
dani, domin bazan iya fad'a maka wacece ni ba, infact ma babu tsarin aure a
rayuwa na, Indai har zanyi tunanin haka burina bazai cika ba, bazan so hakan ba
kuma wani hawaye mai zafi ya zubo mata, lokaci d'aya tasa hannu ta goge tare da
fad'in Yarima na Barka daka yau bazan kara sauraranka ba, dan had'uwa na dakai
na rana d'aya yana kokarin canza min tunani.....
*********
Yarima Aliyu
ya karasa gida gab da magrib, bai shiga ciki ba, masallaci ya shiga inda yayi
alwala dan yana jira a kira sallah sai ya shiga gaba d'aya, har sai da akayi
sallah isha'i sannan ya shiga gida, direct gefen shi ya shiga ya fad'a toilet,
shower ya saki ya dad'e ruwa yana dukanshi ba komai yake tunani ba saina
gimbiyarsa ya dad'e a haka Kafin ya fito, jallabiya ya saka, dan shirin
kwanciya, falo ya nufa inda yaga an jera Mai abincin dinner a table, zama yayi
kuyangi har biyar suka zo domin zuba mai abinci, zuba mai abinci sukayi suka
gama, sannan sukai dan nesa dashi, bai wani ci da yawa ba ya tashi yabar wajan
domin yana bukatar jin muryan princess dinshi.....
Yana shiga
d'aki ya doka Mata kira, amma sai me?
Yaji ance
number din a kashe, abun mamaki ya bashi dan haka ya kara kira amma switch off,
d'an shuru yayi alaman damuwa, tare da fad'in maiya sami wayanta? Kiran Layin
habib yayi
Habib d'auka
yayi tare da fad'in Allah ya taimaki Yarima.
Yarima Aliyu
amsawa yayi da ngd, maiya sami wayan zainab I try her line but switch off.
Habib yace
Wlh Yarima na fita ,amma anjima kad'an zan koma, ina tunanin babu wuta ne, hala
bata da caji.
Yarima yace
ok bari in kira a kawo muku yana fad'in haka ya kashe wayan.
Habib tashi
yayi daka inda yake domin ya koma yaga lafiya bariki ta kashe waya dan yasan
haka kawai ta kashe badan bata da caji ba, sallama yayi ma mutumin da yakai ma
mata har biyu zai kwanta dasu, d'auko kud'i yayi yaba habib sannan yayi gaba.
Yarima Aliyu
shugaban Nepa na kaduna state ya kira, bayan ya d'auka sun gaisa da Yarima
Aliyu, yarima yace Ina son a kaina maraban jos wuta, yanzu akwai..... Sai kuma yayi shuru.....
Shugaban
Nepa yace ranka ya dad'e ai suna da wuta, banyi ko minti biyar da gama waya da
wani dan uwana dake Jaji ba, kuma duk hanyar su d'aya tun daka Barakallahu
birnin yaro har zuwa jaji.
Yarima Aliyu
yace ok nagode tare da kashe wayan, d'an shuru yayi cikin mugun damuwa, maiya
sami wayanta? Kara kiran layin habib yayi.
Habib ya
d'auka tare da fad'in Allah ya taimaki Yarima, ina hanya na kusa zuwa Gida.
Yarima yace
ok am worried Sosai na kira ance akwai wuta, na damu da naji wayanta a kashe.
Habib yace
Ina zuwa zan kira in bata.
Amsawa
Yarima yayi da fad'in OK tare da kashe wayan.
Yarima Aliyu
shuru yayi yana tunani wai yau shine yake kira akan mace, dan kawai ya jita
shuru, ido ya lumshe, yana tuna yanda take magana cikin nutsuwa, tunawa yayi
sanda tace mishi Yarima na. Bai san lokacin daya saki murmushi ba.......
Habib Bayan
ya karasa gida, direct d'akin bariki yayi, nocking ya fara mata
Bud'e kofar
tayi daka ita sai rigan bacci dai dai cinyarta tace wannan bugun kofar kaman
ana bina bashi.
Habib yace
kyaji dashi dai, in banda iskanci kya tashi ki kashe waya Bayan kin San sarai
za'a nemeki
Bariki tsaki
tayi tare da fad'in ai duk mai nema na sun San inda nake, kai baga shi kazo
ne........
Dakata habib
ya Katseta ke dawa? Naji kina kai Waye Kai a nan? Wlh bariki sarai kin San
banda mutunci akan me zaki dinga danganta ni da maza? Gskya bana so wlh, sannan
da kike maganan masu nemanki sun san inda kike aishi Yarima bai San inda kike
ba....
Tace kaman
ya?
Labarin
yanda sukai da Yarima ya bata tare da fad'in yanzu ki kunna waya domin Wlh
Indai baiji muryanki ba yanda ya damu zaki iya ganinshi yanzu.
Bariki tace
na shiga uku na had'u da bala'i, gskya nifa ban son takura.
Habib yace
Mai kike nufi? Toh Wlh bari kiji wannan daman ba kowa ke samu ba, ki kalli
mutum kaman Yarima Yaro Mai Kyau ga sarauta ga kud'i da iko har yace yana sonki
ki dinga gudu, kalli duk wannan Abun nashi baki ga yanda yaita kirana ba.
Bariki tace
kawata ba gudunsa nake ba, nasan duk ranan da yasan wacece ni, zai barni, ban
son sama kaina abunda zai daman, Nasan Yarima yafi karfina rayuwa na da nashi
ba iri d'aya bane.
Habib yace
ke har kina tunanin zai gano gaskiya? Toh ta ina zai gano gaskiyan? Bari kiji
kawai kiyi abunda nace miki Wlh Indai kikayi yanda nace Yarima zai zama naki
sannan bazai taba sanin gaskiya ba.
Bariki tace
taya hakan zai faru gaskiya bazan iya ba.
Habib yace
Toh ko ayabarsa karama ce?
Bariki duka
takai ma habib tare da fad'in uhm ni inama na Lura baki ga yanda ya cika min
ido ba ban ma sami daman Lura ba, amma ai duk Wanda yaga Yarima yasan jarumin
namiji ne dan yana yinshi kawai ya isa ya gamsar da mutum .
Habib dariya
yayi tare da cewa ahaye nanaye
Bariki tace
harda waya Yaban kin ganta iPhone Xs mas
Habib sakan
baki yayi tare da fad'in Kinga harkan arziki? Oh wannan Yariman ko dan arziki
ke bariki arziki na kiran ki kina gudu, jiba dubu d'ari biyu yaban ba tare da
nayi mishi aikin komai ba, wlh Idan kika bari Yarima ya kubuce miki saina tsine
miki.
Bariki
dariya ta kwashe dashi, tare da fad'in sannu uwata wacce ta kawo ni duniya.
Habib yace
Aini haiyuwarki ne kawai Banyi ba, amma ina baki shawaran arziki, wlh bariki ki
kunna waya yanzu tun Kafin ya diro cikin daren nan.
D'auko
wayanta tayi tare da kunnawa tana fad'in oh ni bariki ina ganin abu ni Wlh ban
son harka da mutane masu kokarin canza min tunani, aiko tana kunnawa saiga
kiran Yarima ya shigo, nuna ma habib tayi....
Habib yace
ce dan halak.
D'auka tayi
tare da sawa a kunnenta sallama tayi
Amsawa yayi
tare da fad'in my princess maiya faru kika kashe waya, kin san yanda na damu
kuwa? I thought wani abune ya faru.
Tace na
kashe ne nasa a caji, sai bacci ya daukeni, yanzu habib yazo yasa aka tashe ni,
shine na kunna Ina son kiranka sai gashi ka kira.
Yarima yace
eyya sorry my princess nasa an tashe ki .
Murmushi
tayi tare da fad'in ya hanya da fatan ka koma lafiya?
Yace Alhmdlh
sai dai gskya I really miss you, Anya zan iya jira jibi kuwa?
Murmushi
tayi tace ai kaman yau ne Yarima yaufa kazo muka had'u kuma ka ganni
Yace hakane
amma ban gaji da ganinki ba.... D'an shuru yayi Kafin yace Zainab za'a iya bani
auranki a wata biyu??
Dam taji
gabanta ya fad'i amma da yake y'ar duniya ce saita wayince tace haba Yarima Wlh
har kaban dariya.
Yace am
serious Zainab, ina son insha Allah nan da wata biyu in aureki inda so samu
nema da nan da wata d'aya zan ce, so plz ina son ki bari inga iyayenki nayi
miki alkawarin Indai na gansu suka bani izini Indai bamu dai daita ba zan hakura, bazan bari ayi miki dole ba.
Kasa magana
tayi, domin bata san mai zata cemai ba.
Yace Zainab
nasan yanzu ba Abu bane mai sauki ki yarda dani lokaci d'aya ba, but Ina son
kiyi trusting dina bazan taba cutanki ba, so plz ki bari inga iyayenki
Tace
shikenan zaka ga iyayena amma sai bayan bikin ka, Kafin nan ka sami nutsuwa.
Murmushi
yayi tare da fad'in duk yanda kika ce haka za'ayi, bari in barki ki huta sai
munyi magana gobe.
Tace Allah
ya kaimu.
Ya amsa da
Ameen tare da fad'in I love you
Murmushi
tayi tare da fad'in nagode.
Yace Nop ba
haka zaki ceba, amsa nake bukata nace I love you sai kiban amsa.
Tace shine
nace nagode ai.
Murmushi
yayi tare da fad'in in baki bani amsa ba in nazo sai nasa kin ban
Tace uhm
tare da fad'in I love you too, tana fad'in haka ta kashe wayan.
Yarima wani
irin nishad'i yake ji, tare da mamakin kansa Wai yau shine yake fira da mace
haka ikon Allah.
Habib ganin
bariki ta kashe waya yace Wlh bariki keba karamar yar duniya bace, jiba yanda
kike waya da Yarima kaman wata baiwar Allah.
Bariki tace
eh naji din, kin san mai yace kawata? Wai aurena zaiyi nan da wata biyu yake
son muyi aure.
Habib yace
an gama, inma wata d'aya yace ke ko gobe yace Wlh zamu aurar dake.
Bariki tace
taya?
Habib yace
kaman yanda muka je gidan mutane kika fito a matsayin nan ne gidan y'an uwanku
haka ma za'a ma auran iyayen bariki zamu samo.....
Bariki tace
iyayen bariki kina ganin babu matsala?
Habib yace
koh d'aya kawai kiyi yanda nace
Bariki
murmushi tayi domin wannan ne kadai hanyar da take ganin ya dace..... Kai Anya
zan iya kuwa? Babu tsarin aure a rayuwa na. Murmushi kuma ta kuma saki tunawa
da tayi yace in basu dai daita ba bazai Mata dole ba......
~MARYAM OBAM~
No comments