BARIKI NA FITO (BOOK 1) 15
*PAGE 15*
Jin tayi
shuru yasa Yarima Aliyu fad'in, lafiya kuwa?
'kago
murmushi tayi tare da fad'in sunana Zainab musa haifaffiyar garin kaduna, gidan
mu yana u/kanawa mahaifina yana sana'ar rini, duk da bashi da
karfi ya bamu
tarbiya dai dai gwargwado sannan har yau yana kokari wajan bamu tarbiya,
mahaifina Talaka ne amma yana da Kawa zuci, zaiyi abunda wani mai kud'in ma
bazai iyayi ba, mu biyu iyayena suka mallaka sai yasa duk wani burinsu da
kudirunsu yake kammu nida dan uwana, wajan ganin mun sami rayuwa mai in ganci
kuma Alhmdlh tunda yau saukan mu ranan sati mai zuwa insha Allah zan haddace
al'qur'ani Mai girma, shi yayana mai suna Saddiq ya dad'e da sauke
al'qur'ani, sannan fannin boko inada
matakin secondary domin mahaifina bazai Bari Inci gaba da karatu a gidansa ba
sai gidan mijina, wannan dai shine labari na.
Yarima
murmushi yayi sannan yace y'an Zaria ne kenan ku?
Gabanta taji
ya fad'i dan in tace su y'an Zaria ne toh a wace anguwan? Kai a'a da sauri tace
a'a mahaifina dan Kano ne domin a can aka haifeshi, tun yana dan shekara Goma
sha biyu ya dawo kaduna shida iyayensa har Allah ya musu rasuwa inda mahaifina
ya fara buga buga har yakai da yayi aure aka haifemu a garin kaduna, toh Kaga
inda aka haifa mutum toh nan ne garinsa.
Murmushi
Yarima Aliyu yayi tare da fad'in hakane,. Yace Zainab naji dad'i Sosai da naji
tariyin ki, babban abunda ya kara burgeni daya kasance princess dita maddaciyan
al'qur'ani ce, Allah yasa ya amfana al'umma
Tace
Allahumma Ameen Yarima na..... Shuru
tayi domin jin Kalman daya fito daka bakinta....
Yarima da
sauri ya kalleta domin irin Sunan take kiranshi cikin mafarkin shi, yace Zainab
plz say it again
Jin tayi
shuru kanta na kasa yasa ya kamo hannunta da take wasa dashi ya ri'ke hannun
duka biyu tare da fad'in plz say it again plz.
Ri'ke mata
hannu da yayi yasa komai dake jikinta ya tsaya wannan ne karo na farko da
namiji ya taba, taba mata jiki taji wani abu, danko mazan da take iskanci dasu
bawai tana jin wani abu bane kawai tana dai yine, amma shi Yarima hannunta ya
ri'ke yasa tana jin wani abu tun daka tsakiyar kanta Kar kasan kafanta, kokarin
Fara Jan hannunta tayi daka nashi, amma ta kasa.
Murmushi
yayi tare da fad'in sai kin fad'a min abunda nace zan sake ki, a hankali tace
Yarima na, ido ya lumshe cikin jin dad'i tare da wani kara jin Sonta har cikin
ranshi.
Muryanta da
yaji tana fad'in plz ka sake min hannu shine ya dawo dashi daka duniyar tunanin
daya fad'a, ido ya bud'e tare da d'auko wani Leda, ciro wani karamin kwali yayi
anyi raping dinshi, bud'ewa yayi ya d'auko wani
diamond ring, saka mata yayi a hannunta das ya shige kaman an gwada,
yace this ring is my heart, ina fatan zaki ri'ke min shi dakyau?
Murmushi
tayi tare da saka hannunta a kafanta tana kallon zoban mai shegen kyau Wanda
Yarima Aliyu ya kira da zuciyar shi ce.
Ganin idonta
nakan zoban tana kallo kobai kara cewa komai ba yasan ya samu shiga.
A hankali
tace Yarima wannan ring din bai dace dani ba, hawaye ne ya fara zuban Mata
Sosai
Ganin haka
hankalin Yarima Aliyu ya tashi Sosai tare da fad'in Zainab mai yasa kika fad'i
haka?
Cikin kuka
tace Yarima ni dakai bamu dace ba baka dace dani ba kafi karfina ba Irina ta
dace dakai ba nasan in.....
Dakatar da
ita yayi tare da fad'in ya isa haka zainab. Tissue ya d'auko ya fara goge mata
hawayen da takeyi yace kalla yanda kika batamin Fuskanki da hawaye, yana
maganan ne yana kallon ta, yace Zainab shi so babu ruwanshi dako Waye mutum,
Zainab ina sonki dagaske bada wasa ba, tun Kafin in ganki nake sonki tun cikin
mafarki na, bana tunanin akwai abunda zai saka in daina sonki, zainab yau had'uwa
na dake da nayi na fuskanci abubuwa da dama, kina da addini kin fito gidan
mutunci iya wannan ya isheni, zainab duk irin yanda nake son matar da zan aura
ta kasance kina dashi, ina da kishin abunda nake so, ina son mace Mai suturta
jikinta Wanda ke gashi ko a cikin mafarki na da hijab kike zuwa har a zahiri ma
da hijab na ganki, wannan abubuwan ya isa duk wani namiji yayi burin samunki a
matsayin matar auransa kuma Uwar y'ay'ansa, I don't care ko daka ina kika fito
ke nake so bawai wani abuba, inda kin San yanda nake jinki a raina da baki
tunanin wani abuba so plz karki kara fad'in ni dake bamu dace ba, d'an matsawa
yayi kusa da ita yace kalleni kiga bamu dace ba? Ganin taki d'ago kai yasa yayi
murmushi yace ban taba ganin couple din da suka dace ba kaman ni dake.
Bata san
lokacin da dariya ya sakar mata ba domin maganan shi ya bata dariya.
Ganin tayi
dariya shima yayi murmushi tare da fad'in yauwa na saki dariya am happy now.
Murmushi
tayi tare da fad'in babu kyau son Kai, ai bakai zaka fad'a ba wani ne zai fad'a
yace mun dace ko bamu dace ba.
Murmushi
yayi tare da fad'in Toh Kema ya akayi kika san bamu dace ba?
Kanta na
kasa tace saboda naga haka dinne.
Shima yace
nima na fad'i hakan ne dan Ina ganin mun dace
Murmushi
tayi
Sunanta ya
kira yace Zainab Ina son fad'a miki magana Mai muhimmanci.
Gabanta taji
ya fad'i, amma saita daure tace inaji.
Yace biki na
ranan Friday din nan rana ita yau.
Dam taji
gabanta ya fad'i Wanda bata san dalili ba tare da kallonshi da sauri ganin Sun
had'a ido domin shima ita yake kallo yasa tayi kasa dakai.
Yace Zainab
iyaye na sun sha bani mata amma naki yarda burina kullum in ganki dan muyi aure
sai yasa bana yarda da duk wani zabin iyayena, mahaifina ya gaji da zama na
haka babu mata, musamman daya kasance nine d'ansa namiji guda d'aya yana
bukatan ganin jikansa, sai yasa ya yanke bani auran y'ar sarkin katsina gimbiya
zinatu, bayan na amince da auran domin ko ban amince ba dole Ayi tunda
mahaifina bada wasa yake ba, kawai sai na ganki keda wancan guy din ya nuna
mata habib dake waje yana hararan driver dinshi, Zainab na fad'a miki wannan
maganan ne saboda ina sonki ban son boye miki komai dake tare dani , ina son
Kema ki fad'amin abunda kike ji a game dani.
Bariki kanta
na kasa tunda Yarima ya Mata maganan auranshi rana ita yau, ta shiga damuwa
wanda ta rasa dalili, ganin yayi shuru ita yake saurara yasa tace ina son ka
bani lokaci kad'an inyi tunani akai
Yace Zainab
when no one's around but you and me. A lokacin zaki iya tunanin mai kike ji a
kaina. Kiran sunanta yayi cikin wani irin murya
d'ago dakai
tayi suka had'a ido da sauri ta sauke idonta ta rasa mai yasa bata iya
kallonshi gabanta faduwa yakeyi Sosai, jin hannunshi tayi akan nata.....
Yace my
princess zan baki lokaci amma fah bamai yawa ba, kwana biyu kawai na baki kiyi
tunani akai na Zanzo inji amsa daka gareki.
Kasa motsi
tayi sai gabanta dake faman dukan uku uku, Mai yasa na kasa fad'a mishi abunda
Nayi niya Mai yasa bana jinshi kaman sauran mazan da nake hulda dasu? Mai yasa
ya banbanta dasu? Ga hannuna a ri'ke da nashi amma na kasa yin abunda nayi niya
ido ta lumshe domin ta rasa amsan wannan tambayan nata .
Ganin tayi
shuru yasa yace my princess karki manta kwana biyu na baki Zanzo inji daka
gareki jibi kenan, sannan Saturday shine ranan waliman ki koh?
Kai ta d'aga
alaman eh.
Yace Allah
ya nuna mana ranan, jin kiran sallah la'asar yasa yace bari muyi sallah sai mu
kama hanya.
Tace toh
Bari a kawo maka ruwa, bud'e motar tayi ta fita cikin gidan ta shiga da sauri
habib yabi bayanta..
Tana ganin
habib tace yauwa Kai ma Yarima ruwa yayi alwala, amsa yayi ya fita tare da
kaima yarima ruwan
Sannan ya
koma ciki, inda ya sami bariki na sallah itama, zama yayi yana jira ta idar,
Bayan ta gama.
Habib yace
ya kukayi?
tace Kai
baka je masallacin ba, d'aure fuska yayi tare da fad'in in banda rashin mutunci
kin taba ganin mace a masallaci? Gskya banso.
Bariki tace
Allah ya shirya, jin wayanta yayi kara alaman sa'ko ya shigo yasa ta duba taga
Yarima ne yayi mata message *come out my princess* murmushi tayi tare da tashi
ta d'auko jakarta ta fesa turare sannan ta fita, motar ta bud'e ta shiga inda
ta ganshi zaune yana waya taji yana fad'in lil yanzu zan dawo nace kuyi komai
keda usman Kafin in dawo, kashe wayan yayi sannan ya kalli bariki
Yace my
princess zan tafi, sai nake ji kaman mu tafi tare.
Murmushi
tayi tare da fad'in in lokacin hakan yayi zamu..... Da sauri tayi shuru dan
maganan da taji tana niyan fad'a
Ganin tayi
shuru yasa Yarima Aliyu yayi murmushi tare da fad'in ina ji karasa abunda kikai
niya.
Hannunta
tasa a fuska alaman jin kunya
Yarima
dariya yayi Sosai abunda bai taba yima wani ko Wata ba sai yau, d'auko wani
card yayi ya bata tare da fad'in plz in kin shiga Gida ki turomin Abokina habib
Tace toh har
zata fita ya kira sunanta waigowa tayi
Yace Zainab
Waye habib a wajan ki?
Tace d'an
uwana nane yaron kanwar mama nane.
Yarima yace
ok na gane I love you
Dariya tayi
tare da fita da sauri tayi cikin gida.
Ko minti
biyu batayi da shiga ba saiga habib yazo, yarima wani Leda ya bashi babba tare
da fad'in kaba ma my princess wannan, wata karaman Leda ya d'auko tare da bama
habib yace ga naka.
Habib amsa
yayi yana ta godiya sannan ya fita
Su Yarima
hanya suka kama yana kallon gidan da zainab dinshi take har suka wuce.
Koda habib
ya shiga gida bama bariki sa'kon da Yarima ya bata yayi, bud'e nashi yayi yaga
agogo Mai shegen tsada da kud'i dubu d'ari biyu ihu ya saki tare da fad'in oh
wannan koh dan arziki. Ganin bariki tayi shuru kaman mai tunani yasa yace
bariki lafiya kuwa?
Bariki tayi
firgit tare da kallon habib tace ina son fad'a mishi gaskiyan koni wacece amma
na kasa, mai yasa baiyi min kaman yanda nake ganin sauran maza ba, ya banbanta
dasu, na rasa gane mai nake ji a kansa, na tsinta kaina da tsoran fad'a mishi
koni wacece, Nasan zai tsaneni.....
Habib yace
bariki kin kamu da sonshi
Kai ta
girgiza alaman a'a tace ba sonshi nake ba, ina mamakin kasa gaya mishi abunda
Nayi niya ne Bayan daka ni sai shi, tunda na fito bariki ban taba had'uwa da
mutum Wanda naji ya cika min ido ba sai yau, Indai bazan iya gaya mishi koni
wacece ba ya zama dole inyi nesa dashi Kar in kara Bari mu had'u......
~MARYAM
OBAM~
[8/8, 11:45
AM] 🅰 "🅰 " D'🅱⭕Y🔛🔝: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ 📚📚_*
[8/8, 12:16
PM] 🅰 "🅰 " D'🅱⭕Y🔛🔝: [8/8, 11:46 AM] 🅰 "🅰 " D'🅱⭕Y🔛🔝: *BARIKI NA FITO*
*BY*
*MARYAM
ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*
No comments