BARIKI NA FITO (BOOK 1) 14
*PAGE 14*
*PLZ KUYI
HAKURI DA TYPING ERROR, BANI DA LOKACIN EDITING, NASAN KUNA GANEWA*
Ganin bariki
na dariya.
Habib yace
miye kike dariya haka? Naga kin samu dama kina son wasa dashi, wlh dani yace
yana So da yaga yanda ake zuba
soyayya, baki ga yanda ya had'u ba, kai akwai
y'an maza kyawawa fah, kaman yanda muma muke jerin kyawawan Mata.
Bariki taci
dariya Sosai, sannan ta tsagaita tace yanzu miye Abun yi?
Yace kawai
ki zama ready goben, zamu wani Gida saiki fito daka cikin gidan kaman nan ne
gidan y'an uwan naku.
Bariki
dariya ta saki tare da fad'in Kai kawata kanki naja fah Sosai.
Habib yace
Toh an fad'a miki nita wasa ce, wai mai kika kawo mana ne? Yunwa nake ji wlh.
Bariki tace
tea nake son sha, Bari in had'a mana.
Habib tabe
baki yayi tare da fad'in sai kace wasu 'konannu, Musha tea da wannan daran,
bada niba sa lallan kaza.
Bariki tace
toh mai kake so? Ni tea din kawai garan indomie nama ta Kare.
Habib yace
tashi za kiyi muje wajan mai shayi ya soya mana indomie da kwai.
Tace Kai
kawata kije ki siyo mana Wlh na gaji, ni zan fara shan tea Kafin ki kawo
indomie din dan Wlh bazan iya jira ba, wani irin shegen yunwa nake ji, kaman
hanji na zasu fita.
Tashi habib
yayi tare da fad'in kyaji dashi yanzu inda wani tsohon kwarto zai kiraki ai
nasan tashi za kiyi ki tafi.
Bariki mi'ka
ma habib kud'i tayi tare da fad'in zani mana da gudu Indai ayabarsa tamin, ki
siyo mana da kaza.
Habib yace
oh Ina mace santaleliyan budurwa zani siyan nama, salan kisa su kwa'kuleni.
Bariki tashi
tayi tasa ruwa a heater tare da fad'in dan Allah kije ki dawo.
Fita yayi
yana fad'in sabon salon iskanci, sai kace Nina aikeki kije tama d'id'i.
Bariki had'a
tea tayi tana sha, jin karan wayanta yasa ta d'auka taga Yarima ne, da sauri ta
danna tare da sawa a kunne.
Sallama tayi
cikin sanyin murya.
Amsawa yayi
tare da fad'in Barka da dare, hope baki Fara bacci ba na tada ki?
Tace a'a
bacci tun yanzu, karatu ma nakeyi yanzu Ina shirin in ajiye qur'ani sai ga
kiranka.
Yarima
murmushi yayi cikin jin dad'i domin duk Sanda zaiyi magana da Zainab dinshi
wato bariki sai yaji tana abun islamiya abun addini dai, yace yanzu naga
message dinki, so gobe around 2 zaki ganni.
Tace Allah
uban giji ya nuna mana goben lafiya.
Ya amsa da
Ameen, tare da fad'in ta ina gidan yake?
Tace karka
damu Idan kazo bakin titi ka kirani zansa habib ya kawo ku dan ban san yanda
zan maka kwatance ba.
Yace ok babu
damuwa gimbiya Zainab
Dariya tayi
tace Yarima niba Mai sarauta ba amma kaban sarauta.
Yace mijinki
ai mai sarauta ne, Kinga Kema sarauniya ce koh?
Uhm kawai
tace alaman taji kunya..... Nocking aka fara Mata,
Yarima jin
kaman ana nocking yace ba'ki kikai cikin daren nan?
Tace ba'ki
kuma ina tunanin mum ce, take nocking Bari in gani.
Yarima yace
ok take care tare da kashe wayan.
Tashi tayi
ta bud'e kofar.
Habib yace
bud'e kofar ma sai an batamin lokaci?
Tsaki tayi
tare da fad'in waya nake kin zo kina buga kofa kaman nayi sata.
Habib tabe
baki yayi tare da ajiye ledan kayan daya siyo, yace kyaji dashi, bud'e ledan
yayi ya d'auko indomie ya fara ci.
Ita kam
bariki Naman ta d'auka tana ci tare da fad'in Yarima na yanzu ya kira.
Habib dariya
yayi yace amma bariki Keko y'ar duniya har wani suna kika samai Wai Yarima na.
Bariki tace
eh mana Yarima na Mai son ustaziya
Dariya suka
saki Sosai
Sannan habib
yace ai Wlh har na kosa goben yayi ku had'u ku tattauna inga yanda zata kaya.
Bariki
murmushi tayi tare da fad'in Nasan muddin na fad'a Mai gskya koni wacece Zaima
gudu ne, dan bazan bari ma muyi nisa ba.
Habib yace
amma dai Keko anyi mara wayau, akan wani dalili zaki fad'a Mai koke wacece?
Bariki tace
kawata ban son in cutar dashi in.....
Habib ya
Katse bariki da fad'in ya isa dan Allah ni Kinga saida safe kiyi duk abunda ya
dace tashi yayi ya fita yana gantsaro duwawu.
Bariki rufe
kofarta tayi tare da fad'in shege kana son in cuta mutum, kai ai saika
aureshi, Bayan ta gama abunda take ta
kwanta abunta.
***********
Hjy Umaima
tunda ta shiga d'aki ta tsure Sosai dakyar nutsuwa ta dawo mata tare da fad'in
yau na d'auko ruwan dafa kaina, oh Allah ya soni na tsallake Rijiya da baya,
wannan kyan nata ai dole aljanu su shigeta, kasa fita tayi dan tsoro ranan ko
bacci ta kasa, tana tsaye wajan window da safe taga bariki ta fita, tana ganin
haka ta kira security tace karsu bari yarinyar nan data fita yanzu ta kara
shigowa.
Suka amsa da
ok ma.
Kiran Hjy
habiba tayi tare da fad'in kawata jiya naga bala'i yarinyar nan dana tawo da
ita ashe aljanu gareta, baki ga yanda tamin ba Wlh nayi mugun tsorata.
Hjy habiba
tace Innalillahi, ya kuka kaya?
Labarin
abunda ya faru hjy Umaima ta bata.
Hjy habiba
tace Allah ya kyauta ga yarinya kyakyawa, toh amma sai naga kaman y'ar hannu
ce, kawai dai Nasan an sami matsala ne aljanunta suka tashi, amma bari in
tambayi daughter na, tashi tayi ta nufi falo inda haulat ke zaune tana
breakfast, tace haulat Wai bariki kawarki tana da aljanu ne?
Haulat
dariya tayi tare da fad'in injiwa?
Hjy habiba
ta bata Labarin abunda hjy Umaima ta fad'a mata.
Haulat taci
dariya Sosai sannan tace bariki ko y'ar iska, toh Wlh bata da komai, nidai Ina
tunanin bata lesbians dan zama na da ita ban taba ganinta tayi ba, ita kawai
barta da bin mazanta.
Hjy habiba
tace kenan tayi ma Hjy Umaima hakan ne danta kwaci kanta, Allah ya kyauta itama
Hjy Umaima ta cika jaraban tsiya Wlh tana da y'an mata kala Kala, amma daka
taga wasu ta dinga rawan jiki kenan Allah ya kara mata Kinga aita had'u da
cikakkiyar y'ar bariki tayi maganinta ta rage zari ai yanzu....
Haulat ganin
hjy habiba nata surfa bala'i yasa ta tashi ta nufeta tare da saka bakinta cikin
na hjy habiba ta Fara tsotsa sunyi wajan minti biyar sannan haulat ta cire
bakinta cikin na hjy habiba tace mumy wannan fad'an fah haka?
Hjy habiba
data fara tsumuwa tace Wlh baby raina ne ya baci ta cika kwashe kwashe, tace
muje d'aki daughter sha'awar ki nake Sosai haulat tace muje mum tun daka nan
suka fara she'ke ayarsu.
********
Habib ne
bakin titi daka gani yana jiran wasu ne, sai faman tabe fuska yake da baki a
dan dole shiga mace, yana nan tsaye yaga jerin motoci har biyar kobai tambaya
ba yasan Yarima Aliyu ne, gyara tsayuwa yayi da kyau yana d'an murmushi, dai
dai inda habib din yake motar da Yarima Aliyu ke ciki ta tsaya, glass din motar
aka bud'e driver din Yarima ya gani d'aure fuska habib yayi tare da fad'in mai
ba'kin hali.
driver din
murmushi kawai yayi tare da fad'in kaje motar gaba danka nuna mana gidan.
Habib bai
kuma cewa komai ba yayi gaba aka bud'e Mai motar ya shiga, dai dai kofar wani
Gida suka karasa gidan ginin kasa kana ganin gidan kasan basu da karfi.
Idon Yarima
ya sauka a kofar gidan, gaba d'aya yaji jikinshi yayi sanyi da ganin gidan,
tare da fad'in my princess bata dace da zama a nan ba, Sosai yaji tausayinta
tare da kara Sonta.
Bayan sun
tsaya habib ya fita ya nufi motar Yarima inda driver din Yarima ya fito ya
bud'e Mai, habib shiga cikin motar yayi a gaba ya zauna dan Yarima yana baya,
kallon Yarima yayi yana wani murmushi tare da fad'in Barka da zuwa Bari inje in
kirata.
Yarima
amsawa yayi da yauwa, da fatan kana lafiya?
Habib har
wani fari yake da ido yace eh ranka ya dad'e, tare da bud'e motar ya fita,
kallon driver din Yarima dake tsaye yayi ya banka mai harara tare da fad'in
munafuki.
Yarima Aliyu
yana mota yana kallonsu ya rasa mai yasa baya son habib, kodan yana hulda da
wacce yake so ne oho, kuma ya tabbata badan uwanta bane....
Yana cikin
wannan tunanin ya hangota ta fito ita da habib cikin hijab, idon Yarima na
kanta yana kallon kyakyawan fuskanta duk da batai makeup ba dan dama ita ba
ma'abociyar yin kwalliya bace, Yarima Aliyu kallonta yake har suka karaso inda
yake
habib ya bud'e mata motar alaman ta shiga.
dan cijewa
tayi alaman bazata iya shiga ciki ba.
Habib yace
Zainab kiyi hakuri ki shiga yanzu kawu zai dawo, kuma Kinga ba mutunci bane ku
tsaya a waje koh?
Shiga tayi
ta zauna gabanta taji ya fad'i da taga Yarima, wani irin mugun kwarjini taga
yayi mata, zuciyarta ta Fara buga mata da karfi, duk kallonshi da takeyi ta
gefen ido takeyi.....
Yarima Aliyu
yace tsarki ya tabbata ga Allah da yayi wannan halittar.
Kanta tayi
kasa dashi tana wasa da y'an yatsun hannunta alaman kunya, tace Barka da zuwa,
ina wuni.
Yarima
idonshi na kanta yana kallon bakinta yanda take magana cikin nutsuwa yace
lafiya kalau my princess, d'an shuru yayi yana kallonta wani irin sonta yaji
yana fusganshi... A hankali ya kira sunanta da zainab
D'ago dakai
tayi suka had'a ido da sauri tayi kasa da kanta.
Murmushi
yayi tare da fad'i cikin ranshi tana da kunya Sosai, yace Zainab da farko dai
sunana Aliyu mu biyar ne wajan dad dina nine namiji guda d'aya da iyayena keda
shi, zainab na dad'e Ina sonki tun ina secondary school....
Da sauri ta
d'ago ta kalleshi domin abunda yace ya bata mamaki Sosai, Anya Yarima bai sanni
ba kuwa?....
Katse mata
tunani yayi da fadin tun ina skul nake ganinki cikin mafarkina tun ban d'aukan
abun da muhimmanci harna Fara d'auka har takai ta kawo na Fara zana hotan jikin
ki, dan ban taba ganin Fuskanki ba, domin kina zuwa min cikin duhu ko kuma kizo
min sanye da nikabi, danna wayanshi yayi yace kalla ki gani.....
D'ago dakai
tayi tare da kallon wayan gabanta taji ya fad'i nuna mata hotan yake amma duk
babu fuskanta akai sannan duk colour din hijab din duk tana dasu, harda wani
farin hijab Wanda take dashi Mai leshi a wajan kan, tana kallo tana mamaki ya
fara nuna mata Wanda akwai fuskanta akai, da sauri ta kalleshi ganin idonshi na
kanta yasa tayi kasa dakai sannan tace duka duk Kalan hijjabai nane, abun yaban
mamaki.
Yarima yace
Zainab Nayi imani had'uwa na dake had'in Allah ne, tun sanda nake mafarkin ki
nake ta fama da sonki tare da burin ganinki, sau d'aya na ganki a bakin hanya
na tabbata Kece domin da jikin ki na ganeki.
Bariki tace
hakane Abun yaban mamaki
Yarima Aliyu
yace ba'a mamaki da ikon Allah Zainab, ina son in San koke wacece.
Bariki shuru
tayi ga gabanta dake ta faman fad'i...... Muje zuwa muji bariki gaskiya zata
fad'ama Yarima Aliyu ko akasin haka......
No comments