MIN QALB 48
MQ 48_*
*_THE FLAVORLAND BY ACEEY_*
Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na al’adance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da:
Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa
Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma
Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama
Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da:
Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi DA
Gashe gashe da soye soye kamar su
Kaza
Kifi
Nama
Doya
Dankalin turawa/hausa
Awara
Danwake
Gurasa
Kwado da dai sauransu....
Ba Mu tsaya anan ba——
The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe
da suka hada da
Hoppers wato Fara
Milky candies wato alawar madara da kuma
Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke
buqata...
Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka
IG: @the_flavorland
Whatsapp:08104673847
Sending Some treats your way.... l
Let us satisfy your cravings:
We Deliver anywhere and everywhere.
*******
*********
Suna Isa zabeera Kai tsaye motar data daukota sashen Andi
aka nufa dasu sbd har Modibbo da umme na can dashi kansa MAHMOUD din Wanda
ranar yakoma MD ZABEERA dinsa sak miskilanci da izzarsa sun motsa ko wayoyinsa
duk akashe ma suke Abu daya kawai yakeji atare dashi shine nutsuwar zuciya data
ruhi harma data gangar jikinsa Wanda yagama tabbarwa da kansa cewa tabbas Amatu
tarigada tazama wani babban bangare an zuciya,jiki da rayuwarsa tunda
haryakejin wannan nutsuwar me sanyin Dadi tattare da dawowarta garesa.
Suna shigowa akansa idonta yafara sauka ta dauke Kai Yana
sunkuyarwa ta zauna daga qasa gefen umme dake kallonta fuskarta na bayyanarda
farin ciki da murmushi.
Da MAHMOUD din Andi yafara nasiha akan haqqoqan Mata dake
Kan mijinta dakuma ire iren halayen .ata da Dole namiji saiyayi hkr dasu sbd
rauninta dakuma rashin zurfin tunani da Rashi haquri irin na wasu matan
kafin yadawo Kan Amatu da nasihar zama da miji da girman haqqoqinsa akanta da
girmansa dayafi na kowa akanta yanzu yaqara da nasihar adalci tsakanin mataye
biyu dakuma haqurin zama da abokin zama Dana rayuwa kafin daganan Andi yayiwa
Amatun kyautar aure ta sabuwar mota fil sak irinta zarah datake hawa banbancin
kalane kawai dayace Tata Ash ce ta zarah farace.
Godiya sosai sukayi suka fito umme na riqeda hannun ta saka
Mata wani acikin hannun dayake rufe cikin qaramar kwalbar roba suna shiga mota
tace"
Shanye kiban roba.
Kallon ummen tayi tana sake kallon abun ta Dan 6ata fuska
zatai mgn tace"
Bansan Jin komai hanzarta kishanye kiban.
Marairaice fuska tayi tana kallon abun.
Anty salamatu dake sit din gaba ta juyo ta kwace kwalbar ta
bude tareda Dora Mata abaki tana cewa''
Dallah shanye da abin dadine da yanzu kinfara maganar qari
to wannan dadinsa saikin fi kowa.....
Rufe Mata baki Amatun tayi da sauri tana zaro Ido kunyar
umme kamar ta nitse ta saci kallonta tace"
Haba anty salamatu nidai karki fara zancenki Dan Allah.
Itama anty salamatu kunya taji sbd mantawa tayi da umme da
iyami dasuke taredasu sbd sun Saba zantukansu na banza dasu maman junior
shiyasa.
Shanyewa tayi ta miqawa umme kwalbar daidai isowarsu qofar
part dinta motar har qofar palonta ta faka suka fito umme na riqeda hannunta
tana fada maganganu qasa qasa na rikita miji wainda sukafi qarfin duk rawar Kan
Amatun kunya kamar ta qwace hannunta ta zura da gudu Amma ummen ba ruwanta fada
Mata takeyi har suka shiga suka zauna palon tana sake zayyano Mata zantuka masu
qarfi wainda wasune suka samu damar shiga kanta wasu kuwa nauyinsu yasa suna
kasa shigewa Kan nata.
Turaruka ummen ta fitar cikin jakar hannunta ta fesawa
Amatun ko Ina jikin masu wani irin sanyin qamshi dagaji tasan bazasu wuce ouds
ba masu tsananin tsada take qamshinta ya qaru tana fitarda wani qamshi me
ni'imtaccen sanyin dadi suka Fara qoqarin tafiya anty salamatu tace"
Zarah ko lafiya Naga banganta ba na dauka ma zamu sameta
anan gashi har zamu tafi.
Umme tace'
Eh Kam gashi dai Nima duk yau banganta ba Nima nai zatan
zamu sameta anan din tana jiran isowarmu.
Iyami data miqe tsaye tana gyara zaman mayafinta yace"
Mezaisa zarah tazo ta zauna anan tana jiranmu karku manta
bafa kamar da bane yanzu ana Magana akan Amatu tazama matar mijintane Dole wani
abun zata Kama kanta ba kamar da ba da Amatun take matsayin qanwarta yanzu
kishiyarta ce Dole akwai radadi ko yayane aranta.
Tsit Amatu tayi tana saurarensu sbd duk lokacinda akai Mata
tunin kishiya saitaji kamar hankalinta nason tashi saidai girma da nauyin anty
zarah da haryanxu take gani da ji atareda ita yana danne kishin datakeji
shiyasa take sauke zafin kishinta agun MAHMOUD sbd bazata iya kallon fuskar
anty zarah tayi fitinar kishi da ita ba duk zafin kishinsa kuwa sbd Abu daya
data fahimta takuma lurarwa kanta MAHMOUD da kansa zai iya kiranta butulu akan
zarah idan bata nutsu ta iya zama acikinsu ba yanzu Kam akwai aiki agabansu su
dukan na iya zama da juna.
Bayan tafiyarsu iyami kasa tashi tayi daga Inda take zaune
tashiga tunani daban daban akan rayuwarta da Kuma ranar farko da aka Fara
kawota cikin part dinnan amatsayin matar KHALIL DAHEER ZABEERA yanzu Kuma gashi
ankuma kawota amatsayin matar Dan uwansa MAHMOUD DAHEER ZABEERA,
Duk da ansauya sashen gabaki daya Babu inda zaka iya gane shine
wancan din Amma dai memories diinsa suna cikin zuciyarta.
Hawayene suka ciko idanuwanta suna qoqarin gangarowa taji
bude qofa
Bata dagoba Amma qamshin daya shiga cikin hancinta da
motsinsa da baya qarfi yasa ta fahimci waye yashigo ta rufe idanuwanta ta bude
ahankali batareda ta dago ta kallesa ba saima sake lumshe idanuwanta datai.
Qarasowa yayi cikin nutsuwarsa da kamalarsa ya zauna kusada
ita sosai qamshinta ya Shiga hancinsa yanl dago fararen idanuwansa dasuka Gama
gabalaituwa a sonta ya zuba Mata tareda riqo hannuwanta ya sarqe da nasa ya
sauke ajiyar zuciya wadda itama ta sauke tata a boye cikin cikinta.
Kasa Magana yayi sbd bayajin yin maganar ya kwantarda kansa
Kan kafadarta Yana sake sarqe hannuwansu ya lumshe idanuwansa sukai shiru
ahakan sai numfashi da qamshin juna dasuke shaqa nutsuwa na shigarsu duk da
Babu Wanda yafito yagfada Amma numfashinsu dake fita ya bayyanarda hakan.
Sun jima ahakan Babu wani motsi Saida yagama samun dukkanin
nutsuwar daya rasa kafin ya sauke numfashi tareda dagowa ya kalli fuskarta suka
hada idanu ta sauke nata tana qoqarin rufesu ya Kai hannu ya juyo da fuskar
tata Yana kallon halittar da ita kadai ke iya rikita MD ZABEERA baisan
lokacinda ya saki wani irin murmushi ba yana kallon bakinta daya iya fidda
Magana ta arziki data tsiya.
Fuskarsa yakai dab da tata Yana kallon cikin idonta yabawa
bakinta light kiss Yana sake sakin murmushi cikin taushin muryar data sanyata
dago idanuwanta cikin rashin yadda ta zuba Masa yace"
I can't live without you Mrs MD ZABEERA so kada ki sake
tunanin barina sbd komai zakiyi bazaki iya barin rayuwa Dani ba.
Miqewa yayi tsaye hannunta cikin nasa har lokacin ya miqar
da ita Yana cewa''
Let's have dinner zarah is waiting.
Ba musu tabiyosa suka fito hannunsa na riqe da nata itama
saiyi takeyi tana kallonsa duk da tasan so yake azauna lfy Amma dai mamakinsa
bai daina kamata ba sbd ganin yanda ya sauya din dama ita batada niyar zama da
miji Babu shaquwa Babu Wasa da dariya Babu hayaniya Babu muguwan wasan gudu
gudu idan ma takama to Ina dadin rayuwar auren take tanason morewa sauran
kuruciyarta a tareda mijin aurenta Dan haka Babu wani daga mulki sai oda a
Shirin zamanta dashi.
Suna shiga anty zarah na fitowa daga bedroom dinta cikin
adon riga da skirt na lace maroon tayi Yar simple makeup ga qaramin cikinta
daya Dan fito tayi kyau itama sai qamshi take saidai suna qarasa shigowa
qamshin dake fita cikin Amatun saita ji ta daina Jin natan ta qurawa Amatun
idanuwanta dake son raunana da irin dacewa da kyan dasukai tareda juna ta kalli
hannuwansu dake sarqe tafara Kiran sunayen Allah tana kore shedan daga
zuciyarta ta saki murmushi tana kallonsu tace"
Sannu da zuwa Amatu.
Murmushi Amatun ta saki tana kallonsa da shima ita yake
kallo tace"
Thank you anty.
Kallon MD din zarah tayi tana dauke idonta daga Kan hannunsa
dake riqe Dana Amatu tace"
Dinner is ready fa.
Dining suka nufa su dukkansu suka zauna zarah ce ke zaune
kusada MAHMOUD din sukaci abinci itadai Amatu drink kawai Tasha sai spoon biyu
datai ta miqe tace ta qoshi.
Shima ba wata yunwa yakeji ba Amma ya zauna yaci abincin
sosai tareda zarah haryana yaba abincin sosai sbd Fara sanin halin Mata dayayi
ya fahimci sunfi son ko yaushe ka nuna musu yabawa da kulawa.
Aikuwa hakan ya faranta ran zarah musamman daya nuna Jin
dadin abincin a fili saitaji damuwarta ta ragu sosai suka baro dining din itama
Yana riqeda hannunta suka iso ya zaunar da ita Kan kujera ya zauna gefenta Yana
kallon Amatu data matsu tawuce yafara musu bayani da nasiha tareda roqon Dan
Allah a zauna lfy plus respecting juna duk da yasan suna ganin qimar junansu
sosai kafin ya sanar dasu 2days ne kwanan daga haka aka tashi Amatu tafara
wucewarta shikuma zarah yabi Dan sake lallasarta Abinda Baya faruwa a zamansu
mamakinsa da Jin dadin hakan ya sanyaya zuciyarta sosai harta cemasa yatafi
gurin Amatu tana jiransa.
Bedroom dinsa ya nufa yashiga wanka Yana fitowa Saida ya
tsaya wata waya kafin ya fice.
Bedroom 'dinda ta tabbatarda shine nata tashiga data dawo
daga sashen na zarah ta ajiye wayarta ka bedside drawer ta warware lafayarta ta
nade takai wardrobe
tana budewa ta tsaya kallo cikin mamakin ganin Kaya a shaqe
maqil da hadda wainda aka dinka da wainda ba'a dinkq ba ga qananun Kaya da
jallabiyas ire iren wainda yasan tana sanyawa.
Murmushi ne yaso subuce Mata data Kai hannunta Kan tarin
qananun kayan dake jere Wanda taga bumshorts ne sukafi yawa abin data lura
yafiso kenen wato shigarta zata fiddo cinyoyinta duka a waje.
Rungumeta taji anyi tayi saurin juyowa sbd bataji motsin
shigowarsa ba,
Kallon fuskarsatayi cikin basarwa ta zame daga jikin nasa ta
jefa lafayar ta rufe wardrobe din ta bar gurin ta nufi toilet ta jima ciki Babu
Abinda zatayi tana saqa da warwara kafin dai ta wanke hannuwanta tayi alwala
kawai ta fito tana goge fuskarta da qaramin towel sai ganin lafayarta tayi ya
miqo mata Yana cewa''
Ki mayar inason nizan cire miki inason sake ganinki cikinta
you look innocent acikinta.
Batareda ta kallesaba ta karba ta nufi gaban mirror tana
nadawa ya zauna Kan sofa Yana kallonta hannuwansa nade da qirjinsa.
Tana gamawa ta juyo ta kallesata ta gefen Ido ya taso Yana
murmushi ya Kama hannunta suka nufi bedroom dinsa suna shiga wani sanyin qamshi
ya doki hancinta sbd kalar turarukansa ba Arabians bane nasa designers Eglh
perfumes yake amfani dasu,
As she expected komai na dakin fari ne da milk sbd sune
colours dinsa.
Daddumar sallah ya Ciro itama milk color ce ya shimfada Yana
kallonta yace"
Kinyi alwala right?
Saida ta dauke Kai kafin tabude Baki daqyar tace"
Yes.
Yanda taketa daure Masa din Yana sake burgesane Bata saniba
sbd shi fushin ma nata Yana Masa kallon wani sabon feeling.
Sallah sukayi ta nafila rakaa biyu kafin ya juyo ya riqo
hannuwanta duka biyun Yana kallon fuskarta ahankali ya furta"
Sorry.
Qin juyowa tayi ta kallesa ta zame hannuwanta zata miqe ya matse
hannun Kai tsaye yace"
I love you..
Cak ta tsaya daga qwace hannun dazatayi zuciyarta ta Fara
tsananta bugu takasa motsawa hakama takasa juyowa ta kallesa.
Ya lumshe idanuwansa yasake budewa ya Dora akan hannuwanta
dayake riqe dasu cikin murya me taushi yasake cewa''
I love you AMATULLAH K SALEH and I am saying sorry so please
wannan fushin yakamata ya sauka please.
Juyowa tayi tana kallon fuskarsa zuciyarta na qarasa bugawa
da qarfi ta kasa yadda da Abinda taji idan MAHMOUD ZABEERA dinda tasani ne yake
furtasu saidai zumudin zuciya dakeson kamata gudun bada kanta yasa ta miqe
ahankali tana zare hannuwanta ya dawo da ita jikinsa ta hanyar fixgota ta Fado
qirjinsa ya Bata kyakkyawar runguma Yana fada Mata Magana cikin kunnenta data
sanyata saurin zaro Ido waje tana kallonsa takaici da muguwar kunya suka
dabaibayeta batasan lokacinda ta Fara mintsinansa ba ta bude baki Dole tana
cewa''
Wlh ni sharri ne wannan kakemin, Allah bazan yaddaba....
Dariya yakeyi Mara sauti da hayaniya wadda yaune karonta ba
farko ganin dariyarsa ba murmushi ba.
Ganin ta kunnu sosai da Abinda ya fada din yasashi miqewa
Yana Sosa inda ta mintsinesa Yana cewa''
Zaki fasamin fatane da wannan mintsinin naki..
Biyosa tayi tana sake kunnuwa har lokacin kunyar zancen bai
saketa ba ta nufesa tana cewa''
Saika janye wannan sharrin dakamin bazan yadda ba..
Tana isowa gurinsa ya riqe hannuwan tareda shigar da ita
jikinsa ya Kai fuskarsa Kai tsaye ya hade da Tata ya hade bakinsa da nata yana
Bata wani ni'imtaccen kiss daya kashe jikinta harya warware Mata lifayar
jikinta Bata saniba Saida ya cirata gabaki daya zuwa Kan qaton gadonsa Yana
rage musu hasken dakin ta makunnin gefen gadonsa.

No comments