KIBIYAR AJALI 21
*2___1*
Samun kansa ya yi da jinjina kai alamar yaji sai dai tunanin sa yana ga yadda za'a daura aure baya garin sai kace na asiri. Amman kwarin gwiwar da jarumar zuciyar shi take bashi shine ya sanya shi jingine fargabar tashi da take neman ruguza masa lissafi.
*KHADIJA (DIJE)....*
Tun daga ranar da kawu daddy ya sanar dani ranar aure na ban
sake fita ko nan da compound ba, ma'ana tun ranar da Mas'oud yazo naje gurin
shi. Shi kuwa tun yana kira na ina kin dagawa har ya hakura sai dai ya kira
Shukrah da ya karbi lambar ta dan ya dinga jin bayani game da ni. Hankali na be
sake tashi ba sai ana sauran kwanaki uku kawu daddy ya kira ni wai za a kawo
kayan lefe, a gabansa nace to, amman a raina fata nake Allah yasa motar masu
kawowar tayi hatsari duk su mutu kowa ma ya huta.
Mami kiri kiri tace ba za a soya komai ba dan tasan suma
masu kawo kayan zasu kwallafa rai da cin kaji, dan haka tace yadda suka zo da
tuwo a cikin su, nan d'in ma tuwon za a yi musu dan shi suka saba ci, harda
cewa su kila na dawa da masara suke ci nan kuma na shinkafa za'a yi musu miyar
taushe tasan sai sunyi murna a yau. Ni dai ban yi magana ba saboda ko a jikina
idan ma tace tuwon karfe za ai musu bana jin zai dameni saboda nima ba san
ganin su nake yi ba.
Shiryawa nayi tsab na bar gidan saboda nasan ko sun zo sai
Mami ta wulakantani a gaban su, nasa Tukur ya kai ni gidan su Aisha, ina shiga
ta fara murnar gani na muka shiga dakin ta, kamar jira ni kuma nake yi kawai na
kwanta kan gadon ta na fara kuka mai taba zuciya.
“Ahh kawata menene haka da girmanki? Haba kuka sai kace wata
yar karamar yarinya.”
Still na sake fashewa da kukan ta dinga shafa baya na cikin
nuna kulawa. Tunda aka fara wannan maganar auran ban samu wannan gatan ba na
lallashi sai yau kuma a yanzu da Aisha take ta tausar min da zuciya tun kafin
ma taji abinda nake yiwa kukan. Sai da nayi mai isa ta sannan na sanar da ita
abinda duk ya ke faruwa, ta tausaya min kwarai da gaske sannan ta bani shawara
akan na daure na karbi zabin daddy koda kuwa ace mijin gurgu ne ko makaho na
daure na zauna dashi kodan farin cikin kawu daddy.
Ya zan yi? Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun dole na karbi
wannan auran ko ta halin ya ya ne, gaskiyar Aisha ne ya yi min abinda ko iyayen
da suka kawo ni duniya basu min ba. Ashe kuwa idan hakane ya cancanci fiye da
wannan sadaukarwarma a gareni, dan idan nace zan bijire ni kaina bazan taɓa
yafema kaina ba har randa numfashina zaibar gangar jikina. Haka na zauna a
gidan su Aisha tana ta lallashi da ban hakuri tare da bani labarai makamanta
irin wannan auran da za ai min, da kuma shawarwari masu ƙyau da amfani.
Jinai zuciyata ta rage
nauyin datai min sosai, na kuma samu y'ar nutsuwa duk da banajin son auren har
yanzu. Haka na shiga sauke ajiyar zuciya ina sake godema Allah akan
k'addarorina da suke zuwa gareni daki-daki. Ina fata da addu'ar zama cikin mutane
masu hak'uri da cin ribar hak'urin koda ba'anan gidan duniya ba.
*DR ISMA’ELA RESIDENCE....*
Saboda tsabar wulakanci irin na su Mami ko malmala bata sa
an yiwa tuwon ba, haka tace su juye a kula wai sa dinga zabtara. Wajan ƙarfe
hudu kuwa akai horn mai gadi ya bude motoci tsala-tsala suka shigo harabar
gidan. Tasama su Ya Shukrah suke leken su, hakan yayi da-dai da fara fitowar
mutanan motocin.
Abin daure kan ashe su uncle Hashim ne
da iyalansa sai uncle Kabiru shima da nasa family d'in duk sun zo biki, nan da
nan su Ya Waleedah suka sakko da gudu suna musu oyoyo cike da murnar ganinsu.
“Ya akai babu labari Meenal?”
“Eh cewa akai karmu fada idan muka gaya muku ba za a zo da
mu ba.”
“Ina amaryar take?”
“Ku shiga ciki mana kun tsaya anan zai zance kuke yi."
Cewar Uncle Kabiru yana rufe mota.
Duk sai suka runtuma ciki suna murnar ganin junan su. A
parlorn kasa iyayen suka zauna inda Mami ta fito gurin su. Suna ta hira sai ga
Alhaji Isma'il ya sanar dasu cewa an fasa kawo kayan lefe sai ranar daurin aure
za a hado da su, Mami ranta ya baci dan taso wulakanta duk wanda ya yi kuskuren
biyo masu kawowa sai aka samu aka si. Baki kuwa sai sabon abin ci aka yi musu
dan duk cewa suka yi ba zasu ci tuwo ba, kawu Hashim ne kawai yaci saboda shi
yana son tuwo sosai. Ni kuwa ban koma ba sai da aka yi isha'i sannan Aisha ta
rako ni har mota Tukur ya dawo dani gidan gabana yana faduwa wani dum... Dum...
Dum.. Na shiga cikin parlorn jiki na a sanyaye kamar wace ba ta da laka..
“Oyo yo ga amarya ta dawo.”
Naji sautin muryoyi daban daban, duk a zato na fa yan kawo
lefe ne basu zo da wuri ba har suka kai wannan lokacin. Sai da na dago kai na
sosai na kallesu sannan na fahimci ko su waye, cikin farin ciki nima na rungume
su tare da sakin kuka dan na tabbatar suma daurin aure na suka zo. Na gaida su
suna ta lallashi na sun dauka na dadewa ban gansu bane dan kawu Hashim har da
cewa.
“Last month wallahi naso zuwa na dauke ki, muje kiyi mana ku
sati daya ne Allah be yi ba sai yanzu. Kiyi hakuri Khadija ki bar kuka Allah ya
ji kan iyayen ki da rahama.” A hankali na ce.
“Amin.”
Daga nan suka bani kayan da aka dinko min daga can Lagos
wanda zan yi fitar biki dasu, kawu daddy ya sanar min cewa an fasa kawo min lefe
sai ranar daurin aure. Naji dadi sosai saboda har lokacin banji cewar zan auri
wani ba Mas'oud ba, abin da kamar wahala duk da cewa bana daukar kiran da yake
yi min dan gujewa fadawa fushin ubangiji. Zuwan su Meenal dasu Badiyya yaran
uncle Kabiru da na uncle Hashim yasa na dan rage zaman yin kuka, dole suka sani
a gaba da hira da kuma tursasani wajan cin abinci, wai kar naje gidan miji ina
da ulcer a yi tunanin ba'a bani abinci a gidan mu.
A ranar kam alhamdulillahi na d'an yi bacci, sai dai duk na
riga su farkawa, nayi sallah na zauna ina nemarwa kai na sauki a gurin Allah
madaukakin sarki. Bani da buri yanzu irin naga wannan zakwakurin da yazo ya
rushe min duk wani farin ciki na, yasa na tsani komai na rayuwa a lokaci daya.
Su kuwa sun dade basu farka ba dan babu irin tashin da ban yi musu ba amman
basu tashi ba sai da suka tashi da kan su. Wajan karfe takwas matar uncle
Kabiru ta kira ni, naje take tambaya ta anyi min gyaran jiki kuwa? Na yi kasa
da kai waye zai yi min bayan bani da uwa a duniya? Kawu daddy dai ya yana yi
min iya abinda zai iya, Mami ita ya kamata ta yi min wannan amman ko a jikin
ta, bata ki ma a kai ni ina cikin yanayin kazanta ba babu ruwan ta ita tunda
basu Shukrah bane.
“Amman garin ya hakan ta faru?”
“Babu komai Aunty, kawai ni ce nace bana so.”
“Shine suka kaleki saboda kince bakya so? Toh maza ki tashi
ki shirya yanzu kizo ni zan miki, Allah yaso nazo da komai na yi da kenan haka
za a nannade ki a kai ki gidan mijin. Ai Khadija ko kana da kyau cewa akai ka
kara yin wanka sai kafi haka kyau, musamman ke da zaki doshi gidan girma mai
daraja kamar yanda muke fata.”
Na yi shiru zuciya ta kamar zata kone jin maganar gyaran
jikin nan, sam bana so dan nasan zan gaya yin kyau kuma hakan zai sanyayawa
mijin rai abinda ni kuma bana so wallahi. Na tashi kamar zan fadi sabo da sauri
na bar gurin, ina ta kufce-kufce ta yadda na gujewa gyaran jikin amman sai da
tasa aka nemo ni muka shiga dakin da ba za a dame mu ba ta yi min. Mami kam ko
a jikin ta bama taso taji ance za a min wani abun na kulawa wanda ita ya dace
tayi min amman ta shafawa idanunta kwallin rashin mutunci saboda hassada da
bakin kyashi.
Subahanallahi ni kai na sai da naji canji a jiki na lokacin
da aka gama yi min dilka da halawa na musamman, da yake yar asalin yerwa ce tasan
ta kan kamshi mai zama a jikin ɗan adam. Naji wani dadi fiye da yadda nake
tsammani, sai dai bana jin zan iya bari wanda ba Mas'oud ba ya kwashe wannan
ni'imar.
Koda aka gama cewa tayi na tafi daki karna sake na fito
waje, komai nake bukata nasa a kawo min nace mata to.
Abin da ya bani mamaki duk sunyi anko wai na bikin ne,
lallai sun shiryawa auran nan mu duk bamu sani ba. Ganin kowa ya yi ne yasa Ya
Waleedah da Ya Shukrah suka je kasuwa suma suka siyo irin material d'in sannan
suka kai aka dinka musu saboda kar a yi musu surutu. Sai da naga abin da gaske
ne sannan na tashi na dauki wayata na shiga toilet tare da kunna famfo yadda ko
nayi wayar babu wanda zai iya jiyo ni. Bugu daya tamkar daman ni yake jira
kawai naji ya daga murya shi a can kasa kasa.
“Yanzu ba zaka tsamo ni daga fadawa wannan auran ba daddyn
Waleed? Kar kai min haka dan Allah. Da nace ba zan kuma kula ka ba sai randa ka
samo mana mafita, amman na kasa gashi na kirawo ka da kai na.”
A hankali naji yana magana dan sai na kasa kunne sosai nake
iya jiyo abinda yake fada.
“Ban san me zan iya ce miki ba Oum waleedah, yanzu haka ina
kwance a asibiti tun shekaran jiya. Bana jin zan iya kuma numfashi daga lokacin
da aka ce kin zama mallakin wani ba ni ba.”
“Ya Subahanallahi na shiga uku, Mas'oud yanzu kana asibiti?
Da gaske ba kai zan aura ba? Wallahi nasan ina cikin tashin hankali, dan Allah
karka guje min bazan iya rayuwa ba bu kai, ka tallafawa zuciya ta Mas'oud, idan
ba hakaba wallahi nima gawata za'a kai gidan koma wanene.”
Kasa cewa komai ya yi, sai muryar wata mata da naji tana min
magana cikin lallashi, da alama mahaifiyarsa ce. Cikin sanyin murya take min
magana itama kamar zata yi kukan saboda naji yadda take rawar murya.
“Ina son ku dauki kaddara Khadija, aure dama mukaddari ne,
ki godewa Allah ya baki lafiya damar raya sunnar ma'aikin mu annabi Muhammad
S.A.W. Wannan itace jarabawar ku, ya kamata ace kunyi tawakkali wajan karbar ta
yadda Allah zai ji tausayin ku a wani barin na rayuwar ku ta nan gaba. Muna
muki fatan alkairi cikin auran da zaki yi, daman Allah ya riga ya rubuta ba
zaku auri junan ku keda Mas'oud ba, ki yiwa iyayen ki biyayya mun san tabbas
bake kika guje shi ba daga Allah ne. Sai anjima Khadija Allah ya yi miki
albarka kinji, Allah ya kare rayuwarki kuma a duk inda zaki tsinci kanki.”
Tana kaiwa nan ta katse. Ni kam me zanyi ban da sulalewa
kasa na rushe da kuka, na dinga yi ina yin cilli da duk abin da na gani kusa
dani. Su Zarah suka zo suna bugun kofar saboda sun ji abin nawa ya yi yawa,
naki budewa shine suka je suka kirawo su Mami sannan na bude tare da fadawa
jikin matar kawu Hashimu.
“Ya isa Dije wannan kukan na meye kuma?”
Na samu kai na da cewa.
“Baffa na da Ummata duk basu cikin duniyar nan.”
“Lahhh haba Dije baga mu ba, ko mu baki yi farin ciki da ganin
mu ba sai mu koma inda muka fito dan farin cikin ki.”
“A a Aunty wallahi ba haka nake nufi ba, kawai tuno dasu
nayi.”
“Allah sarki, daman haka ne wata rana zaka ji ina ma kana
tare da su. Amman kiyi hakuri ki dena kuka kinga gidan aure zaki je kar kije
kiyi rama dama gata nan duk kin fada.”
Haka suka dinga lallashi na damin nasiha har sai da nayi
shiru sannan suka rabu dani. Ban kuma yin kuka ba saboda bana so a zauna ayi ta
min magana kar naje na bata musu rai su ji haushi na bayan bani da kamar su a
duniyar nan.
*RANA BATA KARYA...*
(Sai dai uwar diya taji kunya.)
Tun da ya tashi yake jin wata ni'imatacciyar iska tana ratsa
sassan jikin sa, a cikin ransa yasan hakan baya rasa nasaba da auran Khadija
yar jarida da zai yi, yarinyar da ta tafi da rabin imanin sa. Yaji a duniya
yana son kasan cewa tare da ita a cikin gidan shi, komai sabo haka ya tana da,
koda yake an tanade su ne dan yau ce ranar da zai yi tafiyar nan zuwa Cyprus.
Amman shi a nashi bangaren zasu kasan ce ne matsayin na daurin aure. Daure da
towel ya fito ya tsaya wajan dressing mirror yana karewa kanshi kallo. Matashin
sarki kenan mai ciki ta nagartacciyar haiba da cikar zati. Mijin Shaheedah
angon Khadija a yau da ikon Allah.
Lotion d'in sa ya dauka tare da bin sassan jikin sa yana
shafawa. Bayan ya gama tsab ya kuma bin jikin da oil perfume da kuma body spray
masu azababban kamshi.
Shiga ya yi wacce take bayyana cewa shi din sarkin ne ba wai
carki ba. Ya Subahanallahi tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci wannan bawan
nasa, ya kawata shi da gabobi managarta masu cikakkiyar haiba. Lallai ba
karamin kariya rawanin da yake sawa yake bashi ba, dan irin su sarki Salman ne
suke sawa yan mata suna mafarkin mallaka a matsayin mazajen aure, abokan rayuwa
na har a mutu. Kamshinsa kawai ya isa rikita zuciyar mai shaka.
Ya riga yayi
sallama da kowa tun a daren jiya, shiyyasa yana kammala shirinsa kai tsaye ya
fito falon farko na sashen nasa. Cikin hanzari Jakadiya ta zube tana mika
gaisuwarta. Kafin ta mike ta fita da hanzari ta sanar da fitowarsa.
Taku yake tamkar wani
hawainiya, ga kuruciya ga jinin mulki na kai kawo a kowacce jijiya da gabban
jikinsa. Tun kafin bayyanarsa garesu hadiman sashen nasa duk suka zube domin
mika gaisuwarsu gareshi. Tafiya yake kawai batare da amsama kowa ba. Kamar
kullum idanunsa na sake cikin gilashinsa na ka'ida.
Sai da ya wucesu
gaba daya kafin wasu suyi saurin mikewa su dafa masa baya. Sun iske fadawa suma
tsaitsaye a kofar fada suna jiran fitowar mai martaban. A take suma dai zubewar
duk sukayi suna mika gaisuwa.
Suma dai basu samun amsar ba, sai cikin fadawanne ke ansawa
da fadin,
"Sarki yaji ku, shima ya gaisheku".
Lumshe idanu sarki Salman yayi daga cikin gilashinsa yana
sauke wata ajiyar zuya a hankali, wani irin yanayine ke sauka masa a gabban
jiki da baisan na minene ba. Haka dai akai masa rakkiya har gaban jerin motocin
dake a jere zuka-zuka suna jiransa.
Ruf dogarai sukai masa da rigunansu har ya shige daya daga
cikin motocin data fi kowacce koshi da daukar hankali, sai da aka rufe kofar sannan
suka marmatsa suma suka nufi motocin da zasu shiga.
Kamar yanda ya saba sai da ya karanto addu'ar fita a gida a
cikin ransa, kafin motocin su fice daga masarautar zuwa airport.
*_GIDAN BIKI KHADIJAA(DIJE)_*
———-
_Afuwan! Kunji shiru ko? Wallahi kwana biyu inata fama da
chronic ulcer. Har takai na kwanta a asibiti na yan wasu kwanaki shysa kukaji
shiru, Ina fatan na same ku lpy? Nagode k’warai da addu’oin ku. KIBIYAR ajali
zai cigaba da samuwa Insha Allah da zarar naji karfin jiki na sosai.. Na gaishe
ku, Gaisuwa mai kima.._

No comments