KIBIYAR AJALI 15
*15*
Gabaki d'aya sai hankalin mutane ya dawo kan Dije dake yashe a kasa. Shi kuwa sarki Salman tuni motarshi ta bar gurin taron tamkar ba sune suka jaza wannan ta'asar ba. Basu tsaya sunji me yake faruwa ba bare su san halin da yarinyar mutane take ciki. Kafin kace menene tuni aka dauke ta aka sa a
mota sai asibiti domin bata san inda kanta yake ba. Kasan cewar akwai manyan jami'ai hakan ya sanya suna zuwa asibiti babu wani bata lokaci aka shiga bata taimakon gaggawa.Mas'oud dake kan hanyar shi ta zuwa gidan radio saboda yaje
gida ya maida mahaifinsa kenan, kawai yaji labarin cewar Dije na can asibiti
bata san inda kanta yake ba. Ya juyo da motar ya nufi asibitin cikin tashin
hankali da tunanin abinda ya sa har hakan ya afku a kanta. Koda yaje kasa shiga
cikin asibitin ya yi, yan sanda sun hana kowa shiga. Ya ciro id card d'in sa ya
nuna musu amman duk da haka suka hana shi shiga, dama duk sauran yan jaridar da
suka biyo su suna tsaye a bakin gate an hanasu shiga, saboda so ake a boye
maganar cewa bafaden sarki ne ya yi sanadiyyar hakan. Aka fara cewa ai cikowar
mutanan gurin ne yasa numfashin ta ya dauke ta zo faduwa shine ta buge.
Tuni labari yaje wajan Alhaji Isma'il yana kan hanyar shi ta
zuwa filin sauka da tashi na malam Aminu Kano zai je birnin Lagos. 'Innalillahi
wa'ina ilaihir rajiun' ita kawai yake furtawa tare da juyo da motarsa ya nufi
asibitin cike da tashin hankali. Yana hanya ya kira Mami ya sanar da ita cewa
tayi maza-maza taje asibitin shima gashi nan zai je. Cikin mamaki duk kuwa da
cewa tana cike da tsantsar mamakin jin cewar Dije na kwance a asibiti tace
dashi.
“Toh bari na shirya naje, amman kai ya zaka ce ka fasa yin
tafiyar bayan ka riga kayi booking d'in tafiyar.?”
“Hajiya wannan ba wata matsala ba ce, jin lafiya marainiyar
Allah shine kawai burina. Karki manta Dije amanace a gare ni, kuma ya ce a waje
na kamar yadda su Shukrah suke.”
Yana gama maganar ya katse kiran yana jin mamakin matarsa da
sam ba ta son ganin yana kyautatawa yarinyar nan. Ta kasa fahimtar cewa wata
rana itama zata rabu da nata ya'yan kuma ba ta san waye zai kular mata da su
ba. Mata duk lissafin su guda d'aya ne wato za'a riga su mutuwa, duk kuwa da
cewa sun sha ganin Allah yana dauke wanda yaso a lokacin kuma yaga dama. Ita
kuwa bayan taji ya katse wayar sai ta rike habarta, abin da mijin ta yake yi
sam bata jin dadin shi. Haka ta mike taje ta shirya tasa driver ya kai ta bayan
ta tambayi wane asibiti ne, aka sanar da ita.
Alhaji Isma'il na zuwa ya sanar da yan sandan dake tsare da
gare cewar shine mahaifin Dije, suka barshi ya shiga inda suka bar yan jarida
guda uku suka bi bayan shi ciki kuwa harda Mas'oud. Mami ma tana zuwa aka barta
ta shiga ta tarar da Alhaji Isma'il ya fito daga wajan likita yana gyaran
babbar riga. Ta karasa suka hadu a center, kallon da ya yi mata shine kawai ya
tabbar mata da cewar tayi masa laifi wanda ba zai rasa nasaba da nuna cewa
aikin shi yafi Dije da ta nuna masa.
“Ashe zaki zo?”
Ya tambaye ta yana mai lasar lebensa da ya fara bushewa
saboda kaduwar da ya shiga. Kanta yana kasa tana murza zoben zinarin ta tace.
“Me zai hana Alhaji.?”
“Naga kamar baki damu ba ne shi yasa, har na fara tunanin
dakko wacce zata kular min da ita.”
Kamar tace ai yanzu ma ba ita zata zauna ba, sai kuma ta
hadiye kasan cewar yaki sakar mata fuska ta kasa ganin walwalar shi kamar yadda
ya sabar mata.
“A a zan zauna mana Alhaji, yanzu me yaje faruwa da ita?”
Yaja numfashi yace.
“Yanzu likitan ya kira ni yace ta farfado, gefen goshinta ya
fashe. Dole sai ta d'an kwana ko biyu ne a asibitin dan bata kulawar likita.”
“Daman ban da fitina ina Dije ina aikin jarida tsakani da
Allah fa. Duk irin karatukan duniyar nan ta rasa wanne za ta yi sai shi saboda
kawai taso ta dinga shiga cikin ridan-ridan maza. Gashi nan yanzu taje an....”
“Ya isa haka Hajiya naji. Duk da haka ma dai zan kawo wacce
zata kula da Dije, ke sai ki koma gida saboda yara.”
Ta fi nono fari daman ba so take ta zauna d'in ba kawai
fushin sa ne bata so shi yasa ta yadda cewa zata zauna. Yanzu kuwa da yace ta
tafi idan ta gama abin da zata yi bata ja ba saboda kar taje yace ya fasa dole
ita zata zauna. Ya nufi room din da aka kwanta da Dije wacce ke ta faman bacci
tamkar babu abinda ya same ta. Sunkuye suka tarar da Mas'oud a gefen ta yana
sharar hawaye, Alhaji Isma'il ya tambayi waye shi suka tabbatar masa da cewa
abokin aikin ta ne, gidan radio d'in su d'aya.
“Allah sarki, hakuri zaka yi muma duk shi zamu yi. Dubi
goshinta duk da cewar an rufe kasan cewar ciwon ba kadan bane ba. Allah ya baki
lafiya Dije, yasa kaffara ne.”
Sun jima sosai a dakin kafin su fito dan gabar da sallah.
Addu'a kam Dije tasha a gurin Alhaji Isma'il da Mas'oud wanda ya kasa bayyana
mishi alakarshi da ita. Mami ta zauna akan kujera suna waya da Hameedah tana
sanar mata da abin da ya faru wanda taji a bakin wani d'an jarida da abin ya
faru a gaban su.
“Kinji yarinya Mami, ko tayi zaton har yanzu a kauye take
ne?”
“Kema dai kya fada.” Cewar Mami.
“Sarki fa! Taya Dije zata ce zata yiwa sarki interview banda
dai ta latsawa kanta tunani. Ai gashi nan ta jawowa kanta an ji mata ciwo a
banza. Kuma ance masarautar bata yi wani abu ba akan lamarin ko?”
“Uhmmm! Kin san dai ba sarauta bace ta kauye, kuma yanzu ma
rufe maganar aje son yi saboda kar a batawa masarautar suna.”
Haka Mami ta zauna a gurin Dije babu wata alfarma da take yi
mata saboda tsabar wulakanci, Allah ya taimaka ma bacci take ta yi, da watakila
sai tayi hawaye da idanunta. Suna idar da sallah Alhaji Isma'il ya lallaba
Mas'oud ya tafi kar ya damu zata ji sauki harma ta koma aiki da ikon Allah. Ya
tafi ba dan yaso ba sai dan kar Alhajin yaga kamar bashi da kunya ko sabanin
haka.
Gabaki d'aya Alhaji Isma'il ya kasa samun sukuni ko fita ya
yi yanzu zaka ga ya dawo har dare lokacin da Allah yasa Dije ta farka. Da
Mas'oud ta fara yin karo da idanuwanta, kasan cewar ya sake dawowa asibiti da
aka yi salla magariba, ya kasa zama sam shi yasa ya dawo. Dishi-dishi haka ta
dinga ganinshi, ta gane shi tsab sai dai bata iya ganinshi tar-tar kamar yadda
ta saba kallon abu. Ya mike tsaye tare da karasawa gurin ta yana cewa
“Alhamdulillahi ta farka Allah mun gode maka.”
Alhaji Isma'il ya shigo da sauri cike da tsantsar farin ciki
juyowa da ya yi cewar Dije ta farka. Kallon mutane kawai take ba baki taki koda
motsa shi bare a saka ran zata yi magana. Nurse ta shigo wacce ita ce ya bawa
kwangilar kular masa da Dije. Sannu a hankali ya taje ta gyara mata inda ya
kamata cikin haka ne ma suka ji ta furta.
“Kawu daddy.”
Tamkar ta tsira masa wani abun, haka yaji ya nufe ta ya riko
hannunta, hawaye suka biyo ta cikin kyawawan idanuwanta, yasa hannu d'aya da
yake kusa da fuskar ya share mata yana cewa.
“Bar kukan nan Dije, dena kuka zaki warke da ikon Allah.”
Still bakin ba wai budewa ya yi da yawa ba wajan son yin
magana, ta kuma cewa.
“Kawu daddy sarki ne ya harbe ni ko? Wallahi ba bu abin da
nayi masa kawai daga tam......”
“Yi shiru Dije, tsautsayi ne kawai da kuma kaddara suka
fad'a kanki. Allah ya riga ya kaddara cewa hakan zata faru dake tun farko. Kiyi
hakuri zan tsaya tsayin daka, da ikon ubangiji zaki dawo kamar baki yi ba kinji
yarinya ta?”
Lumshe ido kawai tayi saboda yadda take jin kanta ya yi mata
wani irin kato tamkar an dora mata duniya haka take jinsa, saboda raunin da
yake a goshin ta shine ya yi sanadiyyar hakan. Ta sunkuyar da kanta kasa ba
tare da ta kuma cewa komai ba sai zuciyar ta da ta addabeta akan ganin rashin
imani da rashin mutunci a gurin bafaden da ya ce mata yar talakawa. Bata taba
zato ku tsammanin cewa haka suke ba, ashe ba su da kirki kansu kawai suka sani.
Amman ban da haka ba ta ga dalilin da zai sanya su dinga yiwa mutane abin da
suke yi ba. Mas'oud ya dinga kallanta yana son su sake had'a ido ko zai ji
sassauci akan zugi da rada din da yake zuciyar shi, yana son ta nuna masa wata
alama da zata tabbatar mishi da cewa a kowane yanayi take ciki zata iya gane
shi da kuma matsayin da yake a gurin ta.
Ganin tsawon lokaci taki dagowa ya sanya shi juyawa zai fita
daga dakin, kamar an ce ya kuma kallon ta sai yaga ta dago ta kalleshi tana
rausayar da kai alamar damuwa. Ya koma tare da cewa.
“Sannu kinji?”
Ta kifta idanuwa alamun ta amsa gashi yaga taki kawar da ido
daga kansa yace.
“A kawo tea ko?”
Tayi shiru ba ta ce komai ba dan magana da kyar take iyawa.
Nurse d'in tace ya bari a had'a mata suma zasu so ganin ta d'an ci wani abun ko
ya ya ne. Alhaji Isma'il da kanshi ya dinga bata a hankali kasan cewar da kyar
take iya daga lebeanta har a samu tea ɗin. Kadan tashi ba ne yawa ba sannan aka
kuma kwantar da ita.
Haka taci gaba da kwanciya a asibiti tana samun kulawar
likitoci. Yan dubiya kuwa ba'a magana, ta ko'ina zuwa ake ana duba ta, har ta
fara samun lafiya fuskarta tasabe kumburin ya baje sai gurin ciwon kawai.
Mas'oud kam kullum yana asibitin tun safe har dare, hakan ya kuma tabbatarwa da
Dije cewar Mas'oud shine farin ciki da walwalarta a rayuwa. Soyayyarsa ta kuma
ninkewa a duk wasu sassan jikinta masu motsi da kai sakonnin gamsuwa ga abin da
aka hakikance akan shi. Su Hameedah da Shukrah ma kullum sai sunje, a wannan
zuwan ne kuma Shukrah ta fara nanikewa Mas'oud, ko be kulata ba sai ta kula shi
saboda Mas'oud ba baya ba wajan tsarin halitta.
Duk da cewa Dije ba ta da lafiya hakan be hanata jin kishi
ba, yadda Shukrah take nanikewa abin alfaharinta abin yana mata ciwo dan yafi
raunin goshinta zafi da radadi. Yau kwanaki biyar kenan wajan karfe hudu suna
zazzune ana ta hira, duk da cewa shi baya kula su amman wata maganar idan an
sako shi yana magana, yanzu ma hakan ce ta faru, Shukrah tace.
“Abokin aiki gaskiya kana da kirki.” Ba tare da ya kalleta
ba yace.
“Da nayi mene?” Shukrah ta saki murmushi tare da cewa.
“Gani muka yi tunda wannan abin ya faru da Dije kullum kana
nan har ka fimu zama a gurin ta.”
Mas'oud ya juya ya kalli Dije wacce itama shi take kallo,
hakan kuma ya tayarwa da Shukrah hankali tayi saurin katse su ta hanyar cewa.
“Kaga wasu jakunkuna da nayi order jiya.”
Sai ya waiga ta miko masa wayarta yana kallon jakunkuna, ba
karya sunyi kyau, kuma zasu yiwa Oum Waleedah kyau.
“Sunyi kyau sosai kamar na siyawa madam, tana warkewa sai ta
rataya a barta ko.?” Ya fada yana kallanta da murmushi.
Turo baki tayi tare da mai da idanuwa ta rufe ba tare da ta
ce komai ba, abin da yake sake jan ra'ayinsa akan ta kenan wato yanga.
“Kana nufin Dije zaka siyawa?” Shukrah ta tambayesa cikin
mamaki.
“Eh mana na murnar ta tashi lafiya ba.”
“Cab, ai duk an riga an siye su. Jira kawai masu su suke su
dauki abubuwan su, sai dai next time.”
Shi ma daman ba wai da gaske yake zai sai mata ba, koda zai
siya mata abu baya jin zai sai mata a gurin wanda ta sani bare kuma yar uwarta.
Duk iya surutun da Shukrah take yi masa besa shi ya fuskance ta ba, sai
rubuce-rubuce da yake ta faman yi tamkar besan abin da take cewa ba. Haka suka
yini har Mas'oud d'in ya fito zai tafi tayi saurin biyo bayan shi. Dije na
kallon ta fita gabanta ya dinga bugawa, gani take tamkar wani makircin zata ta
yi masa, gaba daya bata yadda da Shukrah ba sam. Cikin ranta ta dinga addu'a
dan tasan babu mai tsare mata Mas'oud sai Allah, shine ya had'a zukatan su a
lokacin da basu sani ba, haka suna fatan ganin Waleed da Waleeda a tsakanin su.
°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°°
*MASARAUTAR BASANNABAS*
Tun a ranar da wannan tsautsayin ya affku ya ke cikin
jimami, ko da suka shiga mota yaso ya daure ya tsaya dan yaga abinda zai faru
da yarinyar da bafadansa ya rafkawa sanda. Amman ya kasa saboda shi baya san
hayaniya, wannan dalilin ne yasa ko kallon gurin be sake yi ba bare asaka ran
zai yi wani abu akai. Har suka je gida bai dena ganin jarumta irin ta wannan
zakwakurar yar jaridar ba, da take son taji wani abu daga gare shi. Sashensa na
musamman ya nufa kowa ya tsaya daga bakin kofa dan wannan ka'ida ne da indai ya
shiga cikin wannan dakin to babu wanda yake shiga sai matarsa ko mahaifiyarsa.
Cikin isa da kasaita ta nufo sashen nashi, Bayan jakadiya ta
mata iso. dan a kan kunnanta motocinsa suka shigo masarautar, bayin ta suna
biye da ita sun sha kaya iri d'aya. Tana zuwa wajan kofar bayin nata suma suka
tsaya yayin da ita kuma ta karasa ciki kamar yadda ta taho cikin tinkaho mai
nuni da cewar ita d'in matar sarki ce. A zaune ta tarar dashi kansa a kasa ko
glasses d'in dake manne a fuskar shi be cire ba. Daman idan da sabo ta saba da
duk wasu dabi'unsa, musamman na shariya da kin kallon mutane tamkar wani
makaho. Banda wani fitinannan kamshe babu abinda take yi, ta zauna can nesa da
shi idanunta a kanshi tace masa.
“Sannu da dawowa, shin me yake faruwa ne naji ko'ina ya
dauki zance nama kasa gane abinda yake faruwa. Shin me ya faru da kai?”
Ya yi shiru tamkar tana magana da gunki da aka sassaka da
dutse. Taja tsaki a can kasan ranta dan tasan ko mahaifiyarshi ce a nan gurin
take tambayarsa ba amsa mata zai yi ba bare ita da taga wajan baccin shi.
“Anyway! Nasan daman ba magana zaka yi. Amman ko da kane ina
son ka yi min alama yadda zan fita daga cikin shakkun da nake ciki. Shin kun
bige wani ko wata ne a wannan fitar da kuka yi?”
Ashe yaji duk abinda take ta fada, sai gashi ya daga mata
kai ba tare da bata lokaci ba. Ta jujjuya idanuwa tare da tabe baki.
“Ance ai ta mutu ma, Allah ya taimaka ba kai zaka sha azumi
sittin ba driver ne da ya yi sanadiyyar mutuwar ta. Sai dai kuma kai ne zaka ba
da diyya, tunda kasan dai kai za'a sanyawa ido kaji ko?”
Kamar wata uwarsa haka ya kuma daga mata kai alamar 'eh'
yaji. Tayi shiru dan tasan ta gama magana dashi ba kuma daga kan zai yi ba.
Kusa dashi ta d'an matsa tasa hannu zata zare masa dark shade d'in da ya yi
mata shamaki da ganin fuskarshi, ya yi saurin sanya hannu ya rike nata da take
shirin cirowa alamar ba ya so. Sai ta kai bakin ta kan hannun nasa tare da
sumbatar shi tana cewa.
“Yau ma ba zanga fuskar ka ba ko? Shikenan.”
Mikewa tayi tabar parlorn dan dama zuwa tayi taji tabbas
daga bakin shi kuma taji. Abin da kawai za ta yi shine tasan yadda kudin diyyar
da za'a kai sun biyo ta hannunta. Shi kuma abin ne ya yi matukar bashi mamaki
jin cewar yar jaridar ta mutu. Ya dinga yin hasbunallahu a cikin zuciyar shi, a
ranshi yana jin ashe daman mutuwa za ta yi shi yasa Allah ya ba shi iko da
damar daga ido ya kalleta? Rabon da ya yi irin kallon nan ya manta, dan ko
mahaifiyar sa ba zai iya tuna rabon da ya kalli kwayar idanunta bare ya gane a
wane hali take ciki. Abinda ya sani kawai shine muryar ta da kuma yadda take
tafiya. Ranar da kyar ya rintsa saboda abin da yaji na cewar badanshi ya kashe
wata yar jarida daga yin tambaya. Duk kafafan watsa labarin da ya kunna da
daddare labarin ake yi, sai dai su sunyi sabanin abinda yake jiyo wa a bakunan
mutane wato.
Yarinyar tana karkashin kulawar likitoci, mutane kuma suna
cewa ta mutu rufe maganar ake yi dan kar ace mutanan sarki ne. Sai da safe
bayan ya fito fada su waziri suke sanar dashi cewar yarinyar ta farfado kar a
damu nan ba da jimawa ba zata koma bakin aikin ta. Be ce komai ba sai da yaji
duk wannan firgicin da yake ji duk ya ware baya ji yanzu.
••••
A ranar da Dije ta cika kwanaki biyar a asibiti ne yasa sarki
Salman ya kirawo wani amintaccen bafadanshi yace yaje ya binciko asibitin da
aka kwantar da wacce aka buga, baya son kowa ya san cewar zai yi wannan
binciken saboda idan suka ji hanawa zasu yi, sunfi son su ji ana zagin shi a
duniya ana cewa bashi da mutunci. Haka aka yi yaje da daddare har asibitin,
wanda ya gano shi ne dalilin binciken da yayi na gidan rediyon da take aiki,
yaje can suka sanar dashi, shi yasa besha wahala ba wajan ganowa. Lokacin da
yaje ya tarar Mas'oud ya fito Shukrah na biye dashi, bafade ya tambayi nurses
d'in dake reciption dakin da aka kwantar da ita.
Daga nurse din da take kula da ita sai Hameedah dake zaune
tana danna waya. Dije kwance idanunta akan kofar tana jiran taga shigowar
Shukrah sai kawai taga kayan fadawa irin na jikin wanda ya yi sanadiyyar
kwanciyar ta a asibitin yanzu haka. Cike da tashin hankali tayi saurin rufe
idanuwa da alama yanzu mugun tsoran shi take ji. Sallamar da ya yi ne tasa
Hameedah dagowa nurse din kuma amsa masa tana mai tasowa dan jin abinda yake tafe
dashi.
“Wani abun ya faru ranka ya dade?” Nurse d'in ta tambaya dan
sanin karin bayani.
“Daga masarautar Basannabas ne aka umarce ni da nazo naga
halin da yarinyar take ciki.”
Cikin sauri Hameedah ta taso, tsayawa tayi tana kallon
bafaden tare da cewa.
“Okay sannu da zuwa, ni Yayar tace.”
“Masha Allah, ko zan samu ganin mahaifin ku dan na kara
bashi hakuri akan abinda ya faru, da kuma jinkirin rashin zuwan wani daga cikin
masarautar Basannabas ?”
Wayar ta dago ta shiga kiran daddyn su amman sam taki shiga
not reachable. Ta sanar masa ta kasa samun wayar shi amman idan yazo zata gaya
masa. Ya kuma kallon Dije wace har lokacin bata bude ido ba saboda haushin su
da take ji, ya juya ya tafi. Yana tafiya babu jimawa Alhaji Isma'il ya dawo,
suka bashi labari ya jinjina kai, kuma sannan haushin su shima da yake je na
rashin nuna kulawarsu akan lamarin ya ragu. Gwamna ne kawai da shugaban yan
makarantar da suka yi saukar sune kawai suka yi wani abu akan lamarin sai kuma
yanzu da sarkin ya yo aiken dubiya, hannu na dukan cinya ba wani ihsani, a
matsayin su na wadanda sune silaaa..

No comments