Breaking News

YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 68-69


 *NUSAIBA*

     *'YAR AMANA*☘️☘️


Rubutawa Karimatu Abdulhamid

( *Mummyn Minal*)



*🌹 SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALLAHIL AZIM*🌹


⚖️

*HAMDALA WRITIN'S ASSOCIATION💪*

        _*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_

https://www.facebook.com/111403834371046

          *✨✨{{H.W.A}}✨✨*


Littafin marubiciyar


1. Auren Lagos

2. Gimbiya Na'im

3. Wani jinkiri Alkairi ne

4. Idan zuciya tagyaru

5. Ummul khairi

6.  Gimbiya Kareemat

7 Samiha 'yar mace

8 Aisha humaira

9 Nusaiba 'yar Amana


*68-69*


_____ A safiyar sunan Anti Amarya  da danginta suka fito da akwatina saiti 22 sabbabbi fil aleda, wanda jama'a suka rufu akai domin aga miye aciki.

Ladidin bariki ce da Anti Amarya suka bubude kaya kowa yagani wanda kowa saida ya kusan daskarewa agurin da mamaki,  domin saiti10 kayan lefe ne da nahaihuwa wanda Mum tasa aka hadawa NUSAIBA, kuma shawarar Anti Amarya tanema, inda aka aiko da kayan tindaga Dubai acikin kwana uku, domin ahanun wata qawar ladidin bariki da take business Dubai to Nigeria suka se kayan. Babu abunda babu na amfanin 'ya mace awanan kayan, domin maqudan kudade Mum takar'ba ahanun ABDULJABBAR da daddy itama kuma tasa nata, yaran ma kowanne yana da akwati, saiti 6, suma kayakan ba kalar wanda babu aciki wani ma, har su shekara biyar zasu sa.

Nan aka gama kallon kaya akashiga bidiri gadan-gadan, domin kuwa shanu biyu da raguna hudu aka yanka, kowanne yana da sa daya da rago daya kenan, abincima kala-kala akayi, inda aka shirya qayataciyar walima aharabar gidan Daddy, domin kuwa har malamai mata ne sukazo, inda kowa da kowa ya hallara agurin akayi karatun AlQur'ani da kuma wa'azi akan bawa yara tarbiya, sanan aka shiga raba abinci domin kuwa kowa abunda yakeso zai fada aka wo masa, nan naga Maman twins takwarar NUSAIBA anatacin nama,  ga Amman aryan ma, tacika baki da Nama sai kora holandia milk mai sanyi takeyi, mum daddy ma sai cin amala da kwamo takeyi tamkar tacinye hanunta dan dad'i, 

Hauwa Abba Kaka kuwa da eashat, da Fatima Buhari gabansu cike yake da tuwon shinkafa miyar agusi yaji namomi sai haqa suke tayi.

 Minalyn liman ma sai kora five alive takeyi, Sa'ada kuwa da Maman Aryan sai cin sharwarma da Pizza sukeyi, suna girgiza kai, can nahango mijin Maman Aryan shida ABDULJABBAR da MUS'AF agefe da kuma dr Musa, wanda suke can gefe kusa da get din gidan ancika musu gabansu da kayan ciye-ciye da tand'e -tand'e.

Maman ilham kuwa da Ummin Ahmed sai cin jalof rice da nama sukeyi suna korawa da whine mai sanyi, can nahango Mumyn Sultan da Mi amor, suna cin sakwara da nama, suna korawa da yagot mai sanyi kai dukka NUSAIBA 'YAR AMANA PANS sunje taron sunanan domin nuna farin cikinsu, kai harma da wasu 'yan group duk sunjeje inda kowanne din su yabawa NUSY 'YAR AMANA gift, niko ina tsaye agefe da alqalamina ina record din komai domin kuwa naga bawanda ma yake ta Mummyn Minal, burin kowa kawai yaga NUSAIBA da ABDULJABBAR.


Haka akayi taro ya watse lafiya, kowa yakoma gida lafiya, washe gari kuwa Anti Karima da taga kayan da Mum tasa akayiwa NUSAIBA DA yaranta taitayiwa Mum fada, inda Mum tasa kuka tana neman gafarar Anti Karima akan musgunawa NUSAIBA da tayi abaya, Anti Karima kuwa cewa tayi, ai bakomai komai yawuce kuma ai NUSAIBA diyarki ce, aranar Anti Karima takoma danqareren gidan ta, wanda suka gada ita da NUSAIBA, da sauran kadarori da kuma uban dukiya, itama NUSAIBA dangin Babanta suka tafi da ita, sukaci gaba da bata kulawa ita da yaranta, sosai NUSAIBA takeson yaran ta, shima ABDULJABBAR yana zuwa dubasu amma ko yaje bayayiwa NUSAIBA magana sai de yagama wasa da yaransa yadawo, inda hakan yakewa NUSAIBA ciwo domin kusan kullum sai tayi kuka itakam ayanzu tagane kuskurenta tana son mijinta abunta, amma gashi ya canjamata.

Baffa ma yanzu yabar aikin gadi ansamo wani, kyautar gida guda Anti Karima tabashi, ya zauna yana ibadarsa abunsa ga kuma maza guda biyu masu kula dashi ansamasa, nanda nan baffa yaware, jikinsa yayi kyau, inda ladidin bariki yayar Anti Amarya taga baffa takyasa, tasamu daddy da zancen tace itakam in zai aureta tana so domin kuwa taringa samun ladan aure, ai kuwa koda daddy yajewa baffa da zancen baffa bai musa ba, nan kwana biyu tsakani aka daura aure tatare, agidan baffa zumunci kuwa yasake qulluwa.


NUSAIBA kuwa sosai sukayi kyau ita da yaranta domin kuwa yanzu har sunyi wata biyu da haihuwa, inda dangin ubanta suka tsaya suka gyarata tsaf, amma duk da haka sai da Anti Amarya takuma daura nata, tini aka fara shirin komawarta gidan ABDULJABBAR inda dangin mahaifinta suka sanja mata komai na kayan daki, ranar da tacika wata biyu da sati biyu kuwa suka medata gidan Mum, daga nan Anti Amarya da ladidin bariki suka maidata gidanta, inda aka hadata da me aiki  guda daya. Sanan kuma sukace za'a samarmata dadtijuwa domin tayata raino

Domin kuwa yanzu zaman lafiya sosai akeyi tsakanin Mum da Anti Amarya, dan komai Mum zatayi sai tanemi shawarar Anti Amarya, inda shima daddy sosai hankalinsa ya kwanta.

Anti Karima kuwa dukiyar NUSAIBA ta dauka tabawa ABDULJABBAR akan yajuya mata ko ya ajiye, amma ABDULJABBAR fir yaqi kar'ba, kuma da Sanin NUSAIBA din amma bayanda Anti Karima batayi ba akan yariqe tinda shine mijinta amma fir yaqi, dan haka dole tahaqura tariqe taci gaba da juyawa.


NUSAIBA kuwa yau satinta biyu da dawowa gidan ABDULJABBAR, inda tacika wata uku cif da haihuwa, amma har ranar bai mata magana ba, dan haka NUSAIBA tasa abun aranta har tafara ramewa, ga wani mugun son ABDULJABBAR da yayi mata kamu, ahaka har tayi wata guda da dawowa amma baya kulata bayacin abincinta, sai de kawai yayi wasa da yaransa, NUSAIBA kuwa tini takasa gaqura tana kuka taqira IKIRAM tasanar da ita komai, inda Ikiram taita mata fada tana cewa "ai laifin kine NUSAIBA domin kuwa kin wulaqantashi da yawa sbd haka dole ne ki koyi dabaru na mata sanan ki yaqeshi da kwalliya da girki da kalamai masu dadi, wlh dolensa ya saqqo ko baya sonki balle ma yana sonki kawai jan ajine irin na yaya na da kuma ke kika 'bata masa rai, kiduba de Anti FINAH duk irin sonda takemar dole sai da ta haqura dashi, sbd haka kibishi ahankali ki lala'bashi domin Yaya ABDULJABBAR akwai zuciya"

Cikin kuka NUSAIBA tace " wlh IKIRAM INASON MIJINA bazan iya rayuwa babu shiba, ashe abaya baso nayi ba shirme ne da yarinta suke damuna, yanzune nasan asalin so, please IKIRAM inaso Yayanki yasoni kamar yanda Mus'af yake sonki tsakani da Allah"

Ikiram tace " karki damu NUSAIBA akwai wani littafi da basiriyar marubiciyar nan take rubutashi bata ma gama shiba amma sbd mutunci da mukeyi da ita taturomin, to karki damu kema zan turomiki"

Cikin dauki NUSAIBA tace " wani littafi kenan Ikiram kuma wata marubiciya ce wanan?"

Hhmm Littafin MUMMYN MINAL NE me sunan *MIJINKI MIJINA NE* wlh NUSAIBA infada miki  sosai Mummyn Minal tatsara wanan Littafin, sanan ga Abubuwan gyaran aure da take sawa aciki, baki gani ba, kwananan yanda MUS'AF yarude akaina sbd shawarar MUMMYN MINAL dana bi"

"Dan Allah IKIRAM nawane Littafin inturo miki yanzu kituromin book din domin nifa wlh nadauka wanan karance-karancen da kikeyi bashi da amfani, amma wlh yanzu nima zan fara"

"To shikenan NUSAIBA zan turomiki ki karanta, kuma ba sai kin bayaba domin ba haka tsakaninmu aini nariga nasiya mana Littafin sbd dadinsa da kuma ma'anarsa

Godiya NUSAIBA tayiwa Ikiram, sanan sukayi sallama.


Tindaga ranar NUSAIBA tashiga yaqar zuciyar ABDULJABBAR da kwalliya iri-iri da kuma girkuna, ga qamshi da tsafta, tini ABDULJABBAR ya sauqo yafara sakewa da ita har yana dan yi mata magana, Littafin da IKIRAM taturo mata kuwa tayi komai na kayan gyara dake cikin littafin,  tini NUSAIBA tafara murmurewa tana mirjewa, ranar da tacika wata hudu da haihuwa ranar ABDULJABBAR yakasa haquri yakawo kansa har dakinta, inda suka sa yaran kowa agadonsa,  ranar de ABDULJABBAR yazubar da girman kai yasaqqo, itama NUSAIBA tabashi haquri, hhmm ranar NUSAIBA taga ruwan soyayya, ita ma kuma ba kunya tazage tanuna wa mijinta so da kulawa duk wata shawarar IKIRAM DA TA MUMMYN MINAL sai da tayi amfani dasu ranar, sosai suke nunawa junansu soyayya, romance iri-iri bawanda basuyi ba ranar qarshe de har yasamu ya cimma gashi,  aranar ne ABDULJABBAR ya san NUSAIBA A 'YA mace kenan sau biyu arayuwarsa daya adakin MUM, sai kuma wanan, ihun dadi de kam ABDULJABBAR yayi shi tare da sawa NUSAIBA Albarka dan tamkar budurwa sabuwa dal aleda haka yajita, dan haka ya riritata tare da nuna mata so zalla, tamkar zasu cinye juna danso, duk da NUSAIBA dauriya kawai takeyi dan tafaranta masa domin bata sababa.


*Hhmm wallahi da wanan nakejan kunen 'yan mata da kuriqe  budurcinku kukaishi gidan mazajenku, domin wlh mutuncinki shine budurcinki karki yarda wani saurayi yamiki wayo yarabaki da budurcinki domin wlh yacuceki, kuma koshi ya aureki bazai ta'ba ganin darajarkiba gani zaiyi kamar bayan shi kinbawa wasu ma, sbd haka 'yan mata ku kiyaye kuyi wa kanku fada ku kuma ji tsoron Allah, domin Allah yaharamta zina, sbd haka budurcinki shine da rajarki ta 'ya mace har abada duk wacce kuma tayi sake sorry for her domin tarasa mutuncinta da na iyayenta kawai, Allah yasa mudace Amin*



Satin ABDULJABBAR daya baya zuwa gurin aiki kawai soyayya zalla suke 'barza shida NUSAIBA, inda ya dingaya mata sharudd'a akan abun da yakeso da kuma wanda bayaso, ya kuma cemata yana qaunar a kyautatawa mahaifiyarsa agirmamata, dan haka NUSAIBA tashiga hankalinta sosai, take girmamashi dashi da iyayensa take kuma kiyaye abunda bayaso, sosai take son mijinta, biyayya sosai takeyi masa, haka ladabi da biyayya sosai takeyiwa MUM tini NUSAIBA tasanje halayenta, takoma matar kikirki salaha, inda kowa ke yabonta.


    *bayan shekaru biyu*


NUSAIBA ce take tuqin mota yaranta Assalam da islam, suna bayan motar suna wasansu, ABDULJABBAR kuma yana gefenta azaune akan kujerar me zaman banza suna hira. Inda NUSAIBA take cewa darling inmunfito daga shopping, zamu tsaya gidan IKIRAM, domin kwana biyu banga takwarata NUSY BEBY ba"

Domin kuwa Ikiram tahaifi 'ya mace tayiwa NUSAIBA mai suna, inda suke kiran yarinyar NUSY BEBY.

ABDULJABBAR kuwa cewa yayi shikenan Sweet wife, amma ni zaki ajiyeni gurin wani abokin aikina"

Wata mata ce tamkar mahaukaciya da kwanon bara tahawo kan titin ba yanda NUSAIBA batayi ba dan takauce mata amma ina sai da takad'e matar nan, da sauri taci birki suka fito ita da ABDULJABBAR Suka dauki matar sukeyi asibiti da ita, inda likitoci suka shiga da matar domin bata taimakon gagawa.

Inda hankali tashe NUSAIBA taqira su daddy tafa damusu, kafin kace me dangi suka cika asibitin ciki kuwa harda Baffa, koda matar tafarfado nan likitoci suka fada musu, ai kuwa suka shiga dubata nan Baffa yaga ashe matar gwaggo ce, inda yafadawa su NUSAIBA ai gwaggo ce sosai NUSAIBA tayi mamakin yanda gwaggo takoma, kwanan gwaggo biyu tana jinya sanan aka salameta inda NUSAIBA takai gwaggo gidan mamanta Anti Karima, gwaggo kuwa koda tagane su suwaye dan haka sosai tayi kuka tare da neman gafararsu, inda kowa yayafe mata har baffa, nan NUSAIBA tatambeyeta akan me tashigo yin birni?

Cikin kuka gwaggo tace " tinda baffanki yafara jinya natatara komai nagudu ni da qawata ahanya 'barayi suka taremu suka qwace komai sukayi mana dukka tasanadin dukka ne nakoma gurguwa, dan haka koda muka shigo birni dole bara mukafara domin kuwa itama qawartawa taraunana, to tindaga ranar har zuwa sanda kika bugeni muka qare arayuwar wulaqanci, sosai kowa ya tausayawa gwaggo, amma kuma halin tane yajawo mata gashi yanzu tazama gurguwa, hakade taci gaba da jinya har tasamu lafiya, gashi kuma baffa yafi qarfinta yayi mata nisa dan haka gwaggo kullum cikin kukan nadama takeyi dan ma tasamu NUSAIBA 'yar albarka ce merama sharri da alakairi, haka gwaggo taci gaba da shara da wanki wanke gidan Anti Karima.


   *Bayan shekara daya*

FINAH Kuwa sosai tayi karatun addini asaudiya inda tazama babbar malama domin kuwa har a gidan tv da redio ake sa, wa'azinta, inda yanzu takoma malama Nafisa, kuma mijinta yarasu bayan sundawo Nigeria, dan haka yanzu bata da kowa dan bata haihuba, sai tarin dukiya da ilimi da take dashi,  ABDULJABBAR da NUSAIBA ma sosai suke ganin wa'azinta da takeyiwa mata a tv, kuma ABDULJABBAR yana da labarin ayanzu bata da aure ita kadai take zaune, ai kuwa yasha wurci Mummy akan zai dawo da ita, Mum da daddy har sunqi yarda amma Anti Karima ita tayi ruwa tayi tsaki yadawo da Finah.

Kuma suka zauna lafiya ita da NUSAIBA kuma  ABDULJABBAR yana adalci a tsakaninsu.


*Bayan shekaru goma*


Ayanzu NUSAIBA Yaranta biyar 'yan biyunta, da kuma Ikiram da me sunan baffa, sai mai sunan anti Amarya wato Rahama, sosai NUSAIBA takejin da Rahama da me sunan baffa wato Usman suna qiransa Abul fatahi .

Ikiram kuma yaranta uku, NUSAIBA da Aisha, sai namiji Najif,  FINAH kuwa bata haihu ba, domin ance mahaifarta talalace dan haka NUSAIBA tabata kyautar IKIRAM, mai sunan Ikiram, domin yanzu ma wani tsohon cikinne da NUSAIBA kuma ance 'yan biyu ne dukka maza.

Dan haka FINAH tayi danasin abun da tayiwa kanta arayuwarta.

ABDULJABBAR da NUSAIBA kuwa kullum cewa sukeyi Alhamdu'lillah.

Dan haka nima Mummyn Minal nace 

ALHAMDU'LILLAH

Anan nasauqe wanan Littafin 123 fad'akarwar dake ciki Allah ya had'amu aladan zunubin dake ciki kuma Allah ya gafartamin dani daku.


Sai munhadu asabon novel anunamin zallar qauna ta hanyar mallakar novel dina mai suna MIJINKI MIJINA NE.


   BISSALAM.


INA JIRAN RUWAN RUWAN SHARHINKU


INA GODIYA GA DUKKAN GROUP DIN DA SUKEYIMIN SHARHI DOMIN SUNAYENSU BAZE QIRGUBA, NAGODE.





*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*🤲👏😭

No comments