Breaking News

YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 64-65

 


*NUSAIBA*

     *'YAR AMANA*☘️☘️


Rubutawa Karimatu Abdulhamid

( *MUMMYN MINAL*)


⚖️

*HAMDALA WRITIN'S ASSOCIATION💪*

        _*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_

https://www.facebook.com/111403834371046

          *✨✨{{H.W.A}}✨✨*


*PAGE  64-65*


___ Itako NUSAIBA jujuya maganganun IKIRAM taringayi a zuciyar ta, "Eh lalle nasan ABDULJABBAR mutumin kirkine amma tayaya zanyi soyayya dashi bayan mahaifiyarsa bata sona tinda gashi ma yanzu aure takeso yayi, tabbas dolene nasan abunyi dan kuwa yanzu nayarda narasa JALALUDEEN har abada dama bason gaskiya yakeyi min ba"

Kuka sosai NUSAIBA takeyi najin haushin guduwar da JALALUDEEN yayi bayan yagama tusa mata sonshi aranta. 

Gawani kishi da takeji aranta akan ABDULJABBAR sbd labarin auren da IKIRAM tabata.


Shiko ABDULJABBAR yana ficewa agidan Mum gurin aikinsa yawuce ko a office bai iya wani aikin kirki ba sbd tunanin auren da Mum tace sai yayi, dan haka yatatara komai ya taho gida.

Yana shigowa parlour d'in yatarar da NUSAIBA kwance akan doguwar kujera tana hawaye.

Da sauri ya k'arasa gabanta ya duqa ya kamo hanunta yariqe yace " lafiya Maman twins kike hawaye me aka miki? Mekikeso please"

Itako NUSAIBA kwace hanunta tayi cikin kuka tace "ina ruwan ka ni karabu dani ba ance aure zakayi ba?"

ABDULJABBAR kuwa Murmushi yayi yace " to ina ruwan ki da aure na tinda ba sona kike yiba ai kinga nasan ina auri Safna zata riritani ta shayar dani ruwan zuma ai yanzuma wanka zanyi intafi gurin ta"

Kuka NUSAIBA taqara sawa tace "ai baka isa ba sai de kabari inka sakeni sai ka auro Safna amma muddin ka aureta inanan sai na 'balamata qafa"

Dariya ABDULJABBAR yayi yace " dagaske? Lalle kishi kummalon mata amma ai kema kinga mijin wata kika aura dan haka yanzu dole kema akawo miki"

Tashi NUSAIBA tayi tashige dakinta tarufe taci gaba da kukanta shima ABDULJABBAR nasa dakin yanufa.


     *Bayan kwana biyu*


Haryau ABDULJABBAR baije gidan su FINAH ba, kuma bai qara komawa gidan MUM ba Domin kuwa yana tsoron had'uwarsa da Mum dan yasan ba dad'i.

NUSAIBA kuwa cikin ta sai qara girma yakeyi yana bud'ata domin cikin jikinta yabi sai qara qiba da hibs takeyi abunta, ga kulawa Na musamman da ABDULJABBAR yake bata duk da har yanzu bata qara yarda dashi ba, jarrabawar su kuwa tini sungama sai de jiran saka mako, IKIRAM itama tini angonta ya angwance abunsa dan haka itama tashiga sahun manya Mus'af sai nan nan yakeyi da ita kamar yamaidata ciki danso haka yakeji dan baida kunya ko a inane nunawa IKIRAM soyayya yakeyi abun har burge NUSAIBA yakeyi domin ko amakaranta idan yaje daukarto ko yakaita haka yake nuna mata zallar so agaban kowa, ga kudi da yasakar mata take bushasha son ranta.


ABDULJABBAR kuwa ko da yagaji da 'buyan da yakeyiwa Mum sai yashirya yanufi gidan gurin daddy yaje yasanarwa daddy komai, nan daddy yasamu Mum yamata fada akan tajanye maganar auren  ABDULJABBAR da Safna, amma Mum tanuna bata yarda ba, ana cikin haka Ikiram ta kawo musu labarin Safna tasamu miji zatayi aure a Sudan, wanan dalilin yasa Mum ta janye domin tasan haramunne nema cikin nema.

Sanan shima ABDULJABBAR yasamu ya wala kullum yake zuwa gidan susha hira da Antinsa karima inda koda wasa besanar dasu NUSAIBA nada ciki ba, haka itama Ikiram ba wanda tafadawa domin gudun masifar mum Domin sunsan zata iya cewa sai anzubar da cikin, Anti Amarya ce kawai tasan Ikiram na da ciki itama kuma taja bakinta tayi shiru sai daddy kawai da tasanarwa.


Ikiram kuwa cikin nata girma domin har tashiga watan haihuwarta, kuma har yanzu bata bari sun hadu da Mum ba domin fir taqi zuwa gidan, yau da ciwon baya tatashi abu kamar naquda tin cikin dare haka takwana gashi ita daya adaki domin bata yarda ABDULJABBAR yashigo su kwana tare, dan haka gari nawaye wa taje tasameshi a dakinsa tasa masa kuka, akan bayanta ciwo yake mata, cikin rud'u ya shirya suka taho asibiti, inda dr Musa yasa Norse din da take mata awu ta bincikata ko haihuwa ce, nanfa sukayi binkicensu suka ga haihuwarma tazo amma ba hanya, domin kuwa kwata-kwata hanyarta arufe take tamkar budurwa gashi kuma har yara biyu ne acikin ta, nan fa suka sanar da dr Musa komai, ai kuwa dr Musa yasa ABDULJABBAR da NUSAIBA agaba yake musu fada, yace " Abokina baka kusantar matarka sbd miye gashi hakan zai jaza mata matsala? Domin kuwa a binkicen da mukayi mungano hanyarta bata bude ba, asalima kamar wacce ba ata'ba kusanta ba haka take, to fa gaskiya akwai babbar matsala domin kuwa rashin hanyar nan zai jawo muyi mata aiki mucire yaran"

Dogon Numfashi ABDULJABBAR yaja yakalli NUSAIBA yace " kinji ko abunda dr yace kuma duk laifin kine domin ke kike qin yarda"

Dr musa kuwa cewa yayi ai kuwa dole kutashi kutafi yanzu kaje ka ringa kusantarta kamar sau biyu ko uku arana nan da kwana biyu  muga abunda Allah zaiyi domin kuwa yin hakan babban taimako ne agareta".


Koda suka fito daga asibitin kai tsaye hanyar gidan su Mum ABDULJABBAR ya dauka kallon sa NUSAIBA tayi tace " yala'bai ya naga kasanja hanya ina zamu?"

"Zamune in sanarwa Anti Amarya abunda dr Musa yace"

Bangane ba tona min asiri zakayi?"

"A'a ai gwanda insanar dasu domin asan abunyi ko za'a samu wani magani"

Magani kamar yaya ina maganin..... sai kuma tayi shiru.

Shima ABDULJABBAR shirun yayi bai sake cewa komai ba har suka isa gidan daddy, hon yadanna megadi yabude musu qofa suka shiga cikin gidan yanayin parking yafito, sanan yabudewa NUSAIBA qofa itama tafito, hanunta yariqe gam tana tafiya tana daga qafa daqar kai tsaye shashin Mum ya nufa dasu, a bakin parlour din ABDULJABBAR yayi sallama Anti Karima ce ta amsar sallamar domin dama zaune suke ita da mum suna hira, ABDULJABBAR ne yashigo hanunsa riqe da na NUSAIBA, haka kawai Anti Karima taji wani abu ya tsikareta tatashi zunbur akan kujerar tana kallon NUSAIBA dake dauke da qaton ciki, itama NUSAIBA wani abu taji yajata ai da sauri takwace hanunta  a hanun ABDULJABBAR tanufi gurin su Mum, kawai sai tazame tafad'i akan tayis d'in, wata qara Anti Karima tasake, tayi kan NUSAIBA aguje shima ABDULJABBAR da gudu yayi kanta, itama Mum da tatashi tsaye dan ganin NUSAIBA da ciki, itama qara tasake ai a guje baba megadi da daddy suka nufo shashin domin shima daddy yayi shirin fita aiki ne, ai Baba megadi yana shigowa ya daga hannu yana nuna Anti Karima yace " dama dama kina raye wlh itace"  

"Itace waye"? Daddy ya tambaya

Amma bai jira amsa ba sukayi kan NUSAIBA inda daddy yace " kudaukota kusa amota ina zuwa bara nafadawa Rahama.

Ai ABDULJABBAR bai jira suba, yadauki NUSAIBA akafadarsa yasa ta amota ajuge yashiga ya tada, da sauri Baba megadi yabude masa qofar, yafice agidan aguje.

Kai tsaye asibitin su dr Musa yanufa

Suma su daddy da su Mum amotar daddy suka biyosu.

Tin ahanya ABDULJABBAR ya qira dr Musa awaya yasanar dashi komai, ai kuwa yana isa asibitin likitoci suka dauki NUSAIBA akayi maternity room da ita, su daddy na isowa kuwa dr Musa yace dole asa hannu amata c.s, haka ABDULJABBAR yasa hannu, cikin sa'a kuwa suka ciro yara biyu daya mace daya namiji, da murna dr Musa yafito yasanar musu nan fa sukadau murna kamar me, Mum harda kuka wai itace yau da jikoki har biyu.

Niko nace Mum kin manta ne bakyafa son uwar yaran.

ABDULJABBAR kuwa sujjada yayi agurin yana mai godewa Allah domin kuwa yabashi abunda kudi baya siyansa.

Zuwa can norses suka kawo musu yaran, da sauri Mum ta amshe namijin tana kuka tana cewa " sannu da zuwa megida na"

Anti Amarya kuwa takar'bi macen tana dariya tana cewa " lalle marhaban Amaryan daddy"

Sanan tamiqawa Anti Karima, Anti Karima tana kar'barta tace " inalillahi wa ina ilaihi raj'un"

"Menene suka tambayeta............


Hmm muje de zuwa my pants


*Ko kinsan cewa Mummyn Minal na nan tafe da qayataccen Novel dinta mai sunan* 

*MIJINKI MIJINA NE* 

*HMM kede 'yar uwa kinemi naki kisha karatu kawai domin kar abarki abaya*

Domin samun novel din kutuntu'bu wanan number 09065120158


Dan Allah inkin karanta kiyi shere please




*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAKA*

No comments