SAI A LAHIRA 25
*🎀SAI A LAHIRA🎀*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
*🅿️age 25*
*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*
*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*
_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE 1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_
_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
......... Yayi sallama gidan hajiya Azumi ta ta shimfida mishi tabarma inda ya zube Mata goro Yana sanar da ita an daure Aure Kuma anjima yake so Atare
"Kar ka damu bilya jeka anjima ka zo ka dauketa ku tafi sai dai ka fadawa shi mijin kur kusa zai sako maka ita. Yayi murmushi "Ai hajiya sati biyu na bashi ya sako min ita....
"Yauwa to gara dai don in kabar shi ya Dade to ya Sha da Kai. Da haka sukayi sallama ya tafi
Ta iske nafisatu akwance ta watso Mata goron da minti
Ta tashi zaune tana kallon Azumi
"Na meye hajiya?
"Na daurin AUREN ki ne sai ki shirya zai zo anjima ku wuce.
"Mu wuce Ina? Ni fa bangane Abinda kike nufi ba hajiya?
"Wai ba da hausa Nike Miki maganar bane? To Zan gaya Miki da ko wane irin yare kike fahimta an daura auren ki da wani can da ko Ni ban San ko waye shi ba auren kisan wutan Nan da kuke fada ke da ubanki shi Zakiyi don ki komawa bilya Ina Nan Ina jiranku ke da ubanki kuzo da komai Zan iya daku.
Tafice ta barta da binta da rakiyar idonu.
Baby ta dauki minti siyama ma ta dauka suka soma Sha suna karawa tayi shiru tana tunanin yaushe ne zata samu yancin Zama lafiya wurin Azumi? Ta kwashi goron ta kaiwa malam lamis
"Baba kana sane da wannan auren haramtacce ? Yayi shiru Yana tunanin yadda Azumi ke yin nasara akanshi . Ya dubeta
"Yaushe aka daura auren? Kuma wa ya tura su wurin shitun?
"Wallahi ban sani ba baba yanzu take bani goro Wai yau Zan tare.
"Kira min shutu da wayarki.
Ta Kira baba shitu a waya sukayi magana inda ya Gane mugun qullin Azumi ne don haka shima yaga Bari yayi musu nasu mugun qullin Wanda ya zarta nasu "kingane nafisatu idan anjima bilyan yazo tafiya dake ki bishi ku tafi idan har Allah ya zano zaman me tsawo a tsakanin ku to ki tsaya ki Gane indai mijin ya kasance me kyakkyawar halayya da dabi a to ki rike shi da kyautatawa irin wadda mace ke samo Kan miji ta yadda zai Gane kece irin macen da manzo ke nunin a aura to Ina har kikayi haka to na tabbata zai yi wahala ya iya rabuwa dake Ni Kuma hikimata anan itace don ki nunawa Azumi da wancan sakaran mijin naki iya karsu ki shige gidan mijin ki ki fitowa ta hakane zasu Gane Ashe sune sakarkari Kuma Ni in kikayi haka kin gama biyana. Ubangiji ya albarkaci auren ki yasa mutuwace rabawa don har ga Allah bana fatan ki fito daga wannan auren zai yi ta rokon Allah yasakawa mijin kaunar ki ta yadda ba zai iya rabuwa dake. Ta amsa har ranta inda itama take fatan daga wannan auren ba za a kuma Tara mutane da sunan ita za a sake daurawa aure da haka ta aje komai ta rungumi kaddara
Misalin takwas da Rabi na dare bilya ya iso gidan da nufin tafiya da ita inda tun maraice Azumi ta Bata sabon leshin da bilyan ya Aiko dashi Wanda zata saka don haka ya sameta ashirye
Inda Azumi ke Mata fadan kar ta sake wa sakaran mijin fuska tunda ma ba dadewa zatayi ba da haka tayiwa yaran wayo inda baby ta makale Mata Wai sai ta bita yayinda siyama ta shige jikin bilya Yana shafa kanta don ita Kam Yana son ta ita da baby ya fita da su ya zuba mota inda yace wa hajiya zai maidosu. Haka nafisatu tayiwa Azumi sallama tafito inda ya Kira wayar sadik yace su hadu akofar gidan da ya Kama musu haya ya Kuma zuba musu abincin da zasu ci har zuwa lokacin da zasu rabu tuni Kuma ya rubuta mishi check na kudin da zai bashi don haka ya dauko ta amota suka nufi gidan da ke kofar marusa low cost gida me kyau da tsari inda gabanta ke faduwa saboda Bata San kalar mijin da Ubangiji ya sake hadata da shi ba me yuwa ya zarce bilyan bakin hali me yuwa Kuma ta samu sanyi daga gareshi
Sai dai tana ganin kamar da wuya burin mahaifin ta yacika Amma sai taji karfin gwiwar cika mishi burin shi nayiwa sabon mijin biyayya.
Suka iso gidan inda suka iske sadik ya iso inda dare bai Bata damar ganin shi ba har suka shige ciki inda baby da siyama sukayi bacci
Suka shiga dakin inda ta lullube fuskar ta inda ya soma yi musu matashiya akan auren na sati biyu ne kacal ya Kuma Kara jaddada mishi ko kallon ta kar yayi itama ya roketa da kar ta sake ta bashi wata fuska sati biyu ne kawai zasu yi kowa ya Kama gabanshi da haka yayi musu sallama ya tafi da su siyama dake bacci.
Ya dubeta lullube da da mayafinta "to amarya Ina neman izinin tafiya don ance in kiyaye dokokin ki Ina fatan banyi laifi ba idan na tafi? Jin muryar shi yasata faduwar gaba inda taga Bari tayi amfani da damarta ta yadda zata hau hanyar cika burin mahaifin ta
"Amma ya na dakyau angon sati biyu ya dubi fuskar amaryar sati biyun shi kafin arabu.
Shima Jin tata muryar yasa mishi shock ba don yayi niya ba ba Kuma don ya bi umarnin ta ba sai don ya tabbatar da hasashen shi ya Kama mayafin fuskarta ya soma budewa tamkar me tsoron wani Abu zai faru dashi cikin karfin hali ya bude fuskarta..........

No comments