YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 46-47
*NUSAIBA*
*'YAR AMANA*☘️☘️
Rubutu KARIMATU ABDULHAMID
( *MUMMYN MINAL*)
*🌹 SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALLAHIL AZIM🌹*
*PAGE 46-47*
Cikin kuka 'YAR AMANA tace " Anti kutambayi wanda yakawo ni gidan nan shi yasan komai"
Numfasawa Anti Amarya tayi sanan tace " Shikenan to baby ki kwantar da hankalinki ki dena kuka zansamu daddyn ku muyi magana"
Ficewa Anti Amarya tayi a d'akin tana mai al'ajabin maganganun NUSAIBA 'YAR AMANA.
Itako IKIRAM zama tayi taci gaba da rarashin NUSAIBA.
ABUDULJABBAR kuwa koda yaga tunanin bazai kaishiba bathroom yashige ya sakarwa kansa ruwa sosai ruwan yake zuba atsakiyar kansa zuwa jikinsa amma duk da haka zuciyarsa quna take masa domin kuwa har yanzu 'YAR AMANA yake hangowa rungume aqirjin JALALULDEEN.
Da qar yasamu yakawar dawanan tinanin azuciyarsa sai kuma yafara tinanin wai ina Amanarsa ne da yabar wa Daddy danshi fa har yanzu baiganta ba?
Wata zuciyarsa ce tace mar " to kode yarinyar da kagani rungume aqirjin wani qato ko itace matarka?"
Da qarfi ABUDULJABBAR yace " NO!!!!!!!!!!
Ba matata bace tabbas matata tayaya matata zata zama haka ai ita tawa matar yarinya ce mai quruciya sanan kuma bakidahuma 'yar qauye"
Wata zuciyar ce tace mar " kana tinanin ahaka zataci gaba da zama tsawon shekaru hud'u batare da taqara girma ba kuma ta waye, kaduba ma na kaga qanwarka IKIRAM ai taqara girma balle ita 'yar qauyen matarka da take da ga'ba"
Shide ABUDULJABBAR qarya tinanin zuciyarsa yayi yatsane jikinsa ya fito abayin kwaliya yayi cikin qananun kaya Jean da riga t-shirt, sanan ya daura agogon diamond ahanunsa yasa takalminsa qirar Dubai yabaza turaruka masu qamshi sanan yafito yanufi d'akin Mum da sallama ya murd'a handle d'in qofar yashiga d'akin Mum.
Cikin fara'a MUM dake zaune agefen gado ta amsa masa sallamar.
Duqawa yayi ya zauna aqasa kusa da qafafun MUM bayan yagai shetane sanan yace " dama Mum wata tambaya ce dani"
"Uhum ina jinka Son"
"MUM nace ba wata yarinya ce naganta a shashin Amaryar daddy?"
Zare ido Mum tayi sanan tace " bangane tambayar da kake min ba Son?"
"Mum wata yarinya nagani a gidan nan kuma ina tinanin kamar nasanta shi yasa nake tambayarki
"ABUDULJABBAR!!!!!!!!!!!!!!
MUM tafad'a atsawace sanan tace " wlh ABUDULJABBAR kafita a idona inrufe wato idonka harya kyallomaka wata yarinya iye?
To bara kaji ni bazan yarda da wanan iskanci ba, mema yakaika shashin wa 'yanan munafukan to kayi na farko kayi naqarshe karka kuma shiga wanan 'bangaren naga yamaka"
"Kiyi haquri Mum tambayarki kawai nayi bawai wani abu bane naga kamar nasan yarinyar nan shi yasa"
"Hhmm ABUDULJABBAR kenan ni zakayiwa wayo nade fad'a maka FINAH ita kad'aice Matarka sanan yarinyar daka gani ba kowa bace face yarinyar da daddynka yakawota daga qauye shekaru4 da Suka wuce wanan jahilar yarinyar bakidahumar mai kyawu irin na 'yan ruwa" shine yanzu anwayar da ita ankoya mata iskanci bata ganin kowa da gashin ido har ana nema ahad'a wani munafurci to mudin ka qara yimin zancenta zanbarwa duniya kai"
Cikin tashin hankali ABUDULJABBAR ya tashi tsaye tini idonsa yarufe yafara ganin duhu ga kuma jiri dake d'aukarsa, laluban hanya yafarayi yana ficewa daga d'akin Mum, itako Mum sai zalzala masifa takeyi batama lura da halin da d'anata yake ciki ba.
Shiko ABUDULJABBAR tafiya yakeyi a parlour d'in yana garuwa da bango yana zancen zuci yana cewa " dama yarinyar da nagani rungume a qirjin wani itace 'YAR AMANAR matata dana kusa mutuwa akanta aqasar Italy sbd tinaninta burina bai wuce kullum nadawo Nigeria ba domin insake ganinta inkuma ga kyakyawar Surar jikinta inta 'ba laulausar fatarta mai kama da auduga amma kash sai ga wani yarigani why? Why not NUSAIBA!!!!!!!!!!!
Yafad'a da qarfi.
Jikin motar sa dake harabar gidan yadaka da qarfinsa sanan ya bud'e qofar motar yashiga ya zauna yai mata key.
Mai gadi yana ganin haka ya wangale masa qaton get d'in yafice agidan aguje kan babban titi ya hau yana ta tsula uban gudu shi kansa baisan inda zaijeba kawai de tuqin yakeyi zuciyarsa cike da qunci aransa kuwa ji yakeyi inda yasake ganin wanan qaton da yarungume masa mata tabbas sai ya kashesa
Gudu ABUDULJABBAR yakeyi sosai akan titin harya kusa fita daga garin kaduna motoci kuwa sai matsawa gefe sukeyi domin susan lalle wanan duk yanda akayi ba lafiya.
Yana cikin wanan tsula uban gudun wata jar mota tazo tasha gaban sa dolensa yaci wani wawan burki, wa'yanda suke ciki jar motar ne suka fito hanunsu d'auke da makamai, motar ABUDULJABBAR suka nufa suka bud'e suka bugamar qasan bindiga akan sa take ABUDULJABBAR yasume a gurin.
Cici'barsa sukayi suka saka atasu motar suka tafi dashi tafiya mai nisa sukayi domin har sunfita daga garin kaduna suka yanki wani daji sukayi tafiya mai nisa sanan wani qaton gida mai kyau ya baiyana qofar gidan da kanta tabud'e kanta suka danna hancin motar su cikin gidan suna shiga qofar tarufe kanta kirif.
******* ********
ABUDULJABBAR bai dad'e da fita daga d'akin Mum ba FINAH tashigo d'akin cikin kuka, ai tini hankalin Mum yatashi nan tatari FINAH tana cewa " lafiya FINAH wa yata'baki kike kuka"?
Nan FINAH takwashe komai da yafaru a shashin Anti Amarya harda qarya ma tafad'awa Mum
Cikin masifa Mum tatashi tsaye tace " (inalillahi wa ina ilaihi raj una) yanzu Yaronan ni zaiwa haka? Lalle yataro mach amma ki kwantar da hankalinki ai bansan haka abun yakai ba domin kuwa yanzunan na koreshi yazo harnan yana tambayata wai wata baquwar yarinya yagani agidan nan"
Kuka FINAH takuma rushewa dashi tace " kingani ko Mum nikam Shikenan tawa taqare domin nasan cewa zaiyi zai auri karuwar yarinyar nan dan Allah Mum kiyi wani abu banaso surabani da mijina kema kuma zasu rabaki da d'anki"
Ai tini Mum takuma harzuqa nan tashiga tsinewa Anti Amarya da daddy, FINAH kuwa sai zugata takeyi cikin kukan munafurci FINAH tace "kuma mafa MUM tunda ABUDULJABBAR yadawo baita'ba shiga d'akina ba balle wani abu ya had'amu.
Cikin masifa Mum tace " au haka abun yake lalle ya nunamin shi d'an zama nine amma tabbas zanunamar ni nafishi iya shege sbd haka ki kwantar da hankalinki MY FINAH yau d'inan Abdul ad'akinki zai kwana adaren yau d'inan kam sai kumsama min jika domin ni dakaina zankawo miki shi d'akinki"
Cikin shaga'ba FINAH tace " Mum kofa kin kawoshi ba abunda zaiyimin domin ko kallo na bayayi balle yahad'a jiki dani.
" haba FINAH karki bani kunya mana tayaya zakice haka aike zakija ra'ayinsa da irin dabarunmu namata sbd haka kije kawai kishirya dan yaukam sai ansamamin jika.
Cikin jin dad'i FINAH tarungume Mum tana mata godiya inda FINAH tatafi d'akinta taqira aminiyarta awaya mai bata magungunan mata lokacin ABUDULJABBAR yana d'an kulata, ringing biyu amaniyarta Zuly tad'auki waya nan sukayi gaisuwar yaushe gamo, inda FINAH bata 'boyewa Zuly komai ba dake tafiya gidan rayuwar auranta, nan Zuly tayi dariya tace " kizo yanzu kawai qawata ina gida kuma kwananan nakar'bo wasu surukan mallaka wanda inkikai amfani dasu hatta uwarsa sai yamanta ya manemiki nan FINAH tayi wani ihu sanan tace " ganinan zuwa Zuly kamar dama kinsan natsani biyayyar da yakeyi wa uwarsa.
Haka kuwa FINAH tashirya tanufi gidan Zuly inda Zuly tatsimata iya tsumuwa dan tin agidan FINAH tafara yoyo gashi dama tadad'e rabonta dana miji, nan Zuly tashiga bata shawarar akan tabi wasu mazan kawai akan me zai tatsaya namiji d'aya yana gwarata, FINAH cewa. Tayi " Zuly inajin bawani namiji danakeso kamar mijina shi daya kawai yayimin acikin maza"
"A'a FINAH haukar banza kawai kikeyi akan wanda basonki yakeyi ba wa yasan iya holewar da yayi aqasar waje kekuma ya ajiyeki tamkar gunki, kawai ina ganin kinemi tsohon saurayinki Prince Aiman kudedeta FINAH yaringa ragemiki dare kisanifa Prince Aiman yasoki kamar me kuma yakashemiki kudad'e amma kika hanashi kanki, qarshe kika nacewa wanda baisan darajarkiba to bara kiji Prince Aiman hargobe yanan da tabon rashinki FINAH dan haka haryanzu lokaci bai quremiki ba ni aganina gwanda ki mori quruciyarki.
Haka de Zuly tagama ziziga FINAH sanan FINAH tabaro gidan cikin buqatar d'a namiji.
'YAR AMANA kuwa tinda abun nan yafaru bata qara zuwa lambun gidan ba gurin da suke soyayyarsu da JALALULDEEN.
Dan haka hankalin JALALULDEEN sosai yatashi yau kam kasa jurewa yayi dan haka dakansa yashiga har d'akin 'YAR AMANA lokacin Anti Amarya tana tare da daddy, JALALULDEEN yana shiga d'akin yasa meta tana bacci atsakiyar gadonta ga shi kayan bacci ne ajikinta gajaren wando da riga singlet masu tsantsi tini sukabi jikinta suka lafe, kitsonkanta ma ko wanne yayi d'a'daya akan katifar tini JALALULDEEN yaji hankalinsa yatashi ji yayi shikam bazai iya danne abunda yake jiba domin kuwa duk namiji mai lafiya balalle bane ya iya jurewa awanan yanayin hanunsa yakai kan fuskarta yana shafawa ahankali gani yayi qirjin ta da yake tsaye cak kamar yafasa rigar yafita yafara harbawa da sauri da sauri kawai sai yaji yana sha'awar yata'ba gurin, yana shirin d'auke hanunsa ne akan fuskarta yaji tariqe hanun gam takawo tsakanin qirjinta ta rungume aitini JALALULDEEN yakusan sumewa danjin laushi da tudun qirjin NUSAIBA tini numfashinsa ya d'auke, Itako acikin baccin take murmushi take cewa karka barni JALALULDEEN kaine rayuwata ina son ka banta'ba son wani d'a namiji ba sai kai ban ta'ba ganin wani namiji mai kyau ba sai kai "
Shiko JALALULDEEN jin haka kawai sai yaqarasa hawa kan gadon yajawo 'YAR AMANA yarungume ta tsam aqirjinsa.
Anti Amarya kuwa bayan tazubawa daddy copy yana kur'ba ahankali ahankali suna hira jefi- jefi sai Anti Amarya tace " wai daddyn yara, nikam wani aurene akan NUSAIBA kasanfa sosai suke soyayya da qanina JALALULDEEN shine ranan naji tana kuka tana fad'awa IKIRAM wai in anrabata da JALALULDEEN mutuwa zatayi domin wai tatuno da aure akanta"
"What!!!!!!!!!!! Daddy yace yajefar da glass cop d'in dake hanunsa.
Cikin tsawa yacewa Anti Amarya "you are very very stupid"
To bara kiji NUSAIBA matar aurece ba kuma matar kowa bace face d'ana ABUDULJABBAR"
Nan jikin Anti Amarya yahau tsima, daddy kuwa take agurin yafad'a mata yanda Auren. 'YAR AMANA da ABUDULJABBAR yakasance.
Ai nan Anti Amarya tafara salati da salallami
Da saurinta tafita ashashin daddy tayi shashinta kai tsaye d'akin 'YAR AMANA tashige kawai sai tayi turus dan ganin qaninta kwance yarungume NUSAIBA ajikinsa yana wasa da gashinta, ai da gudu Anti Amarya taqarasa tazubamar wani uban mari ba shiri yamike damqar sa Anti Amarya tayi cikin masifa tace " dan ubanka me yakawoka d'akinan har karungume matar mutane au abunda da dama kukeyi kenan bansani ba"
"A'a Anti bata da laifi bacci nazo nasameta takeyi'
Wani marin Anti Amarya taqaramar tace" to wlh katatara kayanka kabar gidanan kai garinan ma kabarshi dukka kanufi Lagos kaje can kanemi abunyi domin wlh baza kakashemin aure ba dan kuwa ina son mijina, ita NUSAIBA dakake soyayya da ita to matar aurece domin kuwa d'an Alhaji wato ABUDULJABBAR babban yaron gidan nan shine mijinta tin tana qarama aka musu aure"
Wani ihu mai qarfi JALALULDEEN yasaka wanda yasa Nusaiba tatashi abaccin da takeyi ganin da na miji ad'akin yasata taja blanket tarufe jikinta, cikin tashin hankali JALALULDEEN yace " qaryane Anti ba wanda ya isa yarabani da matata Nusaiba qaryane inasonta ba wani qato dazanbarwa ita" jin haka yasa 'YAR AMANA tatashi aguje tad'auki zani ta d'aura sanan cikin kuka tace " Anti mekefaruwa ne"?
"Nusaiba ashe ke matar ABUDULJABBAR ce mijin FINAH?
To yazama dole kurabu da JALALULDEEN.
"A'a Anti ni bazan rabu da JALALULDEEN ba ina sonsa shine farin cikina tayaya kikeso inyi kishi da FINAH haba Anti So kikeyi Mum takashe ni, ni bansan wani ABUDULJABBAR kukuka sanshi nide JALALULDEEN nasani.
IKIRAM ce tashigo d'akin cikin 'bacin rai tace " naji komai Nusaiba kuma na tambayi daddy yasanar dani komai sbd haka dole ki zauna da Yaya ABUDULJABBAR inde ke bamai manta alheri bace.
Kuka sosai 'YAR AMANA tasaka wiwi
Daddy ne yashigo har d'akin da kansa wani mugun kallo yayiwa JALALULDEEN sanan yace " inaso kayi haquri kabar gidanan tunkafin ABUDULJABBAR yagano kokai wanene domin kuwa bashida mutunci akan abunda yakeso, sbd haka kayi haquri ni nayi kuskure da bansanar da kowa matsayin Nusaiba amma yanzu kowa zai sani sbd haka kabar gidanan banaso kakuma dawoshi har abada.
Haka JALALULDEEN yasa qafa yafice ad'akin yana hawaye itako NUSAIBA yana ficewa tayi luuuuuu tafad'i ta sume agurin.............
Hmm muje zuwa
Dan Allah inkinkaranta kitura asauran groups please
*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*

No comments