Breaking News

FURUCI 41-42

 


🗡 *FURUCI*🗡

         💔💔

       

*(Murd'add'iyar Soyayya)* 💓❣💘


Story and written 

            By 

NPEEDY A AJI 🌸mamyn Zarah🌸



               🅿️ 41 to 42



                   Dedicated 

                          To

                    My lovely  

                     *Ummi*

                         and  

                       Lovely          

                     Daughter 

                     *ZARAH*


           My Novels

*NAYI RAYUWA DAKE* 

*SANADIN ACCIDENT*

*SAKAYAR CUTA* 

*RUFAFFIYAR ZUCIYA*

*HAYATUL MAHAYAT*

*MUGUN SARTSE*

         Loading....🖊

🗡💔FURUCI!!!!💔🗡


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






wani irin dad'i hjy Himla taji miqewa tayi tanufi Part d'inta tana shiga tadubi qawar tata tace " kinga kuwa shawarar ki tayimin matuqar amfani da mama taso hanawa amma nanuna tamkar tsananin kulawa zanje bama matar Saraki hakan yasa ta amince " dariya suka saki had'ida shewa sannan suka cigaba da kulla mugun nufinsu Allah katsaremu a part d'in Umma kuwa su Aunty kurrat ne zaune cikin babban parlour Umma tsaki Aunty kurrat taja akaro na babu adadi dubanta Aunty Faheemat tayi tace " Wai lafiya kuwa Aunty " sefaman jan tsuki kiketayi ? " Wani tsukin tasakeja sannan tace " hmmm wannan lamarin nike jinjinawa Wai Saraki ne dayima mace ciki ? Gaskiya inada tantama Ina yaga hankalin kusantar mace ? " Dubanta Aunty Sumeer tayi sosai cikin nuna mamaki tace " haba Aunty kurrat keda kanki kike dan ganta Sarakin mu da marar hankali haba Aunty kurrat wannan ay ba dede bane  ajiyar zuciya Aunty Faheemat tasauke tace " ayni wallahi kinabani mamaki nalura kina matuqar jin zafin Saraki bayan kuwa ada bahaka kikayiba " tashi Aunty kurrat tayi tsaye cikin tsawa tace " hmmm wallahi kunabani mamaki kunaganinfa yadda ayanzu Abbee bayaji dakowa se Saraki duk yadda kakeson abu idan har Saraki bayaso to Kai sede kahaqura ko kabiyo ta 'bangaran shi nikuwa Allah yasani idan har senabi ta hannun Saraki zansamu abu to wallahi nahaqura kuna ganin ko Mahaifiyar shi tafi tamu matsayi gurin Abbee dan haka yazama dole Kuma kutsani Saraki da Mahaifiyar shi '''''' kul karkusake " cewar Umma datashigo yanzu cikin bacin rai tacigaba dacewa 


" Gaskiya Kurrat kinbani mamaki da hankalin ki kike fad'in wannan maganar to wallahi bade cikin wannan gidan ba rarrabuwar kai wa'iyazubillah Allah yasani tunda nike banta'ba d'aukar Saraki matsayin bare cikin zuciya ta Allah yasani Ina matuqar son shi kamar yadda mahaifin shi yake sonshi banta'ba jin haushi dan anyima Saraki abu ba sabida nasan kafin a mishi anyi muku kuma dukda hakan Abeen naku yana sauke muku duk wani haqqi naku wani abun bansaniba Ammin taku zatasa Abbeen naku yayi muku sede nagani amma kike fad'in irin wannan maganar karki shiga sahun masu baqinciki dazaman Saraki magajin masarautar mu idan bashiba wa kikeso yaza magajin wannan masarautar ? Kinga kenan idan Saraki yarasa mulkin wannan masarautar shikenan tasubuce daga hannun mu sede tarihi Kurrat kiyi gaggawar yin yaqi da shedan d'in dayake kulla Miki sharri cikin zuciyar ki daku da Saraki duk abu 1 ne agareni bana daga cikin mahaukatan kishiyoyi marassa tunanin abin alkairi cikin zuciyar su Ina neman tsari da hakan kusani nice nabama maimartaba damar qara aure Kuma dakaina nace  Batol nikeso ya aure Koda Allah zaibashi magaji sabida banason mulkin masarautar shi tabar jinin shi tunda ni Allah bai bani d'an Namiji ba Kuma banayin baqinciki da hakan sabida nasan babbar ni'ima yayi min sekuwa gashi munsamu magajin wato Saraki inayin farinciki marar misali idan naga yadda kuke son qanin naku Kuma kunsan duk inda qarami yake anfi bashi kulawa dan haka kuma daga gareku kulawar nikeson gani ban yarda da banbanci ba kigani Bahijjat tun kafin hjy Batol tahaihu take hannun ta tariqemin ita kamar itace Mahaifiyar ta babu cutarwa tonima tayaya zan cutar danata ko nabari acutar dashi Ina wallahi inda zanga mashi yayo kan Saraki daniyyar illatashi to zan kare gara ni nacutu akan shi yacutu dan haka Kar naji Kar nagani idan wani yayi ma Saraki wani abu nacutarwa cikin ku to wallahi banyafe mishiba sabida aduk lokacin da akace gawani cikin ku ankamashi da cutar da Saraki to tabbas baqincikin hakan shine zaiyi ajalina sabida nasamu gur'batacce cikin zuri'a ta " daga haka Umma tashiga cikin bedroom d'in ta 



Kallon juna sukayi itako Aunty kurrat wata irin zufa ce taketo mata takasa koda zama ganin su Aunty Sumeer suna kallonta yasata seseta kanta tazauna sosai takejin bugun zuciya akan maganganun Umma 


USA


Cikin sauri da rud'ewa Maher yakamo Iftahal tashiga cewa " sannu bari nakira doctor kinsha magungunanki kuwa ? " girgiza kai tayi cikin wata irin murya yace " haba Iftiih!!!!! to maiyasa ? bari naje na d'akko miki Kisha kinji " kwantar da ita yayi saman bed jallabiyar shi yajawo yazura yafita cikin sauri yana sauka su Ammin suka bishi da kallo ko duban inda suke baiyiba yashiga bedroom d'in ya d'akko magungunan yafito yakoma saman yayi cikin d'an sassarfa yana shiga cikin bedroom d'in yaga babu Iftahal saman bed nufar toilet yayi nanma babu ita fitowa yayi cikin matuqar mamaki sauran bedroom d'in yashiga dubawa amma Babu Iftahal cikin razana da furgicin ya qwala kiran Iftiiiiiiiih!!!!!!! Iftiiiiiiiih Iftiiiiiiiih!!!!!!!! Kina in  ? " Jin wannan Kiran yasa Ammin keey Zaffar Aunty Bahijjat haurowa saman aguje suna zuwa Maher yayi saurin duban Ammin yace " Ina Iftiih ? " sosai Ammin tayi mamakin wannan tambayar tace " a a bakuna tareba " jin haka yasa Maher durkushewa yasaki wani irin ihuuuuu "


Comments please 


_Marmny Zarah Ce_

No comments