SARAN BOYE 35
No. 35
.............Kamar da wasa sai ga Abdallah ya shanye kwanaki ukun da baba malam ya bashi babu shi babu mai kama da shi. Ran baba malam da sauran ƴan uwansa ya sake ɓaci matuƙa, amma duk sunta ƙoƙarin dannewa. Dan hatta Hajjo ranta a ƙololuwar ɓace yake.
Hankalin Nu'aymah ne
ya sake ta shi. Dan koba komai har yanzu tana son Yah Ab, bazata so bari ya
cigaba da munana a idon iyayensu ba akan shima son da yake mata. Tunda duk
abinda yake aikatawa na laifi a garesu a kanta ne.
Kuka sosai Nu'aymah tasha
akan wannan al'amari. Musamman ma da itama tai kiransa da wayar Umm amma yaƙi
ya ɗaga tun a ranar.
Yau ma wayar ta sake ɗakkowa ta
Umm ta kirasa, sai dai bai ɗaga ɗin ba. Haƙura tayi da kiran, sai dai kuma
bayan kamar awa guda kamar an tsikareta ta sake zuwa ta aro wayar again. Test
massege ta tura masa, bakinta cike da addu'ar ALLAH yasa ya duba.
Bayan kamar mintuna biyar kuwa sai ga reply ɗinsa.
Jikinta har rawa yake wajen ɗauka ta duba.
*_“Zan iya amsar gayyatarki akan
dalili guda ɗaya, idan kin amince da shi ko yanzu zan iya dawowa gida na
fuskanci iyayenmu”._*
_Dalilin kawai ki amince a ɗaura
mana aure ranar bikin su Kubrah._
Wani irin mugun bugawa ƙirjin
Nu'aymah yayi, tai mugun waro manyan idanunta waje hawaye masu zafi na
rige-rigen fitowa. A fili cike da karyewar zuciya ta furta, ‘Anya kuwa Yah Ab
bai fara shaye-shaye ba jama'a? Na shiga uku ni Zainab, wane irin tsaka mai
wuya bawon ALLAHn nan yake ƙoƙarin jefani a gidan nan?’.
Kuka sosai ta kuma sha fiyema
dana ɗazun, dan sai da taji kanta ya fara sara mata sannan ta haƙura. Har bayan
anyi sallar isha'i bata fitaba ta cigaba da zama a ɗaki. Wayar Umm ma da
Muhammad ya shigo aran littafinta na *Ahdhari* ta bashi ya kai mata. Yunwa ce
ta fara takura mata, dole ta miƙe ta shiga bayi, wanka tayo ta fito, tai shirin
cikin wando da riga na barci masu taushi. Tanajin yunwa amma bata jin cin
abincin kuma, sha'awar shan lipton ne yazo mata a rai. Dan haka ta miƙe ta ɗauka
hula ta saka a kanta sannan ta fito.
A falo sukaci karo da Rabi ɗauke da
ƙaramin jug da alama ma ɗakinta zata. Baki Rabin ta washe ta na faɗin, “A'a
uwar ɗakina kin tashi ashe? Kamar kinsan kuwa zoɓon nan zan kai miki dama ko
zaki ɗansha dan na sanki da son zoɓo”.
Ɗan lumshe idanu Nu'aymah tayi ta buɗe
akan rabin tana ɓata fuska kaɗan. “No bar zoɓon nan ma dai baba Rabi. Idan ban
takura miki ba dan ALLAH haɗamin lipton kaina ciwo yake min”.
Da sauri Rabi tace, “Ah wlhy babu
wani takura uwar masu gida. Kinga zauna bani mintuna biyar kacal, barama nai
miki amfani da ganyen shayin baba malam, ina dai kina so ko?”.
Kai kawai Nu'aymah ta gyaɗa mata
dan surutunta ya isheta. A ƙasan ranta kuma tana mamakin yanda Rabin ta amsa
dafa mata shayin ɗin babu ko musu balle sukai ga faɗan da suka sabayi kullum.
Ɗakin Umm Nu'aymah ta nufa kafin
Rabi ta kammala, sai dai ta iske tana wanka dan haka ta fito akan idan ta gama zata
koma. Fitowarta dai-dai da fitowar Rabi da ga kitchen ɗauke da kofin shayi dake
ta turiri. Sai da tai mata godiya sannan take tambayarta ko baba malam ya
shigo?.
“A'a bai shigoba, dan naji
Muhammad na faɗin kamar yayi baƙi ne ma”.
“Okay”.
Kawai Nu'aymah ta faɗa tare da ɗaukar kofin
ruwan zafin ta kai bakinta tana ƙoƙarin kunna television da hannunta na haggu.
Sosai shayi yayma Nu'aymah daɗi, harta
shanye wanda Rabi ta zuba mata itama ta sake zuba sauran wanda ya rage a butar
shayin. Tana cikin shan wanda ta zuba ɗinne Umm ta fito...
“Oh dama kin tashi?”.
“Eh, nama shiga ɗakin na tarar kina wanka. Umm kaina ke min
ciwo ALLAH”.
Cike da kulawa Umm dake dubanta
tace, “Ba dole kanki yay ciwoba Nu'aymah, kukan da kikayine ai. Halan ma da
kika tafi ɗakin ba barcin kikayi ba?”.
“Umm barcin nefa bai zoba.
Amma yanzu naɗan fara ji, sai dai zan jira Abba ya shigo sannan naje na
kwanta”.
“Wayasan sanda zai shigo,
ki tashi kije ki kwanta banason sakarci. Miyasa ke wai sam baƙya tattalin
lafiyarkine? Kin fison kullum ki ganmu hankali a tashe”.
“Kiyi haƙuri Umm ba haka baneba wlhy,
dama dan yau duk bamu haɗu da Abba bane shiyyasa. Amma bara nasan insha ALLAHU
da safe zamu haɗu. Sai da safe”.
“Ki tabbatar kinyi addu'a kafin ki
kwanta”.
“To Umm”.
Nu'aymah ta faɗa tana nufar ɗakinta badan taso hakanba.
Kamar jira tana kwanciya sai barci mai nauyi ya kwasheta batare da ko addu'ar
da Umm ta gargaɗeta yi ba tayi ɗin.
★★
Sai wajen sha ɗaya baba malam ya
shigo gidan. Koda ya tambayi Nu'aymah Umm ta sanar masa ta kwanta sai ya nufi ɗakinta.
Yayi sallama kusan sau uku babu amsa, dan haka ya juyo falo yana faɗin, “Nayi
magana shiru, inaga tayi barci ma”.
“Dama tace barci takeji, amma
tsabar fitina wai zata zauna jiranka dan yau duk bata gankaba”.
Murmushi kawai baba malam yayi, amma
baice komaiba.
Kusan ƙarfe sha biyu
saura Nu'aymah ta farka da wani Masifaffen ciwon ciki. Juye-juye ta
shigayi a kan gadon tana kiran sunan Umm. Tun abin na mata sama-sama harya fara
fin ƙarfin tunaninta. Yunƙurawa tai da ƙyar ta tashi zaune tana ambaton
‘Innalillahi.....’ da ƙyar ta iya sakkowa da ga saman gadon. Sai dai yanda
ƙafafunta da mararta suka riƙe sam bazata iya takawa ba.
Ƙasa ta durƙushe hannunta ɗaya
riƙe da cikinta, ɗayan kuma ta dafe gado da shi tana matse idanu da cije baki.
Cikin azabar data isheta ta fara ƙwalla kiran sunan Umm da baba malam tana
roƙon suzo su taimaketa zata mutu. Yanda zufa ta jiƙeta sai ka ɗauka ruwa aka
watsa mata. Wata gigitacciyar ƙara ta saki lokacin da idanunta ke sauka akan
Windown ɗakinta. Gilmawar mutum ta gani, wanda alama ta nuna ya jima a wajen
tsaye koma waye. Ai sai kawai ta daddage ta fasa ƙarar da tafi ta farko badan
taji tsoro ba sai dan wani irin kartawa da mararta tayi tamkar numfashinta zai
bar ganar jikinta a lokacin.......
A rikice baba malam da Umm da
barci ya fara ɗauka yanzun suka farka. Har rige-rigen fitowa sukeyi dan ƙarar
Nu'aymah sun jitane tamkar a tsakkiyar ƙwalwar kansu.
Kwance suka isketa a ƙasa wanwar tana numfashi
da ƙyar. Baba malam yay saurin kunna fitilar ɗakin mai haske, Umm kuma ta
nufeta tana kiran sunanta. Sai dai ina Nu'aymahn ta suma. Sake rikicewa Umm
tayi, ta fashe da kuka itama tana girgiza Nu'aymahn.
Baba malam daya nufosu shima a
rikice yay sauri ja da baya jin ƙafarsa cikin wani abu mai ɗumi. Kallon inda ya
taka ɗin yayi. gabansa yay bala'in faɗuwa ganin jini. Cikin rawar jiki ya
durƙusa da kai ɗan yatsansa ɗaya yaɗan dangwalo. Tabbas jinine kuwa. Dan haka
yace, “Jini kuma?”.
Saurin kallonsa Umm tayi itama. Tace,
“Jini kuma malam? A ina?”.
Da hannu ya nuna mata, sosai zuciyarta
tai masifar harbawa. Tabi jinin da kallo har jikin Nu'aymah da alamu suka nuna
daga nan yake fita. Kafin ta iya cewa wani abu sai ga Hajjo da Addah da Momy
sun shigo a rikice. dan duk wanda yake a gidan yaji ihun Nu'aymah saboda dare
yayi. Sai kuma ga matan Abba Musbahu su maman Yusrah, suma Samarin gidan duk
sun shigo sai dai sun dakata a a falo.
Hankalin kowa ya tashi da ganin
wannan jini. Ga dare ya fara.
Hajjo tace, “Mafita ya kamata mu nema ba wai
koke-koke ba. Ya kamata a tado su Ahmadu dan a tafi asibiti”.
Addah data maida Nu'aymah jikinta
ta share hawayen da ke ziraro mata itama da faɗin, “Hajjo inaga a kira Doctor
Sale tunda nan kusa yake shi. amma yanzu ko asibiti akaje zaiyi wuya a samu
likitan kirki. Gashi yarinyar nan tana ciki wani hali”.
Dukansu sunyi na'am da zancenta.
hakan ya saka Abban Abdallah fita dan ya kiran Doctor Sale a waya. A falo ya
wuce samarin gidan tsaitsaye jigum-jigum. Kusan a tare suka shiga tambayarsa
mike faruwa?.
A taƙaice ya basu amsa yana
ƙoƙarin kai waya kunnensa.
Cikin mintunan da basu
gaza talatin ba Doctor Sale ya iso. Malam ƙarami ne yaje ya shigo da shi, yay
masa iso har ɗakin Nu'aymah. Zuwa lokacin su Momy nata ƙoƙarin saka abu ana
kwashe jinin da har yanzu bai dai na zuba da ga jikin Nu'aymah ba. Su baba
malam kuma sun koma da ga ƙofar ɗaki.
Ko gaisuwa bai tsaya sunyi ba ya shiga.
Su Umm duk suka fito aka barsa da Addah da Umman su Yusrah a ciki. Ƙoƙarin
tsaida jinin ya farayi, kafin ya fara bama Nu'aymah taimakon gaggawa.
Kamar wasa sai da ya kwashe awa guda
domin ƙoƙarin ceto ta, Umman Yusrah nata gyara wajen, Addah kuma na riƙe da
Nu'aymahn har yanzun. Jinin an samu ya tsaya, harma an saka mata ƙarin ruwa
bayan an samu ta farfaɗo. Fita yay ya basu waje dan su ƙarasa gyara mata
jikinta.
Yana fitowa duk suka yo
kansa suna tambayar yaya jikinta. Doctor Sale ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin,
“Alhmdllh malam ku kwantar da hankalinku. Komai ya dai-daita, sai dai kuma anyi
asarar cikin da ke jikinta. Nayi iya ƙoƙarina na ganin cikin bai dalwantaba
amma hakan ya gagara, sai dai haƙuri”.
Ga ba ɗayansu wani irin kallon rashin
fahimta suke masa. Cikin ƙarfin hali Hajjo tace, “Kai ɗan nan bamu fahimci
zancenka ba. Miya haɗa Zainabu da ciki kuma? Ko kuwa kana nufin wani ciki dai
bana haihuwa ba?”.
Shima ɗin dai kallon mamakin
yake mata, kafin cike da son fahimtar da ita yace, “Mama ina nufin ciki na
haihuwa mana, ko bakusan tana da shi ba ne?”.
Kallon juna suka shiga yi ƙirjin
kowa na bugawa da sauri-sauri musamman ma Baba malam da Umm da Hajjo. Da rawar
harshe Umm tace, “Ya zakace ciki a jikin Nu'aymah?”.
“Ikon ALLAH! Hajiya wlhy
ciki ne da ita ɗan sati shida ma kuwa”.
Umm zata sake magana baba malam
da zufa ke karyo masa ta ko ina a sannan jikinsa yay saurin katseta da faɗin,
“Doctor yanzu wane hali take ciki ita?”.
“Ah Alhmdllh malam, yanzu haka
tama farfaɗo, na kuma saka mata ruwa da zai sakata barci, zuwa da safe idan
ALLAH ya kaimu zan dawo na sake dubata sai na taho da magungunan da ya kamata
tai amfani dasu. Zuwa da yamma idan taji ƙarfin jikinta za'a kaita asibiti dan
na sake dubata da ƙyau, a kuma yi mata wankin ciki, dan gaskiya ɓarin yazo mata
da matsala kamar”.
“To shikenan, mungode sosai Doctor,
ALLAH ya saka da alkairi”.
“Amen” Doctor Sale ya amsa saboda jin
daɗin addu'a daga babban malami irin baba malam. Daga haka yay musu sallama ya
tafi ya barsu da ruɗani.
Tun fitar Doctor Sale kowa ya kasa yin
ko motsi. Sai ma Umm da hajijiya ke ɗauka kaɗan-kaɗan ce ta ɗan zauna jin zata
faɗi. Cikin ƙarfin hali Hajjo ta shiga ɗakin Nu'aymahr, ta iske su Addah sun
kammala kimtsata harma sun lulluɓa mata bargo, ga ƙarin ruwan da aka saka mata
yana tafiya dai-dai.
“Kunga kuje ku kwanta dare na
ƙara nisa. Tunda ALLAH yasa ta samu barci. Suma sauran ku sanar musu suje su
kwanta”.
Babu musu sukai mata sallama suka fita.
Su da basusan mike faruwa ba sai suka shiga sake kwantar musu da hankali akan
jikin Nu'aymahn da sauki. Hajjo ma tace kowa yaje ya kwanta.
Su Abban Adawiya ne kawai sukace
Alhmdllh, amma babu wanda yay yunƙurin tafiyar sai da Baba malam yay magana.
Har kowa ya gama ficewa da ga sashen baba malam da Umm basu iya motsawa ba. Sai
bayan kusan mintuna goma sannan ya kama Umm ta miƙe da ƙyar. Ɗakin Nu'aymah
suka shiga. Hajjo dake zaune ta zubama Nu'aymah ido ta ɗago tana kallonsu.
Saurin yin ƙasa da kai Umm tayi, dan sai
yanzu me wasu zafafan hawaye suka sami damar ziraro mata. Har ga ALLAH
zuciyarta ta shiga cikin matsanancin ruɗanin bayanin Doctor Sale. Wani sashe
yana gaskatawa wani sashe na ƙaryatawa. Hakama baba malam a matuƙar ruɗanin
yake. Amma da yake shi namijin duniya ne sai ya shanyeshi tsaf dan a ganinsa
yana buƙatar lokacin yin tunani akan hakan..........
Hajjo ce ta katsesu da faɗin, “Ban
yarda da wannan maganar ta likitan nanba, duk da kuwa koni jinin ya matuƙar
tsoratani tunkan bayaninsa. Sai dai hakan bashine ke nufin mu amince da cewa
ciki a jikin Zainabu ba. To ta yayama hakan ta faru? A ina kuma? Yaushe kuma?”.
Kan baba malam a ƙasa, muryarsa a
matuƙar cinkushe da tashin hankali yace, “Inna bazamuyi saurin ƙin gaskatawaba,
tunda kinga ai aikinsane hakan”.
“Duk da aikin nasa ne ban yardaba. Sai
an nemo wani likitan ya sake dubata tukunna. Kokuma muje asibiti da safe idan
ALLAH ya kaimu”.
Basu iya mata musu akan hakanba
da ga shi har Umm da bata iya furta komai ba har yanzun.
WASHE GARI
Da safe Doctor Sale ya
dawo gidan zuwa 8:30 kamar yanda yay alƙawari. A lokacin Hajjo ta gyara
Nu'aymah da kanta. Yayinda Rabi ta sake tsaftace ɗakin ita kuma.
Ya dubata yanda ya kamata, ya
kuma tabbatar musu komai Alhmdllh dan UBANGIJI ya sauƙaƙa al'amarin. Ita dai
Nu'aymah ba wani fahimtarsu take ba, dan batasan ainahin abinda ya sameta ba
bayan ciwon cikin da zata iya tuna tayi kafin gushewar hankalinta.
Ya bada magungunan da zatay amfani da
su, da waɗanda bashi da su za'aje a sayo. Daga haka yay musu sallama akan da
yamma zai dawo ya sake dubata idan ya taso aiki. Godiya baba malam yay masa.
Hajjo da Nu'aymah dai basuce komai ba. Hakama Umm da tun daren jiya da
hankalinta yabar jikinta har zuwa yanzun bai gama dawowa ba.
Baba malam baiso maida hankali
akan maganar hajjo na nemo wani likitanba. Amma ganin ta matsa sai ya bi
umarninta suka kira wani Doctor Faisal abokin Ahmad. Wajen ƙarfe goma na safen
shima ya iso, a lokacin an maida Nu'aymah sashen hajjo.
Shima dai sun bashi dama yayi aikinsa
yanda ya kamata. Kafin daga bisani yay zaman basu bayanin daya matuƙar tada
musu hankali akan result ɗin shima. Ya tabbatar musu da gaske Nu'aymah ɓarin
ciki tayi ɗan sati shidda da wasu kwanaki, amma babu wata matsala tattare da
ita, magunguna kawai zataita sha jikinta zai koma normal.
Har ya kai karshen bayaninsa babu wanda
ya iya motsawa a falon, sai hajjo ce tai ƙarfin halin masa godiya.
Bayan wucewar Doctor hajjo ta sake
tabbatar musu shima bata yarda da nashi aikinba. Duk yanda baba malam yaso
fahimtar da ita tace bata yarda ba. A yanzu sai su ɗauki Nu'aymah suje asibiti
kawai, kuma na gwamnati take so.
Ɗari bisa ɗari su Abba Musbahu sun yarda da
maganar hajjo, dan suma zukatansu sam basu aminta da maganar ɓarin cikin
Nu'aymah ba sam. Sunfi baba malam yawa, dan haka dole yay shiru ya barsu. Amma
a ƙasan zuciyarsa bai son sake fitar maganar kuma dan hakan tamkar tonama kansu
asirine sukeyi, tunda yasan ba duka likitocinne zasu iya barin maganar a
cikinsu ba duk da yasan basusan Nu'aymah bata da aure ba.
_____________________
Bisa matsawar hajjo suka ɗauki
Nu'aymah da sam jikinta babu ƙarfi zuwa asibiti. Kasancewar su manyan mutane da
ake girmamawa basu wani sha wahalar ganin likita ba, a yanzu kam mace ce ma
Doctor Halima. Itama ɗin dai ta gunar da aikinta cike da ƙwarewa. Bayan kamar
awa biyu ta basu samako dai-dai dana su Doctor Sale. Dan ta sake tabbatar musu
da Nu'aymah tayi ɓarin ciki ɗan sati shida da wasu kwanaki dai, harma ta ɗora
da faɗin Nu'aymahr na buƙatar hutu sosai da yawaita cin abinci mai inganci
saboda jinin data zubar.
Ba ƙaramin tashin hankali suka
sake tsintar kansu ba a wannan karon kam. Dan ko masu tatsuniya sunce Ƙurun
ƙus, anzo ƙarshe. Hajjo mai gardamar bata yardanba a yanzu sai bata iya cewa
komai ba. Haka suka tattaro suka taho, dama ita da Ahmad da Naser da Abban su
Abdallah da Addah ne suka je.
Ganin Hajjo na sharar hawaye
Nu'aymah da ke magana da ƙyar saboda rashin ƙarfin jiki ta matsa da son jin
mike damun kakar tasu?. Banza tai mata, hakan yasa tunanin Nu'aymah ko hajjo
bataji ba ne sai ta sake maimaitawa.
Tsawar data sakata ɗinke bakinta
Hajjo tai mata, ta kuma ja mata dogon gargaɗi akan ta barta taji da abinda ya
dameta. Shiru kawai Nu'aymah tai tana kallon hajjon, a ƙasan ranta ko fal
tambayoyin mike faruwa ne?.
Koda suka iso gida Addah ce ta taimakama
Nu'aymah zuwa sashen hajjo, inda suka iske Abdallah da ya dawo gidan tare da sauran
samarin gidan suna zaman jiran tsammanin dawowarsu.
Kowa ransa babu daɗi ya
shiga yima Nu'aymah sannu, yayinda Yah Ab ya kafeta da idanu kawai yana kallo.
Itama dai kallon nasa takeyi. a ƙasan ranta kuma tanajin daɗin dawowarsa gidan.
Basuyi zaman mintuna biyar ba baba
malam da sauran ƴan uwansa suka shishshigo harda Umm ma da sauran matan gidan
dan Hajjo ce ta aika kiran kowa. Sai dai babu yaran gidan da ƴammata. Yaseer ma
dake falon zaune tun ɗazun korashi waje akayi, Abba Musbahu yace yaje ya
tattara yaran su wuce islamiyya.
Shiru falon yayi kowa na
jiran mi hajjo zata faɗa, Nu'aymah da ganin ita ba'ace ta tashi ta fitaba taita
binsu da kallo a ƙasan ido tana mamakin yanda fuskar kowa ke ɗauke da ruɗani da
tashin hankali........
Maganar Hajjo ce ta katsema
Nu'aymah tunani.
“Alhamdulillahi, kamar yanda na
buƙaci zuwa asibiti dan tabbatar da abinda zuciyata ta kasa gaskatawa ga shi
munje mun kuma dawo. Sai dai abin razanin da tashin hankalin shine babu
banbancin magana tsakanin likitocin farko da wadda ta duba Zainabu a yanzu.
Itama ta sake tabbatar mana cewar Zainabu ɓarin ciki tayi ɗan sati
shidda........”
“What?!!!”.
Nu'aymah ta katse hajjo a zabure tana miƙewa zaune zumbur
tamkar ba itace kejin kamar iska zata ɗauketa ta faɗi ba yanzun. Jikinta na
matuƙar rawa tace, “Hajjo ban ganeba dan ALLAH! Wace Zainabu kike magana badai
ni Zainab ɗinba?”.
Matsananciyar tsawa baba malam ya daka
mata, ai bama tasan ta koma ƙasa rib ba ta zube a carpet saɓanin kujera da take
kwance a kai ɗazun. Baba malam ya nunata da yatsa yana faɗin, “Zainab!! Wlhy
tallahi kinji na rantse, inhar na sakejin bakinki batare da an baki izinin
magana ba sai kinyi nadama”.
Babu wanda ya iya ko motsi, dan jin
ainahin sunan Nu'aymah a bakin baba malam ya tabbatar musu da lallai magana
tazo iyaka. Ita kanta jin sunan daya kiratan ya saka zuciyarta ƙara gudu da
tsitstsinkewa lokaci guda, wani bahagon tsoro da ruɗani suka da ɗa mamaye
dukanin gaɓɓanta.
Hajjo data juyo tana kallonta tace,
“Zainabu bama buƙatar wani ja'inja ko rantse-rantse, nan gurin duk zuri'armune
babu wani bare a ciki. ki daure ki faɗa mana wanda ya aikata miki wannan ɓarna.
Shin da ganganci ne kokuwa fin ƙarfinki aka y? Wanene uban cikin nan da ya
salwanta jiya?”.
Sake rikicewa Nu'aymah
tayi, jikinta na rawa tace, “Wlhy hajjo, na rantse da UBANGIJIN al'arshi ban taɓa
aikata abinda kuke tuhumata da shi ba. ALLAH shine shaidata ni banda
ciki.........”
Wuƙa sharɓeɓiya Abba
Musbahu ya fiddo ya nunama Nu'aymah, sai ƙyalli take da ɗaukar ido, mai kallo
daya ganta yasan ta cancanci a kirata da suna GAYAWA JINI NA WUCE.
“Nu'aymah kinga wannan wuƙar
ko?”.
Kai ta ɗaga masa da sauri jikinta na
cigaba da rawa.
Ya jinjina kansa da cigaba
da faɗin, “Inhar kikace zaki mana wasa da hankali to nan tsakkiyar falon nan
zansa su Abdallah su kwantar min dake na yankaki kamar yanda ake yanka ragon
layya. Ke dawa kuke aikata wannan shaiɗancin anan gidan.....?”
Kai Nu'aymah ta shiga girgizawa tana
kuka tamkar ranta zai fita. Bakinta kuwa sai wani irin karkarwa yakeyi kamar laɓɓanta
zasu zubo ƙasa. Ta buɗe baki zatai magana sai kuma ta sake rushewa da wani
sabon kuka.
Kamar daga sama sukaji a bayansu ance,
“Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku..........”✍
😱😱To wane majanunun ne kuma wannan?.

No comments