MIN QALB 35
MQ 35_*
Godia kawu yasake kafin ya sake gyara zama bayan fitar MD
yace"
To akwai 'yan burirrika dakuma kamar sharadi zance kokuma dai nace alfarma damuke nema bayan auren.
Cikin jinjina Kai Andi yace"
Muna sauraronka Mal Saleh Allah yasa me dubuwace wannan
alfarmar ko sharadin.
Eh wato gskia Amatu dai na sha'awa dakuma ra'ayin zurfafa
karatun zamaninta wato na bokon Nan
Tajima da wannan burin bama ita kadaiba wannan burinane
akansu tun suna Yara gaskia saidai Kuma Hali na rayuwa baibari tasamu ilimin
bokon ba sosai,
Shi kansa mijinta Allah yaji qansa kafin aurensu yayimin
alqawarin barinta tasamu wadataccen ilimi bayan aurensu saigashi Allah bai basa
iko ba Dan haka nake bayarda wannan buqatar ta barinta ta ilmantu acikin Boko
Dan shi na addini Banda haufi akanta tasamesa yanda yakamata Inshallah,
Wannan shine buqatata
Idan MAHMOUD daku iyayensa zaku Bata wannan damar to Ina
godiya da hakan.
Tsit sukayi suna nazartar zancen nasa sbd maganar haqiqanin
gaskia yaransu Mata basa karatu anan musamman masu auren sbd qasarmu na daya
daga cikin qasashen da Basu dauki Mata da daraja ba idan angansu suna yawon
neman ilimi makaranta musamman akan matan aure da akafi buqatar fasikanci
dasuba ayanzu akan 'yan matan shiyasa suka zabi gwara sukai yaransu qararda ba'a
sansu ba suyo karatunsu su dawo,
Amma babbar matsalar anan itace ana maganar karatun Amatun
ne bayan aure Kuma har wata qasar.
Muskutawa Modibbo yayi ya kalla Andi cikin nutsuwa
yace"
Inaga Babu wata illa ko abin damuwa musamman tunda shi
MAHMOUD din nada gida acan yawancin qasashen saita zaunama acan din shikenan.
Numfashi Andi Yakuma saukewa kafin ya jinjina Kai ya kalli
kawu yace"
Yanxu duk ba lokacin wannan neba yanxu idan lokacin yayi
zamuyi maganar insha Allah.
Sake goggodewa juna sukayi tareda maganganu dangane da gadon
da Khalil yabari shidai kawu baida tacewa hakadai suka kammala kafin aka Kira
Salman ta waya yadawo ya daukesa Dan maidashi gida.
***Ahankali tasanyawa kanta hkr ta rungumi qaddarar rasuwar
mijinta tareda rungumar Abinda Allah yabata ta maida hankali gurin renon
cikinta Wanda kusan yanzu tsakanin itada umme da iyami da anty zarah sai oga
kwata kwata MD ZABEERA ba'a San yafi qwallafawa cikin Rai ba,
Iyami tuni tafara siyan robar wankan jariri dasu kujeran
zaunawa akai ayi Masa wanka harma dasu kayan yajin abincin me jego Wanda kullum
lissatafinta kenan,
Umme ma Kam tuni akai nisa gurin tariyar kayan jarirai
hardasu kayan wasansa,
Anty zarah kuwa kayan me jegon tafi maida hankali gurin Dan
siya
Sai oga MD ZABEERA Wanda ya damesu ya shanye gurin Tara
siyayyar kayan jarirai har wainda sai ya iya tafiya da gudu kafin yayi amfani
dasu dan sunfi qarfin jariri Wanda daki guda ake Tara kayan acikin sashen
Amatun duk yayi tafiya yadawo scan ake Kai kayan Wanda yasa Tunanin Yama fisu
zautuwa wannan Rabin ran Anty zarah din.
Tsakaninta dashi gaisuwa ne shima sai idan anci sa'a sun
hade by mistake sbd saitayi fiyeda wata ko wata biyuma Bata gansa ba sbd sosai
yanzu yarage zama sai yawan tafiye tafiye,
Dr Salman kuwa yayi tafiya baya qasar tun cikinta na wata
hudu yayi tafiyar Amma kusan kullum ayini shida USI batasan Wanda yafi wani
kiraba,
Cikinta yanzu Yana wata na bakwai Wanda yayi girma Dan
daidai ba laifi Wanda yasa qafafuwanta Dan kumbura kadan shiyasa ma kullum ake
fita da ita haraba tana Dan zagayowa sbd Dr Fatima tace taringa motsawa tana
Dan zagayowa.
Duk wani bayani da update Akan lafiyar cikin Dr Fatima MD
ZABEERA take Fara Kira sbd agurinsu tamkar shine mahaifin Abinda za'a Haifa din
and kowa yasan irin shaquwarta da qaunar dake tsakaninsa da 'dan uwansa kafin
ya rasu so koba a fada musu ba sunsan Babu Wanda zai dauki responsibilities na
cikin Bayan shi barema Kuma shine yabada wannan odar ta komai asanar dashi har
ranar haihuwar ma'ana EDD dinta duk yasani.
Zaune suke apalo itada anty salamatu da sai umme datazo
dubata and kwana biyu tunda tashiga wata na takwas take fama da ciwon Kai me
tsanani Dr Fatima tayita dubata ta sanar musu da tana fama da matsalar high BP
ne Wanda Dole suyi monitoring dinsa sbd idan bai sauka ba yakoma normal to
yanada wahala ta iya haihuwa da kanta saidai CS.
Magani umme ta miqa Mata ahankali ta karba tareda karbar
robar ruwan dake gabanta ta bude ahankali tana Dan lumshe ido sbd ko Ido ta
bude sosai kanta kamar zai tsage,
Maganin ta shanye tana ajiye robar daidai Dr Fatima na
shigowa palon daukeda sallama suka juya dukkaninsu suka kalleta suna Mata sannu
da zuwa Banda Amatun data kasa ko bude idanuwanta dake lumshe sai kawai taji
hancinta na shaqo Mata qamshin imperial majesty sama sama,
Bata bude idanuwanta ba sbd tasan baitaba shigowaba Kuma
tasan baida dalilin dazai sashi shigowa din dan Daman da cikin yadamu bawai ita
ba to Kuma Dr Fatima ma kafin tafada musu komai dangane da cikin saita fada
Masa tuntuni haka suke Dan haka Bata sakaran akwai Abinda zai taba sanyashi
shigowa....
MAHMOUD Kaine da kanka yau?""maganar umme data
sanyata bude rufaffun idanuwanta cikin rashin sa'a sai acikin nasa daya zuba
Mata akaro na farko daya kafeta idanuwansa Yana kallon cikinta daya Gama girma.
Cire idanuwanta cikin nasa tayi akaro na farko wata irin
tsananin kunyarsa ya kamata sbd ganin irin kallon dayakewa cikinta
Ta 'dan muskuta ahankali tareda Dan Jan wuyar rigarta sama
sbd budadden wuyane Dan doguwar rigace Mara nauyi Sam hannunta ma qarami ne
irin na shimi.
Ahankali ya dauke kansa Yana zaunawa a kujerar dake
fuskantar Tata ya kalli umme ya bude baki cikin yanayinsa na nutsuwa cikin
sauti me taushi yace'
Barka da yau umme,
Na sameku lfy?
Lafiya kalau,
Yaushe kadawo ne Dan last time Dana tambaya zarah tacemin
kana Turkish.
I came back this evening.
Allah sarki to sannu da hanya.
Thank you umme""ya furta cikin qaramin sauti sbd
Sam kwata kwata rayuwarsa bai Saba da a nuna Masa kulawaba musamman daga gareta
shiyasa yaji abin wani irin har baisan Yaya zai amsa Mata dinba Bayan da
qananan kalmomi.
Kallon anty salamatu data kawo Masa drinks yayi tareda Dan
girgiza Kai Yana cewa''
No thank you bana buqatan komai am ok.
Maida kallonsa yayi Kan umme cikin nutsuwa batareda ya kalli
Amatu ba yace"
Umme Dr Fatima tayi bayanin komai dangane da yanayin da ita
take ciki wanda yakamata asan asalin menene yasa takasa kwantar da hankalinta
kodan sbd lafiyan Abinda yake tareda ita,
Meyasa bazaku fada Mata ta kwantar da hankalinta ba sbd high
BP dinnan is a very serious issue and I can't.....sai yayi shiru yakasa qarasa
fada ya 'dan kalli gefenta kadan tareda maida kallonsa Kan Dr Fatima yace"
Please make her understand illolin BP game ciki please.
Kallonsa Dr Fatima tayi kafin tajuyo ta kalli Amatun datake
mamakin yanda Ashe dama Yana Magana haka sosai saidai maganar tasa tafi Kama da
kamar ransa A 'dan bace yake.
Cikin damuwa ma umme itama tace"
Hakane kam Amatu Dan Allah ki cire damuwar idanma damuwar
tsoron haihuwar kika saka aranki ki cire Zaki haihu lfy munanan munata Miki
addua.
Idanuwanta be suka ciko da hawaye har suka Fara gangarowa
Wanda yasa kowa zuba Mata idanuwansa cikin mamaki da damuwa,
Dr Fatima ce ta Kama hannunta tajata daki tareda ce
musu karsu damu zata Magana da Amatun zataji matsalarta.
Daki suka Shiga tareda rufo qofa suka bar su ummen zaune
tsit cikin tsumayi.
Kiran wayarsa akayi ya miqe ya fice a natse tareda daukar
wayar Yana Magana kamar bayason Yi ya nufi hanyar sashensu.
Kallon Amatu Dr Fatima tayi cikin nutsuwa da kulawa
tace"
Amatu karki damu ni likitarki ce duk Abinda na tambaya kada
kiji komai karki boye ki fadamin sbd lafiyanki da abindake cikinki mukeso Kuma
kema nasan bazaki so komai yasameku ba, kinada matsalar da kikeji ne dangane da
cikin?
Kokuma a jikinki?
Numfashi ta sauke tareda sauke kallonta daga Dr Fatima din
ta bude bakinta dayayi nauyi tace"
Dr Fatima kaina ne ke tsananin ciwo sai Kuma kamar na daina
Jin motsin cikin tun jiya.....
Kallonta Dr Fatima tayi da sauri cikin 'yar razana amm
zamtowarta likita saita saki murmushi cikin kulawa da kwantarwa da Amatun
hankali tace"
Jiya tun yaushe ne bakiji motsin ba?
Tun da yamma danaji bansake ji ba.
Sake wani murmushin me sauti tayi tareda dafa hannun Amatun
tace"
Kinga wannan ba wani matsalane babba ba zamu duba mugani
inshallah baby lafiyansa kalau
Bayan wannan menene Kuma matsalar?
Dagowa tayi ta kalleta kafin tayi qasa da Ido cikin damuwa
tace"
Ciwon Mara saikuma gashi dazu Naga jini kadan kadan kaman
Yana zuwa.
Kama ne kokuma kingani din?
Nagani""tafada Kai tsaye tana bayyanarda
damuwarta.
Ok Amatu kinaji karki damu sosai Dan akan wannan insha Allah
yanzu zanje dake asibiti zandubaki acan sbd Kinga gskia lokacin haihuwarki bai
Isa yiba ana haihuwane at 36weeks zuwa 40weeks harma fiye amma ke Kinga yanzu
kina cikin 33weeks atleast Koda za'ayi haihuwar gaggawa ne Kikai ko 35weeks
haka so yanxu zanje dake asibiti zamu duba matsalar mugani Amma kema saikin
taimaka kin rage damuwar komai aranki sbd Kinga damuwace tasaka BP dinki rising
and hawan BP Kuma na iya leading to komai so please Amatu kicire damuwa
inshallah komai zaizo yanda ake so ake Kuma fata kinji ko??
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali kafin ta daga Kai tana cewa
Inshallah Dr.
Dr Fatima ce kawai ta fito tabaro Amatun cikin daki dan
tashirya tafito su tafi.
Zama Dr Fatima tayi ta fuskanci umme data zuba Mata Ido tana
tsumayin jiran Abinda zata fada musu
ta Dan sauke numfashi cikin yanayi na damuwa kadan
tace"
Gskia akwai matsala dangane da yanda tace batajin motsin
cikin gakuma zuban jini datace Dan haka inaga asibiti zamu Bata gado ta kwanta
mufara monitoring BP dinta da lafiyar babyn har musamu takai lokacin haihuwar
saidaima bazance ga komaiba yanzu sainaje asibiti munyi scanning munkuma dubata
mungani musan meye abinyi.
Ajiyar zuciya umme ta sauke jiki a mace yace"
To Allah yasa miji alkhairi
Min barwa Allah komai
Allah yayi Mana jagora.
Amin anty salamatu da Dr Fatima sukace Suma jiki amace.
Dr Fatima ce ta miqe tafara ficewa tana latsa Kiran MD Dan
sanar Masa halinda ake ciki.
Cikin doguwar rigar jikinta ta fito sai dogon hijabin data
sanyo.
Fitowa sukayi umme na riqeda hannunta sbd qafafuwanta dasuka
kumbura sosai daqyar take takasu ga mararta datai nauyi tana Mata ciwo.
Baqar JUGUAR RANGE ROVER suka tarar pake a bakin qofar palon
akunne sai qyalli take tana aiki duk da Basa ganin Wanda ke ciki kowannensu
Saida ya ayyana MAHMOUD ZABEERA ne sbd shikadaine ke dukan irin wainnan motacin
a zabeera duk da kowa na dukan kalar nasa arzikin.
Shine da kansa yake tuqa motar
Umme ta bude baya Amatun tashiga ahankali Yana kallonsu ta
mirror kafin anty salamatu tashiga
Umme tace suje zataje ta shirya zatazo daga baya.
Jan motar yayi suka wuce Yana tuqin ahankali kamar Wanda ya
dauko me naquda.
Koda suka Isa Dr Fatima ta shirya komai Nan take aka karbeta
akai nufi labour room da ita Dan acan zasu dubata suyi Mata scanning.
Anty salamatu ana Shiga da Amatun ta daga waya takira kawu
tafada Masa tana kashewa saiga Kiran iyami cewa gatanan zuwa.
Tashin farko suna Gama dube dubensu suka gano ruwan dake riqeda
babyn saura kadan su Gama tsiyayewa gashi lokaci baiyiba Dan ko kadan Bata Fara
budewar haihuwa ba suna saka ran saidai
CS gashi Kuma lokaci baiyiba da saura Dan haka mun yanke zamu riqeta anan muna
kulawa da lafiyarsu har zuwa Nanda sati biyu tashiga 35to 36weeks sai ayi aikin
saidai gskia babyn zaizo ba qwari muna fatan yazamto rashin qwarin kawai sbd
irin hakan babies din yawanci na zuwa da matsaloli"""Dr Fatima
ce take fadawa MAHMOUD ZABEERA hakan acikin office dinta bayan tabaro Amatun
gurin nurses suna shifting dinta zuwa dakinda zasu ajiyeta.
Zanyi tafiya Nanda 5 days but Inshallah I will be back
before time din yacika Just do the best you can atare matsalar.
Karka damu Mr zabeera Inshallah zaka dawo kasamu both the
mother and the baby lfy.
Thank you"yace tareda miqewa Yana dorawa da cewa''
Stefan zaiyi clearing bills na komai zuwa anjima.
Kamar zaije dakin datake saikuma ya dakata tareda kallon
qofar kawai ya wuce daidai isowar su iyami suka gaisa ya fice asibitin gabaki
daya.
Da daddare iyami ce kawai ta kwana tareda ita anty salamatu
ranar gidansu ta wuce dan dama tanada niyyar zuwa gidan yau yin wani Abu saiga
zuwa asibiti ya kamasu.
Umme da Haj maryam ne suka Zo da daddare suka kawo musu
abinci
Anty zarah ma tazo takawo wa Amatun furar datake so,
Gaba daya Kwanakin busy take da hidimar gidanta data MAHMOUD
da yanzu ta dage sosai take farautar soyayya da kulawar mijinta Wanda Amatun ke
sake zugata da Bata qwarin gwiwa Kuma alhmdlh tana samun ci gaba Dan ko last
month tare sukaje UK sukaga wani likita Akan matsalar rashin haihuwar ta Wanda
itace ta nuna tanason ganin likita cikin sauki kuwa ya amince Mata sukaje UK
din daga can Sudan suka wuce Saida sukai kusan wata daya kafin suka dawo wanda
tafiyar tasa tafara fuskantar asalin irin rayuwar da mijinta MD ZABEERA takeso
wato rayuwar turai shida iyalinsa Wanda duk wayewarta ita Kuma takasa koyawa
kanta sbd Sam ita saka qananun Kaya basa
gabanta tafi ganin kyan kanta da burge kanta idan ta hade cikin kayanta na
yarenta har gwara dogayen rigunan jallabiya taba sakawa sosai saigashi taga
yanda yake rayuwa kamar asalin bature idan yabar qasarsa wato wasu irin
personalities garesa boyayyu na burgewa ga wasu irin kyawawan manyan 'yan Mata
masu aji dasuke huldar business dashi suna jansa da fira sosai Kuma ba laifi
Yana 'dan sake musu shiyasa ta Raina kanta suna dawowa tafadawa Amatu damuwarta
Wanda hakan ya sanyaya jikin Amatun itama saita Fara zugata akan ta zabure
tafara duk Abinda tafara lurada yanaso tunda harta Fara samun Clue.

No comments