SARAN BOYE 34
No. 34
............Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana na neman zama babba. Dan kuwa dai rikici sosai ke wakana a tsakanin Abdallah da Naser akan Nu'aymah. Amma sai suka canja taku yanda iyayensu bazasu fahimta ba. A duk sanda Naseer yasa aka kira masa Nu'aymah sai Abdallah yazo ya tsare. Hakama duk lokacin da Abdallah ya buƙaci ganawa da Nu'aymah sai Naser yazo ya hana hakan ta hanyar zama tsakaninsu kamar yanda Abdallahn keyi.
Hajjo da mafi yawan rigimar a sashenta
akeyi tana kallonsu amma tai kunnen uwar shegu da su kamar bata ganiba. Wani
lokacinma da biyu take sakawa a nemo mata Nu'aymah ta zauna a sashenta dan
tasan nanne wajen zaman su Naser ɗin musamman da daddare.
Duk kuma wannan abun dake faruwa
Adawiya bata nan, dan kwanansu biyu da zuwa sukai tafiya biki ita dasu Hajarah
dangin kakarsu maman su Addah. Da Addah ta ƙarrafa ayi tafiyar da Nu'aymah ma.
Sai dai yanayin jikinta yasa Hajjo hanawa. Shiyyasa suka tafi su uku harda
Kubrah sai Addahn da sauran ƴaƴanta na ma'auri.
Da farko rikicin nasu Naser nishaɗi
yake saka Nu'aymah, amma ganin al'amarin na sake ɗaukar zafi sai hankalinta ya
fara tashi. Dan neman birkita mata tunani sukeyi har takan rasa wanene yafi
cancanta ta mallakama kan nata?.
Al'amarin bai sake tada hankalin kowaba
a gidan sai randa Hajjo take cema Abdallah dama ya haƙura ya barma Naser
Nu'aymah. Tunda shi a yanzu gashi yana auren su Yusrah. A fusace yace, “Indai
su Yusrah ne zasu masa katanga da mallakar Nu'aymah to lallai zai rusa
katangar”.
Babu wanda ya ɗauki furucin nasa da
muhimmanci a lokacin da yayisa. Sai dai ga mamakinsu bayan sallar isha'i sai
gashi da zungureriyar takarda har guda biyu yazo ya dire gaban hajjo.
Kallonsa tayi fuska a yatsine. “Kai
wannan takardun kuma na miye ka ajiyemin kamar wani ɗan saƙon kotu?”. Fuska a
turɓune yace, “Hajjo sakamakon katangar da kika tabbatar min zata shiga
tsakanina da Nu'aymah ne a ciki. Kinga yanzu sai ki daina min baki ko”.
Sam hajjo bata fahimci zancen
nasa ba, amma sai ta saka Omar dake zaune tare da ita ya duba mata. Ɗaukar ɗaya
yay yana murmushin diramar kakar tasu da yayansu. Da sauri ya fesar da ruwan da
ya ke sha yana faɗin, “What!?” saboda abinda yaci karo da shi a rubuce.
A rikice hajjo tace, “Miya faru
Umaru?”. Jikin Omar na ɓari ya ajiye kofin ruwan tare da ɗaukar ɗayarma ya buɗe.
Nanma dai abinda ke cikin ta farkon ce a ta biyu, ai baima san lokacin daya
furta, “Hajjo wlhy Yah Abdallah ya haukace! ko kuma ya fara shaye-shaye ku
bincika!. Hajjo sakin Yusrah da Adawiya fa ya yi.....”
“Saki kuma?!!” Hajjo ta faɗa itama tana
miƙewa zumbur.
“Wlhy kuwa Hajjo gashi a rubuce saki ɗai-ɗai”.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.
Abdullahi!!. A wlhy gaskiyarka kuwa Umaru Abdullahi ya haukace. Ni Zainabu na
shiga uku. Kaga kiramin ɗan malam duk inda yake yazo gida”.
Ɗan jimm Omar yayi alamar
tunani, sai kuma ya dubi Hajjo da ranta ke a matuƙar ɓace. Cikin lallashi yace,
“Amma Hajjo inaga kamar dai kiyi haƙuri har ya dawo gida. Kinga yanzu bamusan
wane uziri yake kan yiba, kiran da za'ai masa zai iya dagula masa tunani, amma
idan kince a kirasan dai sai na kirasa ɗin”.
“Hakane Umaru! Kaima kayi maganar
hankali, amma lallai sai na saɓama Abdullahi fiye da zato a gidan nan. Wane
irin wawancine wannan? Ashe hankalin da ake ganinsa da shi da girma bashi da
shi ɗin?”.
“Kiyi haƙuri Hajjo, ALLAH ya huci
zuciyarki. Ni kaina ban taɓa zaton hakan daga garesa ba. Kinga wannan ai tushen
ɓata zuminci ne, idan iyayen namu basu kai zuciya nesa ba sai kiga al'amarin ya
kawo ɓacin rai. Sannan su kansu yaran an saka wani abu a zuciyarsu gurɓataccen.
Dan zasu iya tsanar Nu'aymahr da yace dominta yayi, hakan kuma bashi da
amfani”.
Ƙwafa kawai hajjo tayi ranta da
zuciyarta na ƙara mata suya da ɗaci. Omar dai yayta lallashinta har sai da yaga
ta ɗan kwantar da hankalinta sannan ya fice cike da jimami. Sashensu ya nufa,
yaje ya faɗama Momy duk abinda ya faru.
Sosai itama ta rikice hankalinta ya
tashi. Dan ta tabbata Abbansu dama wasu a mutanen gidan bazata fita da ga
zarginsu ba, musamman ma da akasan taso ya auri ɗiyar ƙanwarta. Waya ta ɗauka
ta shiga neman Abdallah. Sai dai harta tsinke bai ɗagaba. Bata gajiya ba wajen
cigaba da jera masa kira, amma yaƙi ya ɗaga.
Hajjo, Omar, Momy sun yi yinin
yau ne cikin tashin hankali da damuwar ɓarnar da Abdallah ya tafka. Duk da sun
ƙagara Baba malam ya dawo gidan ransu cike yake da fargabar sakamakon da zai
biyo baya kuma.
Sai bayan sallar la'asar baba
malam da Abban Abdallah suka dawo gidan. Dan dama tare suka fita. Sunje wani
ƙauyene akan maganar wata katafariyar gona da zasu saya. Sunason gyarata su
maidata gidan gona a zuba dabbobi kala-kala na kiwo a ciki. Wannan ma ne
dalilin da yasa har yanzu shi da Abba Musbahu basu koma ba. Suna son sai komai ya
kammala sannan su ɗauka iyalansu su koma inda suka fito sai kuma biki.
Kamar yanda al'adarsu take ta
fara shiga sashen mahaifiyarsu yau ma hakan suna fitowa daga mota can suka
nufa. Yanda suke tafe suna firarsu kowanne fuska ɗauke da fara'a dolene su
matuƙar burgeka. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci ɗunbin shaƙuwa da ƙaunar juna
dake a tsakaninsu.
Sai da sukai sallama Hajjo da ke zaune
cikin ɓacin rai har yanzu ta amsa musu da basu izinin sannan suka shiga. Kallo ɗaya
sukai mata suka fahimci tana cikin damuwa. Kusan da sassarfa duk suka ƙarasa
gareta kowanne na tambayarta tana lafiya?.
Batai magana ba, sai wajen zama
data nuna musu. Sai dai maimakon su zauna a kujerun sai suka zauna ƙasa tamkar
yanda suka saba. Gaisheta sukayi, sannan suka sake jero mata tambayoyi akan
yanayin nata.
Ƙwallar da suka cika mata idanu tasa
bakin ɗan kwalinta ta share. Hakan sai ya sake tada musu hankali.
“Inna dan ALLAH ki faɗa mana minene ke
damunki? Mune mukai muki laifi? Ko matan mu? Kokuwa a cikin yaran nan ne wani
yay miki wani abu?”.
Sake share hawayen data matso
tayi da cewar, “Ni babu abinda kukai min ɗan malam, Abdullahi ne kawai keson
watsa mana gida”.
Hankali a tashe baba malam da Abban su
Abdallah suka kalli juna. Cikin ƙarfin hali baba malam yace, “Innah mi
Abdallahn ya aikata?”.
Takardun da Abdallah ya rubuta ta
ɗakko ta miƙa musu. Amsa sukayi kowanne ya buɗe guda ɗaya gabansa na faɗuwa. A
tare suka ɗago a razane suka kalli juna da ambaton sunan ALLAH. Baba malam har
yana tsallaken kalma wajen faɗin, “Innah shi Abdallah ɗinne ya rubuta wannan
takardar?”.
“Shine ɗan malam,
shine da kansa ya rubutasu ya kuma kawo mani. Wai dan kawai jiya na bashi
shawarar cewar yay haƙuri ya barma Nasiru Zainabu tunda shi yanzu yana da
matansa har biyu. Shine fa yau ya kawomin takardar sakinsu Adawiya wai gashinan
ya rushe katangar dana ce masa tana tsakaninsa da Zainabu”.
Abba da ya gaza cewa komai tun ɗazun
yace, “Innalillahi..., wai inna kina nufin su duka biyun ya saka?”.
“Eh mana Lurwanu, baga takardun nan ba
duka biyu na baku”.
Da sauri baba malam ya amshi ta hannun
Abba, shima ya karɓa ta hannunsa. Da gaske kuwa su duka biyun ya saki. A take
tsananin ɓacin rai ya sake bayyana a kan fuskokinsu. Abba ya miƙe a fusace zai
fice. Kiransa baba malam ya shigayi amma ina zuciyar gadon ta motsa. Dan haƙuri
kawai ya bashi batare da ya juyoba ya fice.
Momy na zaune cikin
damuwa da fargabar jiran dawowar mijinta Abba ya shiga. Jiki a sanyaye ta
dubesa dan ko sallama baiyi ba
Takardun guda biyu ya watsa mata a jiki.
“Da saninki ɗanki yay wannan aika-aikar ko?”.
Gaban Momy na faɗuwa ta ɗauki takardun
ta karanta, hawayen da taketa faman dannewa tun ɗazun suka zubo mata a saman
kumatu. “Wlhy Abban Abdallah ban sani ba. Nima ina zaune Omar yazo yake
sanarmin. na kirashi yafi sau hamsin amma ya ƙi ɗagamin waya ma, kai........”
Baki ya buɗe zai daka mata tsawa Omar da ya
shigo basu sani ba yace, “Abba wlhy babu ruwan Momy, hasalima batasan komaiba
akan al'amarin nan sai da nazo na sanar mata. Abba ko kasan dama tunda Yah
Abdallah ya dawo gidannan baiyi zaman minti biyar da Momy ba. Da ya shigo ya
gaidata da safe bazata sake ganinsa ba sai washe gari. Fushi yake da ita babu
gaira babu dalili. Ta sakani na tambayesa amma yacemin idan na sake zuwa masa
da zancen Momy sai ya ɓatamin rai. Ita kanta nace zan sanar maka abinda ke
faruwa amma ta hanani, wai mu bashi lokaci kozata fahimci abinda ke damunsa”.
Jikin Abba ne yay sanyi, dan
tabbas kuwa ya kula tunda Abdallah ya dawo ƙasar nan bai taɓa ganinsa zaune da
Momy ba, da farko yaso tambayarta sai kuma yayi tunanin ƙila sai ya fita suke
zaman. Wannan ya sakashi yin shiru duk da kuwa yasan yanda matar tashi take da
ƙulafucin ƴaƴa musamman Abdallah.
Nannauyan numfashi ya sauke tare da zama yana
cire hular kansa ya ajiya.....
A ɓangaren baba
malam kuwa Abba na fita waya ya zaro ya shiga neman layin Abdallah. Sai dai
kuma abin mamaki switch off. Ajiye wayar yayi ya maida hankali ga Hajjo da ke
sharar hawaye har yanzun. Kwantar mata da hankali ya shigayi da bata haƙuri.
Yace, “Inna ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, insha ALLAHU mu dai wannan
bazai kawo mana rabuwar kawuna ba. Duk inda Abdallah ya shiga kuma na tabbata
zuwa dare dole ne ya dawo gida ya kwana ai, insha ALLAHU a daren nan sai ya
maidasu su duka biyun”.
“Ɗan malam bazaka gane abinda
nake nufi ba, amma duk yanda kake tunanin sauƙi a al'amarin nan da wahala ya
kasance hakan. akwai abinda na sani wanda kai da sauran ƴan uwanka baku san da
shi ba a gidan nan. Ina barin masu aikatawar ne kawai kafin ranar da zan masu
bankaɗa da tonon silili a gaban kowa. Ni dai abinda zan sanar maka yanzu shine
da ga Abdullahi har Nasiru ka zaunar da Zainabu ta zaɓi wanda tafi so tunda abin
ya zama haka. Kokuma ta auri wani bare can a zauna lafiya. Sannan inason ka
nutsu kayi tsai da hankalinka a wannan karon game da kowa a gidannan, koda baka
fahimci duka abinda na fahimtaba zaka fahimci wasu daga ciki. Dan kai ne uba a
gidan nan, duk da dama nauyi da girman ya rataya a wuyankane tunbayan rasuwar
mahaifinku, ina kuma alfahari da yanda ka riƙe hakan, amma sai randa ƙasa ta
rufe idanuna zaka sake tabbatar da girman dake bisa kanka da tarin fituntunun
da ke kwance a cikin gidannan wanda ALLAH ne kawai hanasu fallasuwa saboda
rahamarsa da ikonsa da kuma ƙarfin addu'ar mahaifinku da har yanzu take biye da
ku. Kai dai ALLAH ya ƙara maka haƙuri da juriya kawai. Tashi kaje ka huta, ka
kumayi ƙoƙarin tausar sauran ƴan uwanka akan duk ma abinda zai iya biyo baya
game da wannan gagarumar fitinar da Abdullahi ya ɗaɗɗago mana”.
Kasa cewa komai baba malam yayi.
Cike da ruɗanin maganganun Hajjo ya jinjina mata kansa kawai da miƙewa ya fice
zuwa nasa sashen. Bai iske kowa a falon ba sai Muhammad dake karatun Al-Qur'ani
na haddar da aka basu a islamiyya. Yaron bai dakata daga karatun da yakeyi ba,
shima kuma bai masa magana ba ya wuce ɗakinsa.
Komai tsaf a gyare kamar yanda
ya saba zuwa ya iske, ga ƙamshi mai daɗi. A ɗaya daga kujerun ya zube hankalinsa
har yanzu baya tare da shi. Dan ransa da zuciyarsa cike suke da tarin ruɗanin
kalaman mahaifiyar tasu. Shi kansa yasan akwai abubuwan dake kwance a gidan nan
ƙwarai da gaske. Waɗanda da yawansu shi da iyalinsa sun cutu matuƙa a cikinsu.
Koma yace suna kan cutuwa. Ya kumayi imani da ALLAH babu wani baƙon ido daga
waje da zasuce yana aikata su, dolene mai aikatawar a cikin zuri'arsu yake.
Yasha yin tunanin tsananta bincike, amma sai zuciyarsa ta gargaɗe sa da yin
haƙuri, sannan yana mai tsananin jin tsoron wanda sakamakon ɓarnar zata tabbata
a garesa. A ganinsa gara kawai a cigaba da tafiya a lulluɓen dan UBANGIJI mai
ji ne kuma mai ganine akan kowa da komai..........
Taɓa shin da akayi ne ya saka
tunaninsa katsewa. Duban Umm da tun ɗazun take masa magana yay. Fuskarta cike
da damuwa tace, “Malam lafiya kuwa? Wane irin zurfafa tunanine haka? lna fatan
dai lafiya ko?”.
“Humm! Jannat lafiyar nan
da dauƙi”.
Saurin zama tayi hannunta riƙe da kofin
data zuba masa ruwa tana faɗin, “Miya faru?”.
Ruwan ya fara karɓa ya sha, ta sake
ƙara masa ya shanye sannan ya ajiye kofin ya labarta mata duk abinda ya faru,
harma da zancen da Hajjo tai masa.
Duk da itama ta jima da ji
a ranta duk abinda Hajjo ke zargi a kwaishi a gidan hakan bai hanata jin tashin
hankali ba. Ita kanta tanason sanin mai aikata musu SARAN ƁOYE a lokuta da
dama. Sai dai tsoron wanda zata gani yana aikatawar ke sakata sama ranta haƙuri
da barin komai hannun UBANGIJI.
★★★★
A yau dai har dare Abdallah
bai dawo gidanba duk jiran da su baba malam sukai zaman yi masa. Dole suka
haƙura suka kwanta al'amarin nacin ransu da zuciya.
Washe gari bayan fitowa sallar
asuba baba malam da sauran ƴan uwansa suka hallara gaba ɗaya a sashen
mahaifiyarsu. Bayan sun gaisheta suka sake haɗuwa gaba ɗaya wajen bata haƙuri
akan abinda Abdallah yayi, suka kuma tabbatar mata insha ALLAH zasu dai-daita
komai ba sai yayi tsamari ba.
Batace da su komaiba dai, sai dai
ta musu addu'ar nasara da nemawa Abdallah dama sauran yaran shiriya gaba ɗaya.
A wannan yinin maganar sakin ta
shiga kunnen kowa dake a gidan ciki harda Addah da yaranta dake can suna shan
biki. Aiko ba ƙaramin rikita musu lissafi Adawiya tayi ba. Dole babu shiri suka
tattaro suka nufo kano zuciyar kowa babu daɗi.
Tunda saƙon saki ya isa kunnen Yusrah
kuwa sai wani tarin farin ciki ya kamata. Bama tasan lokacin data shiga dirga
tsalle akan gadon ɗakinsu ba. Kafin ta sakko da sauri ta shiga bayi ta ɗauro
alwala. Salla tayi raka'a biyu na godiya ga ALLAH daya kawo ƙarewar wannan aure
da ko tarewa batayi ba a cikinsa. Dama tunda su Adawiya suka diro ƙasar bata da
wani sukuni. Shiyyasa ta koma yinin makarantar Tahfiz ɗin gidansu dan kawai ta
gujema ganinsa. Hakan kuwa akayi, dan tunda suka iso sau biyu ta haɗu da shi.
Ɗaya da daddare ya shigo sashensu wajen Abba. Na biyu kuma a sashen hajjo taje
kai mata abinci. Duka a haɗuwar tasu gaisuwa ce kawai ta shiga tsakaninsu.
Yanda baya sakar mata fuska itama bata shiga sabgarsa sam, dan baya wani nuna
alamar akwai ko ɗigon haƙƙinta daya rataya a kansa ma. Hakan kuma bai dameta
ba, to gashi cikin amincin ALLAH komai ya zama yanda taketa fata a kullum. Ba
ƙaramin azumi da ƙiyamullaili tayi ba akan auren nan a cikin watannin nan. Dan
ita kaɗai tasan dalilin rashin son auren.
Duk wannan ruguɗai da akeyi
Nu'aymah batasan anai ba ita kam, dan Umm da baba malam babu wanda ya sanar
mata. Sashen Hajjo kuma yanzu ba wani shigarsa takeba sosai saboda takurawar
Nasir da Abdallah da suka maida sashen hajjo wajen zamansu. Ta gwammaci taita
zama a sashensu, idan Muhammad na gidan susha shirmensu, idan kuma ya fita
makaranta tayi kallo idan akwai wuta ko su zauna hira da Umm. Wani lokacin kuma
tai barcinta dan Doctor ya ce ta dinga yawan barci, shiyyasa ma ya saka mata
maganin barci a magungunanta.
Yauma tana a ɗaki
tasha barcin rana har su Adawiya suka dawo bata saniba. Ta fito wanka tai
sallar la'asar, shiri ta farayi da ƙudirin zuwa islamiyya yau dan tanajinta
Alhmdllh. Tana tsaka da saka kaya ta jiyo kururuwar kuka kamar muryar Adawiya
kuma. Saurin ƙarasa saka kayan tayi ta fito, a mamakinta duk ma sai ta iske ƴan
gidan a tsakar gida kowa ya fito an rufu kan Adawiya. Gabantane ya faɗi da
tunanin ko Accident sukayi a hanya. Da sauri ta shiga bin kowa da kallo sai
taga kowa ma yana nan, harsu Aunty Aysha ma basu wuce gidajensu ba nan sukayo.
Kallon Jafar dake kusa da ita tayi tace,
“Jafar miya faru wai?”.
“Aunty Nu'aymah ban saniba nima. Kawai
dai naga Aunty Adawiya na kuka tana cewa wai indai aka rabata da Yah Ab zata
mutu”.
Kafesa da kallo Nu'aymah tai tana
son fassara kalaman nasa amma sunƙi fassaruwa. Dubanta ta kai ga Umm dake lallaɓa
Adawiya taje sashensu amma taƙi, hakan ya sake tabbatar mata da lallai ba
lafiya ba kuwa. Baba malam daya shigo gidan yanzunne ya dakama Adawiya tsawa.
Jiki na rawa ta miƙe tsaye.
“Wane irin rashin hankaline wannan tun
daga wajen gate anajin muryarki, tona mana asiri zakiyi da shirme ko mi?. To
wlhy bara kuji bama ita ba duk wanda na sakejin bakinsa a wannan maganar saina ɓata
masa rai, naga dai Abdallahn a ƙarƙashin ikonmu yake shima, dolene kuma yabi
abinda mukeso inhar yana buƙatar gamawa da rayuwarsa lafiya. Kowa ya shige
ciki”.
Jan ƙafa kowa ya shigayi zuwa
sashensa. Kubrah ta kama hannun Adawiya suka shige tare. Inda suka bar Addah da
bata fitaba nan suka isketa zaune. Babu wanda taima magana a cikinsu har suka
zazzauna kowa na ƙannun magana. Batace musu komaiba dai har lokacin, saima
jingina da tai da kujera ta lumshe idanu.
Nu'aymah suna shiga
sashensu ta shiga tambayar Umm abinda ke faruwa. Dan ita harga ALLAH bata
fahimci komaiba dai har yanzun. A taƙaice Umm ta faɗa mata, sai ko ta zabura a
matuƙar razane. “Ya salam. Umm Yah Ab kuwa yana da hankali?! Wannan ai gogama
mutane sharri ne da zai ce saboda ni ya aikata saki ga matansa”.
“Wannan sakaki a cikin da
yayi shine ya sake tada mana hankali muma Nu'aymah. Dan zai iya zama wata
fitina daban wadda ba'asan iyakar inda zata tsaya ba a gidan nan. Yanzu dai
Abbanku ya gano inda yake, ya kuma bashi daga nan zuwa kwana uku idan bai dawo
gida ba zai haɗu da ɓacin rai mai tsanani daga garesu”.
“Ai gara yazo ya kwance
wannan ƙullin da yay min nikam, a dalilin mi zai sakani tsakkiya, a barni da abinda
ya damenima nikam ya isheni Umm”. Tai maganar tana fashewa da kuka.
Tausayinta ne ya kama Umm sosai,
ta ruƙo hannunta ta sakata jikinta tana lallashi............✍

No comments