MIN QALB 34
MQ 34_*
Fuska kawu ya sake bayan isowar MD yace"
MAHMOUD sannu da qoqari mungode sosai Allah yasaka yayi muku albarka duk ku duka Allah yaji qan Khalilu yayi Masa rahama tareda albarkar Abinda yabari a baya.
Amin kowannensu yace jiki a sanyaye kafin umme ta Dora da
fadin"
MAHMOUD kayi Magana da kawu Dan Allah yabar Amatu harta
haihu tukuna ayi maganar tafiyarta.
Miqawa zarah takardar dake hannunsa Wanda Fatima tabayar
kafin ya kallesu cikin rashin son Jan dogon zance yace"
Kutafi zamuyi mgn da kawun Zan wuto da ita idan angama.
Kallonsa umme tayi tana miqa dukkanin yardarta akan cika
maganarsa na zai dawo da Amatun zabeera idan sun barta.
Ahankali ya gyada Kai Yana Dan rufe Ido.
Kallon Amatun umme tayi jiki a matuqar mace tace"
Ina jiran dawowarki Amatu.
Gyada Mata Kai tayi tana murmushin Bata qwarin gwiwa kafin
ta kalli anty zarah da ita tayi wani iri tace"
Anty ZARAH saki fuskan Mana saikace Rabin ranki ne akace
za'a tafi dashi.
Guntun murmushi anty zarah din tasake tana Dan hararar
Amatun tace"
Kina tunanin MAHMOUD zai barni yatafi wani gurin bayan
tafiye tafiyensa?
Kece dai abin jimamin sbd ba'a shiga Zabeera family a fita
saidai mutuwa""taqarasa tana dariyar Amatun qasa qasa.
Tafiya sukai suka bar Amatun taredasu iyami dasu kawun Nan
kawun da MAHMOUD suka kebe sukai magana sai gashi sun wuce a motar Salman sun
barta tareda MAHMOUD din
Batareda yayi Mata kallo biyu ba ya nufi motarsa bayan yace
suje.
Drivernsa ita yafara budewa mota tashiga kafin ya zagaya ya
budewa MD din yashiga ya rufe yafada motar shima ya tayar sukabar gurin.
Jinginar da kanta tayi baya tareda lumshe ido ta sauke
numfashi ahankali sbd imperial majesty dinsa daya gaurayu da AC dakuma qamshin
motar saiyake Bata nutsuwa sbd dadinsa.
Shikuma wayarsace datai ringing ya dauka yafara waya cikin
nutsuwa a harshen turancin dayasata Dan bude Ido kadan ta saci kallonsa sbd ya
tuno Mata da Dr khalil dinta idan Yana turanci zaunawa takeyi ta zubawa bakinsa
Ido cikin burgewa da son koya sbd abin na matuqar burgeta tana sha'awar zama
Yar gayun Yar Boko me zuba turanci Wanda tasan da Dr na Nan da yanzu tafara
karatu Inshallah.
Ajiyar zuciya ta sauke afili Wanda yasashi Dan waiwayowa
kadan ya kalli gefenta kafin yaci gaba da wayarsa.
Har bakin qofar palonsu motar ta tsaya direban yafito da
sauri ya zagayo ya bude Mata batareda ta juyo ta kallesaba tace"
Nagode""ta fice ta shige palon tana sauke numfashi
sbd atakure take cikin motar ko dogon motsi bakada ikon Yi kamar an takura Masa
ne shiyasa ko matarsa zarah wata ran basa kwana tare sbd yawan juye juyenta da
motsi Wanda ke hanasa bacci ko kadan hakan Kuma na saka Rabin kansa ciwo.
A palon ta tararda anty salamatu na qoqarin ajiye abincinda
tafito dashi daga kicin akan dinning itada shafa'atu me aikinta.
Wecewa tayi dakinta Kai tsaye tayi wanka da ruwan dumi sosai
kafin ta fito ta sanya jallabiya tayi sallar magriba da akayi suna hanya tayiwa
mijinta addua sosai cikin farin ciki da walwala take sbd cikin jikinta ya dawo
da duk wani farin ciki datake tunanin ta rasa Dan kuwa Dr khalil dinta Jin take
kaman yadawo sbd tasamu Abu mafi soyuwa daga garesa.
Shafa cikin tayi bayan ta miqe ta zauna bakin gado ahankali
ta tuno da cikin qaryarsu Wanda shauqin abin alokacin yayita shigarsu itada Dr
Ashe ita kadai zata qarar da zuwan ranar,
Idan namiji na Haifa baida sunan daya wuce na mahaifinsa
inshallah.
Wayartace tayi ringing ta juya ta kalla screen din wayar
taga sunan USI
Tasaki murmushi me Fadi tana daukar wayar kusan atare
sukace"
Lallaima.
Dariya suka saki lokaci daya Jin bakinsu yazo daya
tace"
Allah USI nakusa gayawa kawu ya yafewa Yan can Kai,
Yanzu duk yinin yau sai yanzu kake kirana.
Dadina dake masifa ko numfashi bazaki Bari mutum ya saukeba,
Yaya jikin to?
Nayi waya dasu kawu yace ansallameki sunkoma gida.
Eh da magribar Nan nadawo.
Amah nayi Magana da kawu akan Zaki koma gida sbd zaifi Mana
sauki harzuwa lokacin haihuwarki tunda ko haihuwa Kikai bana sakaran zasu karba
Abinda aka Haifa din saiyayi wayo sosai kokuma idan Zaki koma makaranta
Dagani har kawu Amatu karatu yanzu mukeson kiyi.
Numfashi ta sauke tareda gyara zamanta tace"
USI Nima naso komawa gidan saidai Kuma yanada wuya su Bari
nabar Nan din shiyasama kawai nabari Bayan haihuwar saina koma gida tunda koba
komai Ina haihuwa na fita takaba ba sauran dalilin zamana anan din Amma dai
kawu yace zaizo gobe zasuyi Magana dasu Modibbon idan sun Bari din zankoma
gidan idan Kuma sun buqaci na zauna harna fita takaban duk Babu illa tunda dai
lokacin zaizo.
Numfashi ya sauke cikin nutsuwa yace"
To Allah ya saukeki lafiya shine fatanmu akan komai.
Amin ya furta afili kafin suka shiga cikin zancen karatunsa
dayayi nisa yanzu gashi Yana bada himma sosai Dan tuni ya goge cikin masu
qoqarin makaranta.
Da daddare umme da kanta tazo tayi musu fira har kusan qarfe
goma kafin ta tafi anty zarah dai ce Bata sake gani ba sai washe gari anacan
ana soyewa da Rabin Rai.
Washe gari qarfe goma sha daya na Rana kawu ya iso zabeera
tareda Dr Salman dayaje ya daukosa akan maganar komawar Amatu gida
Dama Suma su Modibbon suna jiransa sbd tun jiyanma da
MAHMOUD yayi musu bayanin Abinda kawun ya buqata sukaso zuwa har gida su samesa
tun cikin Daren saigashi yace yace zaizo a yau din.
Babban palon Andi suka Isa inda andin da Modibbo ke jiran
isowar kawun
Gaidasu kawai dr Salman yayi ya ficewarsa ya barsu suka Fara
tattaunawa.
Cikin nutsuwa Andi ya kalli kawu zaifara Magana saiga MD
yashigo batareda yasan kawunma naciki ba.
Cikin nutsuwarsa da girmamawa ya gaidasu tareda sanarda
Modibbo zaiyi tafiyane yau takamasa Kuma zai kwana biyu kafin yadawo.
Kallonsa Andi yayi cikin nazari harya miqe zai fice
yace"
MAHMOUD dawo ka zauna Magana zamuyi akanka da Dan uwanka
marigayi tareda Abinda yabari.
Maida kallonsa yayi Kan kawu cikin nuna Masa girma
amatsayinsa na mahaifin 'yar dasuke son abarta cikin zuriar 'ya ko 'dan da zata
Haifa yace"
Mal Saleh tun jiya nakejin saqonka bakin MAHMOUD
Da tun jiyan mukaso ganinka saikuma dai muka Bari yau din
tunda yace kace zakazo din akan maganar,
To Mal Saleh munji zancenka amatsayinka na mahaifin
AMATULLAH Kuma bamu katsi hanzarinkaba amma maganar barin AMATULLAH kwata kwata
zabeera Bata tasoba sbd koba komai dai ga rabo Nan ya ratsa a tsakani Kuma
bayan hakan ma tun asali zabeera shiyasa ba'a auren waje sbd irin hakan duk da
qaddara ce da Babu me gujewa saidai kuma tunda AMATULLAH tashigo zuria mezaisa
ta futa Dan mijinta ya rasu bayan munada Wanda zai Kare mutunci da haqqin
iyalin 'dan uwansa ko ayanzu da babu ran nasa?,
Mal Saleh Kai ubane,bazaka so 'yarka Takoma gabanka ta Dora
sabon zama na zawarci duk da Allah ne yaso hakan shiyasa muke fatan kaima kazabi
barin 'yarka a killace cikin inuwar aure sabanin komawarta gabanka,
'yayanmu idan mazajensu sun rasu suna fita takaba da
qanqanin lokaci muke aurar dasu ga Yan uwa mafi kusanci na mazajensu sbd dorewa
acikin aure shiyasa ba alfahariba bamada tarin zawarawa acikin zuria sbd
zawarcin ba Dadine dashiba,
Maganar aure ga me takabar dake cikin takaba haramun ne
shiyasa bazamuyi maganar auren AMATULLAH ayanzu ba Amma dai muna roqonka a
matsayinka na mahaifin AMATULLAH daka barta anan tayi renon cikinta ta haihu
bayan haihuwarta zamu nemawa Dan uwan mijinta mafi kusanci agaresa aurenta wato
MAHMOUD Wanda Inshallah aranar sunan Abinda ta Haifa tareda radin suna zamu
daura musu aure Inshallah idan harka bamu dama tare Kuma da amincewa.
Numfashi me qarfi kawu ya fitar a fili tareda jinjina Kai
sbd shima kamar yanda suka fada duk duniya Babu ubanda zaiso yarsa tadawo
gabansa ta zauna ta dasa sabon zaman zawarci sai abisa qaddara,
Qaddara ce ta saukarwa Amatu Kuma Dole sunkarba hannu
bibbiyu saidai tunda tasamu wani tayin auren gskia bazaiqi amincewa ba tunda
dama suna tunanin tattarawa ne subar gidan sukoma inda Amatun zatafi sakewa da
Abinda zata Haifa to tunda har mutanen nan na qaunarta harda basa iya barin ta
fita wani gurin dabam tayi aure Babu Abinda yafi Masa wannan saidai tunda ba
halaccin maganar neman aure akanta ayanzu zai tafi da ita still idan lokacin
haihuwarta yakusa tunda zata dawo daga baya.
Aje numfashi yayi tareda koro musu nasa bayanin bayan
amincewarsa akan idan takusa haihuwa Zata koma gida ta haihu gaban uwarta.
Ba wani dogon sharhi suka amince akabar maganar akan Babu
Wanda za'a sanarwa yanda aka aje zancen sai bayan haihuwarta idan lokacin
Daurin auren yayi.
Komai bai iya cewa ba sbd zancen baiyi Masa Kama da zai yiyu
dinba idan har za'a tambaya ra'ayinsu kafin Daurin auren idan lokaci yayi.
Sallama yayi musu tareda 'yar godiyar da batakai cikinsa ba
ya fice Yana duba agogon hannunsa sbd yakusa lattin Isa airport.
##Mamuh#

No comments