SARAN BOYE 31
No. 31
..............Ta ƙaramin gate Yoohan yay ficewarsa. Hakan
yasa Kubrah data biyo bayansa ta rasa ina ya nufa. Har babban gate taje bayan
ta gama dube-dube a harabar gidan bataga wata baƙuwar mota ba duk saina ƴan
gidan.
Yanda ta iso gate ɗin a rikice tana tambayar maigadi sai abin ya bashi mamaki. Amma sai kawai ya bata amsa da cewar babu wanda ya fita.
“What?! Yama zakace dani babu
wanda ya fita a gidan nan? Bayan nasan tabbas idan ba fitaba babu inda zai
nufa”.
“Hajiya Kubrah wlhy babu wanda ya
fita kamar yanda na sanar miki. Shin kodai ɓarawo ne ya shigo gidan ban sani
ba?”.
Wani takaicine ya sake tuƙe Kubrah,
batare data bashi amsaba ta bar wajen tana zuba masa harara. Shima tsit yayi
bai sake magana ba, sai dai zuciyarsa fal saƙe-saƙe.
★★★★
Yoohan na fitowa
waje yay turus dan mamakin ganin motocin gidansu da alamu suka nuna tsayawarsu
kenan. Dan yanzu suke ƙoƙarin fitowa. Mamaki yay masifar sake kamashi ganin
papa harda d.p.o Emanuel da yaransa. Tsuke fuska ya sakeyi ya nufesu ganin
yanda suka tafi kai tsaye ga gate ɗin gidan dan su basu ganshi ba.
“Papa!” ya faɗa dai-dai lokacin
da papa ya kai hannu zaiyi knocking gate ɗin. A kusan tare duk suka juyi garesa
domin shigar muryarsa mai amo da kauri cikin kunnuwansu.
Wata wawuyar ajiyar zuciya suka
shiga saki a jajjere, musamman ma guards ɗin Yoohan da suka san suna a cikin
gagarumin tashin hankali inhar ba'a samesa anan ɗinba.
Papa har yi yay tamkar zai kifa
dan saurin zuwa ga Yoohan ɗin. Yay wani bala'in rarumosa jikinsa ya rungume
yana faɗin, “Thanks you lord. my son are you okay?
“Yes Papa! What is happening? Mi
kakeyi anan? Miya kawoka kano?”. Yoohan ya jerama papa tambayoyin yana zare
jikinsa daga nasa tare da bin guards ɗinsa da ƴan sandan dake zagaye da su da
kallon tuhuma suma.
Sake jawosa jikinsa papa yayi,
batare daya bashi amsar ko ɗaya daga tambayoyin ba, ya shiga duba jikinsa sama
da ƙasa kamar mai tunanin an masa wani abu. Sai kuma ya kama rigar shaddar
jikinsa yana faɗin, “Yoohan minene wannan?”.
Wani irin luuuu da idanu Yoohan yayi
tare da huro iska daga bakinsa. Cikin ƙosawa da abinda ke faruwa yace, “Papa
kaya ne mana. Wai mi kukeyi anan wajen ne? Miya kawoka kano?”.
Cikin
tsananin nuna ɓacin rai papa yace, “John! Yau kaine da kayan hausawa a jiki?
Mike damun kanka da tunaninka?”.
Sake shiga wani takaicin shima Yoohan ɗin
yayi, dan a take fuskarsa ta sake nuna fusata. Tayaya yana tambaya amma batare
da an basa amsaba papa kuma na masa wasu tambayoyi mara kangado sai kace wani
ƙaramin yaro. A tsawace ya kalli su Solomon da faɗin, “Mi kukazo yi anan
nace?!!”.
Yanda ya daka tsawar basu Solomon
kawai ba, hatta Emanuel da yaransa duk da suke ƴan sanda saida suka razana.
Balle kuma ƴan anguwa da suka fara taruwa kallo. Gashi Yoohan yayi maganar ne
da yare.
Solomon ne cikin rawar jiki data
baki ya fara masa bayani,
“Sir! Dama mun zata ko wani abu mara
ƙyaune ya sameka. Tunda muka tashi muka fahimci baka a cikin hotel ɗin. Gashi
an duba ko ina amma babu alamarka. Ma'aikatan kuma duk sun tabbatar mana basuga
fitarka ba, ga kuma wayoyinka mun samu baka fita dasu ba. To shine mukai
tunanin ko anyi kidnapping ɗinka ne shine muka kira boss muka sanar
masa.......”
“To da kuka kawosu nan, sune
sukai kidnapping ɗin nawa kenan?”. Yoohan ya faɗa cikin katse Solomon.
Kasa bashi amsa Solomon yayi, dan harga ALLAH
ba ƙaramin gulma da munafincin su baba malam sukai wajen papa ba akan gaba ɗaya
sun janye ra'ayin Yoohan ɗinma, amma sunyi bakin ƙoƙarinsu suga tun a zuwan
farko bai sake zuwa gidanba sai dai hakan ya gagara. Kuma jiya a yanda suka bar
gidan yana cikin wani yanayi yasa sukai suspecting ɗin kosu baba malam ɗinne
suka turo aka saceshi. Shiyyasa papa na isowa maganar gidan suka fara faɗa
shiyyasa yace su kawosa.......
★★
Baba malam da
Kubrah kusan a tare suka shiga falon. Shi ya fitone wajen Yoohan ɗin dan
yanason su tattauna ta yanda ya kamata Yoohan ya fara neman ilimin dazai
taimakamasa wajen bautar ALLAH. A tunaninsa zuwa lokacin ya kammala cin abincin
da Nu'aymah taje kai masa. Dan rashin dawowar tata baisa sun zargi komaiba da
ga shi har Umm. A tunaninsu ko bayan takai masan ta shiga sashen Hajjo ne ko
kuma Addah.
Da sauri ya ƙarasa ga N'aymah
daya hango ƙasa wanwar, ga kuma falon babu alamar Yoohan ɗin sai ƙamshin
turarensa kawai. Tiren abincin data kawo yana a ajiye a inda ta ajiyesa.
“Ya ALLAH! K lafiya kuwa mamana?
Mikikeyi kwance anan haka?!”. Baba malam ya faɗa yana kai hannu ga Nu'aymahn.
Da sauri ya zabura dan jin jikinta yayi sanyi ƙalau ya saki. Yay azamar maida
yatsunsa biyu wajen ƙofar hancinta. ‘tabbas bata numfashi’ ya ambata a
zuciyarsa yana ɗagota gaba ɗayanta.
Hakan yayi dai-dai da ƙarasowar Kubrah
da tun shigowar baba malam tana biye da shi, sai dai shi bai gantaba sai yanzun
data ƙaraso garesu da dauri tana faɗin, “Abbah lafiya? Miya faru da ita ne?”.
Cikin tashin hankali baba malam
yace, “Ban saniba nima Khadijah, kinga miƙo ruwa dan bata numfashi”.
A hanzarce ta ɗakko masa ruwan da Yoohan yasha
ya bari, ya miƙa hannu ta tsiyaya masa. shafama Nu'aymah yay a fuska. sai dai
ko motsi batayiba balle ai tunanun zata farko. Hankalin baba malam ne ya sake
tashi matuƙa. Ya ɗago idanunsa da sukai jajur ya kalli Kubrah.
“Khadijah maza kiramin Ahmad ko
malam ƙarami ko Omar. duk wanda kakaci karo dashi cemasa ya fiddo mota”.
Amsawa tai da to tana fita da sauri.
Sai dai maimakon ta wuce aiken da akai mata saita samu waje ta laɓe abinta tana
wani taɓe baki da sakin murmushin mugunta. Zuciyarta fes take akan halin da
Nu'aymahr ke ciki. Ita ta mutu kota rayu hakan ba damuwarta bace a yanzu. Dan
ita kaɗai tasan miyasa take bala'in jin zafin yarinyar.
Baba malam da baisan Kubrah bata tafi
aikansa ba ya ɗakko Nu'aymah gaba ɗayanta ya fito. Da sauri Kubrah data hangosa
ta sake maƙewa tana zaro ido waje. dan batai tunanin baba malam zai fito da
Nu'aymah ba yanzun, a tunaninta ko saita kira ɗaya daga cikin wanda ya aiketan.
Oho shi hankalinsa ma bai kai gareta ba.
Jikinsa na tsuma bakinsa na ambaton ALLAH ya nufi harabar gidan. cikin sa'a
kuwa sai hakan yay dai-dai da fitowar malam ƙarami daga sashin su Kubrahn
hannunsa ɗauke da leda da key ɗin mota.
“Abba lafiya? Miya sameta?”. Malam
ƙarami ya faɗa a ruɗe yana nufo baba malam dake ɗauke da Nu'aymah.
Da sauri baba malam ya bashi amsa da,
“Maza buɗemin mota malam ƙarami, yanzu ba lokacin sanin mafari bane ba”. Cikin
sauri malam ƙarami ya cika umarnin baba malam. ya karasa ga motarsa ya buɗe.
Baba malam na ƙoƙari sakata a ciki Kubrah ta ƙaraso wajen. Tamkar an kira Hajjo
sai gata itama ta fito daga sashenta ita da Husnah da alama ma fita zatayi.
A rikice ta nufesu tana tambayar
ba'asi. Dan taga yanda baba malam ya saka Nu'aymah a motar tamkar bata da rai.
Babu yanda baba malam ya iya dole yayma Hajjo bayani a taƙaice. Kubrah na
ƙoƙarin shiga motar dan a tafi da ita Hajjo ta tureta gefe ita ta shi. Yayinda
Husna ta ƙirƙira cikin gidan da gudu tana ƙwalama Umm kira tana kuka. Dan ita a
zatonta Nu'aymah kota mutune. Yarinyace ƙarama bata wuce 9years ba. Itace autar
amaryar Abbah Musbahu.
Fara fitowar mutanen gidan
saboda ihun Husna yay dai-dai da ficewar motar da aka sakata daga gidan. Sai
dai suna fitowa idon Baba malam ya sauka akan su Yoohan. Da mamaki ya tsaida
malam ƙarami dake ƙoƙarin hawa titin layin. buɗe motar yay ya fita yana faɗin,
“Malam ƙarami kuje asibitin ina zuwa. da alama wajen nan babu lafiya dan kamar
Yahya ne”.
Daga malam ƙarami har
Hajjo dake baya riƙe da Nu'aymah tana faman jijjigata da tofa mata addu'a basu
fahimcesa ba. Sai malam ƙaramin yabi umarni.
Cikin nutsuwarsa ya ƙarasa
garesu tare da yin sallama duk da alamarsu bai nuna na waɗanda ya dace yayma
sallamarba. Sai bai saniba ko akwai musulmai a cikinsu. Ai ko cikin sa'a sai
gashi wasu daga cikin ƴan sandan sun karɓa masa. Harda ma risinawa suna
gaishesa dan darajar da ALLAH yay masa ta babban mutum kuma jagora.
Ya amsa musu ne idonsa akan Papa da
sukema juna kallon sani. Kusan a tare papa da baba malam suka ambaci sunan
juna.
“Pastor Goshpower!”.
“Sheikh Sooraj Hashim!”.
Sai kuma kawai sukaga Papa ya
kece da dariya yana tafa hannu. Ya sake nuna Baba malam yana faɗin, “Da gaske
Sheikh Sooraj nake gani anan?”.
Kafin baba malam dake kallonsa
fuskarsa babu yabo babu fallasa ya bashi amsa Solomon yace, “Sir! Ai shine
mutumin da.......”
Malalacin kallon da Yoohan ke masane ya
hanasa ƙarasawa, yay saurin duƙar da kansa ƙasa yana haɗiye sauran maganar.
Kallon Yoohan baba malam yayi. Sai kuma
ya sauke wani lallausan murmushi. Cikin halin dattako irin na masu ilimi da
sanin ya kamata yace, “Yahya ka sanshi ne?”.
Kai Yoohan ya jinjinama baba malam,
kafin a hankali yace, “Mahaifina ne”.
Sosai alamar mamaki ya
bayyana ga baba malam, dan fuskarsa ta nuna ƙuru-ƙuru. Yace, “Yahya da gaske?”.
Kafin Yoohan yay magana Papa da yay
matuƙar tsuke fuska ya matso gaban baba malam ɗin yana faɗin, “Mizaisa ya maka
ƙarya?”.
Kamar baba malam zaiyi magana sai kuma
ya fasa. Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana sake dai-daita nutsuwarsa. Kusan
sakanni goma kafin yace, “Okay! Alhmdllh. Inaga to muƙarasa ciki tunda yau
gashi kazo gidana.....”
“Never!”. Papa ya faɗa cikin
saurin katse baba malam ɗin.
Da sauri Yoohan yace, “Papa saboda mi?”.
Kallonsa papa yayi da tsananin ɓacin
rai. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya sake maida kallonsa ga baba malam
dake murmushi.
Baba malam yace, “Kayi haƙuri,
dan kai yau sunanka baƙona. Ka cancanci na karramaka da masauki da abin ci da
sha. Dan koba komai kazo ƙasata ne, yankina, gidana kuma”.
Tsaki papa ya ja. Tare da kallon
d.p.o Emanuel yace, “D.p.o kama shi, inason sanin dalilin alaƙarsa da yarona”.
“What!!?” Yoohan ya faɗa a zabure yana
ƙarasowa gaban papan. Cikin nuna fusata yace, “Papa mi kake shirin yi haka?
Dammi zakasa a kamashi bayan ba'a cikin gidansa ka ganniba. Sannan ba tare da
shi ka ganni ba”.
“Rufema mutane
baki!!. Karna sake jin bakinka anan. Wannan wasane tsakanin manyan daji
guda biyu. Ka shiga mota yanzun nan zamu koma Abuja da kai”.
“Babu inda zanje papa. Domin
aikina ne ya kawoni nan. Banga kuma dalilin dazaisa na barshi ba akan dalili
mara tushe. Ku kuma (ya faɗa yana nuna police ɗin) duk wanda yay gigin matsowa
koda kusa da shi ne na rantse da ALLAH sai ya rasa aikinsa. Idan kunji ƙarya zaku
iya gwada hakan kuma”.
Tashin hankaline ƙarara ya bayyana a
fuskar d.p.o Emanuel. Dan shi kam an sakashi a tsaka mai wuya. Matsayin papaa a
garesa ya wuce duk yanda mai karatu zaiyi hasashe. Sannan ɗansa Yoohan basai an
faɗaba, yanada faɗa aji ga gwamnatin kowacce jaha saboda rawar da yake takawa
akan harkar lafiya dama matsayinsa na babban likita da duniya gaba ɗaya ke ji
da gani a yanzu. Dan tabbas yaron yana lokaci da lokacinsa.
“Yahya! Iyaye nada
matuƙar daraja ga ɗa. Ka daina tsaurara harshenka ga mahaifinka kaji. Karka
damu da tsakanina da shi, dan a yau a yanzu ya fini gaskiya tunda a wajena ya
sameka. Ba'a wasa da iyaye. Dan haka karka sake maida masa magana kaji”. Baba
malam ya faɗa idanunsa akan Yoohan dake ta faman haɗiyar zuciya da sauri-sauri.
Kai kawai ya ɗaga ma baba malam, dan
zuciyar tazo wuya bazai iya magana ba. Ya watsama guards ɗinsa wani shegen
kallo. Kafin ya raɓa papa da baba malam ya bar wajen batare da yayima kowa
maganaba.
Papa da
yasan minene fushin Yoohan yay saurin bin bayansa yana kiransa. Amma ko
kallonsa baiyiba balle ya saka ran amsawa. Ya buɗe murfin motar a fusace ya
shiga baya, shima Papa ɗayan gefen ya zagaya ya shiga yana cigaba da kiran
sunan sa. Hakanne ya saka drivern sa da Solomon saurin shiga suma, sauran
guards ɗinsa da su Emanuel da suka sami mafita suma suka nufi nasu motocin
batare da suncema baba malam komaiba.
Nannauyan
numfashi baba malam ya sauke lokacin da mitocin suka harba kan titi. Yayinda
can ƙasan zuciyarsa ke mamaki da jinjina al'amarin UBANGIJI. ‘Yoohan ɗan Pastor
Goshpower ne da gaske? Lallai UBANGIJI mai yin yanda yaso, a lokacin da yaso,
ga kuma wanda yaso’. Baba malam ya faɗa a fili. Yasan tabbas UBANGIJI shike
fidda rayayye a cikin matacce, ya kuma fidda matacce a cikin rayayye. Amma
al'amarin akwai ɗunbin ban al'ajabi a cikinsa, dan yasan abubuwa masu yawa game
da papa tun shuɗaɗen lokaci kafin yakai haka.
Da wannan tunanin baba malam ya
koma cikin gidan, inda ya tadda duk jama'ar gidan sun fito sunata tararrabin
abinda akace ya faru da Nu'aymah. Su Abban Abdallah ma shirin shiga mota suke
zasubi bayansu asibitin.
Ganin baba malam ya sakasu dakatawa, duk suka
nufesa hankali tashe suna tanbayar yaya Nu'aymahn.
Tausayinsu ne ya kamashi. dan
haka cikin taushin murya ya kwantar musu da hankali, tare da sanar musu shima
yanzu zai bisu. Basu zauna ɓata lokaciba suka ɗunguma a mota ɗaya Omar ya jasu,
akabar su Umm a gida na binta da addu'a.
Yoohan da tunda suka tafi ya ƙi
kula papa daketa so yayi magana yay kwance jikin kujera hannunsa dafe da
goshinsa cike da tsananin takaicin abinda ya faru tsakaninsa da Nu'aymah yauma.
Yarasa mike jan hankalinsa ga aikatama yarinyar nan wannan banzan ɗabi'ar?.
Abinda ba halinsa ba amma yana ƙoƙarin ɗabi'antar da shi a gareta. Saima yaji
na yau yafi masa zafi a rai fiye da na jiya.
Da sauri ya kwanto jikin papa saboda
wata hajijiya-hajijiya dake neman kwasarsa. Sake rikicewa papa yayi. A matuƙar
ruɗe ya shiga girgiza Yoohan kai kace gani yay baya numfashi.
Sosai takaici da hayaniyar papa
ta sake rufe Yoohan ɗin, amma sai ya daure cikin taushin murya da sanyayata
yace, “Papa Please relax. Ina lafiya fa”.
Da sauri ya rungumeshi yana sauke
numfashi a jajjere. Su dai su Solo suna kallon ikon ALLAH daga gaba. A haka
suka ƙarasa hotel ɗin da har yanzu akwai sauran yaran Ema... Da taimakon papa
Yoohan ya fita, shine ya kamasa har ɗakin da yake. Su kuma su Solomon suka
dakata wajen manager ɗin hotel ɗin suna musu bayani akan anga Yoohan ɗin su
kwantar da hankalinsu.
Papa na zaune kusa da
Yoohan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama
rasa wane kalar tunani ya dace yayi akan matsalarnan guda biyu. Alaƙalar Papa
da Baba malam. Abinda ya aikatama Nu'aymah a karo na biyu. Buɗe idanunsa yay a
hankali kan papa da yay shiru shima yana wani tunani can daban, sai da yay masa
kusan kallon sakan goma kafin cikin nuna kulawa ya kamo hannunsa cikin nashi da
faɗin, “Papa!”.
Firgigit ya dawo hankalinsa tare
da kallonsa. Yoohan ya sake lumshe idanu ya buɗe a kansa. “Papa dama kasan
malamin nan ne?”.
“Yoohan! Wannan tambayar taka bata da
muhimmancin samun amsa. Kai ya kamata nasan minene alaƙarka da shi?”.
Kamar Yoohan ya faɗi ainahin
gaskiya sai kuma wata zuciya ta gargaɗesa dayin hakan. Yunƙurawa yay ya tashi
zaune sosai ya jingina da fuskar gadon. Hannunsa ya sake maidawa cikin na
papansa, cikin kwantar da murya yace, “Papa akwai abinda nake buƙata a wajensa,
shiyyasa na kwantar da kaina nake binsa a sannu harna cimma burina. Sai dai
kuma gashi kai kazo cikin mintuna goma kacal kana shirin rusamin shiri na.
Miyasa zaka biyema su Solomon da shirmensu? Ai koda suka sanar maka na ɓata ko
tunanin inda za'a'a sameni kamata yayi ka jira harna dawo kaji ta bakina. Haba
papa da girmanka a ƙasarnan amma kake abu tamkar wani mara.......”
Saurin katsesa papa yayi ta hanyar ɗaga
masa hannu. hakanne ya saka Yoohan haɗiye sauran maganar tasa. Papa ya gyara
zamansa sosai da cewa, “Naji nayi kuskure, amma kaima harda laifinka. Miyasa
tun tuni baka sanarmin ba, bayan kasan niɗin mai baka goyon bayane akan kowanne
irin business naka musamman a wannan yakin”.
“Nima naji nayi kuskure to. Amma
ina da dalilin ɓoyewar ai. Da ace na sanar maka mi nake shirin yi zaka iya ɓatamin
aiki dan kanada gaggawa papa. kai kafi son komai da zafi-zafi a lamarinka.
Hakan kuma na taɗiyeka daga nasarorinka. Yanzu da ace bakazo ba da cikin satin
nan zan kammala aikina. Amma yanzu kaga ka kawo min togaciya dan zai fara kokwanto
a kaina. Kaga kenan saina sake sabon ginin da zai ƙara yarda dani hundred
percent kamar farko”.
Cikin tsananin jin daɗi papa ya rungume
Yoohan yana faɗin, “I am sorry my sweetheart, kai ɗinne ba'a gane kanka sai
kaso. Yanzu dai na maka alƙawarin da kaina zan gyara abinda na ɓata a yau ɗinnan
kaji”.
Ɗagowa Yoohan yay da sauri,
yace, “Papa da gaske kakeyi?”.
“Ƙwarai kuwa my dear son”.
Wani lallausan murmushi Yoohan ya saki najin daɗi. Dan ya
fahimci lallai sai ya nunama papa akwai manufa a tafiyarsa da baba malam sannan
zai samu nutsuwar samun damar fahimtar ilimin addinin islama da zai kare kansa
anan gaba a wajensu dama duk wani dake a cikin ahalinsa da yasan zai kawo masa
togaciya. Amma a yanzu yasan duk yunƙurin da zaiyi sai sun taɗesa saboda
rauninsa na kasancewa sabo cikin addini mai ɗunbin haske irin musulinci. A yau
kawai daya kasance a ciki jinsa yake tamkar sabon mutum. Tamkar darajarsa ta
ƙaru. Duk wani nauyin zuciya da ƙunci da yakan tsinta kanshi a ciki a baya yau
sai yaji tamkar ansa kwano an kwashesu tas.
Jikin papa ya sake lafewa tare da
lumahe ido. Papa ma dake jin daɗin Yoohan ya fara ɗaukar huɗubarsa ya shiga
shafa kansa cike da jin daɗi da annashuwa. Dan shima har zuciyarsa ta gama
shirya masa babban aiki akan baba malam tsaf............✍
Tofa masu karatu. Yanzu za'a fara wasan😎 dan haka
kumuje zuwa filin daga😉😱🚶🏻.

No comments