MIN QALB 32
MQ 32_*
Gyara zama anty zarah tayi tana sake qurawa fuskar Amatun
datayi haske sosai Ido tana maida kallonta zuwa hannuwanta dasukai haske sosai
har wani yellow yellow sukayi taji hankalinta nason tashi gabanta na faduwa ta
maida kallonta Kan fuskarta tanabinta da kallo ko Ina har zuwa qasanta ta ajiye
cup din furar da Amatun tasa aka kawo Mata tana cewa''
Amatu yanayinki na bani tsoro da rashin nutsuwa sbd
yanayinki na nuna kamar bakida jini,
Ruwa idanuwanta ke qoqarin kawowa tana kallon fuskarta
Amatun dake zaune ka kwantarda kanta jikin sofa idanuwanta a lumshe Wanda yanzu
hakan yazama tamkar dabia gareta sbd aduk lokacinda ta zauna tayi shiru
idanuwanta take lumshewa sbd tunanin rayuwarta data juya Mata kamar upside down
Dan kuwa sai yanzu take sake tabbatarda rashin Dr khalil zabeera arayuwarta
babbar gibi ce ga rayuwarta sbd shine farin cikinta,
walwalarta,gatanta,burinta,alfaharinta, nutsuwarta gatanta dama asalinta gaba
daya...
Hawayen datake riqewane suka gangaro daga cikin rufaffun
idanuwanta Wanda yasa hankalin Anty zarah sake tashi tunanin qilan eh da gasken
Amatun batada jinin tunaninta ya zama gaskia ta dafe goshi tana rintse ido
cikin tsananin damuwa da firgici tace"
Amatu Dan Allah ki bude Ido kiyi magana wannan kukan naki na
zuci Yana wahalardamu masu qaunarki,
A zabeera kaf gaba daya yanzu Babu Wanda akeji dashi ake
tsananin qaunarsa fiyeda kowa kamarki sbd kece Abinda duniya gaba daya ta
shaida Dr khalil zabeera naso fiyeda komai har rayuwarsa,
Damuwarki damuwar kowa ce,
Kukanki baqin cikin mune,
Amatu Dan Allah kiyi hkr ki dauki dangana tareda daukar
qaddarar rashin Dr Khalil sbd ganinki ahaka na karya dukkanin qwarin gwiwar
ummen khalil,
Yanzu Amatu bansan yazanyiba gaki da rashin lafiya ajikinki
ta zazzabin dare kullum Amma kinki ko karban magani gashi yanzu Ina sakaran ko
jini na neman gagararki Amatu meyasa,meyasa......hawaye ne suka katse Mata
takasa qarasa maganar ta miqe da sauri zata bar gurin Amatu ta riqo hannunta
ahankali tana bude idanuwanta dasukai jajir ta zubawa fuskar anty zarah din
dake hawaye tanajin qaunarta tako Ina tana shigarta tareda tausayinsu su duka.
Jawota tayi ta maidata zaune tana kallon fuskarta ta tashi
zaune ahankali tareda sake hannun anty zarah din tana dauke idanuwanta daga
kallonta ahankali ta bude baki cikin yanayi na karyewar zuciya tace"
Anty zarah meyasa kike qaunata har haka?
Meyasa keda Dr kuke min irin wannan son haka?
Anty zarah kinsan arayuwata bantaba samun soyayya irinta Dr
khalil zabeera ba,
Shine ya koyamin sonsa alokacinda zuciyata batasan wata
soyayya ba saita kudi,
Shine yabani sunan mutunci da martabar mace,
Dr khalil zabeera yazabi soyayyata fiyeda komai da kowa,
Yasa zuciyata takamu da zazzafar soyayyarsa me wuyar Bari
bare mantawa Amma yatafi ya barni a daidai lokacin da zuciyata batasan komai da
kowaba bayanshi,
Meyasa yatafi yabarni anty zarah Ina tsananin
buqatarsa.......
Rufe Mata baki anty zarah tayi tana girgiza Mata Kai
hawayenta itama suna gudu tace"
Amatu kada kiyi sa6o ki dauki dangana shima da ana bada
zabin mutuwa da bazai taba zabin barinki ba sbd bazaiso ganinki cikin irin
wannan halin dakike cikiba yanzu..
Kiyi hkr ki rungumi hukuncin ubangiji akanku hakan da yayi
shine daidai kizama me godewa ubangiji aduk halinda Kika tsintsi kanki.
Sauke Kai Amatun tayi hawayenta suka Gama gangarowa ta dago
tana sharewa ta kalli anty zarah datake kallonta cikin tsananin damuwa ta sauke
ajiyar zuciya ahankali tareda lumshe ido ta bude ta miqawa anty zarah din hannu
tana kallon cup din furar data kawo Mata.
Da sauri anty zarah din ta dauki cup din ta Bata tana
bayyanarda Jin Dadinta na sassautowa da Amatun tayi cikin guntun zumudi
tace"
Thank you AMATULLAH.
Da sauri Amatun ta kalleta tana fasa Kai cup din bakinta sbd
duk duniya Dr khalil dinta ne kawai ke Kiranta da cikakken sunanta AMATULLAH.
Fuskewa anty zarah tayi tana qaqalo murmushi ganin tana
neman dawo da gaba baya tace"
Banma iya fadar sunan yayi Dadi ba kaman yanda ake fada.
Ganin tashiga kame kamen fadar sunan datayi yasa Amatu sake
sauke ajiyar zuciya tana Kai cup din bakinta tana kurba ahankali ta
lumshe ido tana gyara jinginawarta sbd dadi dakuma karbuwa dataji bakinta
da cikinta sunayi da furar saita saki jiki tanasha ahankali furan na sake
sanyata lumshe ido.
Anty zarah ganin yanda furan tasamu karbuwa sosai agun
Amatun yasata miqewa da sauri ta nufi fridge ta dauko gaba daya jug din furan
ta dawo dashi ta ajiye gaban Amatun tana cewa''
Kawo cup din aqara zubawa Kisha
Dama nasan zakiji Dadinta sbd har sabuwar Madara na zuba
Miki aciki.
Qara Mata tayi takuma shanyewa Saida ta shanye kusan cup uku
kafin tace ta Isa abarta haka.
Cikin Jin Dadi anty zarah tagyara zama tana Mata fira
ahankali tana matsa Mata qafafunta dasuka Dan kumbura sbd zama guri daya
Ahaka har bacci ya dauketa cikin nutsuwa Wanda rabonta da
irinsa tun kafin rasuwar mijinta sai yau.
Gyara Mata kwanciya zarah tayi kafin ta zame ta fice daga
part din gaba daya takoma nasu Nan ma wani aikin tahau sbd MAHMOUD datake saka
ran dawowarsa ayau din duk da gaba daya yinin ranar basuyi wayaba dama
itace tafi Kira to itakuma yau ganin yanayin sauyin jikin Amatu yasa hankalinta
yadan dauku ko yanzu tana ganin kamar hasashenta gaskia ne Amatu na buqatar
ganin likita jikinta bai nuna tana lafiyaba
Dole zata fadawa umme kokuma MD idan yadawo yau asan nayi
kada wani ciwo ya kamata basuda masaniya.
Aikin gyare gyare da girki suka hau Yi itada hafsatu sbd
tuntuni ta zauna tayi nazari zata dauki shawarar Amatu ta kawo gyara arayuwar
aurenta da tsakaninta da mijinta,
Zata cire shakku da tsoron mijinta ta fuskanci reality
rayuwar aure sukeyi ba zaman darasiba Dan haka zata sauya kanta ta sauya
zamantakewarta da MAHMOUD ZABEERA kada tayi sake lokaci ya qure Mata.
Sai yamma suka Gama komai tayi wanka ta sanya doguwar riga
ta atampa tareda yafa qaramin qyale akanta ta hada abincin data dibarwa amatu
ta jera a tray hafsatu ta dauka suka nufi can.
Koda suka shiga futowarta wanka kenan itama ta sanyo riga da
skirt na atampa ta sanya.,
Abin mamaki maimakon taji kayan sun Mata yawa sbd Rama
saitaji kamar skirt din ya kamata hakama rigar.
Kallon anty zarah dake kallonta cikin yanayi na tunanin
dabasanma na menene ba haka kawai idan tana kallon Amatu wani lokacin saita
Shiga tunanin yanzu saime Kuma zaizo gaba a rayuwar Amatun.
Anty zarah kina ganin na qara jiki ne kokuwa nece naji
hakan?
Numfashi anty zarah din ta sauke tana matsowa gaban Amatun
ta Dan ja rigarta daga gefe gefe taji ba wani space tasaki murmushi tana cewa''
Gskia baki wani qara ba inaga sbd dai kin Dade baki sakasu
bane shiyasa gashi bakida wasu tsofin kayan bare kisaka Amma kiyi hkr kiyi
manage tunda ba abin ado bane Kuma ba fita zakiyi ba bare kice Zaki takura.
Gyada kanta tayi tana sanyawa kanta hula Mara nauyi ta Dan
saki fuska ta qaqalo murmushin yaqe sbd faranta ran Anty ZARAn tace"
Anty zarah wannan qamshin na Rabin ranki ne?
Sbd nasan shi kadaine akewa wannan Shirin na musamman.
Kasa boyuwa farin cikin anty zarah yayi ta saki annushuwa
sosai tana cewa''
Amatun kin bawa MAHMOUD sunan Dole Wanda harya zauna cikin
kaina Nima RABIN RAN ANTY ZARAH.
Falo suka fito suna cigaba da Dan fira sama sama sbd karta
zaqe da yawa ganin Amatun tafara sakewa.
Suna zama tace"
Anty zarah kokinsan meyasa idon mutum ke nauyi wani lokacin
kamar zasu juye ga ciwon Kai me tsanani???
Kallonta da kyau zarah tayi kafin tace"
Kinajin hakan ne?
Gyada Kai tayi ahankali tana cewa"
Qila sbd kukan danakeyi ne koyaushe.
Aa Amatu ba lallai hakan bane ni nafi zargin rashin ishashen
jini atare dake kibari Akira likiti ya dubaki.
Ba buqatan hakan anty kawai daima yanzu Kwan biyun Nan
nadainajin nauyin idon ciwon Kai me tsanani yafi damuna idan akwai maganin
ciwon Kai kawai kiban danasha shikenan zanji sauqinsa Inshallah.
Akwai ibuprofen agurina Yana maganin ciwon Kai sosai yanxu
idan na koma xan aiko hafsatu takawo Miki kisha kafin ki kwant kafin safe
zakiji wasai.
Nagode anty zarah Allah yabarki da Rabin ranki yabaki
zuciyarsa.
Wata Yar dariyar farin ciki tasaki tana qoqarin dasawa
zuciyarta zancen ta hanyar cewa amin saidai Kuma wani sashen na zuciyar na
ganin kamar da wuya samun zuciyar MD ZABEERA koba agurinta ba ko agurin kowama.
Salman ne yashigo palon daukeda babbar ledar fresh fruits da
ledar gasassun kifin dasuka gasu cikin source din veg chips sai qamshi sukeyi.
Da kallo dukkaninsu suke binsa har su hafsatu suka karbi
kayan hannunsa sukai kicin dasu Dan zubowa a tray ya qaraso ya zauna gefen anty
zarah Yana kujerar dake kallon ta Amatu Yana kallonta cikin yanayi na tsananin
kulawa Yana tambayarta Yaya take
Ta amsa Masa cikin yanayin sake bawa kanta qwarin gwiwa sbd
su masoyanta dasuka damu kansu akan damuwarta.
Maida kallonsa yayi Kan anty zarah dake yankawa Amatu
kankana cikin fruits dinda su hafsatu suka kawo bayam sun sake wankowa yasaki
murmushi Yana cewa''
ZARAH Ashe MD yadawo yau.
Dagowa tayi tana Masa kallon mamaki da tambaya tana miqawa
Amatu kankana a qaramin plate da fork.
Ganin alamar batasaniba akan fuskarta yasashi karban plate
din dashima take miqo Masa ya gyara zama yafara Sha kafin yace"
Kafin nafita da yamman Nan Naga shigowar motarsa an daukosa
daga airport Amma sashen Modibbo Naga motar ta nufa Kuma acan mukayi sallar
magrib tare agun Modibbon Amma dai by now inaga yabar sashen Modibbo.
Kallonta Amatu tayi tana sake murmushi ahankali cikin
nutsuwa tace"
Barka anty zarah.
Itama murmushi ta mayar musu tana gatsa apple ahankali
zuciyarta na shiga yanayi na 'yar damuwa tana basarwa sbd qilan yakirata bayan
dawowarsa din Dan tabar wayar acan sashensu tana charging.
Ganin hankalinta bai Kan Yar qaramar firar dasukeyi yasata
miqewa tareda Yi musu Saida safe daidai fitowar anty salamatu daga dakin dayake
zaman nata a zaman dazatai agidan kafin sukoma inda suka fito.
Qarosowa tayi suka gaisa da zarah dazata fice kafin ya
qaraso ta zauna gefen Dr salman suna gaisawa Yana janta da Yar firar dasuka
Saba tun amatu nasaka musu baki hartayi shiru ta lumshe ido tana saurarensu sbd
kanta dake sarawa.
Shigowar hafsatu ce data dawo tasata bude idanuwanta
ahankali ta saukesu akan hafsatun tareda karban maganinda anty zarah din ta
aikota takawo Mata ta juya ta fice.
Miqewa tayi da kanta ta nufi kicin ta bude fridge ta dauko
ruwa ta bude tareda ballo maganin Tasha ta maida sauran ruwan tareda fitowa
tayiwa salman Saida safe ta wuce daki direct tayi sallar ishai ta kwanta sbd
tsanani dataji kamar Kan nata nayi Dan har jiri jiri take gani.
Zarah kuwa bayan tabawa hafsatu maganin takaiwa Amatu direct
sama ta nufa dakin MD bayan tasake fesa turare ta daura dankwalin kayan jikinta
tana sake gyara zaman curves din rigar taje ta hado Masa abincin sukai Masa
marasa nauyi a tray ta Isa qofarsa tayi knocking so daya kafin ta tura qofar
tashiga bakinta daukeda sallama cikin yanayi na nutsuwa.
Fitowarsa wanka kenan Yana tsaye gaban mirror Yana goge
ruwan jikinsa ahankali ya dago ya kallota ta jikin madubi da fararen idanuwansa
ya amsa sallamar ahankali cikin muryarsa data kashe jikinta Nan take.
Kallonsa takeyi da dukkanin idanuwanta da bakinta da
hancinta da nutsuwarta da komaima nata sbd wani sheqi da jikinsa yakeyi na hutu
dayake samu.
Jin shiru yasashi juyowa ahankali ya kalleta yaga yanda duk
ta sake gurin kallonsa ya dauke Kai ahankali tareda bude wardrobe ya janyo
jallabiya Mai tsantsi da taushi brown ya saka tareda fesa spray dinsa na
imperial majesty ya nufa kujera ya zauna Yana daukar wayarsa dake kashe ya
kunna tareda dagowa ya zuba Mata manyan idanuwansa ya bude baki ahankali
yace"
Nasameku lafiya?
Dan firgita tayi da tareda dauke idonta akansa cikin
tsananin Jin nauyin mayen kallon datazo ta tsaresa dashi batareda yimasa ko
sannu da zuwaba bare gaidashi.
Cikin Dan Jin kunya ta qaraso gefensa ta zauna ahankali ta
ajiye tray din akan table tana saita kanta cikin Jan mutuncinta a natse
tace"
Barka da dawowa,ya hanya?
Ajiye wayarsa yafarayi bayan ya saka silent ya Dan juyo ya
kalleta cikin nutsuwa har zuwa adon datayi dominsa ya sauke ajiyar zuciya
ahankali kafin ya dauke Kai Yana Dan sakin fuska yace"
Alhamdulillah,
Ya kuke?
Sake kallonsa tayi sbd yanda gabaki daya ko awaya yawanci
tambayoyinsa suka koma Mata kalmar KU.
Jin shiru yasashi dagowa ya kalleta ya sake maimaita
tambayarsa da cewa''
Kuna lafiya???
Zuba Mata Ido yayi sbd amsa yakeson ji.
Akwai matsalane acan gefen??
Sai alokacin ta kallesa cikin Ido sbd sai alokacin ta
fahimci Amatu yake nufi ta saki ajiyar zuciya tareda sake murmushi tana gyada
Kai tace"
lafiya kalau Nake su Amatu ma lafiya kalau suke saidai duk
da Bata fadaminba inaga kamar batada lafiya sbd sauyawar datayi ga ciwon Kai me
tsanani datace tana........
Tari me qarfi ya sarqesa na abincin dake bakinsa,
Spoon din faten dankalin daya maida cikin plate batareda
yakai bakinsaba kamar yanda yayi Niya yasata kasa qarasa fadar Abinda take fada
tana kallonsa ta kalli abincin cikin mamaki da fargaba tace"
Ya salam,
Sorry,
Lafiya?
Akwai wani Abu ne tareda abincin?
Dan lumshe ido yayi tareda budewa batareda ya kalletaba
yace"
I lost my appetite.
Cikin damuwa ta matsosa da sauri Yana dafasa cikin kulawa
tace"
Bakada lafiya ne?
Ko akawo wani abincin?
Numfashi ya sauke Yana sake kallonta yace"
No I just lost the need to eat karki damu.
Kasa hakura tayi ta zubo Masa coconut drink dinda tafi awa
biyu tana hada Masa sbd sanin Yana qaunarsa ta zubo a cup ta miqa Masa cikin
sauri da kulawa daidai kiran Salman zabeera nashigowa hannun dayayi niyyar
karban drink din datake basa shi ya wuce dashi ya dauki wayar Kai tsaye Abinda
bayayi Kiran farko ya daga waya,
Yanaji a rayuwarsa daga Modibbo sai Khalil ne kawai ke Masa
Kira daya ya dauka.
MD Amatu ce ba lafiya sosai she's ko numfashi batayi and she
is bleeding ba kakkautawa am taking her to hospital...
Aje wayar yayi Yana qoqarin saita nutsuwarsa
Saikuma kawai ya miqe tareda daukar wayarsa da key din mota
yafice.
Bayansa zarah tabi da kallo kafin tabi hannunta dake sangale
da cup din data miqa Masa bai karba ba tanaji wani nauyi na danne zuciyarta
Wanda yasa idanuwanta cikowa da hawayen dabatasan Kona menene ba.

No comments