SARAN BOYE 29
No. 29
.............“Na faɗaɗa maka muhimmanci kalmar shahada ne domin kasan addinin musilinci ba abin wasa bane, sannan bautama UBANGIJI shi kaɗai bashi da abokin tarayya shine cikakken imani. Gujema shirka babba da shirka ƙarama domin dawwama da tsira wajen bautama ALLAH shi kaɗai da tabbatar da soyayyar MANZONMU a zukatanmu wajibine. Zaka karɓi kalmar shaha yanzun nan Yahya, da ga haka ka tabbatar kabar kafircema ALLAH har abada, ka tsarkake ranka da zuciyarka cewa babu wani sarki sai ALLAH, ANNABI MUHAMMADU kuma MANZON ALLAH ne”.
Kai Yoohan ya jinjina a hankali,
zuciyarsa na wani irin tsitstsinkewa, tsigar jikinsa na tashi batare da yasan
dalili ba. Hakama jininsa gudu yake a cikin jijiyoyinsa da sauri-sauri. Wannan
yanayin sai ya saukarma jikinsa da kasala da wani rauni da bai taɓa tsintar
kansa a ciki ba.
Baba malam na faɗar kalmar shahada yana
maimaitawa, suna kai ƙarshe sai kawai hawaye suka ɓalle masa tamkar an buɗe
fanfo. Ya sakko a kujerar da yake zaune a hankali ya durƙushe ƙasa jikinsa na
wani irin rawa. A matuƙar mamakin su baba malam sai gani kawai sukai ya kai
goshinsa ƙasa yayi sujda.
Ɗan yatsa baba malam ya saka ya ɗauke
hawayen da suka sakko masa gefen ido kaɗan. Hakama Abban Abdallah sai da hawaye
suka cika masa idanu, sai jin wata irin ƙauna da soyayyar Yoohan ɗin suke tana
nunkuwa a zukatansu. Kamar yanda shima ƙaunarsu ke sake masa ninƙaya a zuciya.
Koda ya ɗago da ga sujudar da
yayi kamar yanda yaga baba malam yayi ɗazun sai kawai ya matsa ya rungume baba
malam ɗin yana cigaba da hawaye. Sunja tsahon lokaci a haka kafin baba malam ya
ɗagosa yana murmushi, yace,
“Yahya ina tayaka murna.
akwai ayyuka sosai a gabanka. Amma kafin su yanzu zakayi wankan shiga
musulinci”.
Cikin lunshe idanu dajin wata nutsuwa
ta musamman Yoohan ya gyaɗa masa kai.
Bisa jagorancin baba malam Yoohan
ya gabatar da wankan shiga musilinci, tare da tsaftace wasu najasosi dake
jikinsa, kamar tarin gashin kansa, an ragesa, amma ba sosai ba, dan baba malam
ya shaida masa barin gashi ado ne, sannan koyine da MANZON ALLAH (S.A.W), bama
ason ayi aski tas-tas ɗin nan kai na ƙyalli. Yanke masa ƙunba. Duk da shi bama
mutum bane mai tarata, tare da sauran abubuwan da suka dace su kasance a
tsaftace ga ƙa'idar musilinci.
Bayan ya shirya tsaf cikin sabuwar
suturarsa farar ɗanyar shadda tas, da taji ɗinkin da yay masa ɗas a jiki baba
malam suka rungumesa suna sake masa marhaban da shigowa addinin gaskiya, sannan
suka sake zama da shi a karo na biyu domin masa bayani akan SALLAH.
yanzu kam harda su Abba Musbahu suma
sun shigo tawagar. Bayan an kawo musu breakfast sunci tare su biyar abin
sha'awa. Bayyana muku irin farin cikin da nutsuwa da Yoohan ke ciki a wannan
lokaci ɓata lokaci ne.
Shiru falon ya ɗauka duk suna sauraren
baba malam dake zuba bayani cike da nutsuwa da ƙwarewar ilimi da sanin da ALLAH
ya azurtashi da shi.
Yoohan! Sallah na nufin addu'a.
Amma a shari'ance ibada ce ma'abociyar karatu da ayyuka Keɓaɓɓu,
da ake fara ta da kabbara a kuma rufe ta da sallama, sallah ita ce rukuni na
biyu a cikin Addinin Musulunci bayan kalmar shahada, wato *_(ASH'HADU AN LA
ILAHA ILALLAHU WA ASH'HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH)_* sai ita. kuma ita ce
kashin bayan addini, saboda girmanta da matsayinta ALLAH bai aiko mala’ika da
ita ba sai ALLAH Madaukakin Sarki Ya kirawo ANNABI (SAW) a daren Isra’i da
Mi’iraji ya bashi ita. Yana daga girman sallah ambatonta da ALLAH Madaukakin
Sarki Yayi sau hamsin da takwas (58) a cikin Alkur’ani, kamar inda yake cewa:
{وَأَقِيمُوا الصَّلَوةَ} [البقرة: 43]
Ma'ana: "Ku tsaida sallah"
{قُلْ لِعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلَوةَ}[إبراهيم:
31]
Ma'ana: "Ka fada (Ya Muhammad S.A.W) ga bayina da suka
yi imani su tsaida sallah".
Da sauran wurare a cikin Alqur'ani da dama.
Annabi (SAW)
yana cewa: “Bainar rajuli wabainal kufri tarkus salati” (Rawahu Muslim).
Ma’ana: “Tsakanin mutum da kafirci
shine barin sallah”. Kuma ana umartar karamin yaro da yin Sallah tun yana dan
shekara bakwai, kuma in ya kai shekara goma a doke shi in ya ki yi.
Sallah bata yiwuwa sai da alwala.
ALWALA:
Ubangiji Madaukakin Sarki yana cewa:
"يأيها الذين ءامنوا إذا قمتم إلى الصلوة فاغسلوا وجوهكم وأيديكم
إلى المرافق وامسحوا برءوسكم وأرجلكم إلى الكعبين وإن كنتم جنبا فاطهروا وإن كنتم مرضى
أو على سفر أو جاء أحد منكم من الغائط أو لامستم النساء فلم تجدوا ماء فتيمموا صعيدا
طيبا فامسحوا بوجوهكم وأيديكم منه ما يريد الله ليجعل عليكم من خرج ولكن يريد ليطهركم
وليتم نعمته عليكم لعلكم تشكرون" المائدة: 6.
"Ya ayyuhal lazina aamanuu izaa kumtum ilas salati
fagsilu wujuuhakum wa’aydiyakum ilal maraafiki wamsahuu biru’uusakum
wa’arjulakum ilal ka’abayni wa’in kuntum junuban faddahharuu wa’in kuntum marda
au alaa safarin au ja’a ahadun minkum minal ga’idi au laa mastumun nisa’a falam
tajidu ma'ana fatayammamu sa’idan dayyiban famsahuu biwujuuhikum wa’aydiykum
minhu maa yuridul Laahu liyaj’ala alaykum min harajin walakin yuridu
liyudahhirakum waliyutimma ni’imatahu alaykum la’allakum tashkuruun”. Alma’ida:
6.
“Yanzu zamuje kaga yanda
ake alwala kafin salla”. Baba malam ya faɗa yana miƙewa. Gaba ɗaya suka biyosa
ƙofar toilet ɗin dake cikin falon. Yayinda Yoohan da baba malam suka kasance
daga ciki.
*YADDA AKE YIN ALWALA SHINE:*
1-Da farko yin niyya a zuci sannan ka
ce: “Bismillahi” sannan ka wanke tafukanka na dama da na hagu kowanne sau
uku(3).
2-Sannan ka debo ruwa ka kurkure bakinka
ka zubar da ruwan sau uku(3).
3-Sannan ka debo ruwa ka shaka a hanci
ka fatar shi ma sau uku(3).
4-Sannan ka debo ruwa ka wanke fuskarka
gaba dayanta sau uku(3), a lura cewa wanke fuska yana farawa ne tun daga farkon
goshinka har izuwa karkashin haba wato kusa da makoshi a tsayinta kenan, a fadi
kuma tun daga gefen kunnen dama zuwa gefen kunnen hagu.
5-Sannan a wanke hannu tun daga tafuka
har zuwa gwiwar hannu na dama da na hagu shima uku(3).
6-Sannan a ɗebo ruwa a yi shafar kai
wato a tafin hannu a shafo tun daga farkon goshi har a kai ƙeya sannan a sake
dawowa farkon goshi.
7-Sannan shafar fatar kunnuwa na
dama da na hagu.
8-Sannan a wanke kafafu na dama da na
hagu tun daga tafin kafa har izuwa gwiwar kafa.
*ADDU’A BAYAN KARE
ALWALA:*
"أشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له وأشهد أن محمدا
عبده ورسوله" رواه مسلم.
"سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب
إليك" رواه الطبراني.
“Ashhadu an Laa ilaha illal Lahu wahdahu laa sharika lahu
wa’ashhadu anna Muhammadan abduhu warasuluhu”. Muslim ne ya rawaito.
Ko kuma ka ce;
“Subhanakal Lahumma wabihamdika Ashhadu an Laa ilaha illa
anta astagfiruka wa’atubu ilaika”. Dabarani ne ya rawaito.
“Wannan itace alwala Yahya. Da
ita ake gabatar da bautar ALLAH, idan babu ita babu salla. Akwai abubuwan da
suke warwareta, amma zamu ajiyesu zuwa nan gaba a neman ilimi zaka sansu. A
yanzu muna tsinkayar jiran shigar lokacin azhar ne, dan a ƙa'ida ko wanne wuni
musulmai na gabatar da salla sau biyar ne. Akwai nafiloli da mutum kan ƙara
dasu domin samun kusanci ga UBANGIJI. Amma da waɗan nan biyar dazan lissafa
maka sune wajubabbu. Wanda ya barsu ko yayi sakaci dasu, haƙiƙa bai cika
cikakken musulmi ba.
*SALLOLI WAJIBABBU:*
Ya zo a hadisin Dalhatu bin Ubaydullah cewa:
"أن أعرابيا قال: يا رسول الله ماذا فرض الله عليَّ من الصلاة؟
قال: «خمس صلوات في اليوم والليلة.. الحديث…
Ma'ana: "Cewa wani Balarabe ya ce: Ya Ma'aikin ALLAH me
UBANGIJI (SWT) ya wajabta a garemu na daga sallah? Sai ANNABI (SAW) ya ce:
Salloli biyar a cikin (kowane) wuni da dare".
Salloli wajibabbu guda biyar
sune: 1-Asubah, 2-Azzahar, 3-La'asar, 4-Magriba, 5-Isha'i.
*LOKATAN SALLAH DA
ADADINSU:*
ASUBAH: Sallah ce da ake yin ta raka'a biyu, Lokacin yin ta
kuma shine bayan bullowar alfijir na gaskiya. Sannan ana yin karatunta a
bayyane, Fatiha da sura a kowacce raka'a sannan a yi tahiya ayi sallama.
AZZAHAR: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacin yin ta
yana farawa idan rana ta bar tsakiyar sama ta karkata zuwa mafadarta. Sannan
ana yin karatunta a asirce, Fatiha da sura a raka'o'in biyun farko, sai a zauna
a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe, sannan a sake yin
tahiya a yi sallama.
Amma a ranar Juma'a sallar Azzahar tana zamowa sallar Juma'a
a inda take komawa raka'a biyu kuma ana yin karatunta a bayyane, bayan liman ya
kare khuduba.
LA'ASAR: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacinta na
farawa daga inda inuwar abu tayi daidai da tsayinsa. Sannan ana yin karatunta a
asirce, Fatiha da sura a raka'o'in biyun farko, sai a zauna a yi tahiya, sannan
Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.
MAGRIBA: Sallah ce da ake yin ta raka'a uku, lokacin yin ta
shine idan rana ta fadi a mafadarta (a nan Najeriya fuskar yamma). Sannan ana
yin karatun raka'o'i biyun farko a Fatiha da sura amma a bayyane, sai a zauna a
yi tahiya sannan a mike a yi raka'a daya ta karshe a karanta Fatiha kawai a
asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.
ISHA'I: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacinta yana
farawa ne idan shafaki ya buya (wato dan jaja-jajan nan na bayan faduwar rana
idan gari ya fara duhu). Sannan ana yin karatunta raka'o'in biyun farko Fatiha
da sura a bayyane, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in
biyun karshe a asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.
*KIRAN SALLAH:*
الله أكبر الله
أكبر
أشهد أن لاإله إلا
الله
أشهد أن لاإله إلا
الله
أشهد أن محمد رسول
الله
أشهد أن محمد رسول
الله
حى على الصلاة
حى على الصلاة
حى على الفلاح
حى على الفلاح
الله أكبر
الله أكبر
لا إله إلا الله
Allahu Akbar,
Allahu Akbar,
Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah,
Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah,
Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah,
Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah,
Hayya alas-Salat,
Hayya alas-Salat,
Hayya alal-falah,
Hayya alal-falah,
Allahu Akbar
Allahu Akbar
La’ilah aillall-lah.
Wannan shi ne lafazin kiran sallah. An so ga wanda ya ji
kiran ana kiran sallah ya maimaita abin da mai kiran sallar yake fada shi ma,
sai a wajen fadin "HAYYA ALAL SALAT" da kuma fadin "HAYYA ALAL
FALAH" a madadin ka maimaita su idan mai kiran sallah ya fade su, sai ka
ce "LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH".
*YADDA AKE YIN SALLAH:*
- Da farko sai ka fiskanci alkibla (Saitin inda Ka’aba take,
anan arewacin Najeriya ana cewa Gabas domin nan ne saitin inda Ka’aba take daga
nan) sai a yi ikama, ga yadda lafazinta yake:
Allahu Akbar, Allahu Akbar,
Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah, Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah. Hayya
alas-Salati. Hayya alal-falahi. Kad-kamatis-salatu, Allahu Akbar, Allahu Akbar,
La’ilah aillall-lahu.
Sai ka daga hannuwanka daidai
kafadunka ko daidai kunnuwanka sai ka yi Kabbara wato ka ce: “Allahu Akbar”.
-Sai ka dora hannunka na dama
akan hannunka na hagu a kirjinka (kabalu), ko kuma ka sake su (sadalu), duk
wanda ka yi daidai ne.
-Sai ka karanta karatun bude sallah a
asirce ake yinta ita ce:
“Subhankal Lahumma wabihamdika watabaraka ismuka wata’ala
jadduka wala’ilaha gairuka”
ko kuma ka ce: “Allahumma ba’id
baini wabaina hadayaya kama ba’adta bainal mashriki wal magribi, Allahumma
nakkini min hadayaya kama yunakkal saubul abyadi minad danasi, Allahumma
agsilni bil ma’i wassalji wal baradi”.
-Sannan a karanta Fatiha zuwa
karshenta.
-Sannan a karanta abinda ya sauwaka na
daga Alkur’ani sura ko wani sashi na sura daga Alkur’ni.
-Sai ayi kabbara “Allahu Akbar”
ayi ruku’u, a cikin ruku’u ana iya karanta: “Subhana Rabbiyal Azim Wabihamdihi”
ko a karanta “Subbuhun Kuddusun Rabbul Mala’ikati Warruhu” gwargwadon abinda ya
sauwaka.
-Sai a dago daga ruku’u ana fadar
"Sami'al Lahu Liman Hamidahu" idan an dago an tsaya kafin a tafi
sujjada sai a ce: “Allahumma Rabbana walakal hamdu” ko ka ce “Rabbana walakal
hamdu”
-Sai kuma ayi kabbara “Allahu
Akbar” a yi sujjada ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin
sujjada gwargwadon abin da ya sauwaka a (a lura cewa sujjada ana yinta akan
gabobi guda bakwai, goshi tare da hanci, tafuka biyu, guiwoyi biyu da kuma
kafafu biyu).
-Sai ayi kabbara “Allahu Akbar” a
dago daga sujjada a zauna akan kafar hagu ko duwawun hagu, a dora tafuka akan
cinyoyi ana fadin “Rabbigfirli” ko kuma “Allahumma Igfirli”.
-Sannan ayi kabbara “Allahu Akbar” a
koma sujjada ta biyu ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin
sujjadar gwargwadon abin da ya sauwaka.
-Sannan a yi kabbara “Allahu Akbar” a dago daga sujjada ta
biyu, yayin mikewa zuwa raka’a ta biyu (idan an zauna dan kadan kafin mikewa
raka’a ta biyu ba laifi, ana kiran wannan dan zama kadan “jalsatul istirahati”).
Sai a sake kawo raka’a kamar yadda aka yi
wannan ta farko, amma idan an dago daga sujjada ta biyu a raka’a ta biyu sai a
zauna kamar irin zaman da aka yi na dagowa daga sujjada ta farko a dora hannaye
akan cinyoyi, sannan hannun dama ayi nuni da dan yatsa manuniya a yi karatun
tahiya a wannan zama, karatun tahiya shine:
“Attahiyatu Lillah, Azzakiyatu
Lillah, Addayyibatus Salawatu Lillah, Assalamu alaika ayyuhan Nabiyu
Warahmatullahi Wabarakatuhu, Assalamu Alaina wa’ala ibadil Lahis Salihina, Ash’hadu
an La’ilaha illal Lahu Wa’ash’hadu anna Muhammadan Abduhu warasuluhu”.
Haka ya zo a (Muwadda Malik, lafazin
Umar bn Khaddab).
Idan sallar mai raka’a biyu ce, kamar sallar Asubah
sai ka cikasa karatun tahiyar anan da salati Ibrahimi. Shi ne kamar haka:
“Allahumma salli ala Muhammadu wa’ala
aali Muhammad kama sallayta ala Ibrahim wa’ala aali Ibrahim innaka Hamidun
Majid, Wabarik ala Muhammad wa’ala aali Muhammad kama barakta ala Ibrahim waala
aali Ibrahim Innaka Hamidun Majid”.
Sai kayi sallama, ka ce “Assalamu
Alaikum Warahmatullah”. Ko kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma
hagunka.
Idan kuma sallar mai raka’a uku
ce kamar Magariba ko raka’a hudu kamar Azahar da La’asar da Isha’i, idan kayi
kashi na farko na karatun tahiya sai ka tashi ka cikasa ragowar raka’ar da ta
rage ko daya ko biyun (a lura cewa a ragowar raka’ar da ta rage bayan biyun
farko Fatiha kadai za’a karanta ban da sura ko wani sashi na sura) sai ka sake
zama na tahiya a karo na biyu ka cikasa tahiyar har zuwa sashi na biyu na
salati Ibrahimi sannan ka yi sallama ka ce “Assalamu Alaikum Warahmatullah” Ko
kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma hagunka.
*BAYANIN SHARADAN SALLAH
Sharadan sallah sune:-*
1.Musulunci. (ba ta inganta ga wanda ba Musulmi ba).
2.Hankali (ba ta inganta ga mara
hankali).
3.Tsarkin dauda: Shine tsarkake jiki da
tufa da bugire na mai sallah tun daga farawa har kammalawa.
4.Tsarkin Hadasi: Shine duk abin da ke warware
alwala, shima tun daga fara sallah har zuwa kammalawa. Ana bukatar wadannan
tsarki a cikin kowace irin sallah ma’abociyar raku’i da kuma sujjada kai har ma
wanin nan nata.
5.Shigar lokacin sallah.
6.Niyya.
7.Sitirce al’aurar namiji tana kamawa ne
daga cibiya har zuwa gwiwa. Ita kuwa mace baki dayan jikinta al’aurane ga
ajnabinta sai dai fuskarta da tafukan hannuwanta.
8.Fuskartar Alkibla; Sai dai in a halin
rincabewar yaki ko nafila a tafiyar da ya halatta ayi kasaru kuma mutum ya zamo
mahayi ne kan abin hawa.
Wanda ya yi sallah yana kallon watan
alkibla ba yana mai mantawa ko rashin sani har sai da ya yi sallama, to ya
saketa har abada, sai dai malamai sun yi sabani a cikin wannan hukunci, haka
hukuncin ya ke idan ya zamo bai yi sani da alkiblar ba ko ya ganganta yin sallar
ba a alkiblar ba.
“Yahya musulinci yana da ƙa'idoji
da tsare-tsare ga komai na rayuwa musamman ma ibada. Wannan kaɗanne daga ciki
nake tsakuro maka a yanzu, kafin kayi ninƙaya cikin taskar ilimi ka fahimci
manufata. Inaga yanzu mataki na gaba da zamuje domin gabatowar Azhar shine
karantar fatiha daga littafin ALLAH, wato Al-qur'ani. Sauran abinda zai biyo
baya zamu bisa daki-daki mu tsara yanda zaka samu karantarsu. Dan zamu sake
komawa baya muyi cikakken bayani akan tsarki a muhimmancin sa. Ina fatan kana
fahimtar duk abinda mukeyi”.
Cikin raunin murya da
sanyin gaɓoɓi Yoohan ya amsa da, “Ina fahimtar komai Uncle, ina kuma cikin ɗunbin
farin ciki da kasancewata cikin wannan addini dake cike da tarin hikimomi da
ƙa'idoji ababen birgewa da ƙayatarwa. Tabbas tun a yinin farko na fara cin karo
da ni'imomin musulinci, ina fata da addu'ar cigaba da karo dasu har ƙarhen
numfashina. A yau ina jina tamkar wani sabon hallita, tamkar ba Yoohan
Goshpower ba, lallai babu abinda ya kai addinin musulinci nutsuwa da kwanciyar
hankali. Ya ALLAH na gode maka da wannan ni'ima taka, ina roƙon ka cigaba da
tabbatar da ita a gareni batare data yanke ba koda a sakan guda ne na
rayuwata”.
Cike da farin ciki su Baba malam suka
amsa masa. Handkherchief Yoohan yasa ya ɗauke hawayen da suka ciko masa idanu.
Kafin ya durƙusa har ƙasa yana godiya gasu baba malam da suka zamewa rayuwarsu
sandar jagora wajen jawosa daga DUHU zuwa HASKE.
Saurin ɗagosa baba malam yay ya
runmesa. “Yahya bamu bane ALLAH ne, mu kawai mun kasance ne daga cikin
ƙaddararka ta alkairi, ALLAH yayi maka albarka, ya share hawayenka, ya yaye
maka damuwarka, ya karɓi tubanka, ya shafe zunubanka damu baki ɗaya”.
A tare suka sake amsawa da amin.
__________★★★★__________
A
hotel kam hankalin su Solomon a matuƙar tashe yake da rashin ganin Yoohan. Gaba
ɗaya sun tada hankalin ma'aikatan hotel ɗin da barazanarsu. Saboda maigadi ya
tabbatar shi baiga fitar Yoohan ba. Hakama wanda yake a reception yace baiga
fitarsa ba. Ga kuma motocinsu duk suna ajiye alamar Yoohan bai fitaba a
fahimtarsu.
Ganin ƙaramar magana na neman
zama babba Solomon ya kira papa ya sanar masa halin da ake ciki. Cikin
matsanancin tashin hankali papa yace su kira layin Yoohan ɗin mana.
“Sir! Duk wayoyinsa na nan
cikin ɗakin, shiyyasama muka fahimci bada kansa ya fitaba kenan”. Solomon da
jikinsa har tsuma yake ya bama papa amsa murya na rawa. Wata wawiyar tsawa papa
ya sake daka masa daga can, tare da sakin wani irin ihu tamkar zai fasa gidan.
“Solo!!!!!! Inhar yarona ya shiga
wani hali na rantse muku da ALLAH duk sai na kasheku da hannuna, na baku awa
biyar kacal akan nemansa. Idan har kuka bari na iso kano kuyi kuka da
kanku!!....”
Ƙit ya yanke wayar batare da ya bari Solo yay
ko ƙwaƙwaran numfashi ba.
Sosai hankalin Solomon ya sake
ƙololuwar tashi, hakama na sauran ƴan uwansa. Dan sunsan wanene Pastor
Goshpower, sun san kuma abinda zai iyayi, musamman ma akan Yoohan da duk duniya
bai haɗa sonshi dana kowa ba.
Suna cikin tashin hankali da
tararrabin mafita sai ga ƴan sanda kusan mota uku sun iso hotel ɗin bisa
jagorancin D.p.o Emanuel.
Su masu hotel babban tashin hankalinsu
kar sunansu ya ɓaci. suko su Solomon sune sukasan babban tashin hankalin da zai
iya samunsu da su kansu masu hotel ɗin indai har ta tabbata anyi kidnapping ɗin
Yoohan a hotel ɗin ne, kamar yanda kowa yake tunani da hasashe.............✍
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya
kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki
karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No comments