SARAN BOYE 23
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
No. 23
................Tun sakkowar Yoohan daga sashensa Momy tai saurin ajiye kofinta na barasa, dan Yoohan ya daɗe da hanata shan giya, kuma ta masa alƙawarin dainawa. Sai dai wani lokacin damuwar da take ciki kansa tasha abinta musamman da daddare idan zata kwanta barci. duk da dama wani mai yawa take sha
ba. Binsa tai da wani shegen kallo tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, yayinda fuskarta ma ta nuna shauƙi sosai fiye da yanda suke zaune. Yunƙurawa tai zata tashi amiyarta madam Monecca tai saurin riƙe mata hannu tana girgiza mata kai cikin hikima. Duk da bataso hakanba saita koma ta zauna tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciyar da harsu Papa da fira ya ɗaukema hankali basusan da wucewar Yoohan ɗinba suka juyi suna kallonta. “Lafiya Darling?” papa ya
faɗa cike da kulawa a gareta. Murmushi yaƙe ta masa da cewar “Babu komai, bara
naɗan rage kayana dai sun fara min nauyi”. Murmushi yay mata da aika mata kiss
daga inda yake. Ta miƙe tana fadin, “Thanks Honey”.
Rakata da idanu yay cike da so da
ƙauna harta haye sama sashen bedrooms ɗinsu. Sai da ta wuce da kusan mintina
goma kafin Madam Monecca ta miƙe itama tana neman excuse ɗin zuwa toilet. Duk
da kowa yasan dama amintarsu tafi zuwa ɗaya da madam Chioma babu wanda yay
zargin komai a sauran matan. Sai ma maida hankalinsu ga hirar mazajen su da
sukayi kawai.
A bakin gado Madam Monecca ta
iske Momy zaune ta dafe kanta. Ta ƙarasa kusa da ita ta zauna, cikin harshen
nasara take tambayarta damuwarta?.
Ɗagowa Madam Chioma tai
idanunta cike da hawaye tana kallon ƙawarta, tace, “Monecca! Ina cikin damuwa
sosai akan Yoohan, gaba ɗaya ya sake canjamin, ɗan kusancin da nake murnar ya
ƙara shiga tsakaninmu a yanzu neman hanyar kakkkaɓar da shima ya keyi.
Rungumarsa ma yanzu bayason yaga nayi, sai kiga ya kama ɗacin rai. Nifa na gaji
da ɓoye-ɓoyen nan, dan gashi Honey harya fara tunanin wai yay masa maganar
aure.…..”
“Aure!?” Monecca ta faɗa cikin
tashin hankali.
“Ki bari kawai, jiya da yay
maganar naji kamar na bindige shegen nan nama huta da wahalansa, Monecca zan
fitoma Yoohan a mutum kawai da buƙatata, duk da kuwa nasan shegen taurin
kansa”.
Cikin sauri Madam Monecca tace,
“Karkiyi haka, dan zaki samu babbar matsala. kidai bari muyi tunani akai. Wai
ita Mira bazata koma gidansu ba ne. sai naga kamar itace ke ɗauke masa
hankali?”.
Cikin dariyar da Madam Chioma
batai niyyar yiba tace, “Miracle fa? An gaya miki kalloma ta ishesa ne a gidan
nan. Dama fa Zamani ne keta son ganin Yoohan ɗin ya aureta. kuma ni na gama
fahimtar shima akwai tasa manufar akan hakan, shi kuma Yoohan ɗin duk da ƙyan
Miracle ɗin bata gabansa shiyyasa nima zamanta a gidan bai taɓa damunaba”.
Ɗan taɓe baki Monecca tayi tana hararar
Madam Chioma a kaikaice. a ranta kuwa rayawa take duk rintsi saita bi hanyar
mallakar Yoohan ɗin, dan itama wani Masifaffen sonsa take, tana dannewa ne
a gaban ƙawar tata kawai. Sun tattauna sosai ta yanda suke ganin ya dace a samu
Yoohan ɗin a hannu. Kafin su fito wajen sauran ƴan uwansu a cigaba da hira.
Haka gidan ya cigaba da karɓar baƙi har
dare, dan yau ranace ta ziyara a garesu, musamman ma gidan papa daya kasance
babban mutum a wajensu.
Yoohan bai dawo gidanba sai yamma lis,
ya samu giyar dasu Osen suka sha ta ɗan sakesu, harma sun fito daga sashensa
Solomon ya shiga ya gyara. Duk suna harabar gidan zaune dan wasu abokan nasu
sun ƙaru saboda jin Yoohan ɗin na gari, shima sai kawai ya zauna a wajensu duk
da ba firar yakeba sosai.
______________________________
*_SAUDIA_*
Duk da Adawiya na ƙoƙarin ɓoye halayenta
hakan bai hanata sakin layi a wasunl lokutan, dan babu abinda ke sakata takaici
da ƙunar zuciya kamar yanda Nu'aymah taƙi nuna damuwarta akan duk abinda take
mata. Gaba ɗaya Nu'aymahr ma ta maida hankalinta ga ibada ne kamar yanda ta ɗauro
niyya tun daga gida.
Tayi mugun yin watsi da shirmen Adawiyar
dan ta gama karantarta tsaf akan lamarin nata, to dama tasan tun suna secondary
ma Adawiya tasha haɗata faɗa da ƙawayensu, ta kuma koma ta noƙe ta nuna ba ita
tayiba. Amma sai bata taɓa nuna mata ta gane komaiba akan hakan, dan duk sanda
taje ta sanarma Umm Adawiya ta mata kaza sai Umm ta lallasheta da nasiha da
nuna mata muhimmancin haƙuri da ɗan uwa. Hakanne ke daƙile Nu'aymah daga ramuwa
ga Adawiyar gashi har hakan ya zame mata jiki.
A wannan tsukun kuma data
fahimci Adawiya ta canja sabon salon halaye sai itama ta canja takunta a kanta
tana binta da gashi cikin ruwan sanyi, a ranta tana zargin kenan dama Adawiya
na son Yah Ab komi?. A duk sanda tai wannan tunanin takanyi ƙoƙarin ganin ta
ƙaryata zuciyarta, dan bata taɓa ganin alamar hakan ba ga Adawiya a dacan baya.
A ganinta yanzu dai daɗin aurene yasa take ganin tafita kusanci da Abdallahn
shiyyasa take shirya yaƙarta a kansa.
Yau ma kamar kullum Nu'aymah na ɗan
yin barcin rana a falo, dan da daddare tafi maida hankalinta ga ibada ne,
Abdallah ya shigo gidan. Adawiya ta wuce makaranta. daga hajjo sai Nu'aymah. Da
tare suke da Hajjon a falo zaune suna ɗan hira sai barci ya kwasheta, itama
hajjon saita nufi ɗaki ta kwanta danta huta.
Kafe Nu'aymah da idanu
Abdallah yayi ko ƙyaftawa ba yayi, ya ƙaraso inda take yay tsaye kanta yana
cigaba da kallonta tamkar mai nazarin wani abu. Cikin barci Nu'aymah taji
alamar tsayuwar mutum a kanta. A ɗan firgice ta buɗe idanu saboda barcin nata
baiyi nisaba sosai. Ganin Yah Ab tsaye a kanta ya sakata sake zabura tana binsa
da kallon tuhuma itama. Sai kuma ta kumbura baki tana ɗauke kanta cike da
takaicinsa.
Fuskarsa a haɗe ya zauna a
kujerar da take kwance, hakan ya saka Nu'aymah saurin miƙewa sosai tana faɗin,
“Yah Ab minene haka wai?”.
“K kika cancanci wannan tambayar
ai?”. Ya faɗa shima yana miƙewa yasha gabanta fuskarsa a haɗe, ya cigaba da faɗin,
“K harkin isa ki dinga wulaƙantani akan wani banza can Nu'aymah? Kinzo inda
nake amma sai wani basar dani kikeyi”.
Cikin rashin fahimta take
kallonsa, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta raɓashi zata wuce. Sake shan
gabanta yayi yana mazurai, “Nabaki izinin tafiya ne?”.
Idanunta cike da ƙwalla tace, “To idan
na zauna mizan maka? Kodan kaga nazo na zauna a gidanka kakeson ƙuntata
rayuwata?”. Hannu ya ɗaga tamkar zai ƙwaɗa mata mari sai kuma ya fasa ya
dunƙulesa yana taune lip ɗinsa jikinsa na tsuma. Yace, “Uban wanene Ameer?”.
Cike da takaici
Nu'aymah ta kallesa ta watsar, kamar karta bashi amsa sai kuma mamakin abin
nasa yasa ta kallesa da ƙyau. “Ban gane mikake faɗa ba Yah Ab?”. A hasale yace
tayaya zaki gane mara mutunci. Nu'aymah wai harni zaki iya gudammawa a daren
aurenmu saboda wani jaki? Kinsan baƙya sona miyyasa kika yarda aka saka mana
ranar aure?”.
Sallamar Adawiya da batai zato
ko tsammanin Abdallah zai dawo gidan a wannan lokacinba ya hana Nu'aymah da
mamaki ya kume bashi amsa. Turus Adawiyan tayi tana kallonsu, dan wanda bai
saniba zai ɗauka ne wata maganar arziƙi sukeyi da juna.
Binsu take da kallo tamkar idanunta zasu
zubo ƙasa, Abdallah yay ƙaramin tsaki yana barin wajen ya nufi ɗakinsa. Har
Nu'aymah ta cira ƙafa itama zata bar wajen Adawiya ta dakatar da ita ta hanyar
riƙo mata hannu. Juyawa tai tana kallonta fuska a haɗe sosai, “Malama sakeni”.
Nu'aymah ta faɗa a hasale.
“Anƙi a sakekin, idan kin isa kiyi duk
abinda zakiyi. miya haɗaki da mijina?”. Kallon tsantsar mamaki Nu'aymah kema
Adawiya, sai dai kuma a fili saita saki lallausan murmushi da har ya bayyana
haƙoranta. Tace, “Tunda kinsan mijinkine mizai hana shi kije ki tambayesa miya
haɗashi dani? Inaga kamar hakan zaifi birgewa a gareki shashasha kawai”. Ta
ƙare maganar da fisge hannunta tai gaba tabar Adawiya da huci.
Hajjo data hango tahowar
Nu'aymah saita saki labulen cikin ɗakin ta zauna a bakin gado. A haka Nu'aymah
ta shigo ta sameta. “Hajjaju kin tashi ashe?”. Nu'aymah ta faɗa tamkar babu
wani abu daya faru. Murmushi Hajjo tayi tana kallonta, “Ba dole na tashiba
tunda kin gaza zuwa ki tadani mu wuce massallaci”.
Kusa da ita ta zauna tana dariya, “Ho hajjonmu,
yanzu kuma dana tadakin cazaki ban barki kin rintsa ba, gara mu maidake da
ƙwarinki karsu Abba suga kin sake rugurgujewa”.
Duka Hajjo ta kaima Nu'aymah da filo.
Hakanne ya sakata tashi ta shige bayi da gudu tana dariya. Cike da tausayinta
Hajjo ta sauke ajiyar zuciya, a ranta kuma tana ƙulla abubuwa da dama game da
rayuwar Nu'aymahr
A falo kam Nu'aymah
na shigewa Adawiya ta nufi ɗakin Abdallah a fusace, babu ko sallama ta tura
ƙofar ta shiga. Sai dai ganinta yay kawai a kansa kamar an jehota. Kallo ɗaya
yay mata ya ɗauke kansa. Hakan ne ya sake hasala mata zuciya, sai ta fashe masa
da kuka. “Yanzu Yah Ab abinda kakemin kana ganin adalcine? Ni dake matarka baka
da lokacina amma kanada lokacin dawowa gida da wuri dan ka kasance da Aymah?
Badan ALLAH yasa yau na shigo gidan da wuri ba bama zansan hakan na faruwaba
tsakaninku. Shin wai da mi Nu'aymah ta fini ne? Wlhy sai ALLAH ya sakamin duk
cin amanata da akeyi, kuma ni na gaji zan kira baba malam na faɗa masa komai
tunda naga ita hajjo goyon baya take baku ma, ƙilama wataran a gabanta zaku
shiga ɗaki ku rufo bazata tankaba saboda tana tsoronku......”
Wani wawan mari ya sauke mata a
fuska da saida taga stars na mata kaikawo, balle dama ga azumi. A take ta zube
ƙasa da sakin wata ƙarar kuka data kai har kunnen Hajjo.
“Kai Abdillahi lafiya kuwa? Mike
faruwa hakane nakejin kukan Adawiya?”. Ta ƙare maganar tata dai-dai lokacin da
take ƙarasowa cikin ɗakin. Ganin Adawiya kwance ƙasa dafe da kunatu ya saka
hajjo zaro idanu, “Mikai mata Abdullahi?”.
Cikin ɓacin rai yace, “Hajjo barni da
ƴar iskar nan kawai, wlhy tai wasa wataran saina karya ƙasusuwanta a gidan nan
tunda ita kamar dabba take”.
“Ya isa haka”.
Hajjo ta faɗa tana ɗago Adawiya dake ƙasa tana cigaba da sakin gunjin kuka.
Saida ta zaunar da ita saman kujera sannan ta sake tambayar Abdallah miya
faru?. Faɗa mata komai yayi amma banda tsayuwarsu da Nu'aymah, baisanma ita
taji komaiba.
Cikin ɓacin rai Hajjo tace, “Adawiya
dama baki da wayo haka? Ita ƴar uwar takice kuma tazama abar kishi a gareki?
Har kike jifansu da wannan mummunan lafazin ita da mijinki? Adawiya yaushe kika
bari ƙawayen banza suka canja miki tarbiyya ne? Har haka. To wlhy ki shiga
hankalinki, idan kuma ba hakaba ni bazan ɗauki wannan banzan halayen a cikin
zuri'ata ba, saina ɓatama kowa rai a cikinku har iyayen naku ni babu ruwana.
Bandama iya shege kowa na fama da ibadar ALLAH a baki ke kina biyema sheɗan
yana ɗoraki akan dokin zuciya. To idan na sakejin makamancin wannan zancen
lallai sai kinyi nadama shashasha kawai. Banda ƙaddara da yanzu ita wadda kike
cin zarafin ba itace matsayin matar tasa ba”.
Haka Hajjo taima Adawiya tas
sannan ta fito ta barsu. Duk abinda akeyi Nu'aymah najinsu, sai dai ko tari
bataiba balle a fahimci ta sani ɗin. Daga ƙarshema sukai shiri suka wuce
massallaci, suda gidan kuwa sai anyi sallar asuba kuma.
Tun daga wanan ranar Adawiya ta shiga
fishi da kowa a gidan. Daga gaisuwa bata sake tankama wani. Ahmad yamata nasiha
harya gaji ya watsar da ita shima. Bayan kwana biyu da yay dai-dai da cikarsu
kwanaki biyar da zuwa, ashirin kuma ga watan azumi Nu'aymah ta tattara
inata-inata ta koma massallaci zaman ittiqafin.
Abdallah yaso hanata, sai dai
Hajjo tace ya barta tai ibadarta yamafi zaman nata a gidan aita fitina. Badan
yasoba ya haƙura, dan yaso a wannan zaman suyi magana ta fahimta da Nu'aymahr
ya samu ya lallaɓa hajjo dasun koma a ɗaura musu aure.
Bayan barin Nu'aymah gidan sai
ga Adawiya ta saki jikinta, ashe dama Nu'aymahr ce natsalar rayuwarta. Babu
wanda yace mata komai. Saima hajjo ce taima Abdallah magana akan su shirya shi
da Adawiyan dan tare zasu wuce Najeriya ayi bikin salla. Kai tsaye Abdallah ya
nuna cewar bazaije ba, sai dai Adawiya, dan shi bai manta ALLAH ya isan da mahaifiyarsa
tai masa akan zuwan nasaba.
Balbalesa da masifa sosai hajjo tai dan
ita batasan dalilinsa na bijirewarba. da taga dai ya tirje ɗin saita kira baba
malam ta faɗa masa komai. Shine ya kira Abdallahn cikin bada umarni ya sanar
masa ya shirya suzo salla gida tunda suna samun hutu a wannan lokacin.
Abdallah ya shiga tsaka
mai wuya sosai akan hakan, dan yasan dai umarnin mahaifiyarsa dana baba malam
babu wanda yake da damar tsallakewa a ciki, dan duk sunada daraja da kima a
idanunsa da rayuwarsa.
_________________________
*_NIGERIA_*
A kwanaki biyun nan abubuwa sun sake
tsamari akan Yoohan, gaba ɗaya neman birkicewa yake saboda rashin samun barci,
tun daga jiya zuwa yau yaƙi magana da kowa a gidan, yama kulle kansa a ɗaki ya
hanama kowa ganinsa. Momy tayi kukan tayi roƙon amma yaƙi buɗewa. Hakama su
Gebrail sunyi nasu ƙoƙarin ya sharesu.
Amma saboda ƙarfin hali da burinsa
nason cika alƙawari sai gashi a safiyar yau talata yayi shirin tafiya kano.
Tunda safe ya bama Solomon umarnin faɗama guards ɗinsa su tafi kano. Su kuma ya
nema musu ticket guda uku. Solomon nason tambaya akan hakan yanajin tsoro, dan
haka yaja bakinsa yay shiru yaje dai ya cika umarninsa
Kusan ƙarfe huɗu na
yamma sai gashi ya sauka ƙasa cikin shigarsa ta suit blue mai haske. sun masa
bala'in ƙyau duk da yana a yanayin da a kallo ɗaya zaka fahimci akwai damuwa
tattare da shi.
Momy ce kawai zaune a falon sai
Victoria da Abraham. Cikin girmamawa a garesa yaran suka shiga gaishesa. Hannu
ya ɗaga musu kawai tare da ƙarasowa inda suke duk ya shafa kansu batare da yayi
magana ba..
Ya maida dubansa ga Momy da idanunta
suka kumbura saboda kuka, ɗauke kanta tayi ita a dole fushi take da shi. Baice
komaiba ya ƙaraso inda take ya tsaya a gabanta tare da riƙe kunnuwansa da
hannayensa alamar ban haƙuri.
Bata iya dogon fushi da Yoohan ɗinta.
Dan haka tai murmushi tare da miƙewa ta rungumesa. Yau dai ya daure bai tureta
ba, sai da ta gaji dan kanta ta sakesa sannan, ta amshi tie ɗin hannunsa ta ɗaura
masa tana faɗin, “My Boy nikam yaushe zaka fara saka necktie da kanka?”.
Bai bata amsaba, sai dai ya sake ɓata
fuska alamar shagwaɓa. Da ƴar dariyarta ta shafa masa kwantaccen sajensa da
yasha gyara yau, ya kama hannun nata ya sumbata kaɗan.
“Ina zakaje ma wai?”. Ta tambaya
tana tsatstsaresa da idanunta manya. Da ƙyar ya buɗe baki wajen bata amsa da
“Kano”. “Kano!! kuma Yoohan? Mizakayo a kano kaida kake cikin wannan halin?
Badai aiki ba?”. Kansa ya girgiza mata, batare daya bata wani ƙarin bayani ba
yace mata, “Bye” yana nufar ƙofa.
Saurin binsa tai tana kira, amma
sai yaƙi tsayawa, saida ta haɗa daɗan gudu ta cimmasa, duk da kuwa tafiyarma ba
wani sauri yakeba saboda rashin ƙwarin jikinsa. Yanda ta riƙosanne ya sakashi
waigawa ya kalleta. Tace, “Ina tambayarka mizakayo acan amma ka taho baka
kulaniba Yoohan”.
Kansa dake faman masa ciwo ya dafe kaɗan,
kafin cike da ƙosawa yace, “An gayyaceni ne” danshi baison yin ƙarya a
rayuwarsa, kamar yanda ya tsani kuma saɓa alƙawari. Yana gama faɗa ya zare
hannunsa zai juya ta kuma riƙewa. Yanzunkam bai juyoba sai da yaja wasu
sakanni. Muryarta da damuwa ta zagayo gabansa tana magana. Amma maimakon ya
bata amsa sai ya saka yatsansa akan baki yace “Shiii!!!”.
Shirun kuwa tayi tana kallonsa,
ya ɗaura yatsunsa saman baki yay mata alamar *_Smile_* kamar yanda ya saba mata
aduk sanda ya ganta a damuwa tun yana yaro. Duk da batason yin hakan saita
murmusa. Yay mata jinjina yana ɗan lumshe idanunsa dake a kumbure sosai.
Tanaji tana gani ya shiga mota driver
ya jasu shi da Solomon suka bar gidan, gashi Papa bayama ƙasar jiya sukai
tafiya shi da Uncle Zamani.
★★★★★
Airport driver ya kaisu. inda
acan suka haɗu da Manager Hamza Ibrahim yana jiransu. Sun gaisa cikin mutunta
juna Hamza na mamakin ganin Yoohan ɗin a ƙunci fiye da waccan ranar. Ga
idanunsa da fatarsu tai jajur hakama farar fuskarsa. Haka kawai yaji a ransa
akwai abinda ke damun Yoohan ɗin. amma sai baiyi magana ba suka nufi ciki.
Ƙarfe biyar da rabi jirginsu
yabar Abuja zuwa birnin dabo kodami kazo mun fika🤗😜.
Kamar yanda Yoohan ya iske Guards
ɗinsa na jiransa haka suka iske motoci biyu na tarbarsu kuma. Hakan ya sai ya
sake birge Yoohan matuƙa, dan haka bai shiga tasa motarba ya shiga wadda aka
aiko musu, Guards ɗinsa kuma suka bisu a baya.............✍

No comments