MIN QALB 28
MQ 28_*
Cikin nutsuwa da girmamawa Modibbo ya kalli Andi a natse
yace"
Tsit Sukayi kowa na kallon Andi da yanayinsa sbd maganar da
Modibbon yayi ana jiran jin me andin zaice.
Zama batareda ya dagoba ya kallesu yace"
Alhaji qarami na damqa case din a hannunka a shigar da qara
me qarfi akan yarinyar da mariqanta idan ka Gama binciko zancen gaskia ne ko aa
akan laifin qage da shirin batawa zabeera suna ta hanyar qage akan cikin qarya,
Hakama asaka likitoci masu kyau suyi bincikenta aduba idan
da akwai ciki a jikinta ko Babu,
Kada abari Khalil yasan inda aka Kai case din duk tsanani hakama
MAHMOUD ZABEERA kada abari ko kadan yasan Abinda yake faruwa tunda baya Nan sbd
acikin minti biyu zai iya saka agano wa Dan uwansa inda yarinyar take.
Cikin biyayya alhaji qaramin yace"
Angama Inshallah Andi.
Sahirtaccen numfashi Modibbo ya sauke zuciyarsa na daci da
alamarin sbd baiso komai ya lalaceba.
Amatu na isowa sashen motar civil defense din na fakawa
bakin qaton gate din ZABEERA
Alhaji qarami ne yafito daga palon ya kalli khalil
yace"
Ka shiga ciki Andi na zaiyi magana da Kai.
Kasa motsawa yayi ya juya ya kalli Inda Amatu ke tsaye
yanajin kunyar kansa daya Bari har suka tsintsi kansu a irin wannan Matsin
dabai samo mafita ba tuna farko sukai aure tun kafin zuwan wannan ranar.
Kallonsa itama takeyi zuciyarta na sake karyewa da wannan
masifar
Itadai komai tsananin hukunci da zafinsa zata dauka matuqar
ba rabata za'ayi da Khalil din ba.
Sake maimata Masa alhaji qarami yayi Yana kallonsa cikin
fushi Wanda yasashi dauke idanuwansa daga Kan Amatun yafara takawa ahankali ya
nufi qofar palon yashige.
Yana shigewa alhaji qarami ya kalli Amatu dake tsayayo
hawaye masu ciwo tanajin zuciyarta na sake karyewa ya nuna Mata hanya alamar
suje.
Da sauri umme tayi gurinta tana qoqarin riqeta anty zarah
data biyota tayi saurin rungumeta ta baya tana sake sabon kuka sbd su duka sun
San matuqar aka tafi da Amatu ba lallai su
Kuma ganinta arayuwarsu ba.
Daga umme har anty zarah din da Amatu kuka sukeyi sosai
musamman umme datasan idan Amatu ta tafi rayuwar Khalil dinta na cikin hadarin
rasata.
Haj maryam ma a katse take har lokacin sbd Basu Gama sanin
inda Rana zata Fadi ba gashi dai Nuratun ma kuka takeyi sosai sbd wannan
fitinar tasan shikenan Khalil bazai taba sonta ba yanda take fata komai yagama
lalace Mata.
Matane su biyu da uniform dinsu na civil defense manya manya
dasu kowacce tanaji qarfi da rashin Imani sbd Babu kalar bahaushiya acikinsu
bare ace musulmai suna qarasowa alhaji qarami ya nuna musu Amatu sukayi kanta
suka kana hannuwanta biyu suka Fara janta umme da anty zarah suka bisu abaya suna
roqonsu cikin tsananin kuka Amma tuni suka wuce da ita,
Salman kuwa cikin palon yayi da sauri ko sallama baiyiba ya
tsaya gabansu Andi ya kalli khalil dake sunkuye da Kai yace"
Dan Allah Andi a sassauta Amatu a tsaya a fahimci zancen ta
hanyar nutsuwa mace ce ita wlh rayuwarta zasu lalata idan aka Bari suka tafi da
ita aka kulleta Dan Allah....
Da sauri Khalil ya juyo ya kalli Salman din cikin tsananin
firgici bai tsaya gama sauraren Abinda yake fadaba ya turesa ya fice da gudu ko
gabansa baya gani.....
Ba Andi kadaiba hatta Modibbo Saida ya kidima da wannan
alamarin,
Yaransu da Basu taba dago Kai sun kallesuba idan suna musu
Magana,
Yaransu da Babu Abinda suka sani arayuwa bayan yimusu
biyayya da bin umarninsu Koda baiyi musu daidaiba Amma ayau akan mace kamar
abinda sukai shekaru suna Dora 'yayansu akai na neman rushewa,
Yau Andi da kansa Yana zaune ake tafiya abarsa yana magana
hakama shima wannan yau shi Andi da kansa yake kalla Yana cewa ba'ayi Abinda
yakamata ba....da matsala,da matsala babba ma kuwa.
Juyawa Salman yayi yabi bayan Khalil Yana fasa maganar da
yayi niya cikin 'dacin Rai idanuwansa na sake sauyawa.
Koda suka Isa bakin qofar zabeera tuni aka wuce da Amatun
motar alhaji qarami nabin bayansu.
Cikin tsananin tashin hankali Khalil ke qoqarin bin motar da
gudu da qafafunsa Salman yayi saurin riqesa Amma ya fizge yabi motar da gudu
Salman da umme na kiransa cikin tashin hankali umme ke cewa''
Salman dauko mota da sauri kabisa idan yayi gudu ciwonsa zai
tashi Dan Allah kabisa kada kabari komai yasamu Khalil shikadai nakedashi.
Ciki yakoma cikin sauri jikinsa har rawa yakeyi yafada mota
yajawo da gudu yabi Bayan Khalil din.
Koda ya cimmasa harya Fara galabaita numfashinsa yafara
sarqewa.
Da sauri ya tsayar da motar ya fito yakamasa yasaka motar ya
zagayo ya shiga Yana qara Masa sanyin AC din motar Yana janyo tissue da yawa ya
miqa Masa yana qoqarin daidaita muryarsa yace"
Dr kada kayi Abinda zai kaika kwance sbd kana buqatar tsayuwa da qafafunka gurin
fitarda Amatu cikin wannan matsalar.
Kasa Magana Dr khalil din yayi Yana fitarda numfashi cikin
yanayi na azaba ya lumshe idanuwansa dasukayi jajir ahankali yace"
Muje gidansu kawu Ina buqatan daukesu daga gidan yanzu.
Hanyar gidan suka kama Yana tuqi Yana kallon Khalil din
daketa fama da numfashinsa Dan daidaitawa kada yabari yaci qarfinsa.
Koda suka Isa Salman ne ya bude Masa motar yafito Yana sake
qoqarin daidaita numfashinsa ya share zufansa suka nufi cikin gidan.
Zaune kawu yake Yana sauraron radio iyami na zaune gefensa
tana shafawa qafarta daya Jan lalle sai gasu sunshigo da qaramar sallama suka
qaraso iyami na ganinsu ta ajiye lallen datake qoqarin sawa dayar qafar tana
musu maraba da zuwa duk da dai yanayinsu yasata fargaba musamman sbd zufan da
kowannensu yaketa sharewa bama kamar Dr daketa fama da numfashinsa Yana dannewa
sbd kada agane halinda yake ciki.
Kallo daya kawu yayi musu yasan ba lafiya ba
Ya tashi zaune daga kishingiden dayake ya janyo radionsa
kusa ya qure murya sbd kada aji zancen dazasuyi ya kalli khalil daya zauna
gefensa yace"
Likita lafiya naganku kamar 'yan saqon mutuwa???
Salmanu lafiya kuwa??
Numfashi Dr ya sauke Yana lumshe ido sbd azabar dayake ji ya
kalli kawun cikin taushin murya yace"
Kawu zanyi maka bayanin abindake faruwa Amma Dan Allah yanzu
inason ku biyoni muje wani guri muyi maganar.
Kallon juna kawu da iyami sukayi suka sake maido da kallonsu
kansa cikin rawar murya iyami tace"
Akwai Abinda yasamu Amatu ne?
Meya faru ne kafara fada Mana mu musulmaine zamu dauki
qaddara koma menene.
Ajiyar zuciya salman ya sauke cikin sake bawa kansa nutsuwa
yace"
Ba Abinda kike tunani bane iyami Amma dai yanzu muna buqatar
barin Nan ne tukuna.
Kallon Dr khalil kawu yayi da kyau kafin ya miqe Yana cewa'
Iyami sanyo hijabinki muje na yarda da Khalil fiyeda kowa
arayuwata Dan haka koma menene Yana mahimmanci barin Nan din tun sun fada.
Jiki mace iyami ta miqe ta wanke qafa dayar dakeda lalle ta
fada daki ta sanyo hijabi hannuwanta na rawa sbd hakanan takejin tashin hankali tun kafin suji
koma menene yake faruwa.
Babu Wanda suka fadawa suka rufe dakunansu suka fice.
A mota Dr khalil yakira babban yaronsa na asibiti Ibrahim ya
sanar dashi Yana buqatar gidansa daya Gama be tare ba na kwana biyu,
Cikin sauri yace angama likita.
Anguwar can take nesa kusan hanyar wajen gari duk da akwai
mutane da yawa a anguwar Amma kasancewar dukkaninsu sun Saba da anguwannin
cikin gari sai sukaji anguwar wani iri.
Gidane qarami me daki biyu sai bayi da kicin a qaramin
tsakar gidan sai daki 'daya a hanyar shigowa.
Zaune suke akan qatuwar tabarmar da Ibrahim din yakawo suka
shimfida kowannensu shiru sunkasa qwaqqwaran motsi alokacinda Dr khalil yagama
yimusu bayanin dukkanin Abinda yafaru.
Wasu irin hawayen baqin ciki iyami keyi tana sauke kanta sbd
tsananin kunyarsu Khalil din ahankali Tace"
Bantaba tunanin son kudi da rashin hankalin Amatu yakai har
haka ba,
Yanzu wace irin masiface wannan ta dauko wadda bamusan ta
Yaya zamu fuskancetaba.
Shiru kawu yayi sbd nisa da yayi a tunani Yana Dora dukkanin
laifin akansa sbd shine yafara daukar rayuwa da rashin mahimmanci har su Amatun
suka dauka shiyasa tayi irin wannan alamarin me girman gaske Wanda ba mutuncin
Zabeera ba kawai shi kansa idan zancen ya fita da wane Ido zai kalla mutane duk
rashin kunyarsa kuwa.
Ganin yakasa magan yasa Salman yashiga basa Magana Dan rage
Masa nauyin zuciya Amma sam ko kadan yau bayajin komai bayan qunci.
Da zasu tafi Dole yace sutafi dashi gurin neman ofishin da
aka Kai Amatun.
Yawon ofishin Yan sanda da civil defense suka Fara tun abin
na aikin hkr har suka sake Shiga tashin hankali sbd duk inda sukaje ba anan aka
kawota ba tuni suka fahimci Alamarin Babu sauqi acikinsa Babu Wanda baishiga
cikin mummunan tashin hankali acikinsuba musamman kawu dayake ganin kamar
kasheta za'ayi.
Wasa Wasa har dare Babu labarin komai daganan suka nufi wata
local government din dake kusa canma baa kaitaba.
Dawowa sukayi suka ajiye kawun anan gidan Ibrahim gurin
iyami suka nufi zabeera cikin sabon tashin hankali.
Koda suka Isa Kai tsaye gurin Andi suka nufa inda suka
tararda Modibbo acan anan suka zube qasa Khalil din na roqo da ban hakuri
abisaga laifin Amma Sam Babu wani sauqi sbd atake Andi yabata umarnin ya rufe
maganar case din daga ranar kada Wanda Yakuma tayarda zancen.
Kasa komawa ciki Khalil yayi yafice daga zabeera din yaje ya
siyo abinci da kayan buqata ya nufi gurinsu kawu.
Zaune suke tsakar gidan zaune sunyi shiru Babu me Magana
acikinsu kowanne da tunanin dayakeyi yashigo da sallama suka dago suka kallesa
cikin sanyi da mutuwar jiki.
Qarasowa yayi ya zaune gefen kawu tareda ajiye musu abincin
Yana qaqalo qwarin gwiwa yadan Basu Magana kafin ya miqe ya fita yadawo motarsa
ya zauna tareda rintse ido sai kawai hawaye suka gangaro Masa Yana dafe kansa
yace"
Allahumma ajirni fi musibati..
Zaune ya kwana cikin mota a qofar gidan kamar yanda Suma
ciki su kawu Basu rintsiba iyami kwana tayi sallah.
Gari na wayewa ciki yashigo anan yayi sallah dakin farko
yafito yaje yasiyo musu abinci yakawo haka suka takurasa shima yadan ci kadan
yafice zuwa zabeera.
Duk yanda yaso ganin Andi ma abin ya gagara sbd hanyar
sashensa anrufe ga Modibbo ma yaqi
ganinsa sai alamarin yaqara daukar zafi Yana fitowa daga zabeera Salman
yakirasa yake sanar dashi anshigarda qarar maganar sbd gashinan 'yan jaridu
harsun buga zancen ya Basu koina alamarin yayi Muni sbd dukkanin inda amatu
tayi aiki anbinciko kowa yabada shefar qwararriyar barauniya ce Dan haka yanaga
suyi qoqarin sanin inda take ayi belinta kafin case din yashiga Court akwai
matsala sbd itada umme ne zasu kwana ciki musamman idan sunan MD ZABEERA yafito
amaganar Andi da Modibbo bazasu dauka da saukiba.
Cikin tsananin tashin hankalin dayafi na farko Dr khalil
yasake bazama yawon neman inda aka rufeta ga bangare daya su kawu sun matsa
Saida ya maidasu gida saidai tunda suka dawo ake nunasu da Abinda Amatun tayi
inda aketa cewa Ashe shiyasa khalil zabeera ya tsaya musu yaketa kashe musu
kudi tarewa tayi a gidansu Yana muamala da ita.
Duk masifa da fadan kawu yakoma ko zaman waje ya dainayi sbd maganganun hadda
qari da cin zarafi sawa akeyi wainda suke cikin gida dayane kawai suke ganin
mutuncinsu har lokacin suna Kuma tayasu baqin cikin wannan alamarin.
Kwanaki kusan shida kenan Yana bulayi yakasa samunta,
Duk iya inda alamarin yake ya girmama,
Ko abinci baya iyaci sai ruwa idan ummensa ta takura Masa
yasha,
Ya rame cikin kwanki shidan yakoma kamar bashiba,
Ya daina zuwa asibiti gabaki daya sai sakin kudi yakeyi
koina ana bincika Masa kowace station da office din civil defense Amma Babu
haske.
Zaune yake gaban kujerar dake kallon insfector Garba acikin
office dinsa Yana kallonsa da idanuwansa dasuka shige sbd damuwa ahankali
yace"
Zanbaka dubu dari biyar kamar yanda ka buqata cikin awa
biyar zaka bincikamin dukkanin ofishinku na cikin gari da qauyuka.
Murmushi insfector Garba yayi tareda kallon Dr khalil din
yace"
Mutum me mutunci da girma dai kamar wace irin qaddarace zata
kaika batarda kudade masu yawa irin haka akan Amatu da kowa yasan dabadan
kudinkaba wlh ko kallo bazaka ishetaba sbd Ina fada maka yarinyar terror ce
tasan siririn iya sata......
Miqewa yayi Yana katsesa da cewa''
Mungama Magana Ina jiranka Nanda awa biyar din.
Ficewa yayi ransa abace yabar station din Yana sakejin kamar
zuciyarsa zata fashe babu me bude baki yafadi alkhairi akan Amatu duk station 'dinda
yaje.
##Mamuh#

No comments