Breaking News

SAI A LAHIRA 19

 


*🎀SAI A LAHIRA🎀*



              *NA*



*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 19*



*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*





........Ango ya shigo shi da abokinshi Garba inda suka hango ta zaune akan katon gadon Jin motsinsu yasa tayi maza tajawo mayafinta ta rufu inda Garba ya zuba mata ido Yana kallon zanen fulawar hannun ta da kafarta inda yake Jin gaban shi na dukan Zuciyar shi saboda har ga Allah kallo Daya yayiwa nafisatu yaji wani Abu tamkar shock yajashi  bai taba ganin matar da ta firgitashi irin matar abokin na shi ba duk da kasancewar shi Dan bariki me son sheke Aya


Ango ya zauna kusa da Amarya Yana bude Mata rufin da tayiwa fuskar ta

"Daure Amarya ta ki bude min kwalliyar da Kika yi min Mana ai yanzu mun Zama Daya ko"?

Ya yaye Mata rufin inda Garba ya bita da kwala kwalan idanunshi ya na hadiye yawu makwat ya shafi sumar kanshi yasoma magana.


"Nafisatu inayi Miki barka da zuwa gidan abokina  Ina Kuma fatan kuyi Zama na Amana Kuma har karshen Rayuwa 

"Abokina ya Dade da mutuwa a cikin so da kaunar ki ina fatan kema Zaki tallafa mishi da martanin so da kaunar da yake Miki. Duk wannan magana da Garba yakeyi idonshi kyam akan ta Yana Kuma fasalta ta azuciyar shi inda kanta ke sunkuye shima angon idonshi akanta Yana murmushi

Jin shirunta yasa Garba cewa "bakice komai ba nafisatu? 


"To me zance? Ubangiji ya Kade duk wata fitina acikin zaman ibadar mu yasa mu fita hakkin juna . "Maganar kauna kuwa tunda shi Ubangiji ya zano shine mijina ai Dole ne in tallafe shi tunda Arayuwa ta Ina rokon Allah mafi ALHERI gareni da Rayuwa ta kaga duk abinda ya kaddaro sai ya zamo shine ALHERIN.


Su duka sunyi mamakin kalamanta don Basuyi zaton wayonta da hikimar ta sun Kai haka ba don haka tana dire Zancen ta angon ya Riko hannuwanta ya na kissing din zanen fulawar inda yacewa Garba ya tashi ya tafi sai sunyi waya.


Garba yayi murmushi "Abokina korata kake yi dai na Gane ka . To asubah ta gari ya dubi nafisatu "Amarya mu kwana lafiya Amma fa....

Bilya ya katse shi  "Da Allah jeka abinka malam kar ka Dame Ni .

Da haka Garba ya fice nafisatu tayi mishi tsaye cikin ranshi inda ango ke tarairayar amarya Yana ta bare bare


Washe gari ta shiga kichen ta hada girki me armashi bayan tea Wanda yaji kayan kamshi ta Kuma soya kwai da agada sai Kuma farfesun kaza me Romo Wanda tarugu da albasa sai farar shinkafa da miyar dankali  tuni tayi wanka ta shirya inda ango ke ta sharar bacci Wanda sallar asubahi ba tace ya tashi yayi ba duk da ta tashe shi Amma yaki tashi har yanzu da agogo ke neman buga karfe Tara na safiya.


Ta gama Shirin cikin wani material kalar marun Wanda ya amshe ta tayi kyau sosai inda ta nufi dakin don ta tadoshi 

Ya farka Yana binta da kallo don da gaske Bai taba Jin son wata mace ba kamar nafisatu kaf Mata Taran da ya aura Babu ya nafisatu  ganin kallon da yake Mata ne yasa ta hura mishi iska a idon shi

"Na sauya maka ne ? Ruwa fa na jiranka a bayi har Tara ta buga.

Ya riko hannunta "Ai sauyin da kikayi min ba kadan bane nafeesa Anya kuwa akwai wata mace bayan ke? "Mata kuwa don wasu idan na shiga cikin su ko kyalli na ba za agani ba So duniya Fadi gareta in kafi wani to wani ya fika a idonka ne kawai nafi sauran Mata wani ko kallo ban Isa yayi min ba . "Aiko Wanda Bai kalle ki ba nafisa sai dai Wanda hankalin shi bai kawo kina Nan ba 

"Ni dai tunda na Dora ido akanki mukayi sallama da nutsuwa sai fa jiya da na tabbatar kin Zama tawa. "Ka saka ranka inuwa Ni din takace  shiga ka fito abinci na jiranka.

Haka yafito yayi sallar Rana na kallon shi ya Kuma ci abincin da yake ta zuba Santi don gaskiya Babu karya idan yace babu matar da ya taba aurowa wadda ta kamo nafisatu akan komai sai yaji indai zasu dauwama ahaka bayajin zasu samu wata matsala har ta kaisu ga kassaruwar aure matsala gudace wadda baya fata itace ta yin ciki da haihuwa in har nafisatu ta Mara mishi baya akan hakan to shi da ita mutu ka Raba ne.


Haka Zama ya Mike cikin aminci da salama inda ya bijiro da son yi Mata tsari duk da bai fito ya fada Mata gaskiyar komai ba 


Lamarin ya farane da Bata kwayoyin fils na Hana samuwar ciki tunda ya fara Bata kwayoyin Bata taba yi mishi gardama ba don tana ganin ba zai taba cutar ta ba 

Ta dauki tsayin lokaci tana bankar kwayoyin ba tare da ta bijire ba har dai  ayau ta gaji da hadiyar kwayar da Bata ciwo ba ta Kuma nemi ba Asin kwayar 


Shima Bai boye Mata ba ya sanar da ita ta Hana daukar ciki ce. Gabanta ya Sara ta dubeshi "haba  BB sunan da take fada mishi.

"Me yasa kazamo a wannan turbar? "Dama zuciya ta ta bani Amma na kyautata maka zato. Baka San dubu suna nema Allah bai Basu ba? Kuma inda ana haka ai muma ba zamu bude ido a wannan duniyar ba . In don Kuma tsoron talauci kake kowa da arzikin shi yake zuwa duniya me yuwa ma Kai zakaci arzikin Dan da zaka haifa. So ka barwa Allah ikon shi tun kafin muzo ya gama tsara yadda Rayuwar mu zata kasance ka bari mu samu ko yara biyar ne idan kaga anayin haihuwar Kai da Kai sai muyi tsarin shima ba don yiwa Ubangiji gatse ba sai don samawa yaranmu amince da cikakkiyar kulawa 


Duk yadda taso ya fahimce ta yaki saboda kin Allah da gaskiya inda ya nuna Mata shifa baya son haihuwar gaba daya  don haka tabi tsarinshi su zauna lafiya inda ita Kuma tace lallai ta gama Shan waccan kwayar bare allurar da yake son dorata akai.


Rikici ya yi sama agidan inda kowa ya hau Kan tsinin shi. Shi a matsayyin shi na me gida ya kasa daga kafa har ya soma furta Mata muguwar kalmar ta shi bai dauki mace a tsiyar komai ba face Riga wadda zai sauyata aduk lokacin da yaso hakan inda itama amatsayin ta na matar gida me yin biyayya ta kasa yin biyayyar don Babu biyayya acikin sabawa Ubangiji sai gidan ya rikice kowa ya na wurinshi inda a yau ko girki ma Bata yi ba inda Kuma Garba yake begen ganin matar abokin nashi don tunda ya tafi da ita yake kwana da ita yake tashi inda ya iso gidan ya🌞 fahimci cikin da nafisatu ke da shi ba itama dake dauke da cikin Bata sani ba.


Ta farka da wani irin zazzabi da amai  ya shigo gidan ya sameta ajigace duk yadda yaso dauke kanshi akanta ya kasa don da gaske nafisatu ta sauya shi sauyi Kuma me yawa don haka ya kwashe ta suka nufi Asibiti......

No comments