A GIDA DAYA 19-20
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🌹A GIDA D'AYA🌹
🏘️🏘️
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
Wannan shafin nakine halak malak mmn nurul huda🥰
🅿️19&20
Atake jikin Khadija yafara rawa,sbd yadda ta lura da fuskarsa tamkar besan miye dariyaba". atsorace ta dubi Tahir dake cewa"Khadija nalura bakisan kulani ne kawai...kaga dan Allah mlm kayi hakuri "(lacturer d'insu ne)ko a skul bana kula kowa balle agida.ga yayanmu nan tafe,nasan nizai Kira...shiru tayi sbd k'amshin turaren sa yashaida Mata zuwansa.dago kansa Tahir yayi yakoyi arba da Yaya mahmod daya had'e fuska tamkar hadarin gabas.
shikanshi Tahir yaji shakkarsa da kwarjininsa.kallonsu yyi .hakan yasa Khadija saurin jada baya tanacewa "wlh Yaya shine yatareni akan Dole natsaya"wlh nadena bazan komaba..cikin muryansa dake bawa marar gsky tsoro yace".K!wuce kishiga cikin gida"jikin Khadija nakirma ,tana hard'e k'afafuwanta ta juya da nufin ta wuce"mlm Tahir yayi saurin shan gabanta Yana cewa" haba yayanmu pls amatsayi na namalaminsu a sk....wawan marin daya mahmod yad'auke shi dashine" yasakashi yinshiru ,bek'arasa mgn ba." da sauri ya shafa hancinsa dayaji Alamar ruwa....wani mugun kallo Yaya mahmod yawatsamishi"cikin kakkausar muryansa yace".this is the first &last dazaka sakewa wata mace hakan"mitssww lusari kawai.... yafad'a Yana finciko Khadija da k'arfi da hannunsa.yamaidota bayansa"Yana adduar Allah yasa Tahir yayi yunk'urin cewa zairama marinsa.yafitar Masa da hakora...Tahir kuwa ransa yab'aci dayaga jini ahancinsa"yakuma lura mahmod bawani girmansa yyiba.cikin zafin zuciya yace ".aiba marina zakayiba katafi"kamata yyi mugwada k'wanji da juna.yaya mahmod na huci "ya juyo azuciye yamatso kusada Tahir yana cewa "nafi buk'atar hakan "asannan kuma Tahir yagane fusakarsa (d'an jarida Mai gsky da ake yayi)azuciye yashak'i wuyan Tahir yabashi wani wawan punch... k'arar azaba Tahir yasaki Yana k'ok'arin ramawa"yasake kawo wani punch d'in..anan suka fara gwada k'wanji. adedenan kuma Abba suka shigo layin "Yana back sit isah driver najansa..Khadija kuwa innalillahi wa inna ilaihir raju'un kawai take maimaita arud'e"sbd ganin gaba d'aya Yaya Mahmoud yafi k'arfin Tahir"kafin tahir yakai duk'a 2, ya mahmud yakai 3"sbd Yaya mahmod jikinsa ya horu da training...dan Allah kayi hakuri karabu dashi "karkayi kisan Kai mushiga ukku! khadija tafad'a tana k'ok'arin matsawa kusa dasu ,sbd taga bbu kowa alayin...horn d'in da isah driver yyi yaja hankalin Khadija "tana kallon motar,da sauri ta iso sbd hango Abba ta glass datayi"cewa take Abba Kar Yaya yyi kisan Kai yaya mahmod...asukwane Abba yafito Yana kallon su mahmod da Tahir dake artabu...cikin tsawa Abba yace". mahmod karabu dashi nace!karkayiwa d'an mutane illah...
Yaya mahmod na huci ya hank'ad'a Tahir ,kansa yabugi motarsa"cikin fushi yace muddin nakoma ganinku atare da ita" saina canzamaka kamanni.
"mittww! Yanafadin hakan yanufi Gurin Khadija dake tsaye yafinciki hannunta cikin rufewar ido"suka nufi k'ofar shiga get d'in gidan.sbd yamanta da Abba nagurin..
Abba kuwa girgiza Kai kawai yyi"sbd yasan Dole saiya sauka dg dokin zuciya tukum. yatambayeshi meya had'ashi da wannan saurayi?
Rufe motar Abba yyi"yanufi Gurin Tahir dake shafa kunburarrar fuskarsa.abba yace" subahanallahi meya had'ashi da Kai yaro?kasa cewa komai Tahir yayi,illa kawai yyi k'ok'arin bud'e mota zaishiga.abba yyi saurin rik'emishi hannu Yana cewa"kayi hakuri yaro kaji?ni mahaifinsane zankuma d'auki mataki.amma meya had'aku?innabarka katafi kana haka aida damuwa ko?karkayi driving jikinka bbu dad'i, gakuma b'acin rai.
nasan halin waye mahmod baya shishshigi ko fad'a inba mak'ura aka kaishiba...inkuwa hakan yafaru za'ayi bbu dad'i.yanzun kaga ankusa magrib"ga chemist can bayanmu.muje adubamun kai."gaba d'aya sai Tahir yaji zuciyar sa tasaki dg fushi da b'acin ran dayakeji" tunani yakeyi aransa Abba wane irin mutum ne na k'warai haka?kwata kwata be goyi bayan d'ansaba "gashi yanabashi kulawar dakoshine yahaifesa sai hakan.muje Mana kayi shiru" rufe k'ofar motar d key Tahir yayi.hakan yasa Abba yajuya yafara tafiya,Tahir yabi bayansa...yyinda isah driver yawuce ciki da motar...
Ya mahmod suna shiga cikin get"maimakon yasake mata hannu, ta wuce part nasu "saiyajata zuwa d'akin sa."kuka kawai Khadija keyi tana mishi magiyar yayi hakuri karya daketa"sbd azatonta dukanta zaiyi.shikuwa har cikin ransa yakejin kukanta"cikin husky voice yace"inbakiyimun shiruba !zanbige Miki wannan bakin naki...tsit kakeji tayi shiru,jikinta sai rawa yakeyi cike da tsoro.da hannu 1 yasaka key ya bud'e d'akin"suka shiga Yana rik'e da tafin hannunta.sakinta yyi ta zauna kan carpet ad'od'ane..
Khadijaaaaaaa!yakirata cikin wata iriyar murya "yace"
da gaske wannan guy d'in malaminku ne?Murya na rawa tace".eh wlh"
Tun yaushe yafara Miki mgn?um um jiya ne... tsaki yaja yalumshe ido Yana dafe kansa.dukan dayayiwa Tahir besaka yaji sanyi aransaba.khadija ban hanaki kula samariba?cikin sanyin Murya tace".Yaya ka hanani"
shine Kuma kika tsaya sbd raini ko?tace"wlh ah ah Yaya"shine yasha gabana"Dole natsaya su ummi Basu tsayaniba suka shigo gd. kayi hakuri dan Allah bazan komaba.sannan dan Allah zantafi Kar wani yaganni anan"tab'e baki yyi had'e da cewa"Babu inda zakije saikin karb'i hukuncinki"sbd meyasa yanzun bakizowa kimun gyaran d'aki?kanta ak'asa tace"bansan laifin menamaka ba yaya!Inna gaidakai baka amsawa" koyimaka sannu d xuwa Yaya saika shareni "kuma banjin dad'i araina ...wani sanyi yaji aransa"sbd ko Yaya tadamu dashi.waye yaja Khadija?kecefa"yafad'a cikin cool voice Yana kallon ta.kanta ta d'ago taga ita yake kallo"janye idanunta tayi tace" nadena dan Allah.
Khadija meyasa kikafison kib'atan raine?kwanaki nakiraki naga kinmayi blocking nawa meyasa kiyin hakan?
Zancire block d'in Yaya yanzun dan Allah !gayacanma ana kiran magrib...hmmmm nagane wayonki yarinya"kije kiyi sallah,inkin gadama karki cire block d'in nawa da kikayi.hukunci kuma zan hukuntaki akan laifinki"da sauri ta d'ago kanta ta kallesa.taga Yama mike tsaye da nufin yashiga bed room d'in sa..yayaaaaaa!uhummm Khadija bazanfa hakuraba " gara kije kawai..hakan yasa ta tashi tafice batare data ce komaiba...
****************
bayan sallar isha'i"Abba ne zaune da mahmod da Tahir akusa dashi"Abba yadubi Tahir yace".kayi hakuri my son kaji ?Khadija itace wacce mahmod zai aura,ita kanta batasaniba.dg yanzun inkayi yunk'urin tsaida mace bata tsayaba"to kaje gurin magaba tanta ka nemi izini.mahmod kishine yasashi aikata hakan.sbd haka kubawa juna hakuri"kuma dg yau kunzama abokai na had'a abotar da kaina.abba yafad'a Yana murmushi.
Tahir yana murmushi yace". nagode k'warai da karamcinka Abba"insha Allah nayafe masa komai ya wuce"mahmod kayi hakuri bansan asaka muku rana da Khadija ba "da wlh bazan tsaida itaba.na lura a skul bata kula kowa shine nabiyota har gida..
Yaya mahmod fuskarsa bbu yabo bbu fallasa yace ".bbu komai Allah yakyauta gaba"Tahir yace Abba kayi hakuri bazan iya abota da wanda yafi k'arfina ba! yadakeni kuma"dariya Abba da Yaya mahmod sukayi atare.
Abba yace" ah ah aina kullah abotarku"sbd haka asannu zaku saba da juna"mik'ewa tsaye Tahir yayi Yana cewa"to shikenan Abba nagode zan wuce gida.
Abba yadubi Tahir yace" kasan ummi da Maryam dasuke tare da Khadija?”tahir yace"ah ah bazan iya shaidasuba Abba! inadai ganinsu su ukku"amma bazan iya shaidasuba"sbd banfi sati d'aya da Fara lacturing a skul nasuba.kuma a department d'in su Khadija nike koyawa.abba yace" to shikenan Inka dawo wani lokacin zanturo maka ummi da Maryam "acikinsu kazab'i wacce tamaka tunda karasa khadija.naji ka kwantamun arai"inkuma acikinsu bbu wacce tamaka bbu damuwa.tahir na murmushi da yaba kyawun halin Abba aransa yace". insha Allah Abba !jibi Friday zandawo nagode k'warai" Allah yak'ara girma.daga hakan sukayi sallama yafice"
Abba yadubi mahmod ,Wanda beji dad'in had'in da abba yace zaiyiba da tahir acikin yaran.ahankali yafara mishi nasiha akan yarage zafin zuciya da kishi haka"sannan yace" insha Allah dakaina zansanarwa Khadija maganar aurenku nabari adan kwana2 ne...Yaya mahmod kansa ak'asa yace" to shikenan Abba.
b'angaren zee kuwa"tunda ibbi yafara driving d'in tafarajin fad'uwar gaba,sai surutu yake janta dashi "saidai tayi murmushi kawai bata cika mgn ba.sannan ta lura yau ibbi yanacikin farinciki sosai.
Yana k'ok'arin yin parking ta dubeshi tace".Wai sweet heart yau farin cikin da murnar mekakeyine?”wani shu'umin kallo yamata "kafin yyi murmushi yace".ayau wani buri nawa nakesaka ran cikarsa.gabanta taji yafad'i"batace komai ba ta alak'anta abun da tsoron komawa gidane takeyi "sbd Kar daddy ko Yaya Kamal yarawo.
Hotel ne inda za'a yi birthday party d'in,acan wani fili akayi decoration's.acan suka nufa sai shishshige mata ibbi keyi tanaja da baya"har suka iso gurinda za'a yi party suka zauna.
Anata rawa dabawa me birthday d'in gift...har aka Fara Kiran magrib,yyinda zee keta damun ibbi ita gida zataje.
Kallonta yyi yace". muje akwai siyayya danayi miki nabawa abokina ajiya muje kirakani nakarba.batace komaiba saima murna datayi aranta tabi bayanshi.
Acan saman bene room12 suka tsaya"amamakinta saitaga yasaka key yabud'e k'ofar"kallonsa tayi ,kafin tayi mgn yace muje ciki Mana "abokinane yakama d'akin ,yakuma bani key d'in yace" mudakko shopping d'in.nidai gsky bazan shiga d'aki na hotelba amatsayina na budurwa"inwani yaganmu yazargemufa? d'an Jim ibbi yyi,kafin yace ".shikenan shiga suna gefen bed ki d'akko ,saimu wuce namaidamishi key d'insa nakaiki gida ko kuwa?”
batakawo komai arantaba ta shiga cikin room d'in"ibbi yyi saurin binta abaya,yarufo k'ofar da k'arfi yadanna key....

No comments