SAI A LAHIRA 17
*🎀SAI A LAHIRA🎀*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
*🅿️age 17*
*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*
*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*
_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE 1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_
_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
.........Malam lamis ne ya shigo inda ya iske Azumi na kuka ga Kuma tulin kudi agabanta bai tanka Mata ba ya SHIGA ciki ya Kira nafisatu ta fito tana murtsuke ido alamar bacci ta tashi
Ya dubeta
"Me akayiwa waccan take kuka? Tasan Azumi yake nufi tace
"Wallahi baba ban sani ba ta fada tana nufar soron inda tayi arba da Azumi ga kudi gabanta ga kuka tana sharar hawaye
"Lafiya Azumi"? "Dadi ne yasakani kuka Wai nice bana Zan ziyarci dakin Allah bana bilya ya biya min makka. Malam lamis da ya biyo bayan nafisatu don yaji ba Asin kukan ya riski abinda Azumin ke fada Wai an biya Mata kujera bana zata sauke farali
"To ki kwana da sanin indai akan auren nafisatu ne sai dai in sauwake Miki kije ki aure shi don ba Zan taba Bari kiyiwa ya ta sanadi ba don dai kawai Ina zuba Miki ido Ina kyaleki to in ma akwai gari gaba da makka kina iya zuwa Amma Banda sanadin auren nafisatu don ba abinda zai yuwu bane.
Ya dubi nafisatu "shin ko kin yarda Zaki auri Wanda take so ? Idan kinji kin amince ba Zan hanaki ba Amma muddin ba kiso Babu Wanda ya Isa yayi Miki Dole..... nafisatu tayi maza ta Kada kanta alamar Bata so
"To angama tashi kije abinki
Azumi ta ta share hawayenta tana mishi kallon waye Kai agarin katsina
"Babu dai yadda bakin cikin ka zaiyi Dani lamis ko banza dai ai na kamo hanyar arziki Dole Kuma akalle Ni akirani da suna hajiya Azumi auren nafisatu da bilya kuwa in kaga ba ayi shi ba to tabbatar na Daina numfashi ne
Ta kwaso kudinta ta shigo gida inda ta iske nafisatu na sharar hawaye
"Bude kunnen ki ki saurareni kema bayan ubanki zabi koma don ku yakeni? "To maganar da na fada ki dauketa tamkar acikin littafi Baki da miji Sai bilya ki yarda mu wanye lafiya idan Kuma kikace bayan ubanki Zaki koma ki bijirewa umarni na to abune Mai sauki in tsine Miki kibi duniya ki lalace.....
"Ke Azumi fito ki tafi gidan ku na sauwake Miki Aure na don na Gane in ba rabuwa nayi dake ba kece ajalina...
Wata kidima da rudani suka saukarwa nafisatu Jin yau auren iyayenta na rabuwa AUREN da ya yi shekaru talatin anayin shi Babu saki sai dai sabani irin na zo mu zauna zo musaba Amma ba a taba yin saki ba sai akan aurenta ga Kuma maganar tsinuwa da Azumin tace zatayi Mata Kuma tasan zata iya wannan abun biyu shiyasa taji zata iya rufe ido ta karbi zabin Azumi...
Azumi ta dubi lamis"Kai madallah na gode da saki sai dai ai ka baro baya da kura da kake cewa in Zo in fice gidan ka ne da kake bani umarnin tafiya gidan mu ai kasan filina ne ka Dora gini ko? To ka kwashe buloluwanka Nima filina nake so Zan Dora nawa ginin
Ya dubi Azumi Yana kissima lallai in baiyi sannu ba sai tayi ajalinshi don haka tace yafa kwashe bulon shi ya Bata filinta in ko ba haka ba to wallahi shine me fita ya bar Mata gidanta karma ya Kuma cewa gida nashi ne.
Malam lamis ya koma daki Inda yake Jin kanshi na sarawa inda nafisatu ta biyo shi dakin tana kuka
"Kayi hakuri don Allah baba ka Daina biye Mata na yarda Zan karbi Wanda take so din baba bana jin Dadi inga Kuna sa in sa bare sakin da kayi Mata don Allah ka janye shi baba Ina gudun tayi min Baki wani Abu ya sameni Arayuwa Wanda zai wahalar Dani na yarda Zan auri bilyan shikenan maganar ta wuce....
"Ba Zan kyale Azumi akan ta yi Miki AUREN Dole ba Wanda kike so shi za a Baki ita Kuma sai in sauwake Mata taje ta aure shi.....
"A a baba don Allah ka bar maganar Nan wallahi na yarda Zan aure shi ka Taya Ni da addua don nasan abinda Azumin take yi akaina za a fanshe Kuma nasan Babu komai gidan wancan mutumin sai tarin matsaloli Amma nasan darajar biyayya ba Zan tabe ba.
Ya zuba Mata ido Yana tausayin ta inda ya Gane samun irin ta a wannan zamanin akwai wahala don haka yace
"To shikenan nafisatu Ubangiji ya shiryi uwar ki ke Kuma yayi Miki albarka ya kiyaye ki dukkan sharri . Ta amsa da ameen ta fito ta SHIGA dakin Azumi take sanar da ita ta amince da auren bilyan.
Ta auno Mata harara
"Dama Ni nace Miki amincewar ki nake jira? Abinda dai na sani ubanki ma ba zai Hana Ni aiwatar da hakan ba bare ke ko tunda aka fara kinji na nemi yardar ki ko amincewar ki? Kwana talatin ne bikin don haka sai ki zamo cikin shiri don Ni Kam wallahi ba zanyiwa arziki kullin da zai tarwatse tunda har ga kujera ta fito nasan abinda zai biyo bayan kujerar?
Haka aka Sharari kwanaki inda ya rage saura sati daya biki inda malam lamis ke mamakin wannan mutum dake ta hidimar auren shi batare da ya nemi ganin uban yarinya ba duk da yasan makircin Azumi ne don haka ya nemi ganin bilya don yaji shi wane irin mutum ne da zaiyi aure har ya gama magana da mace ba tare da ya nemi dangin ubanta ba......

No comments