Breaking News

HAYATUL MAHAYAT 11-12

 


🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         🦚🦚🦚🦚

               🦚🦚

                 🦚

_Story and written_

            ```By```

*NPEEDY A AJI* 


_Dedicated to_

*My yar amana*



```My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

         typing......✍🏻```


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




🅿 11 & 12




Hawaye suka cika idanun Rayhana cikin zuciyar ta tace " ni Rayhana yau nazama tamkar mujiya acikin mutane wannan itace 'kaddara ta Allah kabani ikon cinyewa kallon yaran tayi tace Allah sarki tunkuna jarire an maidaku marayu sabida zalinci koson abin duniya Allah kasamufi karfin zuciyar mu in sha Allahu bazan barku kuyi kukan rashin mahaifiya ba "



Cikin girmamawa liman yakai gaisuwa gaban maimartaba 


" Allah ya'karamaka  lafiya kamar yadda kasani auran Mu'azzam da Arfat yananan babu abinda yawarwareshi sede idan shi Mu'azzam d'inne yace bazai iya zama da'ita ba amma kafin wata ma'amalar aure tasake shiga tsakanin shi da ita setayi istubura'i zuwa wannan lokaci idan babu 'kaddarar ciki shikenan idan kuma akwai har seta haihu amma babu abinda yashafi auran su sabida fayd'e ne bada yardarta hakan tafaruba "


Sallamar Liman maimartaba yayi zuciyar duk babu dad'i kiran Mu'azzam yayi yasanar dashi hakan sannan yad'aura dacewa 


" Mu'azzam abindayafaru yariga yafaru karka bari mace tashiga tsakanin ka da d'an uwanka karka sake wani yaji cewar baka ta'ba kusantar Arfat ba kaga idan wannan abinyafita  to babu shakka wata matsalar ce idan har Allah yakawo cikin 'kaddara tasanadin  haka to banason kafurta cewa banaka  bane sabida rufuwar asirin d'an uwanka Mu'azzam zuciyata takasa yarda cewa Muzaffar zai aykata haka cikin hankalin shi amma bashida mafita karka daku baza'abar bincike ba kuma bazan baryin addu'a akan Allah yabaiyana gaskiya "


Kuka sosai Mu'azzam yakeyi yarasa yadda zai kwatanta yadda yakejin zuciyar shi tabbas yana matu'kar son Arfat amma  bazai iya fifitataba akan d'an uwan shi tashi yayi yama maimartaba godiya yafita 


Shiko Muzanbil tunda wannan abin yafaru ya'kajin tsanar mace cikin ranshi dan kam shi yayi imanin inde Muzaffar yayima Arfat fayd'e to ita tashirya komi dan yasan halin Muzaffar sosai zaman da Samha tayi kusadashi  yasashi 'kara tamke fuska cikin sanyin murya tace 


" haba mijina maiyasa har yanzu kakasa gane irin son danikeyimaka ? Yarima wallahi zuciya ta tanagaf da bugawa akan sonka dan Allah kabani koda gurin dazan tsuguna ne acikin zuciyar ka koda bansamu gurin zaman ba "


Mi'kewa Muzanbil yayi zaibar gurin sabida jiyake duk ta isheshi saurin kamo hannun shi tayi cikin zafin rai yajuyo a tsora tayi saurin rungume shi cusa kanta tayi cikin 'kirjin shi tana jin wata irin bugun zuciya jin shiru yasata d'ago kanta ahankali fararan idanunta tasauke kan kyakkyawar fuskar shi ganin idanun shi tayi alumshe murmushi tayi sannan tasakeshi  bedroom d'in ta tanufa tana sakin murmushi cikin 'bacin rai yabita da kallo cikin zuciyar shi yace 


" lalle Samha kinfara  rainani amma zanyi maganinki sabida naga kinfara shiga hurumin daba nakiba " 


Misalin 9 Hamdiyya tashiga part d'in Kilishi itada kuyangun ta 2 zaune tasamu Kilishi a parlour anayimata tausar kafa gefanta Zahra tana kishingid'e idanun ta alumshe hannun ta ri'ke da Apple tunanin irin mugun wula'kancin da Aliyu yayi mata takeyi jin shigowar Hamdiyya yasata bud'e idanunta cikin girmamawa tace 


" Ummi barka dashigowa " kamar dagaske Hamdiyya tace " ayni bazan amsaba tun yaushe kikazo amma bakije kin gaidaniba se danazo ? waima mai yakawoki kikabaro gidan mijin ki ? "


Kafin Zahra tace komi Kilishi tayi saurin cewa " mijin natane yayi tafiya kuma zai jima kafin yadawo kasancewar  Allah ya azurtata dasamun ciki kuma yana d'an bata wahala shine taro'keshi akan yabarta tadawo gida har zuwa lokacin dazai dawo to kinji dalilin zamanta "


Yatsina fuskar Hamdiyya tayi dan ita bahaka tasojiba sallama tayima  Kilishi tafita zuciya babu dad'i bayan fitar Hamdiyya da d'an wani lokaci Kilishi tasallami hadimanta tashi tayi tanufi bedroom had'ida kiran Zarah cikin bedroom d'in bayan tazauna Kilishi tadubaita tace 


" Zarah inaso kiri'ke wannan sirrin karkisake wani cikin masarutar nan yasan cewa Aliyu yasakeki sabida akwai masujiran haka dayawa bayan 'yan uwanki banason kowa yasakejin haka "


Jinjina kai Zarah tayi sabida yadda idanunta suka cika tab dahawaye tashi tayi tafita bedroom d'in ta tashiga kan bed tafad'a tasaki wani irin kuka mai tsuma zuciya Hamdiyya tana fita part din Hajiya Ayna tashiga wato kaka zaune tasameta  tanacin  tuwon acca da miyar ku'baiwa wadda tasa manshanu daga ciki kuma hadiman tane ketayimata hidama sabida part d'in kaka baya rabuwa da ba'ki


Gaisuwa Hamdiyya tami'ka sannan tazauna seda tajira kaka takammala cin abincin sannan tace 


" Allah ya'kara miki lafiya uwar sarki kuma kakar sarki dama akan wata maganace bansan ko kinsan da'ita ba naga Zahra tadawo gida kusan kwanaki 3 kenan shine nace ko lafiya ? "


Kishin gid'a kaka tayi sannan tace " inajinki  uwar gulma kokin gama gulmar data kawokine ? wato sabida kin rainani shine zakizomin dawannan maganar lalle ma Hamdiyya wato gulmar taki harta kawo gareni to bari kiji Zahra dayardar mijinta tazo gidan hid'ida abun arziki wato ciki shikenan gulmar taki tayi nasara ko batayiba nasan sokike kiji ance yasaketa ko ? to bahakabane Zarah da Aliyu se mutu idan kika sake zuwamin da wannan maganar wallahi sanasa Abdurrahaman yayi miki mugun hukunci tashi kibani guri mata se gulmar tsiya duk cikin ku Kilishi CE kawai batayin wannan munafurci amma ku Allah yasauwa'ke "


Cikin sanyin jiki Hamdiyya tafita tanaji mugun haushin kaka bayan fitar Hamdiyya kaka takira maimartaba akan yazo part d'in ta yanzu tanason ganin shi kashe wayar tayi korar hadiman tayi bayan sunfita  tace 


" lalle Aliyu senabaka mamaki nizaka tozartama jika inyi jagora wajan baka Zarah kasakamin dahaka  har anfara yin shagu'ban maganar lalle sekayi nadama wallahi "


Cikin sauri maimartaba yashigo dur'kusawa yayi yagaidata sannan yazauna 'kasan carpet tashi kaka tayi zaune tace 


" Abdurrahaman inaso Zarah tadawo nan gurina tazauna sannan kamayar da'ita Skul ta'karasa karatunta  dama can nice nahana hakan sabida auran Aliyu danabayar da umarnin yinshi kuma kakiyaye kamar yadda nace kar kowa yasan wannan maganar "


Cikin girmamawa Maimartaba ya'amsa sallamar shi tayi yafita part d'in Kilishi yanufa yanajin farincikin bari da kaka tayi Zarah takoma Skul dan dama shi yayi takaicin hakan dan babu yadda zaiyine farin ciki sosai Zarah da Kilishi sukayi dajin haka Zarah jitayi gabad'aya  damuwarta ta yaye 


Washe gari Muzanbil yasami maimartaba cikin parlour shi nahutawa gaisuwa Muzanbil yakai sannan yazauna  gaban maimartaba yace 


" Allah ya'kara maka lafiya angano mai wannan abun wuyan tana d'aya daga cikin kuyangun gimbiya Nabila  amma ayanzu bata cikin masarutar nan tun bayan rasuwar  Nabila da kwanaki 8 tanemi izinin Muzaffar akan zataje 'kauyansu wajan kakarta  to gashi mu bamusan  kyauyanba kuma yau kimanin 3 months kenan nazauna da Jakadiya akan tasanar dani wane kyauyene amma tanunamin  ita bama tagane wacece ba "


" kamarya batagane taba ? bayan tanada masaniya akan kowace hadima dake cikin masarutar nan lalle akwai wata a'kasa kanaji Muzanbil karka sake tunkarar kowa akan wannan binciken sabida nalura kamar akwai hannu dayawa cikin wannan al'amarin yanzu mujira dawowar Muzaffar nayi waya dashi nakuma cemai yatabbatar yadawo gida dazaran yagama wannan aykin sabida idan yana kusa zamufi samun nasarar binciken 'kila yasan daga ina yarinyar take kai kuma kaciba da binciken ka shikuma zoban fa ?   


Ajiyar zuciya yasauke yace 


" munyi duk iya binciken mu amma babu mai irin zoban kaf acikin masarutar nan "


Girgiza kai Sarki yayi cikin takaici sallamar Muzanbil yayi Arfat kwance kanta nakan cinyar Mu'azzam cikin shagwa'ba tace 


" Doctor kayi ha'kuri kayafe ma d'an uwanka banaso nazama silar raba tsananin soyayya da sha'kuwa wadda take tun cikin cikin mahaifiya 'kila baya cikin hayyacin shi lokacin dayayi haka kayi ha'kuri nashirya baka kulawa tamusamman fiye da wadda karasa abaya "


Zamar da kanta yayi daga kan cinyar shi yace 


" bazaki iyasamun amincewataba har se lokacin dana tabbatar da gaskiyar wannan lamarin ki adana kulawarki dan 'kila wani zatayima amfani dan dazaran nasan gaskiya idan har ke ce mai lefi  cikin  wannan lamarin to bazan iya cigaba dazama dakeba duk da irin matu'kar son danike miki idan kuma bakida  lefi to zan manta dakomi nakuma yafema Muzaffar dan babu abinda zai iya shiga tsakanina da d'an uwana "


Fita Mu'azzam yayi rai 'bace murmushi Arfat tayi tace Doctor kenan dasannu kuma dagoyan bayanka zan auri burin raina wato Muzaffar "


Cikin sauri Rayhana ke shirya su Sudees dan yau tayi ranar fita kasuwa bayan tagama shirya Sudees tazaunar dashi wanda ayanzu sun iya rarrafe dan kimanin 5 months kenan da haihuwar su cigaba tayi da shirya shureem jin ihun Sudees yasata saurin waigawa cikin sauri tami'ke nufar inda yake tayi ganin jini ahannun shi yasata rud'ewa sosai d'aukar shi tayi amma yashiga jillewa yana nuna mirror duban ta tamayar  kan mirror cikin tsoro darazana tayi saurin juyawa dan ganin bayanta amma babu kowa cikin sauri tasake kallon mirror sake gani tayi 


Wani kyakkyawan saurayi take gani cikin mirror amma yajuya baya bata ganin fuskar shi tsoro taji sosai kwasar  yaran tayi suka nufi cikin bedroom atsorace take gyarama Sudees hannu shiko se nunamata hanyar waje yakeyi tanagama  shiryasu tagoya Sudees tad'auki  Shureem hartakai bakin 'kofa  tadawo d'aukar wannan d'an box d'in tayi sabida wannan aljanar tacemata  kartasake tabarshi  cikin gidan idan har bata ciki  tun kafin ta'idasa shiga cikin kasuwar tahangi motocin sojoji kowa ri'ke da manyan bindigu 



Wasu nacikin shaguna suna bincike kowa ka kalla a tsorace yake itama cikin tsoro taje shiga ciki har wajan rumfar ta zaunar da Shureem tayi tashiga bud'e kayanta ganin sojojin sun nufo gurin rumafarta taji wata irin fad'uwar gaba ganin sun nufi shagon bayanta  yasata sauke ajiyar zuciya waigawa tayi ganin babu Shureem yasata saurin mi'kewa juyawa tayi ganin shi tayi yanufi wajan sojojin cikin rarrafe dasauri binshi tayi amma kafin ta'isa shi yarigata 'kafar wandan wani soja yakama yana 'ko'karin mi'kewa cikin zafin rai yashureshi dede lokacin Rayhana ta'isa gurin 


Saurin d'aukar Shureem tayi sannan tami'ke rai amatu'kar 'bace hannu tad'aga tasauke mai wani irin mari sannan tanunashi tace 


" amma kai daganin ka bakasan ciwon 'ya'yaba bakuma kasan darajar suba dan daka sani dabaza sure wannan 'karamin yaron dabaison komiba "


Azafafe yakai hannu zai sha'kota wannan mai shagon yayi saurin shiga tsakiyar su cikin raunanniyar murya yace 


" dan Allah yalla'bai kayi ha'kuri wannan dakake gani masiface ta'bata dan Allah kayi mata ha'kuri kodan kasan cewarta mace dakuma darajar wa'innan yaran "


Cikin zafin rai yace tashimin  agaba " itad'in 'yar gidan uban wacece ? dahar zata d'aga hannu tamareni yau sekinyi nadamar yin haka " 


Dakewa Rayhana tayi dukka tana cikin tsananin tsoro cewa tayi 


" ni bayar kowa bace hasalima banida kowa wannan yaran dakagani sune komina kuma sune diniyata dasu nike alfahari kuma wallahi bama kaiba  koda sugaban sojojin duk duniya ne yayima d'anah haka senayi mishi irin yadda nayi maka "


Wani irin ba'kin ciki Muzaffar yasakeji cikin izza yace 


" lalle kuwa zan nunamiki kinyi kuskure daga yau bazaki sakeyima wani kwatan kwacin hakaba zaki dauwama kinamin  bauta keda yaran naki sena dasa miki mugun tabo  cikin zuciyar ki  "


Afusace ya kalli sauran sojojin dake bayan shi yace 


" kusamin ita cikin motata  "


Tasata sukayi da kan bindiga cikin tsoro take tafiya suko yaran kallon Muzaffar sukeyi babu ko kuffawa juyawa Muzaffar yayi yacema mai shagon nan inane gidan datake  ?


Cikin jimami mai Shago yace 


" yalla'bai wannan yarinyar dakake  gani tamkar aljana take sabida kusan sau 3 munabinta  abaya har 'kofar gidanta tana shiga se gidan yazama fili babu alamar gida kwata kwata shiyasa kaji nacema karabu da'ita dan wallahi zata jama masifa "


Cikin takaici Muzaffar yace sede ni najamata masifa ciro wayar shi yayi yakira  layin Momy cikin mamaki tad'aga dan baya kiran kowa tun dayatafi tana d'agawa yace 


" Momy barka da warhaka ina fatan kina lafiya Momy naci ganimar wata waiba itada yaranta 2 zansa akawota baiwa tace bata kowaba  tun kafin nadawo inaso tafarayimin  hidima kuma banason asausauta mata zan turo da ita zuwa gobe "


Kafin Momy tace komi yakashe wayar 



 Yau aka d'aura auran Aliyu da Salimat cikin farin ciki Aliyu yashiga part d'in Amarya hannun shi ri'keda leda 



Daga Al'kalamin........✍🏻

No comments