Breaking News

NI DA KE 34 (END)

 ♣️♥️♣️

     *_NI DA KE...!!!_*

                    ♣️♥️♣️




♥️```Dole muyi rayuwa.........```♥️





_By
😘😘fêêbyrh😘✍️_


🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚



Page 3️⃣4️⃣ the end

Bayan shekara Biyu abubuwa da dama sun faru inda xuwa yanxu Affan ya girma sosai idan ka ganshi xaka dauka yafi shekara biyu saboda tsantsar wayo da yake da haka rayuwa ta cigaba da tafiya khal yayi matukar yin dana sani duk da ba laifin sa bane.

Xaune suke a dinning suna lunch cikeda kwanciyar hankali suke komai nasu kallo daya xaka yiwa koh wanne daga cikin kasan yana cikeda farin ciki fried rice ne suke ci tareda pepper chicken Affan ne kadai baya cin abincin ya ajiye spoon dake hannun shi murmushi dad yayi yana cewa

    "My boy lafiya baka cin abinci...."

  shagwabe kyakkyawan fuskar sa yayi yana tura baki yace

     "Uhh uhhm Grandpa yi chocolate yan ci..."

   dan murmushi yayi yana jawo shi jikin shi a baki ya saka mishi abinci tab'e baki yayi yana cewa 

     "Grandpa idan naci xaka kaini inda xakaje anjima...??"

  "Sosai ma amma fa idan kaci dayawa"

   Sallam me gadi yayi yana cewa 

   "hajiya ana miki sallama a waje.."

  yafada yana nuna Firdausi wacce tayi fresh abunta ta Kara xama kyakkyawar mace komai yaci radam 

   "am waye ne...???"

 "gaskiya ban taba ganin shi ba.."

  dan Jim tayi kafin tace "ok kace gani xuwa"

fita me gadin yayi ita kuwa ta yunkura xata tashi tsawa khal ya daka mata wanda tunda aka fara maganar yake faman had'iye rai jin yake kamar xuciyar shi xe fashe dan shagwabe beauty face d'inta tayi tana cewa 

  "Wai ni yaya meyasa kake mun haka duk wanda yaxo nema na sai ka kore shi ni wallahi sai na tafi..."

  cikin shagwaba tayi maganar kamar xatayi kuka mayafinta ta dauko tana kokarin fita ya tureta ya fita tareda rufe kofar direct wajen me nemanta d'in ya nufa d'an matashin saurayin dake tsaye yana ganin Khalil ya washe baki yana gaida shi tsawa ya daga mishi yana cewa "lafiya meya kawo ka...??"

  "am dama naxo ne in bayyana mata soyayyata"

  "kaga malam ka fita kabar gidan nan kafin in sa a illata ka"

Ba shiri yabar gidan karasawa yayi wajen me gadi tsaye yayi ya had'e hannu a kirji yace "baba dan Allah bana ce maka duk Wanda yaxo neman yarinyar nan ba karka bari ya sake shiga gidan ba...??"

  "hakane yanka ya dade kayi hakuri"

"Ba komai.."

yafada a tak'aice yana barin wajen bud'e parlourn yayi ya shiga ya samu waje ya xauna yana Shan kamshi kallonta yayi yana sakar mata murmushi murgud'a mishi baki tayi ta fice daga wajen.






Ranar juma'a bayan massalaci dad kiran  Khalil yayi tareda Firdausi bayan duk sun xo nan ne yake sanarda su cewar an daura musu aure ta shirya tarewa gidan mijinta gobe tashi tsaye tayi tana kuka tana cewa

  "Dad wallahi ni bana son shi baxan iya rayuwa dashi ba..."

  sanyayyar iska khal ya shak'o yana me godewa Allah ya dauki lokaci kafin yace 

  "ki Sani NI DA KE dole muyi rayuwa..."

da sauri ta fice daga wajen direct dakinta ta nufa tana shiga dakin ta daka tsallen jin dadi tana cewa 

  "Allah nagode ma daka nuna mun wannan ranar.."

  "OK Ashe daman kina so shine kike kaiwa kasuwa??"

 juyawarda xatayi sukayi ido biyu da khal rufe fuskarta tayi da tafin hannunta tana cewa "nifa bawai sonka nake ba kawai dai inajin dadin xan rama abunda kayi mun a da cen baya"

riko kumatunta yayi da hannu biyu ya shagwabe fuska shima yanda tayi yace

   "Dan Allah matata karki mun haka koh don albarka cin dan mu pls"

  "nifa kabar cewa dana danka dai"

  "toh naji na yarda ki yafe mun pls kinji Mak'e kafad'a tayi alamun a'a shagwabe fuskar shi yayi yana rik'e kunne alamun roko ya ce "dan Allah mine....kiyi hakuri

   mom dake tsaye bakin kofar ne tace 

   " kaji Mara kunya maxa ka fita daga dakin nan kafin in bata maka rai taki ta hakura d'in "

  tayi maganar tana murmushi shima murmushi yayi yana cewa "haba mom so kike na rasa raina ne baxan iya rayuwa ba ita ba wallahi.."

  "karka damu ya Khalil NI DA KAI dole muyi rayuwa"

Tafada tana rufe fuskarta sakin baki mum tayi tana cigaba da Koran shi har yabar dakin maganin mata masu matukar yawa da kyau ta bawa Firdausi tasha xuwa yamma  gaba daya mutane sun cika gidan inda har luba taxo Ita da momyn Firdausi inda yanxu lafiya qlw  suke xaune a gida daya gidan da dad ya bawa Mallam cikeda xaman lafiya suke rayuwar su.

Ranar asabar gidan ya cika da jama'a inda akayi biki Wanda Saida kudi yayi kuka da dare amarya ta tare gidan mijinta inda a kayi mata nasiha masu ratsa jiki bayan duk Yan kawo amarya sun watse aka bar amarya Ita kadai khal ya dade be shigo gidan ba tafi karfin awa daya tana jiran shi kafin yaxo daddadan kamshin turaren shi ne ya sanarda ita xuwan shi ajiyar xuciya ta sauke tana jin Farin ciki Mara misaltuwa shigowa room d'in yayi Wanda yayi masifar kyau da daukar hankali xama yayi yana facing d'inta tareda shak'o daddadan kamshi dake tashi daga jikinta yace 

   "Amincin Allah ya tabbata a gareki yake kyakkyawar matata wacce samun Irina sai an tonah Allah ya bamu xaman lafiya tareda yaran mu dozen...."

  xaro ido tayi tana dafe kirji tace

  "Saheebyrh dozen fa kace..."

  "Eh mana saheebarh ko sunyi kadan..ne....?" Hmmm...tafada tana jan sassanyar nunfashi sallah sukayi

Nan ya dafa kanta yayi mata addu'oi cikin kankanin lokaci yayi kwanka ya cenxa kayan jikin shi itama dakinta taje ta cenxa kaya xuwa wani mayun sexy night dress suman tsaye yayi ganinta da kayan hamdala yasake yiwa ubangiji kwanciya tayi a hankali yajata xuwa jikin shi yana shafata a hankali janye jikinta tayi daga nashi tana gyara kwanciyarta sake janta yayi tana shinshinarta nunfashi taja ta sauke tana cewa " yaya dan Allah ka bari "

  "A'a yakamata ayiwa Affan kani fa.."

yafada yana shigarda ita jikin shi sosai Daren ranar taci wuya sosai shi kuwa yaji dadi Wanda be taba ji ba da safe suka tashi dan sun makara wanka sukayi a tare inda saida yayi mata gashi bayan sunyi sallah suka koma suka  kwanta rungumeta yayi yana kissing d'in ta yace 

  "Ina sonki Firdausi"

"Nima inasonka fiyeda tunanin ka..."

tafada tana Kara shigewa jikin shi sosai.......





Alhamdulillah a nan na kawo karshen wannan littafin na godewa Allah daya nuna mun na kammala wannan littafin lafiya duk kura kuren da ke ciki Allah ya yafe mun......



Masoya na wa'inda suke Bini daga farkon wannan littafi har xuwa karshe Ina matukar godiya.



*ku biyo ni a next littafi nah me suna NAYI NADAMA*





😘😘FÊÊBYRH😘

No comments