Breaking News

DUK NISAN JIFA 61

 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K'asa zai dawo)_


🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


            _RUBUTAWA_


               *SAJIDA*


        *SADAUKARWA*


                   *GA*


           *MASOYA NA*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_




                            61



A lokacin da ta shiga Bilkisu na sanye da doguwar riga baka saman wani gado gado,  kamar irin na likitar hakorin nan aman na roma sannan yana da laushi wajen zaman da wajen kwonciya, tana reran tana kallon sama sunna darzar jikinta da hadin dulkar da karfi da yafi sai da matar nan ta saudiya ta koya mata kuma take siyo abubuwanta du idan ra je ziyara


Wajen idannuwanta an dora mata kokomber bayan an shafa masa abin gyaran wajen, sosai aka yaye rigar har cen saman cinyarta sannan hannunta Najeeba ke sakawa har cikinta da wajen mamanta ta murje da dilkar nan mai wani irin haske da santsin uwar madarar da aka maka mata


Wajen kanta kuwa yarinyar Najeebar ce ke lalabe kan da wani hadin mai, sai da ta gama ta saka mata hular wanka wace zata baiwa kan damar yin zufa sosai gashi dama sun kashe AC dan kuwa gyaran ba'a so sanyi ko iska ya busar da shi an fi so dumi irin na zafi ya dumama fatar ta yadda zai ratsa jiki sosai


Sai da ta gama zufar har zufar ta shige jikin ya shanye sannan ta saka ta zauna ta murje mata shi sosai ta karkade shi ba tare da an yi wanka ba


Somin tabi kennan domin bayansa aka kawo garwashin wuta tare da kujerar zama sai wani hadin a wata yar silba mai kyau wanda akai masa hadin zuma


Shafa mata ta yi banda fuskarta sannan ta dauko tsumin da take sha ta cika mata katon kofi ta bata ta sakata shanyewa tas dama shine na biyu domin kaza aka fara bata dafafiya da Tukunya ta cinyeta tas domin karama ce sosai dan ta iya cinyewar ta sha hade haden magungunnan sai dabri take aman a haka ta cinye tas sai yanzun kuma ta kira da tsumin nan


Cikin nutsuwa ta lulube mata jiki bayan ta saka pant ja hayakin nan ya shiga shigarta harta da tafin kafarta banda kanta domin kanta ne kadai a waje


Nan suka dora hira da Tati da Najeeba, inda Tati take tambayarta gyaran nan kowama suke yiwa?


Gimbiya ta yi murmushi ta bata amsar cewa eh a saloon din du wanda zai iya biya sunna yi masa, ita dai ce bata zuwa aiki sai idan kannenta za'a aurar ko wanda ta yi niya Mai martaba kan bata wannan dama ta zo ta gabatar


Tati ta gyada kai cike da mamakin tsarin saloon din ta ce" Kuma gyaran na kwana nawa ne? "


Najeeba ta ce" Ai iya yau ne tati, harda inji fa da zata shiga wanda ake saka mutun "


Tati ta yi murmushi sosai ta rage murya ta ce" Nima ina so wannan fata fata tawa da ta dan yakune a jata y'ata"


Najeeba ta yi murmushi ta ce" Tati, shi gyara fa da kika gani a wajenmu ne ya zama sai na yaran mata, shin iya yaran mata ne mutane ko iya sune suke da aure? Ko mazan manyan matan ce masu suka yi basa son gyara?, zaki ga tsohuwa sosai bama wai mai shekarunki ba ta je an gyarata da gyara na ban mamaki tati, shi yasa zaki ga shekarunsu na boyewa a jikinsu dan gyara na boye shi, mace idan ta san darajar kanta tati daga an kwana biyu ta ga ta dan fara fita hayacinta koda bata da kudin ta dan harhada kan sauran na cefane ne kan na dan baki na karin ne ke da kanki ki hada ki je su murje ki su gyara ki su yarfa maki dan kitson nan da dan kunshin nan ki fito das da ke kamar ba ke ba, shi da kansa zaki ga cenjin rayuwa a tare da shi, aman ya zamana mace ba kyau ba tsari baki kirin ina anfani? Gyara aka ce, kowace fata da irin gyaranta , ni yanzu ba baka bace?  Bakina kuma mai yawa ne bama mai haske bane ai kau? To haka ake dilke ni a murje ni na shiga mashin na fito, Allah tati ina cewa  mai martaba a karro min mashin irin ta gyaran nan da nake ko sisina bai amsa ba ya saka aka kawota bayan tsada ne da ita"


Tati sai ta ringa jin kamar wani tsuminta na tashi na yarinta , a sanyaye ta ce" Bale ni kishiyoyin da zamu zauna da su uku larabawa ne su dukansu dayar yarinya cema baki ga ni kaina sai da ta birgeni gasu da gyara kau?"


Murmushi Najeeba ta yi tana kallonta ta ce" A kowani yare akoy masu gyaran akoy wa'inda basa yi, zan iya fada maki ba sakarkarun mata irin farar fata, Tati dan sunna farare wasun ko wajen wanka suka zo basa tsayawa da sabulu da soso su darji kasan hamata da wajen dohi , sama sama suke wankawa su fitowarsu dan kar a ce basu yi ba , sun iya caba kwaliya aman kuma sunna tsami, Tati ai farar fata daidaya suka san cewar bayan farin nasu ana so su zama masu gyara, su ringa tsaftacewa jiki ya kasance cikin dumi, nawa suke fararan aman kuma su ba komai bane gaban bakaken? Ba dan komai ba sai rashin sa'ar da suka ci sun hadu da bakaken da suka san ciwon kansu suka san gyara, kin ga tiket zaki yanka a nan tati itama tuni na yankar mata, du wata uku uku ta zo dilka, a gida kuma ta ringa hawa hayaki komai da komai na gama packaging a rubuce zan rubuta mata komai a bayane na mata gwari gwari, a je a zauna Allah ya bada zaman lafia"



Wayo tati kam ba karamin dadi ta ji hira da yarinyar da a haife ta haifeta aman kuma a wannan fannin ta dameta ta shanye,  sam bata ji wahalar dukawa wada dan ta  san zata tashi da tsayinta ne, a nitse ta ce biyu take so nata da na mama, sai kuma ta samu kanta da yin daria dan ta tabata zasu kwasa ne da mama kafin ta yarda ta wani hau kujera, sai dai sam ba zata mata da sauki ba dan walahi in dai ta hau sai ta haudata, ita kuwa ta darmi niyar hawa tun daga gobe dan da alamu gyaran Billy zai kaisu dare


Tana saman wutar sau biyu ana bata wani hadin aman da ruwa masu dan dumi kadan ba masu sanyi karara ba


Sai da ta dauki awa daya sannan aka yaye mata rufar a lokacin ta gama dafewa fatar tata ta yi wani irin ja na zafin hayaki 


Sai wani luuuuu take da idannuwanta a lokacin da Najeeba ta sakata cikin wani dan lungu ta saki labule ta cire mata abin cikin nata ta shiga murzarta daga ita sai pant


Nadia ce ta miko mata hadin sansanyan madarar da aka hada mata itama wani hadin ta bata shi ta ce" Shanye "


BILKISU ta ce" Aunty, na koshi fa "


Najeeba ta ce" Aa akoy waje ai kin jima da cin kazar shanye kin ji? Yi kokari gyara ne"


Ai kam ta rufe ido ta kafa kai ta sha sosai dan sai dan kadan ta rage ta kasa shanye shi ta mikawa Najeeba abin mamaki tana kallo ta kafa kai ta shanye sauran ta mikawa Nadia


A nan dai ta kuma murza mata dilka ta barta sai da ta bushe ta dawo ta murje mata ita sannan ta dora mata hadin kurkum da madara sosai ko'ina nata kunya kamar ta kashe Bilkisu haka take harhade jikinta ana murzarta ga tarin gajiyar da take shi


Wannan karron sai da ta bata kujera har ta bushe a jikinta sannan ta bata tawul ta umarceta ta shiga bayi akoy wajen wankan gyaran jiki ta yi wanka da ruwan da aka tanada


Bilkisu na shiga ta koma wajen hadin da ta yi na su turaran jiki sansanya mai sanyin kanshi, da man oliv da madara abin kitib da shi sai kanshi yake 


Bilkisu kuwa dake bayi tana zuba ruwan nan masu dumi a jikinta tana lumshe idannuwanta cike da wani irin jin dadin ruwan

Ruwan wani kamshi yake fitarwa na turaran ruwa hadin wajen Hajia Binta (Babar yaya), garai garai da shi haka ta wanka tana ta zubar da ruwan kurkum din da komai


Da mamaki take shafa jikinta tana jin yadda ya yi wani irin santsi da haske a kan na da ga kanshin ruwan nan dake tsaya mata a jikinta sosai


A nitse ta gama ta daura tawul din da ta dauro ta shiga da shi ta fito


Tati murmushi kawai take doka mata cike da kaunarta a nan ne  Tati ta mije tana gannin yadda ake shafa abin shigar


Najeeba nake dibowa da abin shafawa ta zaunar da ita ta shiga bin lungu lungu da sako sako da hadin nan tana shafa mata ta ce" Wannan injin da kike gani da irinsa ne ake saka mata masu bleating, hafin nan ake yi sai a shada maki a saka ki a daidaira duminsa ki dauki awani a ciki, a lokacin da aka ciroki kamar sabuwar haihuwar jariri , aman shi ba dawamame bane ana yi ana sake shiga ne, haka kuma manyan yan siyasarmu da manyan matan da suka san kansu sukan taka kasashe kasar waje su je gyara, to ba wani abu bane ake masu sai wannan, kowa  ana tafe da shi ne da kalar fatarsa, idan fari kake son komawa sai ka koma "


Tati na gyada kanta cike da mamakin ci gaban zamani ta ce" To aman aka ce idan aka dauke wuta mutun na ciki mutuwa yake? "


Girgiza kai Najeeba ta yi ta ce" Eh na farko farkon an ce haka suka ringa yi, aman ai kin san tati ana yin abu ne ana kara kayata shi da gyaransa da komai, yanzun dai wadinnan basa yin hakan idanma aka dauke wuta abin ke budewa sai mutun ya farka ya fito har a dawo da wuta, bale nan  bamu yi hadinsa da wutar Nepa ba duda ba'a dauke mana wuta nan aman sam bana son anfani da wutar baban gida dan gudun kar wutar ta masa kadan, shi yasa aka kawo mana manyan inji aka kafa su iya su suke ba wuta da dogarin dake gadinsu ba dare ba rana yana kula da harkar mansu da lafiarsu"


Tati ta kuma gyada kai cike da gamsuwa da bayanan


Tawul din Tati ta rike Najeeba na tafe da Bilkisu a hankali har wajen Injin dake ajiye mai farin gilas a man kuma ba'a gannin abin cikin


Sai da ta taka zata hau Najeeba ta ce" Pant din zaki cire ki safawa nan hadin sosai ya samu"


Sai da Bilkisu ta zarro idannuwanta, aman gannin iya gaskiyar kennan ya sa ta hadiye yawu ta zare din a nutse ta shashafa ko'ina tana gagawa sannan da sauri ta haye ta shige wajen da Najeeba ta nuna mata ta kwonta saman wani lalausan tawul mai kanshi


A nutse Najeeba ta daidaita komai Gilas din ya rufe aman banda fuskarta


A nan ta dawo ta zauna saman doguwar kujerar rike da auduga da abin goge  fuska ta shiga goge mata wancen hadin da akai mata sannan ta shafa mata madarar peak kadai ta umarceta cewar ko daria kar ta yi


A nan suka barta , dadadan dumin wajen da bashi da zafi sosai yana ratsa jikinta tana jin kamar wada ake bin du wani kofofin jikinta ana murzata da murza dadadan da nan da nan ta ringa jinta a gajimare sai wani nanauyan baci mai dadi ya yi awon gaba da ita


A takaice dai ta dauki awani ukun a cikin abin nan har sai da Injin ya nuna blu cewar ya gama aikinsa sannan ta ji a hankali ana shafa gefen fuskarta, hakan ya farkar da ita a barcinta ta ga an bude gilas din a yanzun sanyin AC na ratsata hakan ya sakata sakin ajiyar zuciya


A hankali ta mike tana daura tawul din cikin dabara sannan ta fito a wajen

Gannin har an kunce mata kanta ta yi mamaki  ainun na barcin da ta yi 


Sosai ta huta kuma jikinta ya amsa

A yanzun Tati ce da kanta zata wanketa dan ta wanke mata kanta sosai 


Sam bata yi gardama ba domin da pant dinta, mamanta kuwa tun daga ranar da tati da Najeeba suka mata murzar nonon rakumi ta fara gane cewa an gama zubar masu da mutuncinsu ba su ba rufa saima da Hamanta ya yi wasan kura da su kan jiya zuwa yau tsaf hannayensa a jikinsu yake


Wanka ta sha na mamaki Tati sai mamakin yada skin dinta ya koma, ya Allah ana gyara a duniya sai dai idan baka da kudin yi ko hanyar da za'ai maka


Sosai take kara binta da kallo har bata so ta kufta idannuwanta dan yadda ta mata kyau


Cikin ruwan hadin sasaken baure kuma yanzun aka sakata ta zauna, ruwan masu dumin gaske domin sai da ta yi da gaske ta iya zama

Aman tana zama ta ringa sauke ajiyar zuciya, a hankali ta jita ta dawo normal wani irin dadi jikin nata ya dawo yanai mata saima wani irin abu mai santsin da ya gayato kansa ba tare da ko an gayato shi ba dan kuwa zuba tare yarari take 


Sai da ya salabce sannan suka fitar da ita 

Wani pant din da rigar mama yar cicib aka bata ta saka sannan aka bata wata doguwar rigar ta auduga mai laushin gaske mai ruwan fari aman kuma tana da manyan fulawowi a jikinta haka kuma bata wuce gwuiwarta ba ta zauna saman shinfidar kafet mai duhu mai laushin gaske wanda aka dora masa bargo shima mai laushin gaske 


Kayan kunshin da yarinyar Najeeba ta gama hadawa take bi da kallo, abin nasu komai special  kuma tsaf tsaf tsaf


A nutse ta zauna ta shiga zana mata kunshi a hannayenta, Najeeba kuwa ta gama hada man gashi ta ajiye kujerar tayani tsegumi sannan ta dora mata abin zama mai laushi sosai ta haye ta kunce tawul din da ta daura mata a kanta ta jona abin busar da gashin nan ta shiga busar mata da shi


A hankali take tsatsagawa tana shafa mata man gashin ko'ina, sai da ta gama sannan ta dauki abin kitso ta yi bisimillah ta shiga yarfa mata wani irin kannanun kitso irin na garari na amare, amarenma masu gata a baki kirin din gashin kanta wanda a hadin da suka masa yanzun ne ya kara yin sidik da shi ya kara mikewa sosai................




Kusan a cen ya wuni, ya wuni ne tare da ita duda ba wani abu ne na a zo a gani ya shiga tsakaninsu ba domin ko hirar  sama sama ne dai kamar yadda suka saba suke yi


Sai bayan sallar la'asar suka zauna dan cin abinci


A sanyaye Aisha ta ce" Ina kanwata? "


Hisham ya dago da cokalin da zai kai bakinsa ya yi murmushi ya ce" Tana gidan Gimbiya "


GIDAN gimbiya?, take tambayar kanta, sai dai ba zata iya tambayarsa me ta je yi ba, dan haka sai ta hadiye tambayarta a cikin ranta  kawai


Wayarsa dake ringin ta mike ta dauko masa ta kawo masa ita


Yana dubawa ya ga sunnan mahaifinta ne rado rado da ya yi serving da Elhaj


Ajiye cokalin ya yi yana gige bakinsa da tissu ya katse kiran sannan ya bi


Cikin mutunta junna suka gaisa sosai da sosai sannan ya dakata tana saurare


Kallon Aisha dake kallonsa ya yi kafin ya kai dubansa kan agogo ya ce" Ina zuwa zan duba na gani idan yauma da halin hakan zata zo in sha Allah "


Yana kashe kiran ya danna kiran Tati


Tana dagawa ya tambayeta idan har sun gama?


A nan tati ke fada masa cewar gaskiya da sauransu sosaima a kadan zasu kai isha


Hakan ya saka shi yi mata salama ya kai dubansa kan Aisha da take ta kallonsa ya ce" Saka hijab dinki mu je Asibiti, papy ne yake ta son ganninki kina ji tun  jiya kece a bakinsa "


Da sauri ta mike cike da farin ciki ta yi ciki ta dauko katon hijab dinta ta saka ta dawo 


Nan suka fito Kader ya dauke su suka yi asibitin


A lokacin da suka shiga dogon coridor din Mahaifiyarta ce tsaye idannuwanta sun yi jajajir alamun ta ci kuka har ta gode Allah


Da sauri Aisha ta karasa gabanta na faduwa ta ce" Mama kuka kika yi? Me ya saka ki kuka? Jikin papy ne?"


Mahaifiyar tata ta kasa amsa mata sai dai ta girgiza mata kai, hakan ya saka Hisham daga kafarsa da sauri ya nufi dakin inda Aishar ta shige da sauri yana tunanin meye hakan? Jikin tsohon ne ya tashi ba'a kiraye shi ba ko meye? Ko iya gaishe da mahaifiyar Aishar bai yi ba ya kutsa kansa


Turus ya yi gannin Mahaifin Aishar zaune saman kujera kansa sade a kasa


Aishar ta haye saman gadon na marar lafia ta dora kanta saman cinyarsa tana daria hadi da fadin" Mama na gani tana kuka , har ta tayar min da hankali ashe a zaune kake da sauki? "


Yana daria ya daki bayanta a hankali ya ce" Ja'ira ashe ke aurenki ya kawo ni jinya Damagaram? Tashi nuna min wanda ya kwace min mata mu yi kokowa dan ba zan yarda ba"


Murmushi  Hisham ya saki gannin tsohon ras da yannayi na yana jin karfi a jikinsa da kuma yannayin farin cikin gannin jikar tasa ya tsaya jikin garu yana ta murmushi, sai dai shima yannayin iyayen na Aishar sun saka masa ayar tambaya, balema  mahaifiyarta dake rizgar kuka a corridor


A hankali ya yi gyaran murya ya ce" Ba kukan wani abu mahaifiyarki take yi ba sai dan na umarci mijinta kan ya je ya ajiye aikin da suke takama da shi har sunna neman kauce hanya da son zuciya a kan aikin nan, shine ta sako shi a gaba kan in dai nashi da aikin nan sun shiga uku karyarsu ta kare ita kuwa ba zata iya zama da shi ba, shine na ce ai ba komai  sai na aura masa wata, domin macen da zata iya zama da kai a halin akoy dinka ko babunka itace mace, shine fa ta fita tana rusa kuka sai hakuri ake bata ji ake majinyacin nata ne ya mutu....." ya karashe yana sakin murmushin  da ya saka Hisham tsura masa ido, hakama Aisha ta dago tana kallonsa


A sanyaye ta ce" Me yasa zaka hanna su aiki Papy? Idan ka hanna papa aiki me zai yi ya ciyar da iyalinshi ya yi bukatunsa da namu? Papa ka fi kowa sannin menene rayuwar Niamey, idan ka hanna shi aiki ina zai kama? "


Hisham dake tsaye ne ya dan yi gyaran murya ya ce" Zan je na dawo"


Da sauri kakan Aisha Ya ce" Aa dawo, maganar ta cikin gida ce, kai kuwa ka zama dan cikin gidan"


Wajen zama ya nunawa Hisham, du sai ya kasa sakewa da kyar ya zauna ya kawar da kansa a kansu , sam baya so su tatauna abinda ya shafe su a gabansa gaskiya


A nutse kakan Aisha ya ce" kudi? Da mulki, ba abinda ke daukan dan adam ya kaishi wuta cikin sauki sannan ya kaishi aljannah cikin sauki irinsu Nana Aisha, shin kin san kafin ya samu wannan matakin me ya faru da shi? Bara ki ji abinda ya ringa faruwa har ya kai matakin da a jiya zuwa yau da bakinsa yake zayane min wai shi din nan da bakinsa har ya nemi da sirikin da ya aurawa yarsa jiya jiyan nan kan ya saka baki kar a kore shi a kujerar da wani aka tayar aka dora shi, shi din nan ya sauki yar ya badata ba tare da ya san takamaiman halayan waye ya aurawa dan kawai ya san cewa wani ne wanda suke iya mora, Nana Aisha da ba dan Allah ya sa matsayinsa bai saka shi alfahari ba da tuni kin ga abubuwa, Nana wai yau har mahaifiyarki ta iya buda bakinta ta nuna min ita din ba mutun bace butulu ce ta hanyar sakawa wa'inda suka amsheta da ita da yarta, suka ba yarta miji, suka kula da lafiar mahaifin mijinta, suka dauke mana abinci abin sha dukan bukatu tamkar wasu shakikanmu cewar an yi maki kishiya ba zata yarda ba mahaifinki ya samu mahaifiyar Mijinki ya fada mata ko ta sa a saki yarinyar ko ya koreta a aiki, bayan ita ta san alfarmar yaron take ci, su dukansuma suke ci, rigimar ce har ta kawo su nan gabana , wai duka a kan kudi da mulki? NANA AISHA shin ina duniya zata da mu ne?"


Ya karashe a zafafe kafin ya dago da kakausan kallo ya ce"





                  👏

No comments