MUGUN DUHU 23-24
⚫```MUGUN DUHU```⚫
_STORY BY MRS ABDULL_✍️
https://chat.whatsapp.com/DvzXXgIpkS09c6HC71vxvf
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
🅿️2️⃣3️⃣_2️⃣4️⃣
''Rana tsaka ta tashi da ciwo, tun asuba a al'adar ta zata tashi ta fara ayyuka ta shirya Khalil zuwa makaranta amma ranan shiru har ya riga ta tashi gaban gadon ta yaje yana faɗin
''yaya SAHLA yaya SAHLA ki tashi mana zanyi latti fa...
''idonta da suka yi jajir ta bude ta watsa masa wani kallo sannan ta lumshe su, Khalil yayi matukar tsorata ganin idon yar uwarsa haka, da sauri ya fita parlou,a tsaye ya samu Abba da umma suna kallon dining da mamaki cike a fuskar su yau kuma lpya dining wayam? Shigowar khalil yasa su juyowa cikin kidima yace ,
''umma yaya SAHLA tana can kwance na rigata tashi kuma da mata magana ko motsi bata yi ba da ta bude idonta yayi ja sosai kuma bata ce min komai ba'' ya karisa maganar kamar zai fashe da kuka.
''muje na gani cewar umma Abba be bi bayanta ba kasancewar yarinya ce budurwa baka san wanne irin shiga tayi ta kwanta ba ko mahaifinta ma bai dace ya shiga daki kai tsaye ba duk da kuwa da ƙanin t take kwana bazata yi wani shiga ba amma ya shi babba ne gwara day mahaifiyarta ta duba.
''dakin suka shiga still SAHLA na kwance Bata k motsi matsowa gaban gadon umma tayi tana kiran SAHLA,shikam Khalil dama yaki matsowa tunda yaga idonta dazu ta bashi tsoro, ke SAHLA umma ta fadi tana matsawa gaban gadon ,
''ware idanun ta tayi da suka yi kamar Borkono sabida azabar ja da suka yi.
''innalillahi wainna ilaihirraji'un,cewar umma tana matsawa da baya sabida yanda idon SAHLA yayi kamar zai kama da wuta.
SAHLA me ya same ki ? Cewar umman ta shiru tayi ba magana , kara matsowa tayi kusa sabida al'ajabi har cikin zuciyar ta idon SAHLA ya bata tsoro amma uwa uwace shin idan ta gudu ina zata?
''matsowa tayi ta rike ta duka tana faɗin menene ya same ki haka nan Khalil kira min Abban ku ,to umma ya faɗa yana juya wa a guje ,
Da sauri Abban SAHLA ya shigo yana faɗin Hajiya lpya kuwa , cikin karye War zuciya tace Alhaji kalli day SAHLA magana nake tayi taki cewa komai da alama ciwo ne ta tashi dashi , ikon Allah cewar Mahaifin ta na matsowa cikin fargaba yace SAHLA!
'' bude ido tayi nan ma jajir suke har yanzu ,cikin dakewa abba yace ''ke SAHLA yi magana mana meke maki ciwo ne? Meke damunki? Shiru ba amsa
''abin ya fara bawa umma tsoro dan haka ta fara share kwalla ,Hajiya shirya ta mu wuce asibiti kunji ko?
Kokarin mikar da ita tayi amma ina bazata iya ba sakamakon wani irin nauyi da tayi ,tayi tayi ta daga ta amma abu ya ci tura ,dole sai mahaifinta ne ya ciccibe ta da kansa yayi mota da ita saurin kiran AHLAN Abba yayi yace yazo ya kai Khalil gidansu ya same su a asibiti SAHLA ba lpya, ba'a rufa minti goma ba kuwa sai gashi lokacin har sun wuce Khalil na wajen mai gadi.
'' AHLAN ke masu tambayoyi,yadda suke amsa masa ne ya sa hankalinsa tashi domin jin mai gadi na faɗin ay alhajin ne ma ya dauko ta da kanshi .
''babu shiri ya kai khalil wajen Rasheeda sannan ya wuce asibiti ,can ya same su hankali tashe , Abba ina kwana ,ya jikin nata ? Jiki sai godiyar Allah babana gata nan day sun karbe ta tana ciki , innalillahi wainna ilaihirraji'un, hasbunallah wani'imal wakilll,cewar AHLAN yana zama gefen umma can kan wata kujera,
Kusan minti 60 sai ga likita ya fito , ka same ni a office kawia yace na Abba,
'' AHLAN da Abba ne suka bishi ,umma kuma tana zaune tana sharar kwalla''
'' a gaskiya maganar Allah da Annabi bazan ɓoye maka ba yallaboi ciwon yarka ba na asibiti bane kai tsaye kenan dalilin da yasa ka na fadi maka haka shine ga ta a kwance tabbas duk wanda ya ganta yaga marar lpya amma kaf mun auna ta mun gwada ta babu irin gwajin da bamuyi mata ba amma babu abinda muka gani ko maleria bata da ita balle wani damuwa da zai hana ta magana ko motsi,lpyar ta kalau komai normal a jikinta ,so bazan ɓoye maka ko na cuce ka ba gwara ayi maganar gaskiya ciwon ta bana asibiti bane ku dauke ta a nemi na gida,duk da bazan iya cewa ga abinda ke damunta ba amma addu'a ma magani ce ku koma da ita gida a nemi malami da zai ringa mata addu'a da kuma bata magani Allah ya saukaka. Duk wadannan maganganun likita ke yiwa su AHLAN bayani a office dinsa.
''gaba daya jikinsu ya sanyaya duk sunji wani iri sihiri kenan fa yake nufi to wa yayi mata me dalilinsa , innalillahi wainna ilaihirraji'un AHLAN har ya fara kwalla tun kafin yaga yadda SAHLA ta dawo dama shi saurin kuka gareshi abu kadan sai ya saka shi kuka bashida taurin rai sosia.
''nagode likita Allah ya saka da alkairi mungode ,bakomai ranka ya dade Allah ya bata lpya ,kallon AHLAN yayi sannan yace kayi hakuri kaji Allah ya saukaka insha Allah ƙanwar ka zata samu sauki ,Allah yasa cewar AHLAN yana goge idonsa da hankici''
Fitowa suka yi inda suka bar umma nan suka same ta lokacin wajen 12 na rana, an sallame mu Hajiya tashi mu wuce ,kafin ya rufe baki aka turo SAHLA a gadon da ake daura mara sa lpya ,likita na biye da nurses din AHLAN ne ya zo gaban gadon ya tsaya ,idon ta kar a kansa har yanzu jajir idon yake yaki canza kala , sannu sannu kinji ?cewar AHLAN ,ko motsi bata yi ba sai idon ta dake kansa ,da tana da hali da tana da dama cewa zatayi ya AHLAN cire min wannan ciwon ita kawai tasan me ke damunta ita kawai tasan abinda take ji cikin naman jikin ta , ziciyarta kuma kamar ana hura mata ballon Sai taji tayi mata nauyi ta huru sosai kamar zata fasa mata kirji.
''Haka nan suka tura ta har bakin mota yanzu ma Abban ta ne ya daga ta cadak ya saka ta a motar ya hana AHLAN taɓa ta ko kadan,
''gdya yayi ma likita sannan ya shiga motar ya ja AHLAN kuma ya tada mashin din sa ya bisu a baya''
Ya ma riga su isa ga dan haka ya hira suka iso , yanzu ma Mahaifin ta ne ya daga ta har cikin gida, AHLAN yabi bayan su umma na ta kuka,
''a parlou ya ijiye ta akan kujera shima ya nemi waje ya zauna ,dukkansu zama sukayi umma tace
''alhaji yanzu menene abinyi da wannan yarinyar? Har yanzu kaina a daure yake da wannan lamarin .
''abban SAHLA yace Hajiya ki kwantar da hankalinki insha Allah zata samu sauki zan samu malamai ayi nata saukar Alkur'ani ayi duk abinda ya dace magani kuma inday kinji ko ina ne in bai shiga shirka ba a yi mata a gaya min ko kuma ko bana nan a kaita ko a karbo a yi mata insha Allah babu wata damuwa , ya kalli AHLAN yace
''babana sai hakuri ko insha Allah zata samu lpya kuyi hakuri kunji? To Abba Allah ya saukaka , da ameen suka amsa duka , umma tace ina Khalil din?
''yana gida umma na barshi wajen khadija don ummi bata gida ta fita unguwa(Rasheeda).
'' to shikenan babu damuwa, babu ayki ne yau cewar umma tana kallon AHLAN?
''umma baza Ni ba wallahi bazan iya komai ba , a'a cewar Abba ban lamunta ba Ibrahim ka kama hanya ka tafi tun daga yanzu daga samun ayki zaka fara wasa da damar baniso bamu muka daura wa SAHLA ciwo ba kuma insha Allah Allah shi zai bata lpya dan haka ka tafi aykin ks na dare ne kake dashi?
''eh Abba zan tafi da magriba ,to Allah ya taimaka ya bada Sa'a'' a tausasa harshe ayi abinda ya kamata
''insha Allah Abba cewar AHLAN yana miƙewa SAHLA shi take kallo kamar mai shirin cewa wani abu amma babu hali ,to da jikin ta yana dan motsi ne zai iya bata ta rubuta amma babu abinda ke motsa wa sai idanun ta,girgiza kai kawia yayi ya juya ya fice.
''tun daga wannan ranan magani ake nema wa SAHLA amma yanda take haka nan take cigaban da aka samu kawai yanzu tana Dan iya tashi ta tafi da kafafun ta amma shima sai an dan riketa, kowa ya jajanta wannan ciwon na SAHLA daga yan uwan mahaifinta har na mahaifiyar ta,ga Hajiya zainab ma duk da ita ake ta fafutukar neman magani ko ina aka ji mai magani za'a je ko ina kuma Jamila da Hajiya zainab sune yan rakiyar umman SAHLA,a haka ne har aka samu labarin wani mai magani,umman SAHLA da kanta ta kira Jamila akan taso ta kai SAHLA bata jin dadi itama ,sai tace mata wallahi anty hajiyar Ja'afar ne ba lpya (sirikarta)to muna ma asibiti wllahi amma a bari zuwa gobe mana tunda bakijin dadi,wallahi Jamila bana iya bari sai naji kamar goben bazata zo ba kawai barin kira zainab ta kaita , a'a anty nifa banison Hajiya zainab dinnan duk tazo ka wani kanainaye ki gaskiya banison take shisshige maki nifa mafarkinta nake tana binki,wallahi banison shirme Jamila tam , sannan ta katse waya ,
''hajiya zainab ta kira nan tace mata bakomai gata nan zuwa zatazo ta kaita ,
''babu jimawa sai gata kuwa da motar ta tana zuwa umma ta kama SAHLA ta saka cikin mota sai kuma ga AHLAN nan ya gaida su yake tanbayar inda zasuje ,umma ke fadi masa fatan alkairi yayi masu sannan Hajiya zainab taja motar haka kawai zuciyar AHLAN ke bugawa ya rasa dalili amma sai yayi ta addu'a cikin ransa
'' awansu uku suka dawo ,daƙyar SAHLA ke tafiya ciwo ya dawo kamar na farko idon nan yayi jajir kamar Borkono,ita kanta Hajiya zainab taji tsoron wannan lamari daga zuwa wajen mai magani shikenan.
''to haka day aka kaita daki aka kwantar da dare AHLAN yazo shima yaji mamaki amma bai ce komai ba kuma zuciyar sa tun safe take bugawa.
Washe gari sassafe umma taji buruntu a kicin babu shiri ta diro daga gado ta fito ,kicin ta shiga ganin SAHLA a tsaye da kafafunta tana shirin daura tukunya yaba umma mamaki, matsowa tayi ta rike mata kafadu tace ke ya jikin ya na ganki anan,
''umma na samu sauki sosia wallahi haka kawai na tashi naga ina iya komai kekam!''
''Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah Allah na gode maka Masha Allah sannu SAHLA Allah ya baki lpya ,
''tun daga wannan ranan ta warke tas kamar bata taɓa jinya ba sai a lokacin hankalin kowa ya kwanta , shirye shiryen bikin su aka cigaba sayi ba kama hannun yaro har Allah ya kaisu ga auren har kuma aka gangaro wannan rana da suka je asibiti bata da lpya aka tabbatar mata da ciki wata uku ba sati daya''
''share hawayen da suka zubo mata tayi sannan tace a fili ya zanyi da raina Ni Asma'u?✍️😭
*Yan Niger da suke saida kaya a kasar su suke sari a Nigeria nesa tazo kusa ku nemi MRS ABDULL ta wannan number domin ganin kayayyakin mu masu sauki da arha da kuma inganci za'a tura maki har inda kike ,siyan na gari maida kudi gida*
_07059305867_
*Dan Allah ina rokon duk wacce take karanta littafin nan da tayi Saving number ta sannan tayi min magana WhatsApp insha Allah zan gaya mata abinda zai biyo baya dan Allah ina rokon wannan Alfarmar plss sai na jiku....*
_07059305867_
*TALLA TALLA TALLA*
*LITTAFIN JANNAT LITTAFIN DA YAZO DA SABON SALO DA HARGAGI DA RUGUNTSUMI WACCE NI MRS ABDULL NA RUBUTA MAKU SHI WACCE BATA KARANTA BA TAYI MAZA TA GARZAYO DOMIN NEMA TA KARANTA KAN FARASHI NAIRA 200 KACAL DOMIN KUWA JANNAT RETURN YANA NAN ZUWA MAKU DA BAYAN SALLA INSHA ALLAH WANDA ZAU ZO MAKU DA WANI SABON SALON MAI RIKITARWA DA CHAKWAKIYA CIKIN SA WADDA SUKA KARANTA JANNAT SUN SANI KU TANBAYE SU KARON HAJIYA SADIYA DA HUDAY KU TANBAYE SU INA NUWAIRAH,KU TANBAYESU ALWASHIN DA TA BUGA KAFIN A KARKARE LABARIN TABBAS KUNSAN DA CHAKWAKIYA KUN SAURARE NI KU TARE NI CIKIN JANNAT RETURN DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA MAI NEMAN JANNAT COMPLETE ZAI YI MAGANA TA WANNAN LAMBAR IDAN BA BIYA ZAKIYI BA PLS KI HAKURA SAI KIN SHIRYA👉*
_07059305867_
*MRS ABDULL ce ✍️*

No comments