Breaking News

HAYATUL MAHAYAT 17-18

 


🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         🦚🦚🦚🦚

               🦚🦚

                 🦚

_Story and written_

            ```By```

*NPEEDY A AJI* 


_Dedicated to_

*My yar amana*



```My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

         typing......✍🏻```


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




🅿 17 & 18



Kafin muzaffar yayi magana Rayhana ta 'karaso hannun ta d'auke da cup da robar ruwa ajewa tayi had'ida tsiyaya musu ruwan murmushi tayi sannan tace


" an canja musu suna wannan shine Hassan wanda yake  Sudees shikuma wannan Husain Shureem kenan "


Murmushi abokin yasaki yace 


" kay gaskiya kun iya za'ban suna nice name " murmushin 'karfin  hali muzaffar yasaki yabasar da zancan dafad'in tashi muje muci abinci ko ? "


Tashi sukayi suka nugi kan dining Rayhana da kanta tahad'a masu abinvin sannan  ta amshi yaran takoma cikin  parlon 


Shiko Muzaffar cikin sakka yafaracin abincin dan yana tunanin kwa'ba zaiji amma abin mamaki seyaji wani irin dad'i namusamman wanda raban dayaci girki mai dad'i irin haka tun  Nabila tana raye  sosai yaci abincin shiko abokin nashi afili yake bayyana had'uwar abincin bayan sun gama kyauta abokin muzaffar yayi ma Twins hadda Rayhana wadda yake zatan matar muzaffar ce


Harabar gidan kawai yarakashi yadawo yana shigowa cikin parlon yawatsa mata wani irin kallo cikin d'aga murya yace 


" ke dagayau idan nasake zuwa dawani kika fito har yaganki wallahi senayi mugun 'bata miki rai Allah yatsareni nazama mijinki dubekifa 'Yar 'karamar yarinya dake ? mai zanyi dake sannan idan nasake ganin kinbar yara wajan kayan wuta hmmmm matsalar ayima 'karamar yarinya aure kenan basanin darajar yara zatayiba amma akan yaran har kika samu 'karfin gyauwar marina hmmm wallahi nasha alwashin sekinyi nadama "


Rai 'bace yashiga cikin bedroom d'in yanajin mugun tsanarta cikin Zuciyar shi


Masarautar Sarki Yazeed cikin taahin hankali Sarki Yazeed yace 


" haba boka sake dubawade amma tayaya za'ace dole se anyi haka ? "


Cigaba dayin  sirkullan shi boka yayi tsayin lokaci yasake d'agowa yadubi Sarki Yazeed yace


" Tabbas Sarki fatine yake  tafe cikin nahiyar ka kuma dole se hakan tafaru amma akwai mafita d'aya  mafitar kuwa itace samun jin ahalin masarautar HAYAT ina nufin doke se ansamu had'uwar jini bakamar yadda yafaru abaya bane a'a wannan shi ba auran jinin gidan yake bu'kataba haihuwa yake bu'kata 


Idan matar Yarima Aliyu tana nan to abin yazo dasau'ki sekusan yadda zakuyi ta haihu bawani abu za'ayima yaron ba  kawai de yazama yana cikin gidan matsayin jikanka sannan dole aji dashi sabida idan yayi fushi kuma zaku fuskanci babbar matsala  "


Ajiyar zucuya Sarki Yazeed yayi sallamar boka yayi bayan boka yafita yakira mahaifiyar Aliyu bayan ta zauna  yadubeta yace 


" Ummin Aliyu ga matsala nan tana tunkaro masarautar mu " sanar da ita komi yayi sannan yad'aura dacewa " dole muje masarautar HAYAT dan amsar cikin jikin Zahra dan nasan iziwa yanzu takusa haihuwa "


Mi'kewa Ummi tayi tace  " agaskiya ni bazan iya zuwaba kamanta irin rashin mutuncin damukayi akan seganta wannan cikin bayan munsan cewa namune munyi dan mu tozarta Sarki Abdurrahaman sekuma mukoma mu tozarta kanmu gaskiya ni bazan iyaba sede idan kai kaje amma bandani "


Cikin tsananin fusata Sarki Yazeed yace " wato koda masarautar tawa zata shiga cikin  matsala ke  baburuwanki kenan ko ? fitamin daga parlour " tashi tayi tafita rai 'bace tana fad'in tayaya za'a d'akko mana jin masarautar HAYAT masarautar da bamuda ma'kiyiya kamar ta shikam Aliyu nasan yanzu bashi dawata damuwa tunda ya auri wadda yakeso "


A'ban garan Aliyu kuwa yama rasa yadda zaiyi dan kuwa yanzu mugun haushin Salimat yakeji ko kallonta bayason yi bashida ayki sena tunanin zahra amma yasaka yarda santa yakeyi shi yana d'aukar kawai bu'katar shice akan ta 


Zaune yake cikin parlour shi yana zu'kar shisha babu ko saurarawa cikin mamaki abokin shi dake  gefanshi yace " kai Aliyu karfa kacikama kanka  wannan abin kasan ansa mata manyan sinadarai masu 'karfi acikifa ? " 


Hararar shi Aliyu yayi yace " nasoma ace sunfi haka bazakagane irin halin danike cikiba narasa farinciki kwatakwata nakuma rasa yadda zanyi nadawo dashi kabarni hakan yanasawa naji sau'kin damuwata "


Murmushi abokin nashi yayi yace haba Yarima Aliyu saban aure garekafa amma kazauna da damuwa gaskiya abin da mamaki " mi'kewa Aliyu yayi rai'bace yace 


" kai Jamilu fitamin daga parlour ko yanzu nasa afita da kai " ganin yadda ranshi ya'baci yasa Jamilu tashi yafita dan yasan zai iya aykata haka bayan fitar Jamilu Aliyu kwantar da kanshi yayi saman cushion yana jin tsananin bu'katar Zahra cikin jikin shi jin shigowar Salimat yasashi jin wani irin mugun 'bacin rai tun kafi ta'karaso gareshi yami'ke cikin bedroom d'in shi yashiga kullewa yayi dan bamayason ganin fuskarta balle tara'be shi 


Yau kimanin 2 months kenan da kwanciyar maimartaba ciwo har izuwa yanzu babu sau'ki se gurin Allah dan ayanzuma bayako iya magana cikin nuna isa kawu Yusuf da kawu Idris sukace 


Kai Abubakar nagafa kanaso kadinga wuce matsayinka bafa kaine cikakken Sarkin ba dole kabari mukai yayanmu wajan magani bazai yiyu muna kallonshi ahakaba "  murmushi Abubakar yayi yace 


" kuyi ha'kauri dukda bankasance cikakken Sarki ba amma yanzu iko nawane to a gaskiya bazan yarda akaimin mahaifina wani wajan 'yan tsubbu ba sede kukawo mai maganin nan idan nayarda da da irin tsoran Allah shi shikenan idan kuma naga bokane to bafa zanyarda yaga mahaifinaba ballema yata'bashi nagama magana "


Rai 'bace kawu Yusuf yace " lallema Abubakar wato mu kake gayama irin wannan maganganun ko ? to wallahi kabi ahankali idan kayi wasa semu saukeka daga kan kujerar nidama banga amfanin d'auraka saman wannan mulkinba sabida kwata kwata baka cancantaba "


Murmushi Abubakar yasakeyi yace " ay kawu sede kuyi ha'kuri sabida koda babu ran mahaifinmu sede aza'bi wani a cikinmu sabida mune keda gadon wannan kujerar a yanzu ballema in sha Allahhu mahaifinmu zai warke yacigaba da gudanar da mulkin adalci cikin masarautar HAYAT  ammafa kuyimin afuwa idan maganganuna sunyi tsauri "


Daga haka Abubakar yatashi yabar cikin parlour tattaunawar rai 'bace Yusuf yace " lallema yaron nan shi haryakai matsayin yazauna yana gaya mata maganganu balefinshi bane lefin yayane daya bashi damar jagorancin wannan masarautar amma zanyi maganin shi dafashi Idris yayi ya a'a Yusuf nifa tawani fannin banajin haushin abinda Abubakar yakeyi sabida kaduba tunda yafara gudanar da irin nashi  mulkin har yanzu bamuga wata matsalaba dan haka kabarshi tunda yace baya bu'katar akai maifin nasu gurin magani to kabarshi mukira mai maganin gida seyaduba shi "


Wani irin kallo Yusuf yayi mai batare dayace komiba tashi Idris yayi yafita bayan fitar shi Yusuf yasallami sauran yarage daga shi se waziri da wambai ajiyar Zuciya Yusuf yasauke yace 


" kunga irin aykin yaron ay seda nace tun wuri musan abinyi akan shi kukace ay yarone bazai hanamu aywatarda aykinmuba toga irin tanan yaro yanason yazame mana hakin wuya mai yuwar fita "


Cikin takaici waziri yace " barshi tunda yanuna mana taurin kai zamusan yadda zamuyi dashi nide fatana mugama aykinmu kafin dawowar wancan masifaffen yarima muzaffar d'in dan shifa bawanda yake kallon damutunci kaf cikin masarautar nan gara sauran sunajin maganar kaka amma shi bayaji kuma kunga wani abin dole setasa maba suke yarda amma shi babu ruwanshi dasa bakinta yanzu kaje kasamu kaka akan maganar wajan maganin kasanfa boka yace karmu wuce kwanaki 3 yau gashi munci kwana d'aya saura 2 gara musan abinyi yazama dasanadin dawowar muzaffar mutuwar mahaifinsu "


Jin haka yasa Yusuf saurin tashi yafita bayan fitar shi waziri yayi dariya ya kalli wambai yace " barshi yagama yimin ayki daga baya nima  nayi mishi irin nawai aykin dan wallah bazan bar mulkin masarautar HAYAT yasu'bucemin ba duk sena tar watsasu baki d'aya yazama nine zan hau kan kujerar masarautar HAYAT kaima wambai daganan seka samu matsayin wazirina "


Wata irin  dariya suka saki su duka wambai yace " godiya nike Sarki gobe  "


Tofa Allah ya kyauta wato cuta zataci cuta kenan 


Koda Yusuf yasami kaka akan maganar itama 'kin amincewa tayi sabida haka akayima mijinta daga zuwa gurin magani sede aka dawomata da gawarshi duk yadda Yusuf yayi akan sata baki amma ta'ki a'karshema cewa tayi yatshi yabata guri dole yabar parlour nata Zuciya shi cike da d'inbin haushi


Hankali tashe muzanbil yasake kallon Samha yace 


" ke wai  har yanzu babu wata alama ko ciwon mara baki fara jiba ? " jinjina mishi kai tayi alamar eh iska yafesar daga bakin shi yace " yanzufa watan shi 4 kenan tun yana wata 2 nake fama dashi akan yazu'be amma har yanzu babu labari yaya zanyi kenan " tashi yayi yafita afusace bayanshi  Samha  tabi da kallo cikin Zuciyarta tace 


" in sha Allah bazai fitaba sena Haife shi dukda bansan waye ne uban shiba amma nikam inason baby na "


A'bangaran Arfar kuwa yanzu cikinta yakai 5 months cikin kissa take shafa cikin gaban mu'azzam tazo tatsaya cikin raunanniyar murya tace 


" haba doctor jifa cikina harya fito amma ace ankasa sanarda muzaffar maganar cikin dolefa shine ubanshi gaskiya bazan iya boye wannan sirrin ba dan haka nizan kirashi nasanar d......... "


Cikin tsawa mu'azzam yace " karkisake kafara idan kuma kikayi haka koda bayan yadawone wallahi sena nuna miki irin mushin mu'azzam "


Tashi yayi yabata guri rai 'bace itama tashiga cikin bedroom 


Tsawa kaka tadakama Zarah tace " zaki sanye wannan maganin kosena 'bata miki rai ciki wata 8 amma bakyason San magani se idan kun haifi d'anku kununa mana iyayi akan shin babu ko kunya maza ki shanye shi tass "


Dole zahra tashanye maganin badan ranta yasoba cikin tsananin damuwa kilishi tace 


" haba Ahmad har yanzu ace ankasa samo wani cigaba akan rashin lafiyar mahaifinku innanillahi wa'inna ilaihirraju'uuun wannan wane irin ciwone da babu sau'ki kullum se gaba ? yakeyi ya Allah kakawo mana sau'ki cikin wannan masifar " 


Amin Ahmad yace yami'ke yafita jiki babu 'karfi 


Pakistan 


Cikin rashin jin dad'in kwanciyar muzaffar yatashi zaune afili yace 


" anya kuwa babu wata matsala dake faruwa a gida kuwa ? tsayin lokuta Zuciya ta takasa natsuwa gaskiya bazan iya bari senan da 1 month nakoma gidaba dukda babu shi'awar gidan cikin raina amma dole naje idan har lafiya to tabbas mahaifina yayi fushi dani tsayin lokaci banga kiranshiba idan nakirakuma baya shiga gashi su yaya Ahmad suna tabbatar min da kowa lafiya amma gaskiya nakasa gamsuwa in sha Allah cikin satin nan zan koma BIHAR zansa wani yamaye gurbin aykina nasan manyana zasu yarda dan 1 month tunda nayi har 5 months nasan bazan samu matsalaba "


Koma yayi ya kwanta addu'a yadingayi cikin ikon Allah bacci yayi gaba dashi babu jimawa dayin baccin shi yafarayin mafarkin Nabila amma wannan cikin wata siga ba wadda yasaba ganiba 


Murmushi takeyimai cikin kyawun siffa tace 


" Sojana ha'kika ina cikin farinciki wanda bazan iya misaltashiba please kamaye gurbina dawata idan har kanason farin cikina Sojana tahakane zaka samu nasarar gano wa'inda sukayi sanadin rabamu please kafin kabar Pakistan kayi aure shine zai zama babbar nasara akan gane wa'inda suka rabani da niyarka bazan dauwama cikin farin cikiba har se kagane yadda akayi aka kasheni kuma kad'aukarmin fansa dan bazan yafeba sun rabani da Sojana sun rabani da yarana dan Allah my soja kayi aure kodan samun wannan nasarar dakuma samun wacce zata kulamin da Twins d'ina 


Banajin farin ciki idan bana tare dake haka kuma bazanyi farinciba idan har ka kasa d'aukarmin fansa amma zanyi farin ciki idan kayi aure love so much my Soja ......... " tashi yayi afurgice yana kiran Nabilahhhhhhh 


Jingina yayi da fuskar bed d'in shi yana sauke ajiyar Zuciya afili yace 


" haba Nabila taya zaki sani yin aure bayan kinsan bazan iya kallon wata mace dasigar soba bazan iya ba ammafa nagamsu da kikace idan nayi aure zan gane wa'inda suka kasheki tabbas hakane sabida nasan zasu kumyin yun'kurin haka akan duk wacce zan sake aura hakane Nabila zanyi aurene kawai dan wannan dalilin badan inason hakanba amma bazan ta'ba kallon matar amatsayin mataba sede amatsayin wadda zatayimin ayki akan wannan binciken Nabila babusu farooq balle tayi dan kula dasu sede nayi dan cimma wancan burin nayi farin ciki dakikacemin kina cikin farin cikin my Nabila "


Kallon agogon bangon cikin bedroom d'in yayi cikin sauri yami'ke yana salati har 10 amma baikoyi sallah ba wannan wane iri  baccine kodan nakwana 2 bansamun baccin ? sauka yayi daga bed d'in cikin sauri yashiga toilet alwala yayi yafito yagabatar da sallah sannan yakoma yayi wanka  misalin 11:30 yagama shirin shi cikin kakin shi na Soja fita parlour yayi kamshin parlour yasashi lumshe idanun shi kan dining yanufa cikin sauri Rayhana tazo du'kawa tayi ta gaidashi beko amsaba se cewa dayayi 


 " ina yaran suke  ? " 

" Cikin ladabi tace suna cikin bedroom wasa sukeyi wasa ? gafa kukan su can inaji dallah jeki d'akkomin su barshi nizan zuba acincin da kaina shashanci kawai yarinya batasan darajar yaraba " 


Cikin sauri yagama cin abinci bawani sosai yaciba sabida yatafi tunanin ida zai samu yarinyar dazatayi mai wannan aykin dan bawai zai zauna da ita bane dazaran yaci nasarar aykinshi zai saketa cikin parlour yadawo cikin murna yaran suka nufoshi rungumaisu yayi yace 


" morning my Twice ina fatan lafiya kuka tashi ? " gwaranci suka shiga yimai dariya yasaki yace " inani ina jin wannan yaran naku sumbatar kumatun su yayi yan hannun su yayi yana musu tatata had zuwa kan custom shima zama yayi kallon Rayhana yashigayi takenan ya yanke shawarar itace zatayimai wannan aykin kiranta yayi cikin ladabi tazo seda yayi jim wata Zuciyar tana sake tabbatar mai zata iya wata Zuciyar kuma tana cewa wannan 'yar yarinyar saurin cewa yayi ay bazama zanyi da itaba nawani lokacine "


Tamke fuska yayi sosai yace 


" kee zaki aureni ? " zaro ido Rayhana tayi tanajin wata irin fad'uwar gaba tsaki yaja  yace 


" Ke dalla zan aurekine sabida kiyimin wani ayki badan ina sonkiba dazaran kingama yimin aykin zan sakeki zamu koma masarautar mu kuma dole kafin mukoma yazama na aureki sabida wannan dalilin zan baki era million 30 nasan bazaki iya barin a'innan kud'ad'an ba sannan kinga zaki shiga cikin masarautar mu kina mai 'yanci kuma bayan kingamayimin wannan aykin zan baki damar tafita duk inda  kikaga dama afad'in duniya sannan inaso idan muka koma gida duk wanda yatambayeki waye uban yaran kice nine nikuma zan tabbatar makowa ked'in matatace tunda dad'ewa sauran bayanin zanyi miki bayan nadawo kiyi shawara da Zuciyar ki koki shiga cikin masarautar HAYAT kiname cikakken 'yanci koki shiga kina baiwa tahar abada shigada yaran nan kinsan idan sukaga tafiyana kuka  zasuyi "


Cikin sanyin jikin Rayhana tad'aukesu zuwa cikin bedroom amma dukda haka seda sukasaka ihu saurin fita  yayi sabida yadda yakejin kikan yaran har cikin ranshi yarasa maiyasa hakan cikin matu'kar damuwa Rayhana tace  


" tabbas dana shiga ina baiwa gara nashiga ina mai 'yanci nasamu girmamawa wajan wasu amma nasan zansha wahala wajan Muzaffar ayanzuma yana'kare balle ina matsayin matar shi matarma dan wani ayki badan cikakkiyar mata ba towaima wane irin aykine wannan ? Allah kabani ikon zurewa zanyi komi wuyar shi in sha Allah amma dan Allah dakuma su Shureem badan kud'iba dan bazan iya amsar koda neraba daga hannun ka dan wani abuba Allah katsaremin mahaifiyata kasa watarana mugana "


Cikin sigar lallashin yaudara Alhaji Tanimu yace 


" haba Fatima yakamata kisancewa nayi nadama nabar wannan muguwar har'kallar kiyimin murna dan Allah kicema Rayhana tadawo ina matu'kar kewarta nashirya bata kulawa irinta uba wadda nakasa bata awancan lokacin dan Allah Fatima kiceceni "


Tashi tayi afusace tace  " wallahi Alhaji se Allah yayima sakayya akan cutar dakayi mana kayi sanad'in rabani da 'yata 'kwaya 1 ni bansan inda Rayhana takeba kuma koda nasani wallahi bazan fad'i makaba dan ni banyarda katuba ba  "


Shigewa kitchen tayi tabar shi yana binta dawani irin kallo cikin Zuciyar shi yace 


habawa wallahi sena baki mamaki Fatima duk wannan lalla'bawar inayimiki itane sabida cimma burina dazaran nasamu bolama tafiki daraja agurina kuma nasha alwashin se gunkiya tasha jin Rayhana "


Daga Al'kalamin.......🖊

No comments