MIN QALB 14
______________________
#MIN QALB❤️
Mamuhgee
ZAFAFA BIAYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
YANKAN BAYA
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[3/23, 1:35 PM] Zafafa: *_MIN QALB 14_*
_mamuhgee_
ANNUR PERFUMES ANNUR PERFUMES!!!!!!
JAMA'A MA'ABOTA SON QAMSHI DAN SANYAYA ZUCIYA Ina kuke kuzo
ga sabuwar duniyar turare sabon tashe ANNUR PERFUMES sunkawo muku,
Turarensu qarshene,
Qamshinsu na daban,
Kayansu tabbataccine,
Aikinsu ingantacce ne
shin kataba/kintaba amfani da ANNUR PERFUMES kuwa?
To maza qarzayo karki Bari ayi badakeba dankuwa kayansu
lamba dayane Kuma amintaccine masu guarantee domin kuwa mun tabbatar.
ANNUR PERFUMES donjindadin customers munkawo muku
dadadan turaruka na musamman masu nishadan tarda Amarya da uwar gida
harma da angonta kamar haka turaren wuta humra kala daban daban kwalaccha
Dana matsi na infection biki ko suna dyadya ko sari ina kano gaida
layin massanlachin imamu malik koku kira number waya kamar haka
07086341096 ko 07069037534 muna munamaraba daku saikunzo.
ANNUR PERFUMES
TURAREN WUTA
KHUMRAH.
KULACCAM
MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)
DECORATIONS ..
KAYAN INFECTION DANA MATSI (STEAMING)
TANA KANO: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!
**************
Ringin numbern usi din keyi harta katse bai daga ba tasake
Danna Kiran tana cewa'
Usi idan muka hadu saina fasa maka baki da kai tunda har
zaka iya bacci baka kirani kaji Yaya ta kasancemin ba a wannan zabeerar da
kallo daya Andi da Modibbo sukewa mutum sai cikinsa ya mur'da,
Uwa uba arasa gurin ajeni sai anan cikin wannan me bada
tsoron da matarsa.
Kira biyar tayi Masa Amma baa daukaba takira wayar iyami
cikin sa'a kuwa ta dauka Nan suka jima suna mgn iyamin na maimaita Mata karta
taba duk Abinda zata gani na kowa karkuma ta jawowa kanta fitina ko rigima ta
jawo musu kafin aka miqawa kawu wayar Shima dai yayi Mata maganar karta taba
abun kowa sbd kada 'yan kudin Nan dasuka samu su qare a gun kashe rigima Shima
usi sunfada Masa kada ya kuskura ya janyo rigima sbd tanadin kudin Nan zasuyi
sbd abinci dakuma qarasa hada takardun komawarsa karatu.
Fadawa lafiyayyan gadon tayi ta kwanta tana lumshe ido bayan
tagama wayar
Tai wani juyi tana lulluba da bargon me shegen laushi sbd
sanyin AC dake ratsata ta lumshe ido tana cewa'"
Masu kudi wato ko a gurin bacci sunfi talaka samun nutsuwa
Da agidanmu ne da yanxu radion kawu da qarar dakan turmin
maman junior da qarar bude tukunyar maman basiru sun Hana mutum bacci,
Rufe idanu tayi tana sake gyara kwanciya take bacci me dadi
yayi gaba da ita ga gajiya ga lafiyyan abinci dataci ga lafiyayyan gurin
kwanciyar dakuma sanyin AC ga ba hayaniya ai Dole baccinta yau yayi dadi.
Saida garin ya hantse ta tashi tana wata irin miqa me Dadi
fuskarta a sake da farin cikin irin baccin data samu tana qoqarin saukowa gadon
ne zarah tashigo daukeda sababbin brushes da toothpaste masu kyau tana kallonta
tace"
Amatu Yaya? kintashi lfy? Ya babyn dr?
Qarasa saukowa gadon tayi tana sake yin wata doguwar miqar
datasa zarah saurin ajiye kayan hannunta tana riqeta tace"
Amatu zakiwa kanki illa idan kina irin wannan miqar
Idan kinajin gajiya ne za'asa ayi Miki tausa ahankali Amma
Dan Allah ki daina kinji??
Kallon sakarai amatu ta Mata Jin hadda miqar ma yanxu wani
tsurku zaa kawo sbd ciki...
Amma dai ko yayane bazata Bari banxa ta wucetaba tubda
damace tasamu gwara ta dama kafin Takoma inda tafito Dan haka sai ta 'dan
yamutsa fuska tana 'dan dafe bayanta tace"
Anty zarah ko Ina jikina ciwo yakeyi na gajiya shiyasa nake
'yar miqar ko zanji jikin ya sake Amma tunda kince za'amin tausa inaga idan
anyi zanji jikin ya saki.
Murmushi zaran tasaki tana sakinta Takoma gaban mirror ta
dauko toothpastes din different flavors kusan kala biyar tace"
Ga Macleans ki bude kowanne kiji Wanda qamshinsa ya Miki
Wanda bazai tayar Miki da zuciyab saiki ringa amfani dashi.
Karba tayi tana washe baki tana duddubasu tace"
Duka ma sunmin abarminsu kowanne ma qamshinsa zaimin
sauran gida zanje dasu idan zantafi.
'yar dariya zarah tayi tana girgiza Kai rashin damuwar
amatun na sake burgeta musamman data 'dan Fara lura tun jiya inda amatun tafito
tana tareda yunwa gskia Dr be kyautaba barinsu su wahala haka tana matsayin
matarsa bayan duk arzikin dayakedashi.
Fita tayi Takoma kicin ita Kuma amatu toilet tashiga tafara
yin brush da kusan toothpaste kala hudu kowanne saidata fasa ta 'dan lakata
tayi dashi take bakinta suka ringa bada wani qamshi masu Dadi dasuka sakata yin
wanka cikin nutsuwa da annashuwa.
Tana fitowa saidatayi sallah kafin ta shirya cikin doguwar
rigar jallabiya Mara nauyi Wanda duk zaran ce takawo Mata daga gani duk nata ne
Amma suka sabbi ne Babu Wanda ta taba sakawa.
Tana cikin fesa turare tana lumshe ido cikin jin Dadi
tace"
wainnan turaren dasu zankoma gida idan zankoma ma komai
saina dauka naje dashi bazanga irin wannan Batinba nabariba.
Turarukan ta kwashe duka tabude wardrobe tazubasu cikin
Jakarta daga can qasa ta rufe zip din tadawo gaban mudubin tana gyara zaman
rigarta a jikinta saiga zarah tashigo tana kallonta Jin dakin yacika da qamshin
turaruka yasata Dan 'yin tari tana cewa'"
Amatu wannan turarukan bazasu cutatar dakeba kuwa¿
Qamshin yayi yawa Zo muje dining muci breakfast idan Kuma
akwai Abinda kike buqata ba Wanda akayi ba sai hafsatu ta Dora miki ga Dr
khalil ma yazo Yana palon MD suna Magana.
Ba qaramin Jin Dadin zuwan Dr khalil tayi ba sbd sanar dashi
Abinda su zarah din ke shirin Yi na Kiran wani Dr shiyasa ta farayin gaba tana
cewa''
Ni komaima aka dafa yamin zanci Amma Dr nakeson Fara gani
anty zarah Dan Allah kinji.
Biyota tayi tana cewa''
Wannan rashin hkr haka amatu bazaki jira yagama yazo
yasameki har dakin ba.
A palon ganin Dr khalil baida lokacin fitowa daga gurin MD
yasa ta marairaicewa zarah fuska tana taba cikinta
Take zarah ta tashi da kanta ta hado Mata nata abincin a
tray sbd kada yinwa tai Mata illa sbd cikin dake jikinta bazata iya jiransu ba.
Dakinta Takoma acan tayi zaman Yan bori akan carpet tafara
cin lafiyayyan breakfast din tana bude plate din farfesun kifin da akayi kawai
sbd ita dayaji kayan qamshi da 'dan yaji batasan lokacinda tasaki dariyar farin
cikiba tana diba takai bakinta saiga Dr khalil yayi knocking yashigo fuskarsa
tayi wani iri na yanayin damuwar dake tattare da ita.
Tsayawa yayi daga bakin qofar ya qura Mata ido yanda take
cin abincin sosai cikin Jin dadinsa dakuma bayyanarda baqone agareta sai yaji
jikinsa yasake yin sanyi ya rintse ido Yana Jin zafin zuciyarsa na qaruwa sbd
baisan ta Ina zaifara da wannan qaqqarfar rigimarba sbd Nan ana Magana ne akan
ciki da aure Wanda baa Wasa dasu sbd komai dadewa gskia zata fito idan akwai
idan Babu,
Ta Yaya zaifara neman mafita?
Ta Yaya zaifara neman inda mafitar cikin amatu zata fito?
Gasu usi yanxu da Dole nauyinsu zai dawo kansa sbd inganta
rayuwarsu su duka din ta yanda har abada komai zai faru bazasu Yi shaawar sake
komawa rayuwar dasuka fito ba,
Idan har amatu zata iya saka kanta acikin irin wannan
masifar me hadari akan kudi to tabbas zaiyi amfani da kudi da qarfinsa ya
wadatasu da dukkanin abin buqata har sai amatu ta cire kwadayin kudi a ranta,
For now Abindake gabansa shine mafitar cikin jikinta da ake
zaton akwai Amma bazai Yi rushing abubuwan ba tunda tana Nan hannun MD yasan
Babu abin dazai sameta she's morethan safe anan Dan haka zata cigaba da zama
anan zaije gurinsu kawu zaifara aikin kulawa dasu daga yanzu.
Gyaran murya yayi Yana sake gyara tsayuwa tayi saurin dagowa
tana ganinsa ta miqe tana qarasa kwankwade sauran kakkauran tea din dake
hannunta cikin cup tace"
Dr tun jiya kaina ke neman bugawa da son ganinka na.....
Quite amatu""yafada cikin 'yar tsawa ransa a 'dan
bace.
Cak ta tsaya tana kallonsa ganin yanda bacin Rai ya bayyana
a fuskarsa sosai sai hakan yasa jikinta yin sanyi tayi qasa da Kai tana
kallonsa fuska a marairaice.
Ya dauke Kai sbd ganin zata sa zuciyarsa saukowa yace"
Kinsan zaman da kikeyi acikin zabeera?
Saurin matsowa tayi tareda katsesa da cewa"
Wlh dr aiki Na....
Amatu just keep quiet please,
Wane qarya kike tunanin zakimin bayan duk abin daya faru
jiya gaban kowa and yanxu Ina tambayanki kinason kawo min wani different story
Ki saurara kiji usi yafadamun komai Wanda yasa nake
mamakinki har yanzu
Amatu har kudi yayi mahimmancin dazaki 6ata sunan wani
akansu,
Rayuwarsa kike neman batawafa gaba daya
Shin kinsan shi Wanda kikaso batawa rayuwar shine Wanda
nafiso a rayuwata fiyeda kowa bayan iyayen dasuka haifeni???
Tsit tayi tana sake yin qasa da kanta cikin rashin Jin dadin
yanda yake maganar cikin tsananin 'daci da bacin Rai
akaro na farko a rayuwarta dataji nauyin wani mutum.
Juyowa yayi Yana kallonta yacigaba fa cewa"
Amatu wannan duk Abinda kike tunani ya wuce Nan
Wannan alamarin babbane bazaki ganeba sbd tunaninki kawai ya
ta'allaqa ne kawai akan kudin dazaki samu
Meyasa kudine kawai Abinda kike gani amatu wannan alamarin
babbane meyasa bazaki ganeba,
Umme mahaifiyatace duk Abinda tasaki kizo kiyi tayine sbd
rashin mafitar datake gani tana ciki
Gashi yanzu kunsani a tsaka me wahala bansan yazanyi da
kowannenku ba,
ku duka bazan iya barin wani Abu ya sameku ba kokuma wani
mummunan hukunci ya hau kanku sbd kowaccenku nada matsayi me girma agurina
gashi yanzu ta kowane bangaren nine zansan Yaya zanyi.
Kuna tunanin MD sakarai ne daza'a Zo Kai tsaye afadi wannan
alamarin ace shine ya zauna ya dauka kawai sai
sunansa ya baci?
Tabbas dakun aikata babban kuskure sbd ilimi da matsayin MD
yawuce inda umme ke tunanin ke bakyama ciki sbd komai ma qaramin kanki bazai
ganeba gameda waye MD Dan haka ki saurareni da kyau kiji,
Daga yanzu dakike cikin zabeera duk Abinda zakiyi da Wanda
yake faruwa ki tabbatarda kina sanar Dani,
Karki kuskura Koda Wasa kiyi maganar Abinda yake ainihin
gskiyar maganar Nan da kowa Koda kuwa zarah ce ko a waya karkiyi maganar da USI
sbd kadama wani yaji,
Kince kinada ciki Dan haka zakici gaba da zama a me cikin
harsai na samu mafitar fita cikin wannan shirmen da kuka faro,
And bayan zarah karkiyi muamala da kowa acikin zabeera
batareda izininaba lastly Kuma karki yarda kiyi Abinda za'a zauna meeting
akanki kokuma asan asalin waye ke acikin zabeerar Nan hakama karki yadda kiyi
Abinda zaisa a fahimci bakida ciki idan nace karki kuskura I mean kada Koda
Wasa ki kuskura
Duk Abinda kike so kifadamin zan kawo Miki shi Kuma kullum
zan ringa zuwa Nan dubaki kafin na wuce office da idan nadawo and you better
behave yourself duk da MD baida lokacin batawa agurin matarsa bare ke to yanada
lura sosai zai iya ganoki a lokaci daya hakan Kuma na nufin samun matsalarmu..
Kin fahimci dukkanin abubuwan Dana fada right??
Gyada Masa Kai tayi ahankali tana Dan satar kallonsa sbd
ganin yadauka zafi yanda yaketa fadan.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda kallonta Yana sassauta
fushinsa yace"
Shikenan karki saka damuwa ko tsoron komai aranki Ina Nan
Babu Abinda zai sameki,
Usman ma tun jiya ninace kada ya dauka wayanki Koda kinkira
sbd nasan zakuyi Magana Kuma wani zai iya jinku idan nafita zan Masa Magana
yadauki wayarki tun jiya nasan labari Yana bakinki Wanda zaki basa.
Sai alokacin ta saki murmushi tana kallonsa Jin ya sauko
gaba daya ta washe baki tana cewa"
Duk da haka saina fasa Masa baki idan nagansa tunda yaqi
daga wayar.
Kallon fuskarta yayi Yana sauke wata ajiyar zuciya sbd gaba
daya tagama sauke fushin dayazo dashi ya sakar Mata murmushi Yana cewa'
Shikenan basai idan kingansa ba zaki fada bakin
Makaranta zai tafi Kuma hostel zai zauna infact idan yatafi
bazai dawoba saiya Gama karatun Amma dai zai dawo Daurin aure inaga.
Kallonsa tayi baki sake tace'
USI zaije makaranta?
Haj Mama ta biya ne???
Batareda ya kalletaba yana duba Kiran dake shigowa wayarsa
yace"
Duk wani deal ko aiki ko kwangilane ma dake tsakaninki da
umme babusa yaqare so ki cire zancensa completely a kanki Babu wannan zancen.
USI zaije school ne sbd shine burinki nikuma nauyine Dana
dorawa kaina na cika dukkanin burinki.
Wani tsallen murna tayi tana Kiran sunansa daidai shigowar
zarah tayi saurin kallon amatun tana cewa'
Amatu wannan tsallen fa
Zaki yiwa kanki illa.
Kansa ta mayarda kallonta zatayi Magana ya rigata da
cewa"
Zarah amatu sai kinyi da gske she's stubborn..
Cikin tsananin farin cikinta daya kasa boyuwa tace"
Anty zarah Dr jarumi ne
Babu kamarsa.....
Tsit sukayi zarah na dariya cikin Jin nauyin Abinda amatun
ta fada shikuma idanuwansa ya zuba Mata jikinsa na mutuwa da qaunar yarinyar.
Atakam batama kawo tunanin komai gameda maganar yataba sai
sake sako maganganunta takeyi ganin haka yasa zarah ficewa da sauri shikuma ya
fito sbd yayi lattin zuwa asibiti itama biyosa tayi tayi Masa rakiya zuwa mota
suna tafe tana Masa sambatun irin farin cikin datake ciki har suka Isa motarsa
dayazo da ita har qofar part din nasu zarah ta kallesa tana sake cewa idan kaje
Dr Dan Allah Ina sake gaidasu kawu
Iyami ma kace Mata Inshallah bazan jawo rigimar kowaba.
Harya zauna cikin motar yace"
To nikuma fa Abinda nace?
Dariya tasaki kafin tace'"
Kai duk Abinda kafada narigama nafara aiki dashi tun
lokacin.
Murmushi yasaki tareda gyada Kai Yana cewa"
Good AMATULLAH.
Juyawa tayi zata tafi cikin taushin murya yace"
Me zan kawo Miki idan zandawo.
Kallonsa tayi Wanda yasashi Jin wani iri kafin tana 'dan
tunani tace"
Duk Abinda masu ciki keci shi zaka siyomin naci Kona rage
zafin sunan me cikin da ake Kirana dashi.
Girgiza Kai yayi Yana cewa"
Shikenan koma ciki ki kula Kuma.
Sam yau farin cikinta yakasa boyuwa tana shigowa ciki Palo
ta zauna tareda miqewa akan doguwar kujera tana kallon zarah data fito hanyar
zuwa saman mijinta tasake bajewa tana cewa'
Anty zarah qafafuwana tsami sukemin sosai Kuma.
Qoqarin kawar da damuwar data sauko da ita daga Daman tayi
tana qaqalo murmushi tace'
Bari na dauko man massaging sai a Dan mammatsa Miki qafar.
Dauko oil din tayi takirawo hafsatu Nan suka zauna tana
yankawa amatun manyan gwaiban datace tanaso tana Mata fira ita Kuma hafsatu na
mammatsa Mata qafafunta dake miqe Kan glass table din da aka Fara Dora Mata
pillow me laushi kafin tadora qafafun.
Sunyi nisa zarah ta Dan 'dago tareda juyawa ta kalli hanyar
saukowarsa sbd qamshin turarensa na IMPERIAL MAJESTY data Fara shaqowa Yana
doso palon.
Jin zarah tayi shiru daga labarin datake Bata tana yanka
Mata gwaibar yasata dagowa ta kalleta saitaga tana kallon wani gefe fuskarta
kamar da damuwa ahankali itama ta juya ta kalli inda take kallon Wanda yayi daidai
da saukowarsa gaba daya Yana sanye cikin suit din _Alexander vanquish 11
bespoke_ ash kala dasukaiwa fatarsa kyau
sosai sai wani irin kwarjini da sirrin kyau dake fita daga fuskarsa da Babu
sakewa acikinta.
##mamuh#

No comments