MIN QALB 15
MIN QALB 15_*
_mamuhgee_
Jin idanuwa ajikinsa yasashi 'dan dagowa ya kalli inda suke
Yana qarasa fitowa palon gaba daya
Su kuwa duk su biyun idanuwansu zube suke akansa Babu ko
qyaftawa musamman amatu dake qare Masa kallon tsaf zuciyarta na harbawa sbd
yaune karo na farko a rayuwarta datake kallon wani namijin data kasa dauke
idanuwanta a kansa.
Ko inda suke bai qara kallaba ya dauke Kai fuskarsa na sake
fitar musu da annuri ya nufi qofa zai fice zarah tayi saurin ajiye wuqa da
gwaibar hannunta tana miqewa ta nufesa tana cikin kulawa tace"
Fita zakayine gashi har an jere maka komai na breakfast a
dining,
Ko zaka daure kaci ko ka.....
Zanyi a office idan naje I'm late already excuse me"
Rabata yayi ya wuce Yana daukar wayarsa datai ringin
batareda yasake waiwayartaba ya fice.
Shiru tayi agurin tareda bin qofar daya fice din da kallo
jikinta a matuqar sanyaye sbd a zaman aure kulawa da lokacinsa ne tasan bazai
taba Bata ba gashi abin Yana damunta matuqa musamman idan a gaban mutane ne.
Qaqalo murmushi tayi tareda boye damuwarta ta juyo tadawo
gefen amatun ta zauna tana kawo wani labarin daban sbd wancan datake Bata na
farko ta manta Abinda take cewa.
Tsura Mata ido amatu tayi tana kallon hannunwanta dake yanka
gwaibar duk sai taji bataji dadiba
Sbd me zai dizga anty zarah din bayan ita kulawa ta nuna Masa¿
Dafa hannunta tayi tareda karban wuqar da gwaibar ta aje
cikin plate dake Kan table tana qoqarin kawar Mata da damuwa ta saki murmushi
tana cewa"
Anty zarah gwaibar Nan ta isheni haka babyb harya Fara zama
qato daga zuwanmu jiya sbd ciye ciyen da kike basa.
Sai alokacin tasaki fuskarta sosai cikin Jin dadin Abinda
amatun ta kalla tace"
Ai dama so nakeyi yayi qatoto cikin qoshin lfy ta yanda
iyayensa da kakanninsa zasu bani lambar yabo ta musamman.
Hmm anty zarah waye zai baki lambar yabo acikinsu Dan kin
kula da renon cikinda ba'a so?
Dr ne kawai ke sonmu sai ke Dan haka Kona haihu ke zanbarwa
babyn har sai kema kinsamu nai.
Dariya sosai anty zarah tayi tana cewa''
Waye yake kyautar ciki tun baa haifesaba amatu,
Kuma ki daina cewa ba'a son abin dake cikinki sbd idan har
ana maganar gata to na tabbata abin dazaki Haifa gata yagama yimasa yawa,
MD ZABEERA Dr ne Wanda yafi kowa qauna fiyeda komai da duk
abin daya mallaka Dan haka Ina tabbatar Miki da Babu wani uba bayan Dr dazaifi
MD qaunar abindake cikinki musamman sbd ni ba haihuwar nakeba Kinga kuwa Dole
zai qaunaci 'dan Dan uwansa uwa uba Kuma Dr khalil shi yanzu ai bashida kamarku
keda cikin Dan hakama ki daina cewa ba'a sonku mu Muna sonku Andi ma Yana sonku
hakama Modibbo.
Gyada Kai kawai tayi tana daukar sauran fruits din dake
gabanta tana cinyewa tana lumshe ido Dan dai tunda tazo idanba da daddare data
kwanta ba bakinta bai zauna a rufeba komaima cin cire haushi take Masa sbd
ganinsa kamar ba kudi aka saka aka siyoba komai akwai kamar a banza.
******
Zaune take tana sauraren 'yar guntuwar da nasiha tareda
lallashi da 'yarta juwairiyya ke Mata cikin kulawa da tausasa harshe Amma ita
Sam hankalinta baya kanta tayi nisa gurin tunanin abindake damunta,
Ganin hankalinta baya kanta yasa juwairiyya yin shiru tareda
miqewa tana cewa"
Umme tafiya zanyi ga dadynsu Fatima na kirana Kuma gobene
tafiyarmu Lagos sai gaf da azumi zamu dawo Inshallah.
Dagowa tayi ahankali ta kalleta batareda tace komaiba ta
gyada Mata Kai tana shafa Kan Ahmad 'dan qaramin 'danta tace"
Allah yakaiku lfy.
Amin tace suka shiga bedroom din umme suna qarasa dauko
sauran kayansu suka fice.
Shiru tacigaba dayi tana saqa da warwara,
Yarinya qarama kamar amatu itace tayi Wasa da tunaninta
tasakata cikin wannan tunani da halin na baqin ciki har ana cewa itace Zara
raini cikinda Babu ubanda yayishi,
Wlh bazata yarda ba tunda shirinta ya lalace na kowama saiya
lalace Dan kuwa sai ansan wa aka taba,
Idanma MD ne ya ninkawa wannan makwadaiciyar kudi datake iya
komai akan kudi ta kuwa kowa sai yaji ajikinsa wlh,
Amatu cikin dayayi sanadin baki Jin Dadi da gata acikin
zabeera shine zaizama mugun sanadin barinki zabeera da mummunan hukunci tareda
wulaqancin da sai Yan jarida sun buga,
Zanga yanda za'a haifi cikin da Babu.
Shigowar Haj maryam ce tasata kallon qofa tana sake ajiyar
zuciya ganin yanda itama haj Maryam din duk ta hargitse sbd burinsu na shekara
da shekaru ya lalace cikin mintuna goma a hannun yarinya qarama.
Zama tayi ummen nace mata' Yaya nuratu?
Nuratu na can haryanxu kuka takeyi
Wlh Nima aishatu nakasa yadda da khalil wata yake aure ba
nuratu ba,
Yarinyar Nan fiyeda shekara goma take fama da son Khalil sai
yanxu da ake maganar aure kwatsam wannan mugun labarin ya fada,
Labarin da mune muka qirqiresa Amma sai asamu wani juyin
Masa a zancen
Ni dai wlh Kam wannan Abu ban amince dashi ba nabawa nuratu
wuqa da nama nace ta qetare duk wata iyaka ta qwato Khalil dinta mukuma maji da
sauran.
Cikin quluwa itama ummen tace"
Dukkansu zasu raina kansu ne harshi Khalil din saiyaga bacin
raina.
***Da Rana lafiyyan faten dankali da Naman kaza da carrot
akayi sbd ita kawai
Haka ta zauna tacinye Wanda aka kawo Mata tas ta kora da
ruwan roba masu sanyi Danma lemu masu sanyi taso Sha anty zarah din ta hanata
da cewa saidai Tasha fruits drinks ba lallai su bawa baby lafiya ba
Haka ta hkr badan taso ba Dan ita wannan cikin badan Shiba
da duk abindake gidan saita ringa cinsa ba kakkautawa.
Baccin Rana tayi bayan tayi sallah sai yamma sosai ta tashi
bayan tayi la'asar suka Fara waya da USI Nan yake fada Mata Dr yazo gida
yafadawa su kawo shine 'dan wadda ta daukeki aiki Kuma zai ringa zuwa Yana
dubamu kafin kidawo hakama ya tafi dashi anyi cike ciken makarantar dazashi har
ilorin.
Saidatayi sallar magrib tukuna ta fito Palo ya zauna tareda
miqe qafafu hafsatu na matsa Mata tana kallo cikin ranta tana cewa"
Amatu kinfa zamo hajiya
Irin wannan Jin Dadi haka
Gashi dama ba wani ciwo da qafafunta keyi tsaban son Jin
Dadi da wuce wurine yasa take cewa ciwo suke Mata Dan a matsa Mata.
Wata tashar turawa take kallo ana wani film na adventure sai
washe baki takeyi tana cin cake din data sa anty zarah tasa hafsatu tayi mata
na inibi me laushi yaji butter sai ci take tana lumshe ido tana kallo tana Jan
hafsatu da labari itama hafsatun na tayata fassarar qanxon kurege na turancin
da akeyi Dan itama ba wani iyawa tayiba Amma ta dage tana fassara Mata.
Anty zarah ce ta fito daga dakinta ta nufosu cikin ado da
kwalliya me kyau sai qamshi me Dadi take fitarwa amatu tabita da kallo cikin
farin ciki tace''
Anty zarah kinyi kyau sosai
Amma meyasa zakiyi kwalliya yanxu da dare tunda kwantawa
zakiyi?
Zama tayi kusa da ita tana murmushi tace"
Amatu MD na hanyar dawowa shiyasa.
Ohhh ohhh nagane anty zarah"
Taqarasa fada tana dariya.
Miqa Mata plate din cake din tayi tana cewa''
Anty zarah kici kiji yayi Dadi sosai.
Har takai hannu zata dauka saita fasa tana cewa"
Idan naji cikina zai cika bazan iya cin wani abincin ba kada
MD yadawo nakasa tayasa cin abinci a dining.
Kallonta tana cewa' kici ko kadan anty zarah tunda kinaso.
Girgiza Kai tayi tana gyarawa amatun pillon data jingina
dashi tana jawo Mata wani labarin take amatun tahau dariyar labarin datake Bata
anty zaran na tayata sunyi nisa sunata nishadinsu saiga bude qofar palon
aka shigo Dr ne hannunsa daukeda qatuwar ledoji da amatu ta ajiye plate din
cake din hannunta ta taso kenan saigashi a bayansa Shima ya shigo fuskarsa
kawai ta kalla ta janye daga gefen Takoma gefen Dr ta tsaya tana Masa murmushi
zatai Magana yace"
Baki gaida MD ba amatu.
Kallonsa tayi kafin ta kalli inda MD din yake Yana qarasa
shigowa palon tayi qasa da murya tace"
Ina wuni sannu da dawowa.
Hannu kawai ya daga Mata ya nufi hanyar samansa anty zarah
dake zaune ta miqe itama tana Masa sannu da dawowa to ita ya bude baki ya amsa
Mata tareda Dan tsayawa ya kalleta kafin ya dauke Kai Yana cewa'
Karki jirani dinner nariga nayi dinner agurin Modibbo.
Kallonsa tayi Yana qoqarin wucewa tace"
Akawo maka ko fruits ne?
No thank you.
Wucewa yayi ya barta a tsaye tana binsa da kallo fuskarta na
'dan canzawa Amma Jin duk idanuwansu akanta yasa ta washe fuska tareda juyowa
tadawo inda suke tana cewa"
Dr ko zakayi dinner tareda mu ne to?
Kallonta duk su duka sukeyi girmanta na qaruwa a idon Dr
Tausayinta da qaunarta na shiga a zuciyar amatu tareda
takaicin MD din ta yanda anty zarah ta Hana kanta cin komai sai yadawo Amma ya
take hakan ya wucewarsa ko kwalliyar datayi danshi bai tsaya yayi Mata kallon
ko mintu biyu ba ko me ya dauki kansa Dan ma yasamu mace me kirki da kyau kamar
anty zarah tana sonsa wlh da itace koya Masa hankali zatayi taga qarshen kyau
da Jan ajin banzansa.
Kamo hannun anty zarah din tayi suna zama palon tace"
Anty zarah Zo kici cake din Nan kiji Allah yayi Dadi sosai.
Ledojin hannunsa Dr ya miqawa amatu Yana cewa"
Nima a gajiye nake kamar MD shima yau a gajiye yake sosai
Nima tunda muka hadu baicemin ko qala ba sbd gajiyar dayake tareda ita zanje na
kwanta Saida safenku
Amatu ki kula ok?¿
Gyada Masa Kai tayi tana cewa''
Nagode Saida safe.
Yana fita zarah tasaki murmushi tana cewa"
Dr kayaushe kanason gyara Abinda MD yakeyi Dan kada aga
laifinsa
Kadaina damuwa Dan Nima Babu ranar dazanga laifin nasa.
Takaicin MD din yasake Kama amatun tasake dagewa Saida anty
zarah din taci cake din sosai Tasha apple drink suka cigaba da firarsu
Ganin hankalin zarah din na Kan hanyar sama yasa amatu sakin
tsaki qarami tana miqewa tace"
Bacci zanyi Saida safe anty zarah.
Tana shigewa zaran tasa hafsatu ta kashe komai itama tashige
Suna shigewa taje dakinta ta shirya ta nufi dakin MD.
Ahankali amatu tasaba da zarah da hafsatu sosai kamar sunyi
shekaru atare,
Kulawar dasuke Bata da gatan datake samu daga garesu yasa
hankalinta ya kwanta sosai acikinsu musamman ma da kullum tana waya dasu
kawu dasuketa sawa Dr khalil albarkar yanda yake kula dasu sosai Dan yanzu
ranakun matsuwarsu sun qare ga USI anata shirye shiryen zuwa makaranta,
A duniya yanzu mutanen datake so a rayuwarta fiyeda komai da
kowa sune USI,kawu,iyami,Dr da anty zarah sbd sune mutanenda tasan tabbas qaunarta
sukeyi Babu wani qyama ko munafurci.
Dr ya Gina qaunarsa cikin ranta danasu kawu sbd Suma shine
mutum daya qwal daya fito ya tsaya musu a rayuwa yake qaunarsu batareda qyama
ba ko buqatan wani Abu daga garesu shiyasa dukkaninsu kowannensu ya bude baki
Dr ne abakinsa sai anty zarah dinta.
Qaunar data kewa anty zarah din yasa take Jin tsanar MD
matuqa cikin ranta sbd yanda tagama lurada Sam baya damuwa da alamarin zarah
din kullum shine damuwarta shine kukanta shine jimaminta ko tausaya Mata bayayi
da yanda take matuqar qaunarsa/sonsa da ganin girmansa,
Duk yanda zarah din take qoqarin boyewa hakan baya boyuwa ga
Wanda yake zama taredasu shiyasama Sam ta tsani ko ganinsa matuqar Yana gida
Bata fitowa sbd kar wataran tayi amsa zagin maguzawa akan Abinda yakewa antyn
saidai duk Abinda zai faru yafaru ba ruwanta.
A bangaren Jin Dadi kuwa zatace itakam gwara da akayi Dan
kuwa rayuwa ta sauya Mata sosai Dan ko jikinta da fatarta sum nuna suna cikin
hutu sbd lafiyayyar rayuwar datake ciki,
Banza ta Fadi" kaman yanda take fada
Dadinta takeci ba qaqqautawa duk wani Abu me Dadi cewa
takeyi tanaso ba Bata lokaci kuwa Zarah zatasa akawo Mata shi,
Hafsatu kanta ta qararda 'yar ta'addace a gidan Dan kuwa
tunda amatu tazo Bata zaman awa biyu batai aikin hada mata wani abuba,
Itace ayi Mata gullisuwa,
Tuwon Madara,
Kwakwameti,
Cake,
Dambun nama,
Dambun kaza,
Furar Madara da Milo
Komaima ci takeyi ita Bata taba ganin me ciki irin wannan na
amatu ba da baya tadar komai
Komai ci takeyi hadda Wanda masu ciki baya shafa musu lafiya
Gashi ko ciwon Kan Nan na banza da masu ciki keyi ita batayi
kullum daram dam take
Ga Dr ya Hana asa kowane likita ya duba matarsa yace shine
zai ringa dubata musamman da kwanakin umme tasaka fitinar sai Modibbo yasa anyi
scanning Dan asan ranar haihuwar cikin su Fara shiri.
Hankalinta bai wani tashiba sbd tasan Dr na Nan shine zaisan
yanda za'ayi da Maganar scanning din itadai damuwarta 'dayace shine anty zarah
data Fara maganar cikin baya girma sbd ta shanye kusan wata biyu a gidan gashi
Koda tazo tace ciki wata biyu wata hudu kenan Amma Babu alamar tasowar cikin
shine anty zaran ta daga hankalinta cewar cikin baida lafiya itama tanason ayi
scanning.
##mamuh##

No comments